← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 113

Sashe 10

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Love Story💗🫂

Free Book

By
Real Rahma Ladingo

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVEL. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

Page 6

Daga can Ammar da wutar kishi take cin zuciyarsa, duk yayi watsa da kayan da suke bedroom ɗinsa, ya farfasa na fashewa ya yanke hannayensa suna zubar da jini.
Ya zama kamar mahaukaci.
Cikin wata irin murya kamar zai tashi duniya yana haƙi ya fara magana.

"Baby ai dole bazaki ɗauki kirana ba, na rantse da girman Allah idan kika kuskura kika auri wani bani ba Ammar, zan kashe wanda kika aura, na kasheki na kashe kaina, akan dai naga kin rayu da wanina gwara mu duka mu mutu.
Kinsan a halin da kika jefani a yau furucin zaki auri wani? wai har kina ikirarin shuga daddy zaki aura sunfi iya soyayya, ni kin aurenin kinga ban iya soyayyar ba? Ke ko kunya bakya ji yadda Allah ya tsaraki ki auri tsoho? Shin Ni me na rasa a halittar namiji? Toh ki shirya ɗaukan duk abinda da zanzo dashi, bye I love you..."

Ya gama faɗin abinda ya yake ransa ya katse kiran yana huci ya kalli yadda hannayensa suke fitar da jini.
Yah Boss ko ƙwaƙwaran motsi baiyi ba, har ya gama jin abinda Ammar yace ya katse kiran.
Wayan ya cire daga kunnensa yana jujjuyata a hannunsa, yana sauke numfashi mai ɗumi tare da furza iskar waje, har ƙamshin ɗumin iskar bakin nasa na zuwa hancin Juhainah da tayi mutuwar zaune, ganin dogon lokacin da Yah Boss yayi da wayarta a kunnensa, tasan koma meye ya gama jinsa.
Ji tayi ta sake shiga tashin hankali yadda yake buso iskar bakinsa waje akai-akai, idanunsa sun ƙanƙance.
A cikin zuciyarta ta furta.
"Innalillahi wa'inna alaihir raji'un! Shi kenan na mutu, yaji abinda banida mafita"
Manyan idanunta ta zuba wa kyakkyawar fuskarshi, jikinta na sake ɗaukan zafi, haka kawai ta tsani ganin ta ɓata ransa ko yayane, duk da tana son tsanarsa a cikin zuciyarta.
Hawaye sun wanke mata fuska ɓata ma san tanayi ba, ganin yadda idanunsa suka canza sosai.
Wani irin kuka ta saki tana haɗe hannayenta gu ɗaya tana fuskantar shi sosai ta matso dab da kujerarsa tace.
"Don Allah My brother kayi haƙuri bazan sake sakaka baçin rai ba daga yau, kuma na amince kamin duk hukuncin da kaga dama, zan ɗauka Ni dai ka daina fushin dani Please ko dan my Babies."
Waigowa yayi ya zuba mata Mayun idanunsa masu mugun nakasa ƙudirinta, na ƙiyayyarsa da take son sakawa acikin zuciyarta abun yaci tura.
Seconds 10 yayi yana kallonta fuskarshi a haɗe, ya janye idanunsa yana kallon titi.
Rinannun idanunta tai saurin lumshewa tana sake haɗe hannayenta alamar yayi haƙuri.
Muryanta cikin kalar tausayi ta sake faɗin.
"Please my brother kayi haƙuri bazan sake rashin jiba, zanyi karatun bana son auren......"
Tattausan hannunsa ya sake kaiwa bakin nata ya ɗan buge shi, tare da murɗa kunnenta ta mayafin Abaya, ya riƙosa sosai yana ɗan muɗawa.
Kamar zata saki fitsari dan azaba.
Wuya ta sakata fara ƙoƙarin kamo hannunsa.
Cikin ɓacin rai hannunsa ya ɗaga zai sauke mata mari, sai yaji abun yayi yawa zata illata sosai.
Fasawa yayi yana sauke hannunsa.
Da wani irin sauti ya furta.
"Idan kika kuskura kika kamo hannuna zaki raina kanki a yau. Matsa gun zamanki."

Fasawa tayi tana ɗora farin tattausan hannunta akan siraran cinyoyinta, tana ƙanƙame jikinta, azaba na shigarta.
Sakin kunnenta yayi, yana ɗauke kansa ya maida fuskarshi kallon titi yana saka wayan tata cikin aljihun gaban rigar Uniform ɗinsa.
Kukanta bai fitowa ciki² take yi, laɓɓanta sai raɗaɗi suke, ga kunnenta na zafin kamun da ya mata.
Cikin muryan da take nuna gargaɗi ya furta."Ki kama min bakinkin nan, you are a hypocrite."
Haɗiye kukanta tayi tana haɗa kai da guiwa, tana sauke ajiyar zuciya.
Fu'adh ta madubin motar yake kallonsu, shi fa wlh dariya suke basa sai yaga kamar Film yake kallo.
A kofar police station ɗin ya bada umarnin Walid ya tsaya kar shiga da motar ciki.
Parking ya yi fito dan buɗe masa ƙofa, sai dai kafin ma ya iso police biyu sun iso suna riƙe da bindiga sun buɗe masa motar cikin girmamawa.
Juhainah ta shiga raba idanunta, tana kallon yadda ake girmamasa, wasu narka² motoci biyu kusan tare suka buɗe motar suka fito suka nufo motar alamunsu sunji daɗin ganinsa.

Idanunta ta mayar akan yayanta nata wanda bai sake kallon inda take ba.
Anutse cikin kamewarsa muryansa mai daɗin saurara ya furta.
"Fu'adh! idan kunje gida tayi ƙoƙarin cin abinci, ka bata maganin da zai fitar mata da zogi da zazzaɓin, ta sha idan bata sha ba ka kirani zan zo in sha Allahu, idan ta warware inason ta kula da yarinyar nan ta hospital kafin na dawo gida zuwa dare a mayar da ita gun iyayenta."

Yana ƙara faɗin haka ya fara ƙoƙarin fito da ƙafafuwansa waje.
Fu'adh ya waigo yana kallonsa yace.

"Ok Sir, amma ita mara lafiyar zamu tafi da ita can gidane?"
Baice uffan ba sai da ya gama fitowa a hankali cikin tsare gida ya furta."Yes, or will you stay in the hospital until the night?"

Fu'adh yace A'a zamuje gidan mu jira ka."
Ya ƙarasa mgnar ya fitowa dan kai masa mug ɗin Madaran office.
Cikin girmamawa mutanen nan suka baiwa Yah Boss hannu suka yi musabaha yana ƙoƙarin ɗan sakin fuska.
Alhaji Hamza yace."Nakai 1 hour zaune, ina jira"

Yayin da Alhaji Badamasi yace."Nakusa 2 hours ni ai."
Yah Boss ya ɗan saki ƙaramin murmushin da ya masa wani irin kyau, a hankali ya furta."Ok ok yanzu ai nazo right? Muje ciki."
Ya faɗa yana yin gaba cikin wani irin takusan mai ɗaukan hankali.
Police nan na biye dashi, yayin dasu Alhj Badamasi suka take masu baya cike da farin cikin tarbar da Commissioner ya Masu.
Juhainah duk da tana cikin azabar ciwon kai da ƙafa da raɗaɗin marukan da ta sha, sai da murmushin Yah Boss ya burgeta, da yadda yake tafiya cikin Uniform ɗin da take fito da asalin kyawunsa da kwarjininsa tare da cikar halittarsa.
A hankali ta buɗe kumburaran bakinta ta furta.
"I hate you Yah Boss, May God punish you for not forgiving me."
Kuma ai ko mai kaji cikin wayan kai ka jawa kanka, ah Toh."
Ta ƙarasa mgnar tana share hawaye tare da shafo lips ɗinta da ya kumbura.
Side ɗin da ya zauna ta kalla, ƙamshinsa ya kama gun kamar yana nan.
Hararen gun tayi, sai ta matsa dai-dai inda ya zauna ta jingina kanta da kujeran tana rufe idanunta.
Fu'adh yana ajiye mug ya fito ya shiga mota, Walid yaja suka tafi.
Fu'adh ya waigo yana kallon Juhainah zai mata magana ganin idanunta a rufe kuma ta canza gun zama yaja bakinsa yayi gum.


Har suka iso ƙaton haɗaɗɗan gidan Yah Boss, Juhainah bata buɗe idanunta ba, har sai da aka buɗe gate ɗin aka shiga can asalin gidan akayi parking kafin ta buɗe idanunta, tana sauke ajiyar zuciya.
Kafin ma Walid ya zagayo ya buɗe mata har ta ɓalle mirfin motar ta fice, tana ɗingisa wa, bata ma son kowa ya mata magana.
Ganin hakan ya saka Fu'adh ƙyaleta ya barta idan ta shiga cikin sai ya bita ya cika umarnin Sir.
Ma'aikatan gidan saboda sun mata farin sani ƙanwar mai gidan ne, tun wancan tsohon gidan lokacin marigayi nada rai tana yawan zuwa, yanzu ma wani lokacin tana biyo su Suhaima, sai dai ba sosai ba.
Sunnu suka fara mata suna gaisheta, ganin tana ɗingishi.
Hannu kawai take ɗaga masu ba wanda ta kula.
Masauki tayi a lafiyayyan parlon saman lallausan Turkish Chair, tana kwanciya tare da rufe idanunta, zazzaɓi ya rufeta ga yunwa na cin hanjinta.
Fu'adh tun kafin ya shigo ya kira Jamilu ya sanar masa Juhainah na falo ya kai mata abinci kan dining room.
Can yakai ya jera ya iso inda take kwance yana faɗi.
"Ranki shi daɗe ankai komai kan dining."
Chapter 10 · 0% Book details