← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 113

Sashe 19

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dady Najib ya riƙo hannunsa yana kallonsa, cike da mamakin ramar da yayi a kwana ɗaya kacal.
A hankali yace.
"Ammar! Ni mahaifinka ne mi zaka ɓoye min? Tsakanin ka da Allah akan yarinyar nan ne zaka sakawa kanka cuta?"

Ammar ya rungume mahaifinsa yace.
"Dady kayi haƙuri ina sonta ne, amma tunda na ɓata maka rai sanadinta na haƙura"
Dady Najib yayi murmushi yana girgiza kansa yace.
"Ta shi muje muyi breakfast in sha Allahu zaka sameta na amince zan nema maka aurenta..."
Wani irin ihu yayi yana rungume Dady Najib yana faɗin.
"Nagode Dadyna Allah ya saka maka da alkhairi ya ƙara maka lafiya"
Dady Najib ya kamasa yace.
"Ameen Ammar muje toh ayi abinci ciwo ya ƙare muna gamawa ka shirya munada meetings Kasan hakan?"
Ammar ya zare hannunsa yace.
"Eh Dady na sani bari na shirya ma, kuje ku fara ci ganinan..."



Juhainah babba tunda tai sallar asuba take zaune tana azkhar, bayan ya idar ma ta daɗe zaune kafin ta miƙe, kitchen taje ta kamawa Jamilu aiki, yana ta bari ma amma komai tare sukayi, ita ta jera komai a dining room, ta koma tayi wanka ta canza abaya, ta yi zamanta cikin ɗaki, anan Jamilu ya kawo mata abincinta taci tasha maganinta, ta shafa Hempvana cream a goshinta, ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita.

Yah Boss sai ƙarfe 9 saura minti biyar ya farka ya yi wanka ya shirya cikin shirin juma'a, shiga ta alfarma idan ka kallesa sai ka kuma kallonsa saboda yadda manyan kayan suka yi masa masifar kyau, Yadi ne Brown colour mai masifar tsada ya sha ɗinki mai kyau da tsada.
A gaggauce ya yi breakfast suka fice daga gidan, zuwa police station, saboda yana da meetings idan anjima.

Fu'adh yau ma so masa maganar Juhainah babba, ganin yau Sir ɗin ya kame fuska sosai fiye da baya ya saka shi yin gun ya ƙyale, yaga wani matakin shi zai ɗauka akanta, aikatau ɗin zatayi ko jarin zai bata oho ya dai ja bakinsa yaga me uban gidan nasa zai yi.
Shi dai Allah ya sani yana masa kwaɗayin aurenta, saboda nutsuwarta da tarbiyyata.

Ɓangaren Juhainah ƙarama sai ƙarfe goma da ƴan mintina ta faraka daga bacci, tayi wanka ta sauko saboda wata irin yunwa da take ji.
Ta cika cikinta dam ta ta yi zamanta a parlour ta kunna Tv tana kallon tashar Mbc Bollywood.

Su Suhaima ƙarfe sha biyu suka baro school.
Acikin mota ta zaro wayanta babbar Samsung Galaxy da Yah Boss ya siya mata take game da abubuwa dai har da layi a ciki suna waya da shi, da ƴan gidansu Mom ɗinta da suke Abuja.

Al'amin ya kalleta yana riƙo hannunta yace.
"Aunty Suhaima yau zamuje gidan Dadd gun Auntie Juhainah nayi missing nata"
Suhaima ta juya idanunta masu kyau irin na Yah Boss a hankali tace.
"Yeah Amiin ai Dadd ɗin ne ma zan kira"
Cikin farin ciki ya rungumeta yana dariya.
Ta danna number Dadd ɗinta.

Lokacin yana ɗakin taron basu gama ba, yana tsaka da jawabi special Phone ɗinsa Samsung ta ɗauki ringing.
Kamar ba zai kalli wayar ba da take gabansa saman ƙaton table ɗin ajiye, Sai kuma ya kalla.
Ganin sunan
*Baby Suhaima*
yana yawo akan screen ɗin wayan ya saka shi yin picking call ɗin ta jikin Glass da yake manne a kan fuskarsa, a hankali ya furta.
"Assalamu alaikum, Hey Baby Suhaima! I hear you."

Suhaima ta amsa sallamar ta shagwaɓe murya a hankali cikin miskilanci irin na Dadd ɗinta ta furta.
"My Dadd I miss you I love you, we want to go to Aunty Juhainah house, the driver has gone now, will you come and take us? Please, my father."

Numfashi ya feso yana ɗan juya idanunsa masu kaifi, a hankali ya furta.
"No! Baby kuje gida Ba na hana daga school direct kice zaku wuce wani gurin ba? Wannan ba tarbiyyar mai kyau bane, wucewa wani gurin daga school, Duk da gidan mahaifinki zakije, amma ban yarda ba, ku wuce gida"

Ɗan shagwaɓe fuska tayi tana marairaice murya a hankali ta furta.
"I'm sorry My Dadd bazan kuma ba, amma dan Allah idan muje gidan mun huta direba ya kaimu?"
Cike ƙaunar ya'yansa ya furta.

"No! Babies ku jira zanzo mutafi tare, bani My Amiin"

Suhaima ta ba Al'amin wayan ya amsa yana kai kunnensa a hankali ya furta.
"Assalamu alaikum my Dadd, I love you"
Yah Boss ya amsa sallamar yana maida masa.
"Love you too My Amiin, oya ku wuce gida zanzo mutafi bayan sallar juma'a Ok?"
Al'amin yana murna ya furta.
"Yeee thank you My Dadd bye"

Murmusawa Yah Boss yayi yana katse kiran cikin jin daɗin yadda ya'yansa suke farin ciki.

Kallon jama'ar yayi yana basu haƙuri akan yayi magana da ya'yansa ne.
Abinka da babban mutum mai faɗa aji, ai Sai kawai Kowa ya washe baki ana jinjina masa yadda yake son iyalinsa, akaci gaba da meetings, sha biyu da rabi suka tashi, daga nan ma masallaci Yah Boss ya nufa...

Yah Boss ana tashi daga Masallaci ya bada umarnin a maidasa gidansa akwai saƙon da zai ɗauko, ya kai wa mahaifiyarsa.

Juhainah tunda tayi sallar juma'a ta cire hijib ta shiga shirya kanta, jajayen laɓɓanta masu kauri, ta saka masu lipstick pink, ta saka riga da skirt na Material marar nauyi pink colour, sai shegen kyau da tsada, tsaf ɗinkin ya zauna ajikinta, duk da batada tsoka amma tayi kyau, hallitarta ne saka kaya duk ramarta su mata wani Irin sahihin kyau, saboda dukiyar fulaninta masu wani irin cika da suke ƙarawa yanayin zubinta na sirintaka kyau.

Takalmi shima pink sai ta kame gashinta da headband, ya baje gadon bayanta, sai mayafi ta cukuikuiyesa a hannunta saboda ɓacin rana koda Yah Boss ya dawo tana parlour sai tayi sauri ta yafa kafin ya shigo.
Gaban ƙaton dressing mirror ɗin Suhaima ta tsaya tana fesa turare mai daɗin gaske, tana fari da dara-daran idanunta irin na Maah sak, tana juyi gaban madubin tayi murmushi tace.
"Yarinya Matar Manya, Allah Kawo babban Rabo, nifa Wlh bazan auri Ammar duk da ina sonsa, nafi son babban mutum, ah toh can ya gama haukansa, ya haƙura, kamar yadda zan ɗauki hƙr, Allah yasa Yah Boss yamin auren dole, ya aura babban mutum, nayi haukan gangan kamar bana so, daga baya rungume abuna, sbd duk wanda zai aura min nasan ba maganar bai haɗu ba.
Bari naje na take cikina da abinci Kafin wannan Yah Boss mai ciki cike da mugunta, najirasa naga da me yazo ah toh"

Ta ƙarasa maganar tana dariya harda tafa hannayenta ta shiga tafiya tana murguɗe² ita dole sai ta fito da mazauna wanda babu su.
Bata tsaya parlour ba ta buɗe ƙofar ta fice.
Har ta wuce ta waigo ta kalli ƙofar Yah Boss.
A rufe, ta saɗaɗa ta kama handle ƙofar parlon taji ta buɗe.
Ƴar dariya tai tana sanya kanta ta shigo ta rufo ƙofar, tana buɗe hanci tana shaƙar ƙamshinsa wanda ya gama kama parlour kamar yana ciki.
Baki ta murguɗa tana shiga tsakiyar parlour, tana kallon ko ina tsaf a gyara sai ƙamshi, pictures cikin frame shida Khadijah dasu Suhaima, a tsiwace tace.
"Wannan Yah Boss ɗin aniyarsa ta bisa baida kirki wajan cin uwar mutum Wlh, ni wlh jiya nazaci mutuwa zanyi sbd nadaku kamar sakwara, amma da yake bai cika mugun ƙwarai ba harda cewa Fu'adh.

Fu'adh! idan kunje gida tayi ƙoƙarin cin abinci, ka bata maganin da zai fitar mata da zogi da zazzaɓin, ta sha idan bata sha ba ka kirani zan zo in sha Allahu, idan ta warware inason ta kula da yarinyar nan ta hospital kafin na dawo gida zuwa dare a mayar da ita gun iyayenta.
Ta ƙarasa kwaikwayon maganarsa tana riƙe ƙugunta tana dariya, sai ta haɗe face tana faɗin.
"Ai wannan mayyar sai ta bar gidan ɗan uwana, ko na gana mata azaba, kana kallon idanunta Kasan munafukace"
Ta ƙarasa maganar ta nufar bedroom ɗin, ko me ta tuna ta fasa, ta juya dan ta fice daga parlon, saboda yunwa take ji Sosai.
Juyawan da zata yi ta gwammace a yau ba'a haifeta ba a duniya.

Me zata gani, Yah Boss a tsaye ƙofar parlon ya zuba hannayensa cikin aljihunsa, fuskarsa kaɗai idan ka kalla sai ka shiga tashin hankali, bare idanunsa da ya zare glass ɗin.
Mayafin hannunta ta saki tana dafe ƙirjinta cikin matsanancin tashin hankali jikinta ya ɗauki rawa zuciyarta wani irin harbawa take yi, wanda azabar tsoron da ta shiga ya sakata taji jiri na ɗaukanta sosai.
Zubewa tai ƙasa saman Carpet tana dafe ƙirjinta da gaske zuciyarta wani irin bugu suke yi.

Rararrafe ta fara zuwa gurinsa.
Tana isowa da rarrafen ta kamo ƙafafuwansa ta ƙanƙame, tana ɓoye fuskarta tsakanin guiwowinsa, ta fashe da kuka tana jin zuciyarta na ƙokarin tsayawa daga harbawa, ta fara kokowa da numfashinta, wanda da gaske ƙoƙarin ɗaukewa yake daga gangar jikinta.
Kamar wasa ko ƙarshen kukan da ta fasa bata kaiba, Cak numfashinta ya tsaya, ta sulale kan ƙafafunsa sumammiya...
[06/01 16:45] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVELS. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

Page 11

Yah Boss ya daɗe rabon da ya shiga wani yanayi mai muni da zafi irin wannan rana, da dukkan abinda Juhainah tai akan idanunsa, yaji ya gani.
Kallonta yayi da gaske ta suma amma baya jin ko ruwa zai iya zuba mata dan farfaɗo da ita.
Shi da zai yiyuwa ma daga wannan suman ta wuce mutuwa zaifi nutsuwa, saboda wannan ba ƙaramar bara gurbi bace cikin family's Janfar. Abun takaicin yanzu idan ba'aci Sa'a ba, tana farfaɗo Wa da shegun aljannunta zata tashi, duk wanda ke kusanta yaci tsinannan duka.
Chapter 19 · 0% Book details