← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 113

Sashe 86

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasir ya saki ɓoyayyen murmushi ya san ya gama lalata zuciyar Surayya akansa.
A hankali yakai wayan kunnensa Farid yanata masifa.
"Inzo gidanku inyi miki me? Bayan ga wanda kike so can kina binsa yawo, bakida damar aiwatar da komai sai abinda yaso dake, tun farko duk abinda yake faruwa da yawunki, in dai kina sona gobe inason ki nuna min haka na turo iyayyena idan kuma shi kike so na haƙura mata dubu ɗari nawane cikin Jihar Adamawa ko ina zanje na samo wata, gobe na baki, aikin banza kawai..."
Yana gama faɗin haka ya katse kiran.
Nasir ya kamo hannunta ya manna mata wayarta.
Ido ta buɗe ta kalleshi tana hawaye.
Shi kuma hankalinsa agun driving.
A hankali ya furta.
"Yace gobe zai turo iyayensa ki sanar daga kin sauka"
Fashewa tayi da kuka tana kallonsa.
Parking yayi a gefen titi yana kame fuska yace.
"Fita ki hau keke napep Malama na tsani raguwar mace, kuma bana son yawan magana"
Surayya dan taga zai barta cikin daren nan ta hau keke napep ta rage kukan ta buɗe ƙofar ta zura ƙafafuwanta tana ƙoƙarin fita.
Wani irin fizgota yayi ta dawo motar har tana faɗowa jikinsa, yayi saurin ja baya.
Gyara zamanta tayi.
A hankali yace.
"Kina hauka ne ina zaki?"
A hankali tana hawaye tace.

"TOH ba ka korani ba Yah Nasir ya zanyi?"
Nasir ganin yana ƙoƙarin tonawa kansa asiri ya haɗe face, shi ya rasa tun randa suka fara sa'insa yarinyar ta tsaya masa a zuciya haka kawai, ba ma randa ya azabtar da ita nan, yana basarwa ne Sbd miskilanci.

Ya ranƙwafo har numfashinsu na haɗewa ya rufe ƙofar ya gyara zamansa baice uffan ba, ya kunna motar yaja ya nufi hanyar gidan su Surayya.
A hankali tace.
"Nagode Yah Nasir, amma don Allah ka daina tsananta ni inason duk jinin Aunty Juhainah"
Fuska ya kame yana kallonta a hankali ya furta.

"Ok kina sona kenan dai?"

Idanunta ta zaro ta dafe ƙirjinta tace.
"A'a Wlh ba son soyayya ba, son ƴan uwantaka nake nufi, ina Ni ina kai, ai kafi ƙarfina sai Aunty Hanifah, kalli fa irin abinda naga tana maka, ai sai kishi ya kashe..."
Ai da sauri taja burki tana rufe bakinta da tafin hannunta.
Ɓoyayyen murmushi yayi ganin tana son tonawa kanta asiri.
Bai sake magana ba yaci gaba da driving ɗinsa.
A bakin gate ɗin gidansu Surayya yay parking, bai kalli inda take ba yana jiran ta fita.
Ajiyar zuciya ta sauke ta gyara mayafinta, ta kalleshi a tace.
"Yah Nasir nagode"
Bai kalleta ba a hankali ya furta.

"Riƙe godiyar ki"

A hankali ta buɗe ƙofar jiki a sanyaye bataji daɗin abinda yace mata ba, ta zura ƙafafuwanta waje ta sauko tana kallonsa ta rufe masa ƙofar, ta nufi gate ɗin gidan su.
Motarsa yaja yabar gurin, tana waiwayan shi, ta buɗe gate ta shi cikin gidan.

"Amarya har ta zo kenan wannan mugun yana yawo dani, ban yafe masa ba azzalumi kawai, mutum sai girman kai da miskilancin tsiya"
Kai tsaye part ɗin Jamal ta nufa wajen Juhainah.

Yah Boss
Da sauri Yah Boss ya furta.
"Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil, La Haula Wala Quwwata Illah Billah"
Mustapha kansa yaji furucin Zarah abin ya basa mamaki matuƙa.
Anutse ya tako ya ƙarasa isa gun Turkish Chairs ɗin ya zaunar da Suhaima.
Zama yayi kusanta yana riƙe hannunta, takaicin Zarah na son fito da asalin ɓacin ransa akan kyakkyawar fuskarsa, da wuya kaga ɓacin ransa akan fuskarsa ya iya ɓoye kowacce irin damuwa da tashin hankali cikin zuciyarsa.
Suhaima ta jefo masa tambaya.

"My Dadd haƙƙinta na me ka cinye mata naji tace na aure?"

Lumsassun idanunsa ya kafe Suhaima a hankali ya furta.
"Kuɗinta ne na sadaki na ranta ranan banda canji, yanzu zan bata, My Babie ina matar da kika ce zaki samo min? Inason ki kwantar da hankalin ki, Aunty Bilkisu duk inda taje ai taki ce, bare gari ɗaya, karki saka damuwarta a ranki, itama zata dinga zuwa dubaku, kuma zaku dinga zuwa dubata"
Suhaima taji daɗin kalaman Dadd ɗinta, da kuma tambayar da ya mata.
Ɗan sakin fuska tai kamar ba ita ne ta gama kuka ba, Yah Boss yasan halin ƴarsa yasan yadda zai shawo kan abunsa.
A hankali Suhaima tace.
"Ni Wlh my Dadd ban samu kalarka ba, ka kwantar da hankalin ka zan samo maka in sha Allahu koma yaushe ne, ko ba kwanan nan ba, nafi son na samu mai nutsuwa da gayu irin na Aunt J ɗita, ko nasaka ta samo maka da kanta"

Dogon hancinta yaja yana goge hawayen fuskarta da ya fara bushewa.
A hankali ya furta.
"Zaku zauna anan ne ko gidan Maah zaku tafi yanzu na kaiku da kaina ?"
Shagwaɓe fuska tayi ta maƙale kafaɗa tace.
"Gobe da jibi weekend ba school zamu zauna gun mahaifinmu, ran Monday idan Hamza ya kaimu school, idan mun tashi sai ya wuce damu gidan Maah"

Kiss ya mata a goshinta a hankali ya furta.
"Thank you My Babies I love you, ALLAH ya albarkaci rayuwar ku, ya jiƙan Khadijah"

Suhaima ta rungume Yah Boss tace.
"Ameen Amin My Dadd love you too"

Mustapha ya iso ya zauna Al'amin yana jikinsa, ya kalli Yah Boss yace.
"My brother zan koma, yarana sunƙi su kwana gidana"
Yah Boss a hankali ya furta.
"My boy Amiin bazaka bi Uncle ba?"

Al'amin ya maƙale kafaɗa yace.
"A'a My Dadd nan zanyi weekend, wani weekend gidan Aunt J wancan weekend sai naje gidan Uncle"

Yah Boss ya ɗan murmusa a hankali ya furta.
"Mustapha kaji fa, sai kabi layi Babie Suhaima Mai jama'a"
Mustapha yayi murmushi yace.
"Ya na iya my brother dole nabi, amma fa idan ranan tazo Babie ba canza akala"

Suhaima tace.
"Bazan canza ba uncle. My Amiin tashi muje Stairs muyi shirin bacci, nagaji gobe sai naje gidan Aunty J"
Al'amin ya miƙe yana kamo hannunta yace.
"Nima zanje Aunty Suhaima"
Riƙe hannunsa tai tace.
"Toh Allah ya kaimu zamuje ai. My Dadd good night, uncle Mustapha good night"

Mustapha yace.
"Night My Babies sweet dreams bye"

Suhaima bata sake magana taja ƙaninta suka nufi hanyar Stairs.
Yah Boss ya kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa akan ƴaƴansa, yana faɗin.
"My Babies kuyi addu'ar kwanciya bacci Ok?"
Suka amsa da.
"Ok My Dadd"

Bayan su Suhaima sun tafi Mustapha fuskanci Yah Boss, a hankali cikin kwantar da murya yace.
"My brother wannan wace irin mata ka auro? Anya nan gaba kaɗan bazata ɓata maka tarbiyya ya'ya ba?"

Yah Boss ya ɗauki ƙaramin Flask mai shegen kyau ya tsiyaya Black tea ɗin yakai bakinsa.
A hankali ya furta.
"Yanzu Babie Suhaima har ta tambaye Ni wani haƙƙine take son na bata, basan wace irin ƙaddara bace wannan Wlh natsani matar nan bana son ganinta, zan saketa na huta, nayi ƙoƙarin jure wasu lokuta da ita dan biyayya wa Hajiya Mama amma yanzu ban iyawa sam"

Mustapha ya kamo hannun yayansa ya riƙe a hankali yace.
"Toh akan wani dalilin ma zakayi wannan gangancin ka auri wacce baka ƙauna Sbd biyayya? Ko Ni Wlh bata min ba, ba wai ina zugaka ba"

Yah Boss yaja tsaki a hankali ya furta.
"Zan ɗauki mata akanta, tunda na fahimci abinda yasa ta aure Ni..."

Sun ɗan jima suna hira Mustapha ya masa sallama ya tafi ganin dare yayi.
Yah Boss lokacin da ya hau Upstairs su Suhaima har sunyi bacci Sbd gajiyar biki.
Bedroom ɗinsu ya shiga.
Bed Al'amin ya fara zama ya tofa masa addu'a, ya sumbaci kumatunsa ya gyara masa kwanciya ya rufa masa quilt har ƙirjinsa Sbd yadda Ac'n ta ɗumame ɗakin.

Bed ɗin Suhaima ya koma ya zauna ya tofa mata addu'a, ya sumbaci goshinta ya rufeta itama ya kashe fitilun ya kunna masu ta gefen Bed ɗin Suhaima ya fito ya rufe masu ƙofar.
Bathroom ya shiga ya ɗauro alwala ya fito ya kunna Ac'n ƙasa² ya kashe fitilun ɗakin ya kunna ta gefen Bed ɗin yayi bismillah ya haye katafaren Bed ɗinsa yaja Duvet ya rufe iya ƙugunsa, ya lumshe idanunsa anutse yana karanto addu'o'in kwanciya bacci yana tofawa cikin tafin hannunsa, yana idarwa ya shafa jikinsa.
Ko mintina goma baiba da kwanciya bacci mai daɗi da nutsuwa ya ɗauke shi, Sbd agajiye yake.

Da ace za'a samu mata masu irin halin Zarah da mu mata masu jin zafin halin Zarah, damun haɗu muyi masu Allah wadai-wadai Aradu.😒
[28/03 16:05] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

_Masoyan JUHAINAH Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kadan-kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books Ɗina, A Channel Ɗin. Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku._

*Page 45*

Lokacin da ya ajiye Hanifah tana shiga ciki ko Ankon bikin bata cire ba, ta zauna parlour ta kira Ummah tana ɗauka Hanifah tace.

"Umma! Wai ya ake ciki zancen Hairat ɗin nan, naji shiru? Ko Malam bai duba miki lamarin ba? In ya gaza a nemi wasu malaman mana"

Ummah tace.
"Hanifah kinga yadda pictures ɗin da kika min a iPhone ɗinki, gaskiya sunyi kyau?

Ai Wlh ya duba yace babu soyayya tsakanin su, mijinki baya sonta ƙawarsa ce tun bai sanki ba yake tare da ita, kinga kuwa da yana sonta bazai aureki ba, shiyasa ma nabar batunta.
Yarinya ki kama mijinki da hannu biyu, akwai ƴan wawa rututu a waje"

Hanifah ta sauke ajiyar zuciya tace.

"Alhamdoulillah! Ni daman nasan Nasir nice ruhinsa babu wata shegiya Wlh.
Ai Ummah ina gaya maki Nasir nawa ne ni ɗaya.

Ai ko MAAH tana baƙin cikin son da taga yana min ne, haihuwa ba nufin Allah bane.
Ummah tace.

"Ai kuwa baƙin ciki ya kashesu ki kame kurwarsa mana."
Hanifah ta ƙyalƙyale da dariya tace.

"Na rantse da ALLAH Ummah ke muguntarki yawa ne da ita.

Kenan haka kika wa Babanmu? Nasir bana iya kame kurwarsa ina sonsa dayawa bana son na dinga juya shi, kamar waina, kuma baya kamuwar ma, na faɗa maki gaskiya, bansan wace irin kariya bace a jikinsa.
Wannan MAAH muguwar dattijuwa ce, bata zama akan ƴaƴanta bata fiye bacci ba.
Chapter 86 · 0% Book details