Sashe 40
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yah Boss
Gaban Juhainah ya duƙa yana kamota ya ɗagota cikin tsananin tausayin halin da take ciki, ya riƙeta a jikinsa yana buga bayanta a hankali ya ma Gaza yin magana, saboda jin jikinta zafi rau alamar akwai zazzaɓi mai ƙarfi a cikin jikinta.
Wani irin yinƙurin take yi, babu komai acikin nata sai ruwan juice da tayi ta sha ɗazun, saboda ta gaza sauka taci abincin.
Daƙyar aman ya tsaya ta kwantar da kanta saman murɗaɗɗan damtsen hannunsa, tana maida numfashi, idanunta sunyi jajir, sai damƙe damtsen hannunsa take tana nishin zazzaɓin.
Yah Boss ya ɗago kanta daga damtsen hannunsa yana riƙeta da hannunsa yana goge mata bakinta da tafin hannunsa, ya shafa goshinta da ya kumbura, jini na fita kaɗan².
Handkerchief da baya rabuwa da shi, ajikinsa ya zaro fari ƙal yana ƙamshinsa, ya tallafe fuskarta ya ɗaure mata goshin.
A hankali ya furta.
"Bilkisu! Tun yaushe kike zazzaɓi baki faɗa min ba? Me yasa dole sai kin sauka zakiyi aman bakiyi shi a saman bed ɗin?"
Dara-daran kyawawan idanunta da suka nuna tsantsar ciwon da take, ta buɗe a hankali sunyi jajir, ta kalleshi cikin rauni da abazar ciwo a hankali ta fara motsa laɓɓanta masu kauri zatayi magana.
A hankali ya furta.
"Ok... Ok alright nayi haƙurin basai kin ba kanki wahala ba, karki sake hakan kalli kin jiwa kanki ciwo a goshi gun sauka kiyi aman, miye damuwa idan kunyi akan bed ɗin? Inace wanke kayan shimfiɗar kawai za'a yi?"
Hawaye ta fara tana kallonsa ta lumshe idanunta.
A hankali yana kallonta ya furta.
"Mi kike wa kukan kuma? Akwai damuwa ne bayan zazzaɓi Juhainah?"
Ya ƙarasa maganar
Yana kwantar da ita akan bed ɗin, ya lulluɓeta da Duvet, ganin tana rawar sanyi.
Jin tattausan hannunta yayi cikin nasa ta riƙe gam tana shasheƙar kuka.
A hankali ya furta.
"Oh My God! Bilkisu! Minene? Goshinki yana zafi sosai ko?"
Idanunta a lumshe tana girgiza kanta.
Ranƙwafowa yayi cikin nutsuwarsa a hankali ya ɗora hannunsa saman goshin ya ɗan hura mata isar bakinsa akan handkerchief ɗin da ya ƙulle goshin.
Ƙasa² ya furta.
"Ok alright naji ba goshin bane toh zazzaɓin ne?"
Shima kai ta girgiza tana sake ƙamƙame tafin hannunsa.
Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya ƙura mata, yana furzar da isar bakinsa waje, a hankali cikin harshen fulatanci ya furta.
"Ok matsalan auren dana matsa ki auri Jamal?"
A hankali ta ƙara sakin kukan tana buɗe jajayen laɓɓanta daƙyar take magana, tace.
"Yah Sadeeq karkayi auren don Allah, karka aureta don Allah ka taɓa saitin zuciyata kaji Bugu take da ƙarfi, ni bana son kayi auren, kuma Babie Suhaima ma bata so..."
Gani yayi a wannan lokacin ko tsawar ya mata tayi nisa a rikincin ƙin auren nasa, Suhaima na zuwa taji abinda ya saka Juhainah ciwo akwai damuwa sosai itama tana iya kwanciya ciwon shi kenan su haɗu su ɗaga masa hankali gaba ɗaya.
A hankali ya furta.
"Ok alright bari kukan bakida lafiya kanki zaiyi ciwo, karki ɗaga hankalin ki Bilkisu babu damuwa cikin wannan auren, ki cireta a ranki, kinaga ko gun ɗaura auren naƙi zuwa ma, ke yanzu saboda auren ne kika neman kashe kanki a banza?"
Idanunta ta buɗe tana kallonsa ta ɗaga masa kanta a shagwaɓe alamar Eh.
Dogon hancinta ya kamo yaja yana kame fuska sosai ya furta.
"Daga Yau kar naji kar na gani, karma ki bari Babies su gane Ok?"
Kai ta ɗaga a shagwaɓe tana kallonsa sai taji zazzaɓin na ragewa, a hankali daƙyar a shagwaɓe tace.
"Karka kulata Yah Sadeeq, kuma karka mata abin nan da kake yi wa Aunty Khadija..."
Bakinta ya buge da sauri, fuskarsa babu wasa ya furta.
"Uwar me kika taɓa ganin nayiwa ita Khadijah ɗin dan ƙaniyarki?"
Idanunta ta rufe tana girgiza kanta tace.
"Babu kayi haƙuri ina nufin yadda kake sakarwa Aunty Khadija fuska kuna hira harda murmushi, ita karka mata"
Tsaki Yaja yana murɗe kunnenta ya furta.
"Juhainah! Karki sake haɗa waccan abar da Matata"
Rawar sanyi ta fara yana ganin haka ya miƙe, yaja Duvet ɗin ya rufe mata fuskarta.
Remote ya ɗauko ya kashe Ac'n yaje ya zauna akan Sofa.
Number Dr Majid ya kira.
Cikin Sa'a ya fito daga emergency room ya shigo ofishinsa ya iske wayan na ringing.
Ganin Yah Boss ne ya ɗauki wayan yana picking call ɗin yana amsa Sallama.
A nutse ya amsa yana faɗin.
"Dr Majid Please kazo ka da duk abinda ya dace, Bilkisu batada lafiya zazzaɓi da amai yake damunta"
Dr Majid ya amsa da.
"Yallaɓai afuwan bari na turo wife Dr Nafisa ta dubata, akwai ƴan emergency dayawa yanzu wanda nine zan duba su."
Yah Boss a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Ok tazo yanzu thank you"
Ya ƙarasa maganar yana katse kiran.
Number Amina ya kira bugu ɗaya ta ɗaga da sallama ya amsa a nutse yana faɗin.
"Amina! Kizo bedroom ɗin su Suhaima ki gyara gun da Bilkisu tai amai"
Yana gama faɗin haka ya katse kiran, ya miƙe tsaye yana kallonta bata buɗe rufewar da ya mata ba.
Kansa ya kauda ya fara tafiya yana faɗin.
"Sauran ki kunna Ac, Kafin na dawo"
Ya ƙarasa maganar yana buɗe ƙofar bedroom ɗin ya fito parlour kai tsaye ya wuce saboda yaje ya buɗewa Amina ƙofar tunda ba ɓangaren take ba.
Yana saukowa su Sumayya danna doorbell.
Zatonsa Amina ce, a nuste ya isa ya buɗe ƙofar.
Aunty Sumy da Hanifah tsaye.
Hanifah ta rusuna tana faɗin.
"Yaya Barka da yamma ina wuni"
A nutse ya amsa yana kallon Sumy.
Cikin fara'arta ta riƙe hannunsa tana faɗin.
"Ango kasha ƙamshi, Allah yaya Sadeeq kayi kyau yau sosai"
Hararenta yayi yana jan hannunta a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Wuce idan kina wucewa zan fasa maki baki idan kika kuma kirana Ango..."
Dariya tayi tana faɗin.
"Tuba nake na bari amma ba'a sauyawa tuwo sunansa"
Hannunta da yake cikin nasa ya mille da ƙarfi sai da ta saki ɗan ƙara.
Zama tayi a lafiyayyar Royal Turkish Chairs tana faɗin.
"Washhh! Allah! My brother ina Autar Maah?"
Jin ƙaran danna doorbell ya nufi ƙofar yana faɗin.
"Tana Stairs bata da lafiya, Dr Nafisa na hanyar zuwa dubata, zan fita parlour baƙi inada baƙi sun kusa 1 hour na jira Dr tazo ne, tunda kina nan natafi."
Ya ƙarasa maganar cikin gajiya da surutu yasa kai saboda baya son wata magana kuma yanzun, ga baƙi na jiransa dole suma sai ya tanka masu.
Kiran Jamilu yayi yana ɗauka a nutse ya furta.
"An kaiwa baƙin duk abinda ya dace?"
Jamilu ya amsa da.
"Eh Yallaɓai tun yaushe"
Katse kiran yayi.
Yana buɗe ƙofar Surayya da Amina na ƙoƙarin danna doorbell kamar kusan tare suka iso.
Surayya ta gaishesa cikin girmamawa.
Ya amsa ba tare da ya kalleta ba.
A hankali tace.
"Brother tare muke da yaya Jamal, yana kiran Juhainah baya samunta"
Yah Boss da har yayi gaba ya tsaya a hankali ya furta.
"Kuma bata da lafiya, amma zata buɗe wayan nata, kije ki faɗa masa"
Ya ƙarasa maganar yana tafiya saboda ya ɓatawa baƙin lokaci dayawa.
Surayya ta koma gun Jamal yana tsaye fuska shafe da toka.
Surayya tace.
"Yaya Jamal! Batada lafiya likitar da zata dubata tana hanya, yayanta yace kana iya tafiya zata buɗe wayan anjima bari natura maka number ta message sai ka kirata"
Baki ya taɓe ya shiga motarsa yana faɗin.
"Allah ya yaye mata"
Surayya ta juyawa tana amsa da.
"Ameen toh mai baƙin halin asara, mutum babu cikekken imani, ko ya nuna alamar tausayi..."
Aunty Sumy tace.
"Hanifah! Muje muga halin da take ciki, abu baiyi daɗi ba Sam wlh, Maah na can na jiran Autarta ashe ba lafiya"
Hanifah tace.
"Allah dai yasa idan Dr Nafisa tazo ta dubata ta samu sauƙi sai mutafi da ita"
Aunty Sumy ta amsa da.
"Ameen ya Allah"
Amina ta iso tana gaishesu Aunty Sumy ta amsa a tare suka nufi Stairs.
Tana kwance yadda Yah Boss ya kwantar da ita bata motsa ba, dukkan ta lulluɓe take cikin Duvet.
Aunty Sumy suka shigo parlour tana kallon ko ina fes sai ƙamshi suka nufi bedroom tana faɗin.
"Hanifah! Inaga fa Suhaima batada masaniyar wannan aure, Allah yasa kar tai mana daru"
Hanifah tace.
"Wlh kuwa Aunty Sumy Amin Ya Allah, Allah yasa uwa ta gari suka samu."
Aunty Sumy ta amsa da.
"Ameen"
Suna shiga Aunty Sumy ta nufi bed ɗin tana faɗin.
"Hajjah Mama babu lafiya haka a rufe ɗaki ba Ac, a lallai Uwarmu ba lafiya"
Ta ƙarasa maganar tana isa bed ɗin ta zauna tana janye Duvet ɗin tana sanya hannayenta ta kamo Juhainah tana faɗin.
"Innalillahi Baby zazzaɓin ne haka? Me ya fasa maki kai?"
Ta ƙarasa maganar tana rungume ƙanwarta a jikinta.
Juhainah ta fashe da kuka tana ƙamƙame Aunty Sumy, cikin kukan take faɗin.
"Aunty Sumy ki kaini gun Maah bana son zama gidan Yah Boss baya ƙaunata baya sona so yake na mutu..."
Aunty Sumy ko ɗar bataji ba saboda tasan shirmen Juhainah.
Bayanta ta shafa a hankali tana faɗin.
"Babyn Maah da Papa da Yah Sadeeq, me yayan namu yayi maki haka? Yi shiru kinga bakida lafiya jikinki zafi rau, me ya fasa maki goshi?"
Rage kukan tayi tana faɗin.
"Wajan na sauka nayi amai na faɗo, na buge goshi, Yah Boss ya ɗaure min"
Aunty Sumy tana sake rungumeta tana gyara mata ɗaurin goshin tace.
"Ayyah! Sannu Babynmu, Hajiya Mama akwaiki rigima Yah Sadeeq da baya sonki zai damu dake haka ne?"
Baki ta Turo gaba tana faɗin.
"Aunty Sumy Ni dai ki tashi muje gun Maah kewarta nake, ni bana son Yah Boss yayi aure matar babu wani aji wlh..."
Da sauri Aunty Sumy ta rufe mata baki Sbd ita fa ko miye bata son magana ta wuce iya tsakanin su ga Amina ga Hanifah bazata so wata magana ta fita ba.
A hankali cikin lallashi tace.
"Ke fa idan baki da lafiya sai shirme, kwanta kafin Dr Nafisa tazo"