← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 113

Sashe 44

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammar Allah ne ya gyara dan motar ta ƙwace masa, ya fara yawo akan titi kafin ya taka Burki yana samu daƙyar motar ta tsaya, ya gangara bakin titi.
Sakin wayar yayi daga hannunsa yana wani irin huci.
Jikinsa baki ɗaya rawa yake idanunsa sun firfito, sunyi jajir, kai idan kaka yadda jikin Ammar yake kyarma dole kaji tsoronsa.
Baki ɗaya jijiyon kansa sun minmiƙe.
Da wani irin sauti yace.
"Juhainah nine taci amana? Ni ta wulaƙanta? Kenan daman bata sona da gaske yaudarata take? Tabdijam! Ai Wlh bata isa ba, babu macen da zan so ta wulaƙantani na ƙyaleta taci banza, zan rama sannu a hankali ba zanyi gaggawa ba, amman zasu sani daga ita har wanda zata aura sai na saka sun shiga ƙunci da baƙin ciki sha Allahu..."
Yafi minti ashirin zaune a motar kafin ya iya kunna motar yaja yana ɗaukan wayan da ya jefar ƙasan ƙafafunsa.
Rivers yawa motar yana wani irin gudu.
Number Zuby ya kira.
Kamar tana jira Bugu ɗaya ta ɗaga.
"Ki sameni a Abuja raod yanzu kina wuce minti ashirin bana buƙatarki, karki kuskura ma kizo.."
Bai jira Zuby tayi magana ba, ya katse kiran.
Ɓoyayyen gun da yake zuwa a anguwan Abuja raod, can ya nufa....


Aunty Sumy ana kiraye² sallar Maghreb suka iso bakin gate ɗin gidan su Surayya.
Anan bakin gate tayi parking, tana kallon Juhainah da take kusanta zaune Suhaima ninniƙe da ita.
Murmushi tayi tace.
"Toh ku fita muje ana kiran Sallah idan munyi Sallah sai mu wuce"
Juhainah ta Turo laɓɓanta gaba tana faɗin.
"Allah inajin kunyar Mamy kuje zan shigo"
Aunty Sumy ta buɗe ƙofar ta fito.
Su Surayya da Hanifah suka fito, harda su Suhaima, amma ƙememe Juhainah taƙi fita.
Surayya ta kamo hannunta tace.
"Don Allah muje Mamy ai mamarki ce"
Su Aunty Sumy sunyi gaba, har sun buɗe ƙaramin gate sun shiga.
Juhainah ta fito tana faɗin.
"Wlh inajin nauyin Mamy ne"
Dariya Surayya tayi.
Juhainah tana hararenta.
Suna saka kai zasu shiga gidan Jamal yana ƙoƙarin fitowa zuwa masallaci.
Surayya tai saurin matsawa gefe ta basa hanya.
Ko kallonsu baiba zai wuce Juhainah ta tare masa hanya tana shagwaɓe fuska tace.
"Yaya Jamal! Ina wuni mubar faɗa yayana baya so fushi yake dani, akanka bana jure hakan"
Ta faɗa cike da shagwaɓa tana langwaɓe kanta.
Matsawa yayi baya yana haɗe fuska a hankali ya furta.
"Zanje masallaci ne, ban hanya"
Matsosa ta sake yi tana faɗin.
"Ok baka son mu dinga magana ne? Nace kayi haƙuri akan abinda na maka bazan sake ba kaji?"

Manyan kyawawan idanunsa ya ɗan zuba mata baice komai ba, ya juya ya nufi babban gate, saboda lokaci zata ɓata masa.
Hawaye suka fara cikowa idanun Juhainah abinda bata taɓa yiwa wani na waje ba, ya sakata kuka da garaje, saboda taurin zuciyarta, sai dai idanunta suyi Ja.
Surayya ma Haushin Jamal ya kamata ta kama hannun Juhainah tana faɗin.
"Dalla can akan me zaki zubar da hawayen inda ba'a san darajarki ba, muje Wlh tsaf sai na zayyanawa Mamy abinda ya faru"
Juhainah dai batace uffan ba, Sbd ranta yayi masifar ɓaci, ba wani ɗa namiji da ya taɓa dizgata sai yau Jamal ya wulaƙanta ta, tabbas sai ta nuna masa ita ƴar halak ce, ta ruwan sanyi.

Su Aunty Sumy suna shiga parlour Mamy na miƙe wa zatayi alwala, ganinsu ta tarbesu cikin karramawa, tana faɗin.
"Sannunku da zuwa Sumayya! Nima ban jima da shigowa gidan ba, daga gidanku, Bismillah ku zauna"
Aunty Sumy da Hanifah suka gaisheta, suna zama.
Mamy ta amsa tana faɗin.
"Ina Ɗiyata Bilkisu da mutuniyar Tata?"
Aunty Sumy zatayi magana Surayya ta shigo riƙe da hannun Juhainah tana masifa.
Mamy tace.
"Ke kuma kina kumfar baki ke da wa?"
Juhainah ta rusuna ta gaisheta cike da ladabi.
Mamy ta kamo hannunta tana amsawa cikin farin cikin ganinta.
Surayya tace.
"Allah Mamy sai kin shatawa Yaya Jamal layi akan sister Juhainah, kinga wulaƙancin da ya mata yanzu..."

Ta zayyana wa Mamy komai.
Ai kuwa Aunty Sumy ranta yayi bala'in ɓaci, tamkar a gabanta yaciwa ƙanwarta mutuncin, dan har kana iya gane yadda fuskarta ta canza lokaci ɗaya, duk da tayi ƙoƙarin ɓoyewan.
Mamy kanta ranta ya ɓaci tana riƙe da hannun Juhainah tace.
"Don Allah Sumayya kuyi haƙuri Wlh idan dai nice na haifi Jamaluddin da cikina in sha Allahu bazai sake ba, ko kwatanta hakan, kuje kuyi sallah, Surayya kuje ɗakinki suyi sallah, Daughter muje bedroom ɗina"

Ta ƙarasa maganar tana jan hannun Juhainah Allah ya sani tana bala'in sonta bazata bari ta rasa Juhainah matsayin surukarta ba, zata basa mamaki idan dai itane mahaifiyarsa.
Aunty Sumy ta miƙe suka nufi hanyar bedroom ɗin Surayya tana ɗan jin sanyi ganin yadda Mamy take son ƙanwarta.

Bayan Juhainah ta idar da sallah, tana zaune kan darduma tana azkhar.
Mamy itama ta idar ta kalli Juhainah tace.
"Don Allah daughter kiyi haƙuri ki barni dashi, duk Adamawa baki ɗayanta bai isa ya samu wacce ta fiki ba, ki rabu da shi zai shiga hannunki namiji ne fa"
Juhainah kanta a ƙasa a hankali tace.
"Mamy babu komai ai yaci darajar ku"
Mamy ta shafa kanta tace.
"Nagode karki damu in sha Allahu Jamal alkhairi ne a gareki"
Juhainah a hankali tace.
"Mamy Abba bai shigo ba, daman mun biyo ne inaso mu kwana da Surayya can gidansu Maah"
Mamy tayi murmushi tace.
"Sai bayan isha'i zai shigo kuje zan sanar da shi"
Juhainah tayi mata godiya.
Aunty Sumy suna gama azkhar suka fito parlour.
Basu daɗe da zama ba Mamy da jin suka fito.
Mamy tana murmushi tace.
"Sumayya zaku iya tafiya idan Abban nata yazo zan sanar masa."
Aunty Sumy tace.
"Mun gode Mamy Allah ya ƙara girma..."

Surayya ta ɗauko kaya kala biyu ta fito.
Aunty Sumy tayi wa Mamy sallama suka tafi.
Juhainah sai farin ciki take ta ma manta ɓacin ran da Jamal ya sakata.


50 Houses

Maah zaune daga ita sai Sadeeq ɗan Aunty Sumy sai little Maah da Rumaisa ta barta Sbd Maah tace a barta.
Su Ruwaida su Haj Jamila duk sun tafi gida kafin Maghreb, Maah da kanta tace su Rumaisa su tafi gidajansu.
Saboda ance sai zuwa gobe su Yah Mustapha zasu iso da amarya kwanan hanya zasuyi.

Da sallama suka shigo parlour.
Juhainah da gudu ta isa gun Maah, tana janye Sadeeq da little Maah.
Jikinta ta faɗa tana rungumeta tare da sumbatar Maah a kumatunta.
Ashagwaɓe tace.
"I miss you My Maah I love you My Maah"

Maah cikin farin cikin ganin Autarta ta sanya hannayenta ta rungumeta gam tana murmushi tace.
"Love you too Babyn Maah da Papa and Abbah ko?"
A shagwaɓe ta ɗaga kanta tana ƙamƙameta.
Aunty Sumy ta zauna tana faɗin.
"Oh! Ni Sumayya shi ne aka ture mana ya'yan sbd Allah"
Maah tayi dariya tana faɗin.
"Ah toh haka kawai sai na hana Autata taji ɗumina saboda ya'yan ku"
Ta ƙarasa maganar tana kallon Surayya tace.
"Daughter Surry inji Auta"
Surayya tana dariya tace.
"Maah kin iya faɗi kuwa, inata gaisheki Juhainah ta ɗauki hankalinki"

Suhaima ta rungume Maah tana Turo baki tana faɗin.
Ni ba'a gani ba, sai Aunty J."
Maah ta janye Juhainah tana rungume Suhaima da Al'amin tana faɗin.
"Wace Ni na naƙi ganin Suhaima Mrs Yakubu Janfar, da mijina Muhammad Al'amiin Janfar, sannunku da zuwa nayi kewarku sosai"
Dariya Al'amin yayi yana sumbatar kumatunta.
Khairat ta turo baki tana faɗin.
"Maah ni dan inada haƙuri baza'a rungumeni ba?"
Ta janyo hannunta tana rungumesu da su Suhaima tana faɗin.
"Haba Khairiyya tah wai dan naga ke babba ce, ya karatun?"
Khairat tayi murmushi tace.
"Alhamdoulillah Maah"

Hanifah ta gaishe da Maah.
Maah bata kalleta ba ta amsa tana faɗin.
"Duk sun tafi ashe ke kina can gun su Sumayya, toh sai kiyi niya ki tafi, mijinki yau bazasu dawo ba"
A hankali kanta a ƙasa tace.
"Maah zan kwana nan can babu daɗi ni ɗaya"
Maah batace komai ba.
Aunty Sumy tace.
"Eh kiyi kwanciyar ki gobe idan Nasir yazo sai ku tafi"

Juhainah ta miƙe tana kama hannun Surayya tana faɗin.
"Maah muna Stairs idan Papana yazo a taɓoni, my Babies ku kirani"
Maah tana murmushi tace.
"Toh Autah"
Aunty Sumy ta kalli Hanifah tana faɗin.
"Hanifah ki bisu mana kuyi fira, kije bedroom ɗin Khairat zaki fi hutawa, Juhainah da Surayya bazasu barki kiyi bacci ba.
Ni yanzu gida zanje, naga wata wainar su Habibullah da Fatima suke toyawa"
Hanifah ta miƙe tana faɗin.
"Tom Aunty Sumy a gaida gida"
Hanyar Stairs ta nufa.
Maah dai hira take dasu Suhaima.
Aunty Sumy ta kalli Suhaima tana faɗin.
"My Babies kuje gun Aunty J ɗin ku"
Suhaima tace.
"Toh Momy, Maah idan Papa yazo zamu dawo fira"

Hannun Al'amin ta kama suka tafi Maah tana faɗin.
"Yau ƙwace mijin za'amin kenan?"
Al'amin yana dariya.

Aunty Sumy ta matso kusan Maah tana kamo hannun mahaifiyarta ta marairaice fuska tana faɗin.
"Maah! Wai mi Hanifah ta miki ne?"
Maah ta kalli Sumy tana faɗin.
"Kinga ku rabu dani nifa Uwace.
ba wai matar ɗana da haifa da cikina ba, ɗiyan wasu ma so nake, amman wannan yarinyar ca nake tun kafin aurensu nace masa ta yi masa girma yaƙi dudu shekara biyu ne ko ɗaya ne ma ya bata, kalli yadda yadda take zama shi yana ramewa, duk bana ce auren sa'anka ko wanda ya girme maka haramun bane, tunda Manzon Allah yayi.
Matsalar da take damu na Sumayya, wlh magana babu ƙarya haka take cewar uwarta mayya ce, Cin mutane uwar take wai ita an bata nonon Jakka ne shiyasa bata ganin kayan cikin mutane, amma ai ba tabbas ɗin bazata cin ba, ko bazata ciba idan ta haihu da Nasir ya'yan nata za'a kirasu da jikokin Mayya ne, an ɓata mana zuri'a, wannan yaro nawa ya cucemu Wlh.
Chapter 44 · 0% Book details