Sashe 25
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammar cikin farin ciki ya shigo parlour iyayensa yana washe baki.
Kusan Dady Najib ya zauna.
Haj Maimuna tana kallonsa fuska a sake tace.
"Ammar! Wannan farin cikin fa? Bamu musha"
Ƴar dariya yayi yana kamo hannun Dady Najib yace.
"Dadyna albishirin ka?"
Dady Najib ya shafi kansa yana faɗin.
"Goro fari Ammar bamu musha"
Cikin farin ciki yace.
"Yayan Juhainah ya kirani yace na shirya a ko wani lokaci zai iya kirana yace an bani daman nema aurenta na turo"
Dady Najib ya jinjina kansa ya a faɗin.
"Ma sha Allahu naji daɗi sosai, Allah ya kaimu lokacin"
Ammar ya amsa da.
"Ameen ya Allah Dady"
Haj Maimuna tace.
"Ah lallai an kusa bikin ƙasa da ƙasa Kenan"
Sai washe baki yake yi, haka sukaci gaba da hira, Haj Maimuna tana faɗin irin yadda zata haɗa ƙawayenta na kece raini a bikin babban ɗanta...
★
Maah da Papa suna parlour suna kallon Tv tashar Sunnah Tv.
Sai Khairat zaune tana tsefe kanta.
Ƙaran taɓa Kofar da sukaji suka juyawa.
Surayya ta shigo da sallama.
Suka amsa cikin sakin fuska.
Maah tana faɗin.
"Surayya! Kece da rana nan? Ya gida yasu Mamynki?"
Cikin girmamawa ta duƙa tana gaishesu.
Papa ya amsa yana faɗin.
"Ya karatu Surayya?"
Zama tayi kusan Khairat tana amsawa da.
"Alhamdoulillah! Papa, Aunty Khairat ina wuni"
Khairat ta amsa tana murmushi, tace.
"Yasu Mamy?"
Maah tace.
"Kin biyo mutuniyar ko?"
Surayya tace.
"Eh Wlh Maah bana samunta a waya, shine hankalina yaƙi kwanciya, nazo naga lafiyarta"
Maah tana murmushi tace.
"Tana gidan yayansu Abbah ta bugo ruwa"
Surayya zaro idanunta tana faɗin.
"Maah! Ya zanyi inason ganinta, can ba gun wargi ba, daman gidan yaya Mustapha ne ko yaya Umar ko Yaya Nasir sai na bita"
Maah dariya tayi tana faɗin.
"Karki damu bazai maki komai, ki tashi na saka Hamza direban su Suhaima ya kaiki kai tsaye zai shigar dake gidan"
Surayya ta haɗiye yawun tsoro tana raba idanuwa a hankali tace.
"Aunty Khairat! Muje mana Please"
Khairat ta ɓata fuska kamar yadda Yah Boss yake yi, tace.
"Tabb a'a Wlh bana zuwa, ni Salon ma zan tafi"
Papa yace.
"Wai duk Abbah Na ake gudu haka? Allah kawo min wacce zata sauya min shi"
Maah kamar zata yi kuka tace.
"Allahumma Ameen ya Allah Harɗo"
Ta ƙarasa maganar tana kiran number Hamza.
Yana ɗauka ta sanar da shi zai kai Surayya ƙawar Juhainah can gidan Abbah ya tabbata ya sata asalin ɓangaren Abbah.
Surayya ita dai cikin ɗari² ta shiga lafiyayyar motar Hamza yaja suka tafi, saboda sanin shi waye ba'a masa shamaki da shiga gidan.
★
Yah Boss dukkan abinda Juhainah ta faɗa caraf acikin kunnensa, dan da ya rufe ƙofar bai gusa ba, saboda yasan halinta batada mutumci zata iya faɗin wani abun tunda tasan baya kusanta.
Yana gama jin sambatun da take yi wani irin ƙaramin murmushi ya suɓuce masa akan kyakkyawar fuskarsa, wanda har dimples ɗinsa na loɓawa, ya girgiza kansa ya nufi hanyar parlour sa, dan lamarin na Juhainah ya girmamesa, shi yanzu lamarin nata, yanzu ya rage basa takaici, tunda idan ya biye mata zai mata bugun da zata iya mutuwa, ko ta nakasa, sai dai kuma bazai zuba mata ido ba.
Kai tsaye ya kira Fu'adh, yana ɗagawa cikin nutsuwarsa muryansa cike da izza ya furta.
"Fu'adh! A fasa bincike bata son Ammar kuma nima Sam bai kwanta min ba, bazan ba shi ƙanwata ba, amma ita zanyi maganinta yau ɗin nan, a shirya mota zamu koma can gidanmu yanzu"
Fu'adh ya saki baki galala cike da mamaki, sai ya amsa da.
"Ok Sir sai ka fito, amma maganar Juhainah babba, don Allah ka duba yarinyar nan, karka biya Suhaima yarinya ce bata san so ko ƙi ba, Wlh zakaji daɗin auren Ju..."
Diff Yah Boss ya katse kiran Yana kama fuska sosai, ya buɗe ƙofar parlour nasa ya shiga, a hankali ya furta.
"Wai mi yake damun Fu'adh ne? Wlh ba dan na masa farin saniba sai ince itane take aikinsa gurina, toh sam ba haka bane, kawai masifarsa ne kawai, kamar yafi kowa tausayi, zan iya mallaka tarin dukiya harda gida da mota, amma aure kam a'a tunda bana sonta, zuciyata ba kara zube take kama son kowani kalar mutum ba, duk Kawun mace da class ɗinta, kai ko maza bada kowa nake mu'amala ba, bare mace mai hatsari.
Idan yana son yarinyar nan ya Aureta alright, haba! Koda Suhaima bata nuna ƙiyayya ba, Ni bana jin Zan iya haɗa jikina da wannan matar fa! No! I'm possible, me yasa baya gane ni waye ne, mi zanyi da mace a yanzu ko mai class ma bare wannan abun"
Ya ƙarasa maganar idanunsa na ƙoƙarin canza kala.
A gaggauce ya canza kaya cikin wata ɗanyar shadda Brown Sai dai ɗinkin babu tarkace simple ne, wani irin kyau da kwarjini shaddar da ɗinkin suka ƙara ma Yah Boss.
Tsaye yake gaban madubi yana canza agogo.
Agogon da ya canza yadda take ɗaukan ido kawai ta sanar dakai wacece ita, a nuste ya fesa turarensa mai tsayawa a rai.
Takalmin da ya saka dogayen fararen ƙafafunsa rufaffe ne baƙi sai ɗaukan ido yake, hula Mai uban kudi Brown ya saka ya manna tsadaddan Glass akan idanunsa.
Juhainah sai da taci kukanta ta ƙoshi ta miƙe saboda azabar yinwa da takeji ta shiga bedroom ta samo biscuits ta dawo parlour ta zauna ta buɗe tanaci tana hawaye.
A haka ya buɗe ƙofar ya shigo parlourn.
Ƙamshin sa ya saka ta gane shine ya shigo.
Ledar biscuit ɗin ta zazzage sauran a hannunta tayi jifa da ledar tana miƙewa tsaye ta fashe da kuka tana nufo gunsa tana kuka harda majina.
Yah Boss yaja ya tsaya yana kallonta ta cikin Glass fuska a kame.
Ƙasa tayi da kanta saboda farin Glass ne tana ganin idanunsa.
Sai da tazo dab da ƙafafuwan sa, ta zube gabansa tana tura sauran biscuit ɗin hannunta acikin bakinta, tana taunawa.
Da mamakin yake kallon ikon Allah mi haɗin wanda yake cikin tashin hankali dacin biscuit? tana kuka tana cin biscuits ɗin.
Haka kawai ya tsinci kansa da murmusawa, iya Fatar bakinsa.
Hannayenta duka ta saka ta kamo ƙafafuwansa da suke cikin rufaffen takalmi tana faɗin.
"Don Allah yaya Abubakar Sadeeq kamin rai ka ceceni karka aura min Ammar Wallahi ƙaddara ce ta haɗa soyayyata da tashi, amma bana masa son aure, ni ka aurawa min wani bana sonsa da aure"
Yah Boss baice uffan ba ya zuba mata lumsassun fararen kyawawan idanunsa, takaicin ta ya saka baya ma jin zai iya ce mata wani abin ma.
Ƙafafuwansa ya janye ta tafi luuuuu kanta zai bugu da ƙofar parlon, yayi saurin duƙowa ya tare ƙofar da hannayensa, kanta ya faɗo saman hannayensa.
Ƙamshinsa da yake mata azabar daɗi ga tattausan hannunsa da tayi pillow da shi ta shaƙi ƙamshinsa har buɗe hancinta takeyi, tana ƙoƙarin ƙamƙame hannayensa da kanta yake sama, yayi saurin hana hakan, sama ya miƙar da ita cikin tsawa amma muryan bata ɗagawa sosai sbd rashin don hayaniyarsa, bai koyawa kansa ɗaga murya ba, duk da yana ɗan sanda, kuma a haka ake tsananin tsoronsa.
A hankali ya furta.
"Tsaya min da ƙafafuwan ki, ko kiji mari yanzu nan."
Ai kuwa sai ga Juhainah, daram a tsaye da ƙafafuwanta sai dai jirin da take ji neman faɗuwa take ta riƙe gefen rigarsa ta riƙe cikin tsananin shagwaɓar da take masa, duk tsoronsa da take sai ta masa shagwaɓar nan, a hankali tace.
"Yaya Sadeeq jiri nake"
Baya ya matsa yadda bazai fizge rigar ba dan karta faɗa, a hankali ya furta.
"Kije ki zauna, na riƙe ki ne? Kuma kiyi ƙoƙari ki fito da wani mijin Daga yau zuwa kwana uku.
Wallahi tallahi bazanyi kaffara ba, idan baki fito da shi ba, zan aura miki duk wanda naga dama, kuma ƙwalelenki auren shuga Dady, yaro zan aura miki, talaka ko mai kuɗi nima ban yanke ba, dan haka ki cece kanki ki samo wanda zaki aura, ke yanzu bakya jin kunya kice sai babba kike so?"
Bakinta yana rawa ta buɗe tana faɗin.
"Yaya Sadeeq! Bana son kowa ni bansan wanda nake so ba, amman dai banda kowa Duk na korasu sai Ammar kuma ni bazan iya aurensa ba..."
Hararenta yayi tai saurin rufe bakinta tana lumshe idanunta.
"Ki nomo ko nayi abinda nace, baki isa kisani inyi kaffara ba"
Ya faɗa yana fizge rigarsa daga hannunta, ya juya ya buɗe ƙofar ya wuce abinsa.
Juhainah mutuwar tsaye tayi a gurin.
Jin jiri na ɗaukanta ta dafa bango ta nifi bedroom tana hawaye.
Suhaima tana hango Dadd ɗinta ta miƙe ta nufosa tana faɗin.
"My Dadd wai ina Auntie Juhainah?"
Hannunta ya kamo yana nuna mata hanyar Stairs.
Cikin farin ciki ta nufi hanyar Stairs ɗin da gudu
Yah Boss ya kamo Al'amin a hankali ya furta.
"Please Babies Amiin kaje ka huta ka samu bacci, kaje gun Juhainah ga Suhaima can ta tafi."
Al'amin yayi wa Yah Boss kiss a hannu Yana masa bye-bye ya tafi shima.
Idanunsa yakai akan pictures ɗin Khadija.
Ajiyar zuciya ya sauke ya furta.
"I love you Dijetah"
Fu'adh dai yayi murmushi yana faɗin.
"Sir an fito?"
Yah Boss yaƙi kallonsa bai kuma amsa ba yasa kai ya fara tafiya cikin izzarsa da take jinin jikinsa.
Sun zo dab da zasu iso ƙofar parlour aka danna doorbell.
Fu'adh ya ƙarasa ya kama handle ɗin mai shegen kyau, wanda key ce idan bakada key ko hoton yatsarka toh idan ba'a buɗe maka daga ciki ba, toh na waje baya shiga parlour.
Surayya ganin wanda yake ƙoƙarin fitowa fuska a mugun kame, babu damar ka samu ka ƙare masa kallo, hakan ya sakata suman tsaye, wani bala'in kyau da kwarjini ya mata, masofaffiyar ƙaunar da take masa ta bijuro mata, sai dai ba gurin nunawa ba.
Bata san lokacin da rusuna ta gaishesu cikin girmamawa.
Ba tare da ya kalleta ba, ya amsa yana wucewa ba tare da ya tsaya ba, ya furta.
"Ya akayi kika san tana nan? Akwai waya hannunta ne?"
Surayya tana inda² tace.
"A'a inata kiranta bana samunta shine naje can gida Maah tace tana nan, ta saka Hamza direba ya kawoni"