← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 113

Sashe 97

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zuwa gida part ɗin Jamal suka nufa suka tisa shi gaba ya faɗa masu gaskiyan.
Ya tsaya yana raba idanuwa.

Abba a harzuƙe yace.
"Wallahi idan baka faɗa mana gaskiya ba, sai dai kaje can ka ƙarata dan commissioner yana cikin ɓacin ran da ko gate ɗin gidansu baka isa kaje ba, ba ruwanmu tunda bazaka faɗi abinda ka mata ba"

Jamal
yace.
"Zan faɗa maku amma don ALLAH kuyi haƙuri wasa nake mata ba har cikin zuciyata na faɗa mata ba..."

Kakaf abinda ya faru ya basu labari.

Ai wani irin mahaukacin mari Mamy ta ɗauke shi da shi, Abba ma ya kama mata.
Kamar wasa ƙato da shi suka rufe da duka cikin takaicin abun da ya aikata, na tozarta su da yayi.

Shiru yayi bai ce komai ba yasan ya cancanci hakan.
Sai da suka daka suka gaji suka zauna suna maida numfashi.

Mamy tace.
"Bazan maka baki ba, amma nasan dole sai alhakinta ya kamaka, bakin duniya ma ya isheka, daman ana wasa da saki sakin ma har uku, sbd kuna tutiyar ana barinsa a zaman ɗaya? Allah tsare Ni naje neman biko zanje dai bada haƙuri, na mata fatan idan ta gama iddah ALLAH bata miji nagari"

Jamal kamar yaro ya fara kuka yana faɗin.
"Don ALLAH Mamy kuyi haƙuri Wlh yanzu ina sonta ku taimaka min na maidota zan zauna da ita tsakani da Allah..."
Mamy tace.
"Ƙarya kake alhakinta ya fara aiki, agaba ma"

Ta miƙe tsaye ta nufi hanyar fita.
Abba ya bita yana faɗin.
"Na tabbata watan zinɗan familles namu ya kama, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!"

Tafiya suka yi suka barsa.
Mmay tana shigowa su Surayya na zaune ta kalli Mamy tace.
"Mamy lafiya naga ranki a ɓace?"

Mamy ta kama hannun Surayya Sbd bakin Dijeh tsoro yake bata ba zatayi zancen sirri a gabanta ba.
Sai da suka shiga bedroom ta sanar da ita ɓarnar da Jamal yayi.

Surayya ta zube ƙasa tana sakin kukan takaici da baƙin ciki.
Mamay
Tace.
"Yanzu dai ki tsayar da ƙafafuwanki zuwa gidansu, dan yadda suke cikin zafin nan zansu miki korar kare. Muma zuwa gobe zamuje basu haƙuri, muga ko akwai maslaha."

Surayya bata ce komai ba, kukanta take kamar anyi mata mutuwa.



Ɓangaren Zarah
Da gaske taci kukan sakin da aka mata, amma ta rantse bazata tafi ba, zata je ta samu MAAH tasan zata basa haƙuri ya maida.

Su Suhaima ko da suka dawo basu ga Yah Boss basu damu ba, sanin baya zama.
Abubuwan cinsu suka baje suka ci na wasa kuma suka ajiye abunsu, suka zauna nan down stairs, suka kunna Tv suka saka Game suka fara.

Zarah sai leƙasu take ta ƙofar parlournta.

Sai dab da Maghreb Juhainah ta farka, tana farkawa Dr Majid ya sallame su suka tafi gida.
Suna zuwa gida Maah ta mata ruwan zafi da kanta ta gasa ƴarta.
Bayan tayi wanka ta fito tayi sallar Maghreb, tana zaune saman darduma tana azkhar, da ta gama ta buɗe Qur'ani ta fara karatu, har ta manta yaushe rabon ta da karatun Qur'ani ta buɗeta sai dai bitar kai, shi ma ba kullum ba.
Maah na zaune gefenta.
Bayan sunyi sallar isha'i Maah ta fita ta kawo abinci.
Kallon MAAH tayi ta girgiza kanta tace.
"Bana jin yunwa MAAH"

MAAH ta rungumeta tana faɗin.
"Me kikaci? Ko na kira yayanki shi a zai sakaki kici?"

Juhainah tace.
"Bakina ɗaji MAAH, da tea nema zan sha da bread zan ci. Ko me zanyi abinda ya faru ya faru, babu mai canzawa kansa ƙaddara Maah zagina za'ayi na lokaci ne, ALLAH yasan zuciyata"

Maah tana rungume da ƴarta tace.
"Alhamdoulillah! Naji daɗi Autah da kika san ba maiyi sai ALLAH"

Juhainah tace.
"Hummmm!"

Maah ta saketa tace.
"Bari na dafo maki tea"
Kai ta ɗaga batayi magana ba.

MAAH tana fita Juhainah ta miƙe ta hau saman bed ta kwanta.
Idanunta ta lumshe tana istigfar.
Wayan MAAH da take ajiye saman bedside ta fara ringing.
Juhainah tanaji taƙi buɗe idanunta.
Har kiran ya katse bata buɗe idanunta ba.

Kira na biyu ya shigo.
Tsaki taja ta buɗe idanunta ta miƙe zaune ta matsa ta janyo wayan.
Ganin Yah Boss ne ta ɗaga kiran.
Kafin tayi magana daga can cikin daddaɗar muryansa anutse yayi sallama yana faɗin.

"Maah! Ki matsa Bilkisu taci abinci, sai ki bata magungunan kowane guda 1 ake sha. Sai da safe Allah ya bata lafiya, da juriya amsar ƙaddarata"

Juhainah jin muryan Yah Boss sai rauni ta ya ƙaru, sai hawaye suka fara zuba akan kyakkyawar fuskarta, a hankali cikin sanyin murya tace.
"Yah Sadiq nice ma, Ameen Nagode sai da safe, a gaishe min da My Babies"

Taja bakinta gum ta ƙyale, tana jiran ya kashe kiran tunda idan shi ya kira ba'a kashe masa kira, sai idan MAAH ce ko Papa.
Kuka ta sakar masa jin yaƙi magana yaƙi kashe kiran.

Yah Boss a hankali ya furta.
"Bilkisu! Ki daure kici abinci kisha magani banda gardama Ok? Toh kuka me kike kuma? Ko inzo yanzu ne?"

Da mamakinsa a hankali ta amsa da.

"Ok My brother in sha Allahu Nagode, ƙaddara kuma na amsa haka Allah yaso, a'a ka kwanta ka huta Please."

A hankali ya furta.
"Alhamdoulillah! Thank you Bilkisu good night, zan zo na dubaki da safe"

A hankali tace.
"Night My brother ina kewar Babies ɗina bye"

A hankali ya furta.
"Ok zasu zo ki nutsu"

Kittt ya katse kiran.

Hawaye ta fara ta kwanta rungume da wayan tana lumshe dara-daran kyawawan idanunta.
Ba daɗewa MAAH ta kawo mata tea ɗin da bread ɗin.
Ai kuwa ga mamakin MAAH taci fiye da rabin bread ɗin, kunsan mutuniyar da ci.

Maah tana bata maganin ta amsa ta jefa can cikin maƙogwaronta ta kora da ruwa ta sha.
Ba daɗewa sai bacci.
MAAH tayi dabara ta cire mata kayan jikinta ta saka mata rigar bacci wacce taje Stairs ta ɗauko cikin sauran kayanta.

Maah parlour ta fito ta zauna suna jimami da Papa da su Mustapha da suka dawo, Sbd MAAH ta kirasu ta faɗa masu komai.

Jamal yau dai yadda yaga dare haka yaga wayewar gari, dan ya gaza bacci har kusan asuba.
Dan kwana yayi kusan yana salla yana roƙon ALLAH yasa a maida masa matarsa.

Ɓangaren Yah Boss yasan Zarah bata tafi ba, tunda ya ganta a Wayarsa.
Washegari ta kama Lahadi.
Yah Boss tunda ya dawo daga masallaci yaje yayi gym ya haye Stairs tayi wanka ta koma, baccinsa.
Su Suhaima ma bayan sunyi sallah bacci suka koma.

Tun ƙarfe 8 Zarah ta shirya tabar gidan zuwan gidan su Maah, sai tayi rashin Sa'a su Hajjah Mama sun koma babu baƙo ko ɗaya jiya kowa ya tafi inda ya fito, rabon basa nan wannan tashin hankalin zai faru.

Juhainah ma tunda Maah ta tasheta tayi sallah asuba, bayan tayi azkhar ta taɓa karatun Qur'ani ta koma bacci, dan zuciyarta ta rage zafi ba kamar jiya ba.

Lokacin da Zarah tazo Maah tana ɗakin Papa, sai masu aiki Halima na kitchen Zuwaira na gyaran parlour, ta gaisheta.
Zama tayi a parlour tana jiran fitowar Maah.

Ƙarfe 9:00Am, Khairat ta sauko tayi breakfast, taci karo da Zarah a parlour zaune.
Khairat ta ƙaraso tana faɗin.
"Aunty Zarah good morning, yanzu kike tafe?"
Zarah ta saki fuska tace.
"Na ɗan daɗe kaɗan Khairat Maah bata fito ba"

Khairat tace.
"Ok bari na kirata"

Bedroom ɗin Maah ta nufa.
Maah bata nan sai Juhainah tana bacci.
Khairat zuciyarta ta karaya, ta iso bakin bed ɗin ta zauna, ta shafi fuskar Juhainah tana faɗin.
"ALLAH yasa hakan yafi alkhairi Autar Maah"

Miƙewa tayi ta fito.
Tana fitowa Maah da Papa suna fitowa daga bedroom ɗinsa.
Ta isa gunsu ta gaishesu.
Papa ya riƙe hannunta yace.
"Khairiyya kin tashi? Ya Juhainah ta farka ne?"
Khairat tace.
"A'a tana bacci Papa, Maah Aunty Zarah ce tazo"

Maah tayi gaba tana faɗin.
"Allah yasa dai lafiya da safe haka? Kuzo muje dinning toh, kafin Autata ta motsa"

Zarah tana hango Maah da Papa ta gyara zamanta, suna isowa ta sauko ƙasa ta rusuna tana gaishe su.
Suka amsa cikin sakin fuska.
Maah tace.
"Muje ayi breakfast Zarah"

Zarah tace.
"A'a Maah sai da nayi na fito"

Maah tace Ok jiramu."

Khairat tayi serving ɗin Maah da Papa, ita ma tayi nata ta zauna.
Da tea ta fara.

Zarah tana zaune parlour tana raba idanuwa.
Suna idarwa suka dawo parlour Khairat ta tafi gun Juhainah dan tabar Zarah ta faɗi abinda ya kawota.

Maah tana kallonta tace.
"Zarah! Ina mijin naki Lafiya dai ko?"

Zarah kanta a ƙasa tace.
"Ashe su Hajjah Mama sun tafi tun Jiya da rana? Maah daman wani ɗan akasi aka samu yace na tafi ya sakeni saki ɗaya"

Papa yace.
"Subhanallahi me yayi zafi haka Abbah? Yanzu yana ina?"

Zarah tace.
"Na barosa gida"

Papa yace.
"Kiyi haƙuri karki tafi Jigawa ki koma ɗakinki zan kirasa tashi kije"

Maah tace.
"Abbah sha'aninsa sai haƙuri, kije zamu kirasa kar ma ayi katari ya iskeki anan"

Zarah tayi masu godiya ta miƙe ta masu sallama ta tafi.
Papa yace.
"Baiwar Allah, ko me ya haɗa su?"

Maah tace.
"Wlh baya sonta ne, sai haƙuri dan bazai maida ta ba, karma ka matsa masa"

Papa ya riƙe hannunta yana kallonta yace.
"Zainab! Mu haɗu mu roƙesa ba wai umarni zamu basa ba, hakan tirsasa wace da farko ma haka aka masa, idan kuma yaƙi babu dole ta tafi kawai"

Maah tace.
"Shi kenan Allah yasa mudace..."

Juhainah koda ta farka wanka tayi wajan 11am. Ta fito tayi breakfast sama² tayi zamanta parlour shiru ba wannan hayaniyar.
Yah Boss yau ba inda ya fita hana hutawa gidansa shi da ƴaƴansa, bai zo ganin Juhainah ba ma dan kar tayi rikici.

Zarah na ƙunshe ɓangarenta.
Jamal kuwa sai biyu yana zuwa gidansu Juhainah security's suka hanasa shiga, kamar yadda Yah Boss ya basu umarni jiya, idan ya shiga akan aikinsu.
Ya rasa yadda zai yi ba'ayi katari Papa ya gansa ba , Sbd ya fita ya dawo.

Da yamma bayan anyi sallar la'asar Mamy da Abba suka shirya suka tafi gidansu Juhainah......
Chapter 97 · 0% Book details