← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 113

Sashe 58

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Parloursa ya nufa da su.
Yana shiga ya saki hannunsu yana kafe ta da lumsassun fararen kyawawan idanunsa, ya furta.
"Kina son saka min damuwa ne a banza ko mi yake damun ki har haka? Aure kike buƙata da gaggawa Bilkisu? Me yasa bakya tauna magana kike sakinta?"

Cikin sauri tana sake riƙe hannunsa tana hawaye tana kallon sa tace.
"A'a bana so Ni irinka kaɗai zan iya so, Ni bana son Jamal, idan ba irinka na samu ba Wlh zan......"

Bakinta ya buge yana kallon Suhaima da Al'amin ya furta.
"My Babies please kuje ɗakinku yanzu zata zo, bazan dake ta ba"
Suhaima kamar zata fasa wani kukan tace.
"Ga shi nan ka buge mata baki, tana riƙe laɓɓanta, kayi min alƙawarin bazaka ƙara buge wa Aunty J bakinta ba?"

Yah Boss ya jinjina kansa a hankali ya furta.

"I promise you my Babies."

Suhaima ta ɗaga kanta tana kama hannun Al'amin suka nufi hanyar fita daga parlourn.

Suna ficewa suka rufe ƙofar.

Yana ganin sun tafi, ya fizge hannunsa ya nufi hanyar bedroom ɗinsa cikin kakkausar murya yana faɗin.

"Ki fita ki ban waje banason ganinki na fita daga sabgar ki daga yau, tunda so kike ki ɓata rayuwar ki da kalaman da basu dace ba, a matsayin ki na budurwa wacce ta fito daga gidan mutunci, karki kuskura ki nuna kin sanni ko a titi, ki tattara ki koma can gida gun Maah..."

Ya ƙarasa maganar iya gaskiyar sa babu alamar ma da zata kawo masa wargi.

Juhainah idan hankalinta yayi dubu toh ya tashi a yau, jin kalaman Yah Boss wai ko a titi ta ganshi karta nuna ta san shi.
Wani irin kuka ta kece dashi ta nufo gunsa da gudu.
Anutse ya kama handle ɗin ƙofar master bedroom ɗinsa ya buɗe zai shige ta iso da gudu ta zube ta riƙe ƙafafuwansa cikin kuka tace.
"Please Yah Sadeeq karka min wannan hukuncin yayi min tsauri, kamin kowane hukunci karka raba zumunci dani, bazan jure ba, kayi haƙuri ka yafe min ba bazan sake rashin ji ba..."

Yah Boss ya fizge ƙafarsa cikin izzarsa ya fara mata magana a hankali ya furta.

"Bilkisu! you're lying, the promises you made me, are over a thousand, yet none have you fulfilled."

Cikin kukan da zai tausaya mata Juhainah tace.
"Allah my brother, this time I promise I won't disappoint you again..."

Katseta yayi ta hanyar furta.

"Shut up, you won't be able to.
Kawai kije kiyi sabgarki babu ni babu ke, tunda bakya jin magana, ai bani kaɗai bane yayanki, akwai Mustapha Umar Nasir, ki koma can ginsu, maybe su baza su hanaki yin duk abinda kike so ba, alright"

Ya ƙarasa maganar yana sanya ƙafarsa cikin bedroom ɗinsa.
Tsaf ya shige yana ƙoƙarin rufe ƙofar ta sanya hannayenta bakin ƙofar tana wani irin kuka ta kwanta bakin ƙofar ta fara birgima tana harba ƙafafuwanta, tana faɗin.
"A'a nafi sonka, bana jure rashin ka, nafi son zama gunka, karka rabu dani..."

Wata irin tsawa ya daka mata wacce ta firgita ta, yana faɗin.
"Ki tashi ki bani wuri ko in sumar dake yanzun nan, Ni bana son zaman dake kije kawai..."

Ai tuni Juhainah ta miƙe da wani irin sauri jikinta yana tsuma tsoronsa ya yi mugun saukar mata, tare da kalaman baya son ganinta, har bata ganin kirki ta nufi hanyar fita daga parloursa da gudu tama gaza ma kukan sai hawaye.

Tana kaiwa bakin ƙofar ta kama handle ɗin ta saki wani irin ihu ta yanke jiki ta zube ƙasa tana shura ƙafafuwanta kumfa ta fara fitowa daga bakinta, idanunta suka juye baki ɗaya, anan take kamarta ta fara canzawa.

Yah Boss da har ya shige bedroom yaji ihunta wanda har ya gane ba na lafiya bane.
Kansa ya dafe yana faɗin.
"Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil La Haula Wala Quwwata Illah Billah"

Juyowa yayi ya nufi parlour.
A halin da ya ganta ne kuma yaji hankalinsa ya fara ƙoƙarin tashi.
Da sauri ya ƙaraso ya duƙo gunta yadda take harba ƙafafunta.
Da wani irin amo ya furta.

"Bilkisu! Meye kuma?"

Yana shirin kamata yaga kamar aljana ta miƙe zaune ta masa wata irin cafka ta riƙe masa wuyansa ba riƙon wasa ba.
Da baida ƙarfi a yau tabbas sai sun sumar da shi, ko kisa ma.

Ƙoƙarin cizonsa take tsakiyar kansa suna faɗin.
"Akan me zaka mana tsawa kasan yadda zuciyar Babynmu ta buga kuwa? Kasheta kake son yi kenan? Idan kai baka sonta ai ni ina sonta Wlh sai mun kasheka"

Yah Boss ya damƙe hannunta daga wuyansa ta ƙarfin tsiya tare da addu'a ya finciketa, ya riƙe hannayenta ya gamata da ƙofar ya matseta ya mata riƙon ba na wasa ba, ya fara mata karatu da ƙarfi.

Khairat da gudu ta iso bakin ƙofar parlour tana ƙoƙarin buɗe wa taƙi buɗewa saboda ya tare hanyar.
Yah Boss jin murya Khairat ya matsar da Juhainah yajata ta ƙarfi ya nufi saman Chairs da ita, ya zauna yana faɗin.
"Shigo Khairat, kina shigowa ki shiga bedroom cikin drawer ki ɗauko min zam-zam ki zuba a Cup ki zauna a nutse ki saka imani da yaƙi sosai acikin zuciyarki, ki karanta min, ki dinga tofa wa yawunki yana shiga fa.

Bismillah arqeek, min kulli shay'in yu'dheek, min sharri kulli Nafsin aw'ainin haasid, Allahu yashfeek, Bismillah arqeek.

Allahumma Rabban Nasi, mudhhidba-l Basi-shfi antasha shafi, la shafiya illa anta, shifa'an la Yughadiro saqaman.

Kin iya su?"

Khairat ta ƙaraso gaban su da sauri cike da tsoron halin da Juhainah take ciki tana amsa wa da.
"Eh na iya harda wasu ma"

"Toh tsayuwar me kika min? Kije"

Da saurinta ta nufi bedroom ɗin.

Yayin da Yah Boss ya riƙe Juhainah yana tofa mata addu'a, a hankali ya furta.

"Ok kana nufin baza'a mata faɗa ba idan tayi ba dai-dai ba? Ai ni baka isa ka kasheni ba, sai kwana na ya ƙare.
Kuma na rigada nafi ƙarfinka, Sbd na riƙe Qur'ani mai girma ina bautawa ubangijina dai-dai iyawata inabin dukkan sunnonin Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, kuma ina tsoron Allah, ban taɓa jin son abin da Allah da Manzonsa suka haramta min ba, dai-dai gwargwado ina kiyaye saɓonsa, bance ni mai gaskiya ne ɗari bisa ɗari ba, ko ban taɓa saɓawa ALLAH ba, amman ina kiyaye wa a sanina, kuma ina azkhar safe da yamma ya zaka iya da Ni? Ba kai ba ko ma waye sai ya jira Wlh.

Kuma In sha Allahu nine ajalinka"

Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tana tofa masa yawu akan fuskarsa tace.
"Allah ya wadaranka azzalumi, inason samun dama akanka ka guji ranan da zanyi nasara a kanka, zaka ga abinda zan maka, sai nayi wasan Kurah da kai..."

Yah Boss ya buge bakin yana riƙe laɓɓanta da ƙarfi ko me ya kanto oho ya tofa mata yawunsa cikin bakinta, tare da rufe bakin nata yana tofa wa fuskarta addu'a, ya cire ɗan kwalinta.
Wani irin ihu marar daɗi jinnun suka fasa.
Kokowa suka fara sosai har Yah Boss yayi galaba akansu.

Khairat a can bedroom ɗin ta zauna ta tofa addu'ar da Yah Boss yace tayi ta miƙe ta kawo masa.
Cikin Sa'a ya amshi Cup ɗin, Juhainah ta harba Khairat da ƙafafuwanta da suke saitin inda take tsaye.

Ai sai ga Khairat a ƙasa wanwar ta saki ihu tana dafe kanta da taji kamar an buga mata guduma Sbd taji zafi sosai a kan nata.

Duka jikinta Yah Boss ya fesa wa ruwan zam-zam ɗin me addu'a ya matseta ya bata ruwan addu'an tasha.
Ya fesa mata a kunnuwanta.
Ai kuwa kamar mahaukaciya ta dinga ihu tana faɗin.
"Wayyo na mutu kayi haƙuri zan tafi na ƙara ƙonewa..."
Attishawa Juhainah tayi mai ƙarfi harda wani hayaƙi yake fita daga ƙofofin hancinta.
Sai amai ya biyo baya alamar ya fitan.
Riƙeta yay sosai yana buga bayanta a hankali tare da shafa kanta.
Fuskarta ya leƙa Manya dara-daran kyawawan idanunta a rufe.
Hakan ya saka ya gane bata cikin hayyacinta.
A hankali ya ɗago kanta ya kirata.

"Juhainah! Ya kike ji ajikinki yanzu?"

Shiru.
A hankali ya sake furta.
"Bilkisu! Kina jina?"
Jikinsa ta zube tana minshari.
Goshinta ya taɓa yana ɗago kansa ya kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa akan Khairat.
Kwantar da Juhainah yayi ya miƙe ya nufi gun Khairat, wacce take dafe da kanta harda ƙwallar ta, sbd azabar da take ji a kanta.
A hankali ya furta.
"Sannu Khairat, ina yake miki ciwo?"
A hankali tace.
"Kaina my brother"

Anutse ya kamota ta miƙe yana riƙe da ita, ya taɓa kanta.
A hankali ya furta.
"Ki shiga bedroom akwai maganin ciwon kai ki ɗauka ki shi, yau ku kwana a bedroom ɗin da take jera da ta Khadijah Sbd Babies kar suyi ta surutu su hanata bacci. Zaki iya zuwa ɗauko maganin?"

Khairat tsoron Juhainah ya kamata sosai amma babu halin nunawa Yah Boss.
Wani yawu ta haɗiye tana amsawa da.
"Toh eh zan iya"
Yana riƙe da hannunta har ƙofar bedroom ɗin ya sake ta shiga shi kuma ya juya ya dawo gun Juhainah.

Ɗaukanta yay ya nufi ƙofar fita.
Yana fitowa da ita Suhaima da Hajjah Mama suna fitowa.
Suhaima ta nufo gun mahaifinta ganinsa ɗauke da Juhainah.
Cikin damuwa ta iso tana faɗin.
"My Dadd me ya samu Aunty J? Bata da lfy ko abunta ne yazo?"
Ta ƙarasa maganar tana kamo hannunta tana hawaye.

A hankali ya furta.
"My Babie karki tasheta zan kaita bedroom ɗin can su kwana da Khairat"
Hajjah Mama ta iso da sauri tana faɗin.
"Subhanallahi Abbah! Ihun da nake ji sama² Namesake ce? Mutanan ne?"
Suhaima ta kalleta tace.
"Jinnu ake cewa su ai ba muta ne bane"

Yah Boss yana wucewa yace.
"Eh Mama sai haƙuri Sbd na mata faɗa ne suka kawo ziyara baza'a mata faɗa ba ai rayuwa bazata tafi a haka ba"

Suhaima da hajjah Mama suka bi bayansa.
Key a jikin ƙofar Sbd ana gyarawa.
Saman lafiyayyar Bed ɗin ya kwantar da ita ya ranƙwafo yana tofa mata suratul Fatiha da Falaki da Nasi.
Hajjah Mama ta tofa mata addu'a tana riƙe da hannunta cike da tausayinta.
Suhaima ta haye Bed ɗin ta rungume Juhainah tana tofa mata addu'a iya wadda ta iya.
Yah Boss ya kallesu yana jin daɗin yadda suke ƙaunar Juhainah.
Chapter 58 · 0% Book details