← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 113

Sashe 41

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juhainah zata sake magana tana hawaye Aunty Sumy ta maka mata harara.
Baki ta turo tana faɗin.
"Ni daman an tsaneni ai baza abarni na faɗi damuwata..."
Bakin Aunty Sumy ta rufe tana faɗin.
"Hanifah buɗe handbag na ki ban wayata na kira Yah Sadeeq tunda Ni Ban isa nace tayi shiru tayi ba..."
Ƙamƙame Aunty Sumy tayi tana faɗin.
"Nayi shirun karki kirasa ransa zai ɓaci, nayi shirun Aunty"
Aunty Sumy tace.
"Ok ni ran nawa ya ɓaci ko, Juhainah Allah ya shirya"

Hanifah dariya tayi tana faɗin.
"Autar Maah zata saka ka nishaɗi ko baka shirya ba, Allah ya baki lafiya"

Amina ma murmushi take tana mopping gun ta gyara ko ina tsaf ta kunna turaren wuta ta fice tana faɗin.
"Autah Allah ya ƙara sauƙi Amin"
Aunty Sumy tace.
"Au kinga na manta Surayya na downstairs fa, Hanifah je ki kirata tunda ƙawarta ba lafiya."
Hanifah ta amsa da.
"Toh Aunty"
Ta amsa tana tafiya.

Dr Nafisa bata wuce minti talatin ba ta iso gidan.

Surayya na zaune kusan Juhainah tana riƙe da hannunta, Amina ta shigo da ita da sallama.
Aunty Sumy suka amsa tana faɗin.
"Dr Nafisa Barka da zuwa"

Nafisa ta amsa tana faɗin.
"Aunty Sumy ina yini kwana biyu?"
Aunty Sumy tace.
"Alhamdoulillah! Ai Yah Sadeeq kwana biyu Alhamdoulillah babu yawan mura, Mun bar yawan zuwa, yana can gida ma na baraso baiga fitowar mu ba"

Dr Nafisa tace.
"Alhamdoulillah haka ake so ai, Juhainah! Meke damunta yau kuma? Bari mu gani"

Ta ƙarasa maganar tana isowa ta ajiye akwatin kayan ganin ta taɓa jikin akwai zafi.
Gwaje-gwaje ta shiga mata.
Allura take ƙoƙarin yi mata amma taƙi fur sai kuka take, sbd ta tsani allura da shan magani matuƙar tana hayyacinta, ba tare da Yah Boss yana kusa ba.
Aunty Sumy ta riƙeta tana faɗin.
"Don Allah Autah ki tsaya wai kasheki zatayi"
Juhainah taƙi sai motsi take yi.
Surayya tace.
"Please my sister J ki tsaya ba zafi"
Harara ta makawa Surayya tace.
"Ke ayi miki mana Wayyo Maah ki temakeni"

Aunty Sumy ta ɗauki jakarta ta ciro wayanta ta kira Yah Boss.
Lokacin yana tsaka da jawabi wa baƙin nasa kiran ya shigo, kasancewar wayoyin duk a gunsa yau tunda Fu'adh baya nan, kasancewar da special number ta kirasa.
Ganin Sumy ce ya yi picking call ɗin da gilashin idanunsa.

Kukan Juhainah yaji yana tashi tana kiran Maah, ita bata son allura.
Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya ɗan lumshe.

Baƙinsa ya kalla cikin harshen turanci hankali ya furta.

"I have something important to say, be patient, I'll be back soon"

Ya ƙarasa maganar yana taku a nitse ya nufi ɗan ƙaramin tsararren parlour da yake cikin babban parlour baƙin, a hankali ya furta
"Sumy! Ki saka mata wayan a kunnenta"

Aunty Sumy ta amsa da.
"Toh"
Ta sanya mata wayar a kunnenta"
A hankali cikin kamewarsa murya a tausashe ya furta.

Hey Juhainah, calm down and get yourself an injection. Do you want me to come?"

Juhainah tunda taji Yah Boss akan layi tayi shiru, tana hawaye, a hankali cike da shagwaɓa tace.
"Yeah my brother"

A hankali ya furta.
"Idan nazo me zan miki?"

Ashagwaɓe tace.
"Looking at you eases my fever, my brother"

Bakin window ya tsaya yana ɗan janye Glass a hankali ya furta

"No! you're not telling the truth."

Ɗan ƙaramin kuka ta sakar masa na zallar shagwaɓa tace.
"God my brother, I am truly in my heart.
Please kazo kaji."
Yah Boss murmushi ya ɗan suɓuce masa a hankali can ƙasa² ya furta.

"No! Ban zuwa tunda kuka kike yi"

Cikin sauri ta haɗiye kukan tana cire handkerchief ɗin da ya ɗaure mata goshin ta goge hawayen, a hankali tace.
"My brother na daina kukan na goge hawayen, kazo ka hana Aunty Nafisa zata min allura"

A hankali ya furta.
"Ban zuwa ki tsaya ta miki alluran idan ba haka ba, Wlh ina zuwa marinki zanyi na ƙara miki ciwon, tunda garma kike son min"
A hankali tace.
"Tom zan tsaya yaya ka kawo min abu mai daɗi zanci"

A hankali ya furta.
"Ok zan kawo maki, ki daure kiyi wanka, zaki fi jin ƙarfin jikinki"

Yana ƙarasa maganar yana katse wayan.

Dr Nafisa Aunty Sumy Hanifah Surayya duk sun saki baki suna kallonta har lokacin da ta turo jajayen laɓɓanta masu kauri tana faɗin.
"Ya katse min wayan, Aunty Nafisa kiyi min à hankali don Allah"

Dr Nafisa tayi murmushi tace.
"Ok shalelen yayanmu Commissioner of police"
Aunty Sumy ta riƙeta tana faɗin.
"Yi sauri ki mata batada Tabbas"

Ai kuwa ana tsira mata allura ta fasa ihu tana son ƙwace wa daga hannun Aunty Sumy.
Hanifah da Surayya suna mata dariya.
Nafisa tace.
"Meke damunki Juhainah?
Sbd zazzaɓin ki akwai tarin fargaba aciki, da yunwa yau ba'ayi ciye² ba ko? Ga wannan maganin zai ƙara sauke zazzaɓin in sha Allahu.
Ta ƙarasa maganar tana beƙawa Aunty Sumy maganin.
Tayi wa goshin Juhainah dressing ta masu sallama ta tafi, Aunty Sumy ta rakata har downstairs.
Tana dawowa ta ɓallo maganin ta bata daƙyar ta sha tana hawaye.
Aunty Sumy ta haɗa mata ruwan zafi ta kamata suka shiga ta fito ta barta....

Jigawa
Kasancewar motocin masu gudune sabbi cikin ikon Allah kafin yamma tayi sosai sun iso Jigawa, yayin da suka iske ƙofar gidansu Zarah cike da jama'a ma sha Allahu.
Tarba suka samu ta musamman, misalin ƙarfe biyar na yamma aka ɗaura auren Abubakar Yakubu Abubakar Janfar da Fatima Zahra Zakaria Babagana akan Sadaki Naira Miliyan ɗaya.
Mai shela da lasifika yana ta famar shelar an ɗaura auren Abubakar da Fatima Zahra.
A yau idan kaga ƙofar gidan su Zarah yadda ya ɗauki jama'a abin ba'a cewa komai, sai son barka.
Su Hajjah Bilkisu ƙirjin biki Umar amarya Uwar Ango.

Zarah zaune ƙawayenta da ƴan uwanta na zagaye da ita sai guɗa suke, ita kuma tana sakin murmushin farin ciki yau itane matar Abubakar Janfar Tabbas ita ɗin uwarta ta haifeta da Sa'a.
Wani irin fitinannan ƙunshi aka mata ƙafa da hannayenta na asalin amare haka kitsonta ma Wow!
Hajiya Bilkisu ce ta shigo tana washe baki tace.
"Zarah kin gama shiri angwaye zaku wuce saboda sun ce kwanan hanya zakuyi"

Zarah kanta a ƙasa tace.
"Don Allah Mama ki rakani da kanki a matsayin ki na mahaifiyata ba suruka ba"
Hajiya Bilkisu tace.
"Inada niyar hakan surprise naso miki."
Zarah harda hawayen farin cikinta tasan zata samu kulawa gaban Hajiya Mama bazai mata cin fuska ba, gaban ƙannenta.
Ƙarfe 6 dai-dai motocin suka jero ɗauke da amarya Zarah da ƴan uwanta da ƙawarta ɗaya sai Hajiya Mama da ƙanwar mahaifin Zarah Laure.
Zarah na cikin motar Yah Boss wacce Fu'adh ya tafi da ita...

A can Yola Juhainah bayan tayi wankan ta lallaɓa ta rama Sallah, Amina ta kawo mata abinci bataci sosai ba, bacci ya ɗauketa saboda maganin da ta sha ba.
Ganin haka Aunty Sumy tace su sauka downstairs.
Yah Boss kuwa ƙarshe dai fita ta kamasa tare da baƙin nasa, bai dawo ba sai ƙarfe shidda saura, har lokacin Juhainah bata tashi ba.
Aunty Sumy da Hanifah Surayya suna parlour sunata hirasu sunacin kayan marmari.
A nuste ya shigo parlour bakinsa ɗauke da sallama.
Suka amsa yana kallon Aunty Sumy fuskarsa a kame ya furta.
"Ina Bilkisun?"
Aunty Sumy tana kai kai Apple bakinta tace.
"Yah Sadeeq bacci take kusan awa uku munata jira bata farka ba, ga Maah tana ta kirana Wlh, ga shi bataci wani abincin kirki ba, bacci ya kwasheta"

Ledar hannunsa ya ajiye akan Center table ɗin, a hankali cikin kamewarsa yana faɗin.
"Kuje kawai idan ta farka zan kawota, lokacin su Suhaima sunzo zamu zo gidan duka a can zamu kwana ma... "

Aunty Sumy ta zaro lumsassun fararen kyawawan idanunta irin nasa tana faɗin.
"Yah Sadeeq!"
Sai tayi shiru bata son wata magana sirri ba iya su ba.
Miƙe wa tayi tana bin bayansa.
A nuste yake taka Steps ɗin yana faɗin.
"Please Sumayya karki min wata magana yanzun kuma, ina buƙatar nutsuwa, kuje kuyi bikin tunda haka kuke so"
Sumy ta marairaice fuska tana binsa taƙi komawa batace komai ba dai.

Suhaima ce ta buɗe ƙofar ta shigo rataye da Bagschool ɗin, agajiye take shigarta tsaf cikin uniform, da ya mata kyau.
Al'amin ya jefar da Bagschool ɗinsa yana rugawa gun Hanifah yana faɗin.
"Oyoyo Aunty Hanifah"
Hannayenta ta ware masa ya faɗo kanta yana dariya.
Suhaima ta ƙaraso yau miskilancin akanta a hankali tace.
"Ina wuni Aunty Hanifah, Aunty Surry ina wuni."
Ta ƙarasa maganar ta juya tana nufar hanyar Stairs.
Surayya ta amsa tana goge hawaye a ɓoye, Allah ya sani tana son Yah Boss amma yafi ƙarfinta, zata so taga wannan mai sa'ar da ta auresa yau.

Hanifah tace.
"Babies yau ba rungumar Aunty Hanifah dan zakuyi sabuwar Momy"
Suhaima ta juyo tana ƙurawa Hanifah manyan kyawawan idanunta ta taɓe baki tace.
"Uncle Nasir zai ƙara aure ne?"
Da mamaki Hanifah take kallonta, dan Sam ta manta ɗazu Aunty Sumy tana faɗa mata Suhaima bata san Dadd ɗinta zai yi aure ba.

Hanifah tayi murmushi tana rungume Al'amin tace.
"Wani Nasir bawan Allah, tun yanzu Suhaima? Yaya Sadeeq ne yayi aure a Jigawa yau..."
[22/01 15:12] أم الأمين😘: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo
Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVELS. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

Masoyen Juhainah Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kaɗan-Kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books ɗina, A Channel ɗin.
Wanda Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku.💃🏻

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 23*

Ai Hanifah ta gwammace bata furta wannan kalmar daga bakinta ba.
Saboda kallon da Suhaima ta mata na tsanar ma wanda taji kalmar a bakinsa bare wanda ya aikata hakan.

Bagschool ɗin tayi jifa da ita, da ƙarfi tace.
"Da gaske aure ko wasa Aunty?"
Hanifah tsorata tayi da yanayin na Suhaima.
Cikin ƙaraji tace.
"Nace aure fa? Wa ya aura? Aunty Surayya da gaske Dadd ɗina yayi aure?"
Surayya ta tsorata sosai da Suhaima, sai taga kamar Yah Boss ne tsaye.
Da sauri Surayya tace.
"Haka naji Suhaima Banda tabbas."
Chapter 41 · 0% Book details