Sashe 101
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali yace.
"Yes ke zaki haifa kin shirya na faɗa maki yadda za'ayi ko gobe idan kina so, za'a fara sai ki jira idan nazo Babyn kawai zan baki Twins ma"
Surayya tace.
"Allah Yah Nasir ban ganeba"
A hankali yace.
"Kizo muyi auren kwangila na shekara ɗaya, da zaran kin haifa min Ɗa ko Ƴa sai na sake ki, ki bani ɗana, na bawa matata Hanifah"
Surayya tace.
"Tabdijam! A'a ban yarda ba, ramuwa zakayi ko?"
A hankali yace.
"A'a da ramuwa zanyi Bazan faɗa maki ba, sai dai ki gani a aikace"
Baki ta turo gaba tace.
"Toh idan ka sake Ni wa zai aura? Nifa da hankali na, kawai ka fito a mutum kace min kana sona muyi aure zan iya Manage na aureka ko bana sonka"
Nasir ya ƙyalƙyale da dariya abinda bata taɓa ganiba ko jini ba.
A hankali yace.
"Toh shi kenan kije ki auri wanda kike so bana auren wacce bata sona, idan ban kwangila bace, ai shi yasa nace muyi auren kwangila tunda bana sonki bakya sona.
Amma zamu nuna iyayyenmu muna so.
Idan kin shirya gobe zan masu magana a shirya zuwa gidan ku.
Surayya tayi shiru tana wani nazari sai tayi dariya tace.
"Na amince ai iya shekara ɗaya kace ko?"
Nasir yace.
"Eh Surayya, kin tabbata zaki haifa min Babyn?"
Surayya tace.
"Allah ne mai yi bani ba Yah Nasir"
Murmushi yayi yace.
"Shi kenan Bazan sake kiran ki ba sai kin zama matata bye"
Surayya zatayi magana ya katse kiran.
Surayya ta ajiye wayar ta miƙe tana rawa zuciyarta fara Tass dan ta gama mutuwa a soyayyar Nasir da daɗewa tunda suka fara samun matsalar nan, juriya take, amma yanzu dama ta samu bazata bari ta wuceta ba, sai dai Aunty Hanifah tace taci amanar ta, har mamakin son da tayiwa Yah Boss da ya dawo gun Nasir take, dan ko bacci take ta kama mafarkin sa kenan....
★
Yah Boss
Yazo wuce wa dai-dai ƙofar ɗakin Khairat yaji baƙuwar muyar yarinya tana zuba Surutu Khairat na faɗa mata.
"Dan Allah Dijah kiyi shiru, wai ba kin gama karatun ba? TOH ki tashi ki kwanta"
Yah Boss ya taɓe bakinsa, ya gane yarinyar da Juhainah ta kwaso daga gidan su Jamal ce.
Al'amin har ya gama ɗaukan karatunsa ya kwanta.
Suhaima ce zaune saman Bed ɗinta ta barbaje littattafai.
A hankali ya buɗe ƙofar ya shigo bakinsa da sallama.
Suhaima ta zaro lumsassun idanunta tana faɗin.
"My Dadd Surprise us! Oh wow, how wonderful my dad is back! Welcome, my Dadd."
Ta ƙarasa maganar cikin farin ciki, ta saukowa ta faɗa jikinsa tana murna.
Sama ya ɗaga kamar Baby yana juyi da ita.
Dariya take ta riƙe shi, tana faɗin.
"My Dadd kaina yake juyawa"
Murmushi yayi
Kiss ya manna mata a goshinta ya ajiyeta.
Bed ɗin Al'amin ya isa ya zauna ya kamosa ya rungume yana sumbatar shi.
Al'amin ya buɗe idanunsa.
Ihun farin ciki ya saki yana ƙamƙame Dadd ɗinsa.
Yah Boss yayi murmushi a hankali ya furta.
"My Babie Amiin ya kake?"
Al'amin ya sumbaci kumatun Yah Boss yace.
"Ina lafiya my Dadd sannu da zuwa. My Dadd ka kawo mana tsaraba?"
Yah Boss ya amsa da.
"Yes suna can gida"
Murna sosai sukayi Amiin da Suhaima suka rungume mahaifinsu.
Books ɗin makaranta ya amsa yana duba masu, suna hira har ƙarfe 11 na dare yana gun yayansa, a jikinsa sukayi bacci.
Lumsassun idanunsa ya kafe ƴaƴan nasa.
Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin.
"My Khadijah! Allah ya jadadda rahma a gareki."
Addu'a ya masu ya kwantar dasu kowa saman bed dinsa.
Ya tattare Books ɗin ya rage masu hasken ɗakin ya fito ya rufe masu ƙofar.
Lokacin da ya sauko Papa da Maah ba kowa har sun kwanta.
Tafiyarsa yayi bai ma yarda ya nemi Juhainah ba, dan zai barta har ta huce.
★
Washegari ta kama Monday gidan Maah ba kowa duk sun tafi school, har Juhainah.
A ranan aka kawo akwatin auren Khairat.
Yau auren ya rage kwana biyar, sai shiri ake yi.
Nasir bayan sunyi magana da Surayya da kwana biyu, ya kira Yah Boss ya sanar da shi yana son Surayya sunyi magana aje nema masa aurenta, yana son ayi harda ɗaurin aure.
Yah Boss sai da ya tabbatar ba ramuwa yake son yi ba ya amince da maganar.
Bayan ya dawo daga wajan aiki da dare ya shiryar ya tafi dan faɗawa su Maah.
Ƴan gidan duka suna kan dinning room Banda Juhainah, dan bata wani cin abinci yanzu sai kayan kwaɗayi.
Juhainah zaune yanzu ma jeans ne ajikinta mai shegen kyau, sai riga ƙarama fara Tass ta mata kyau ta fito da cikin nata.
Anyi ruwa garin daɗi yake mata, ta kashe Ac'n parlour ta buɗe Windows iska mai daɗi da ƙamshin ruwa tana shigowa.
Gashinta sakinsa tayi yau sai yawo yake har wucin tsakiyar bayanta.
Bakinta sai sheƙi yake tasha lipstick.
Plate ne a hannunta tana cin haɗin salad, Cup a gefe na lemon tsami da sugar.
Anutse ya shigo parlour da sallama.
Dam taji ƙirjinta Ya buga, har ɗan cikinta yana motsa wa.
Jurewa tayi tana amsa sallamar ba tare da
ta kalleshi ba, ta tsakuro salad ɗin takai bakinta tana taunawa, ta kame fuska, dan ya ƙara laifinsa tunda ya dawo yau kwana 6 bata sake ganinsa ba.
Anutse ya iso parlour, idanunsa a kanta.
Zama yayi kusanta, ya ɗan duƙo da fuskarsa dab da tata, ya busa mata iskar bakinsa a kofofin hancinta.
A hankali ya ɗore yatsunsa biyu saman laɓɓanta masu kauri, ya goge mata abun tomate da ya manne ƙasan laɓɓanta.
Kallonnsa tayi fuska kame tana ƙanƙance idanunta.
Abun dariya ya ma ya basa, ya dai kame fuska ne kawai.
Ido ɗaya ya kashe mata.
Ya janye idanunsa daga idanunta.
A hankali ya furta.
"I'm just joking, my sister."
Banza ta masa.
Hannayensa ya saka ya kamo gashinta ya fara tattara shi gu ɗaya, ya fara tufƙe mata.
Yana sakin gashin ta miƙe tsaye da niyar tafiya ya kamo hannunta ya zaunar da ita kusansa, ya amshi plate ya ɗauki salad yakai bakinta.
Kanta ta kawar.
Bakinsa ya kai salad ɗin ya tauna.
Kallonnsa tayi tana ɓata fuska.
Ɗan cikinta ya fara motsi ta zaro idanunta tana dafe cikin nata.
Kallonta yayi a hankali ya furta.
"Me ke damunki?"
Harara iska tayi tana turo bakinta ta miƙe tsaye ta ɗauki Cup ɗin lemon tsami ta nufi bedroom ɗin Maah.
Bai dakatar da ita ba.
Ajiye plate ɗin yayi ya ciro Wayarta da ya kawo mata ya saka mata charge ta cika ya saka mata data, ya loda mata katin waya na kuɗi dayawa.
Miƙewa yayi ya bita.
Tana zaune a Sofa ya shigo bedroom ɗin.
Kanta ta ɗauke, ta cika tayi fam.
Gabanta ya tsugunna,ya kamo hannunta ya saka mata wayar, a hankali ya furta.
"Good night"
Miƙewa yayi ya fice anutse cikin nutsuwarsa.
Da kallo ta bisa tana harara ta lumshe idanunta tafiyarsa ma gwanin kyau da burgewa, ƙaunarsa take kamar zata mutu takeji, amma ta fita sabgarsa shima ya shafa mata lafiya take so, ko zata iya dangana.
Kallon iPhone ɗinta tayi ta kaita bakinta ta sumbata, ƙamshinsa ya baibaye wayan.
Ajiyar zuciya ta sauke ta miƙe ta hanye Bed.
Zaune yayi a parlour yana amsa waya cikin kamewarsa Anutse a harshen Ingilishi, har su Maah suka ƙare suka fito.
Suhaima da Al'amin suka zauna kusan Dadd ɗinsu Khairat ta gaishe sa.
Dijeh ta kuwa kallo ɗaya ta masa taji tsoronsa ganin yadda ya kame fuska ta gaishesa bataji ya amsa ba, gaza zama tayi ta gudu ɗakin Maah gun Juhainah, tana bata labarin Balarabe baya amsa gaisuwarta.
Juhainah tace tayi haƙuri taci gaba babba girmansa ake basa.
Yah Boss yace Khairat da su Suhaima su tafi Stairs hira zaiyi dasu Maah.
Suna tafiya ya fuskanci Papa da Maah a hankali ya basu labarin Nasir da Surayya akan suna soyayya yana son aje nema masa aurenta idan da hali a ɗaura lokacin da ALLAH ya kawo sa sai ayi bikin.
Maah tace.
"Ma sha Allahu Alhamdoulillah! Abbah ka iya kawo labari, ai kuwa za'ayi in sha Allahu, amma shi da yace an ƙara masu lokacin wata 9 ko 10 zasuyi?"
Yah Boss ya amsa da.
"Eh wannan ai ba damuwa bane"
Papa yace.
"Toh Matarsa ta sani ne?"
Maah tace.
"A'a abari tsakaninsu ya faɗa mata, Harɗo gobe aje gaskiya idan yaso sai a saka maku ranan da ya dace aje ɗaurin auren"
Papa yace.
"Ok shi kenan Allah ya kaimu zan kira Abdallah ɗin gobe da safe.
Ya turo kuɗin sadakin?"
Yah Boss yayi ƙaramin murmushi a hankali ya furta.
"Ba yanada Ni ba? Ko yana nan nine in sha Allahu."
Maah ta dinga sakawa Yah Boss albarka.
Ya daɗe kafin ya masu sallama ya tafi.
Washegari da safe wajan ƙarfe goma Papa ya kira Abbansu Surayya bayan sun gaisa ya sanar da shi zasu zo neman aure gidansa, Surayya da ɗansa Nasir Soja sun daidaita kansu.
ALLAH Sarki Abba farin ciki yayi yace babu damuwa sai sun zo.
Suna gamawa wayar Abba ya kira Surayya ya tambaye ta tace Eh tana son Nasir yana sonta.
Mamy tayi farin ciki Sosai.
Da yamma kuwa da Papa da Kawu Nasiru da Yah Boss suka tafi gidansu Surayya neman aure, An basu aka saka ranan juma'a za'ayi ɗaurin auren a masallacin juma'a da yake bayan gidansu Surayya.
Juhainah da gaske ta ɗauki zafi da Yah Boss.
Dan ko kiranta yayi bata ɗauka messages bata masa reply.
Hakan ya saka ya tattara ya watsar dan ya bata dama har ta huce, Sbd yaga kamar yana ƙara zuga ta ne.
Juhainah koda taji Nasir zai auri Surayyatah harda rawa tayi dan murna.
Ranan juma'a bayan tashin sallar juma'a dubban mutane da suke sallarta juma'a a masallacin suka shaida ɗaurin aure tsakanin Abdulnasir Yakubu Abubakar Janfar, da Surayya Abdallah akan sadaki mai daraja.
Nasir ana gama ɗaurin auren labari yazo masa, sai dai bai samu damar kiran Surayya ba network ɗinsu ya ɗauke, ana daɗewa kafin ya dawo, yaji takaicin hakan bai san ranan da zai kuma samun Surayya ba a waya.
Anata shirin auren Khairat wanda ya faɗo ranan Lahadi. Juhainah ciki ya yi wata biyar harda kwanaki.