Sashe 8
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Page 5 Numfashin ta ne ya kusa ɗauke wa daga gangar jikinta gaba ɗaya, a lokacin da ta juya dan zuwa gun mahaifiyarta taji Yah Boss ɗin ne yazo, ko kuma tsoro ne ya sakata jin ƙamshinsa ya buwayi hancinta. Ido huɗu suka yi da shi yana tsaye cikin Uniform ɗin da take maida shi tamkar police ɗin Saudiyya, haka na ƙara saka mata tsoronsa. Gadan² ya nufota babu sassauci acikin al'amarin, saboda har ya gama mata gargadi da idanuwansa masu firgitata, akan karta kuskura ta gudu, ko tai masa kuka. iPhone ɗinta ya suɓuce ya faɗi, saboda yadda jikinta yake wani irin kyarma, ta shiga ƙololuwar tashin hankali, ko daga kallon da yake mata kaɗai ya isa tasan yau sai tanada tsawon kwana zata ga gobe. Idanunta ta rintse da ƙarfi tana haɗe jikinta gu ɗaya, dan bata isa ta gudun ba kamar yadda ya hanata da idanunsa masu dafi. Yana isa gunta ya ɗauketa da wani irin gigitaccen marin da ya saka taji kamar zata saki fitsari, bata dawo ba ya sake wanke ta da wani irin marin da ta zube ƙasa, jinta da ganinta na ɗauke wa na wuccin gadi. Ga shi babu damar ihu ko kuka, bata san lokacin da acikin zuciyarta ta fara karanto. "LA ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINA ZALIMIN" Sai faɗa take cikin zuciyarta bata san sau adadin da ta faɗa ba, kuma taƙi daina faɗa sai maimaici take tayi ko Allah ya taimake ta ba dan halinta ba, ya sassauta mata. Duƙo wa yayi ya damƙon hannunta ya miƙar da ita tsaye, ya kamo dogon gashinta yaja da ƙarfi. Cikin muryan da ta sake tsananta tsoronsa ya furta. "Open your eyes, you useless hypocrite." Cikin sauri ta buɗe dara² fararen idanunta da azaba ta saka su yin Ja. Cikin tsawa ya furta. "Look at me, let's talk, hypocrites." Da sauri jikinta na ɓari ta ɗago kyakkyawar fuskarta da kumatunta sukayi Ja sbd marin da ta sha, a hankali ta kalleshi tanajin kamar zata suma sbd tsoron idanunsa da shi ma baki ɗaya. Sai maimaita kalmar "LA ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINA ZALIMIN" Take ta maimaita wa a zuci, cikin ikon Allah Gashinta ya saki yana faɗin. "Bilkisu! What's bothering you?" Cikin matsanancin tsoronsa tana zubar da hawaye ta buɗe bakinta da babu damar kuka tace "Nothing now, I'm healed brother." Hannunta na hagun ya kamo cike da takaicin ganin false nails,da ta saka ya cire su yana zubar wa, cikin wata irin murya ya furta. "You are a hypocrite. Tell me the truth, what's bothering you? Do you really want to get married? Are you going to stay married? Don't you want to study? Idan kika bani amsa da ba dai-dai ba sai na kusa kashe ki wallahi. Kin maida kanki aniyar dole wannan shigar idan bana kusa ita ce kike yi kullum ko?" Juhainah ta shiga wani tashin hankali tana raba idanunta ga shi babu mai cetonta. Da sauri ta girgiza masa kai, tana saurin faɗin. "Kayi haƙuri bazan sake sakawa ba daga yau..." Bakinta ya buge sai da gefen bakinta ya fashe a take. Azaba takeji sosai ta dafe jajayen laɓɓan nata masu ɗan kauri, raɗaɗin yana shigarta ba damar kuka sai hawaye.Cikin wata irin murya ya furta. "Saki hannunki daga gun. Go change your clothes and come back." Ba shiri ta janye hannun nata daga bakinta, ta fara tafiya tana ɗingisawa saboda taji zafi a ƙafarta ta hagun faɗuwar da tayi saboda zafafan marin da ya mata. Kamar daga sama taji muryan Yah Umar da Fu'adh suna shigowa falon suna magana cikin kwanciyar hankali, saboda har lokacin basu ga abinda yake faruwa ba.Tana ƙoƙarin juyowa dan nufar hanyar da suke shigowa taji daddaɗar muryansa cikin wani irin fushi yana faɗin. "If you come back, I will be your hair, go do what I left, I am waiting for you." Jikinta na rawa ta cira ƙafarta ta nufi Stairs tana wani irin kuka ta toshe bakinta, tama rigada tasan gidansa zai kaita ya titseta sai ta faɗa masa auren take so bata son karatun. Tana amsawa sati bazata ƙara ba a gidansu zai aura mata duk wanda yaso, kuma ba yadda zatayi. Yah Umar da Fu'adh gilmawarta suka gani ta nufi hanyar Stairs. Suka maida idanunsu akan Yah Boss da ya duƙa ya ɗauki iphone ɗin Juhainah ya saka cikin aljihun rigar Uniform ɗinsa, ya zauna yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ya ɗaga wayansa ya amsa kiran wayarsa da ya shigo yanzun. Umar zaiyi magana Fu'adh ƙasa² yace. "Karka masa maganar Juhainah, kuyi magana wata daban. "Umar ya ɓoye dariyarasa ganin duk duniya Juhainah take sakawa Yah Boss ciwon kai, sai dai itama tana ji a jikinta. A hankali Umar yace. "OK ok Bass, bari naje na bada gaisuwa. "Umar ya ƙaraso ya zauna kusan yayan nasa da yake amsa waya cikin harshen turancin da ya gama zama akan harshen shi. Fu'adh yana ƙoƙarin zama Maah ta fito daga kitchen, riƙe da mug fuskarta cike da fara'a ta nufo gun Fu'adh tana faɗin. "Fu'adh ga Madaran. "Ya miƙe ya amsa cikin girmamawa yana faɗin. "Thank you Maah, da kanki kika dafa ko?" Murmushi tayi tana maida idanunta kan kyakkyawar fuskar ɗan nata, da ya kame yana amsa waya cikin nutsuwarsa, sam babu alamar fuskar da zaka tunkaresa da wata magana akan Juhainah. Cike da zallar ƙaunarsa tace. "Abbah da kasan halinsa Fu'adh matuƙar Madara ne sai ni zan dafa masa ko Jamilu tunda muka rasa Khadijah..." Da ƙarfi suka ga ya rintse idanunsa yana ciza lips ɗinsa wayan ma da yake ya dakata yana zare wayan daga kunnensa. Hakan ya saka Maah da sauri ta ƙarasa gunsa ta zauna tana buga bayansa tare cire hular Uniform tana shafa kansa a hankali cikin kwantar da murya tace. "Shi kenan Abbah ya isa, ka yawaita addu'a, kuma ai ta samu shahada gun haihuwa fa Abbah! Don Allah ka rage jin zafi idan an ambaci sunanta, Umar! ɗauko masa gorar ruwa mai sanyi yi sauri." Umar ya miƙe dan cika umarnin mahaifiyarsu. Shiru yayi a jikin mahaifiyar tasa yana sauke ajiyar zuciya. Fu'adh ya zare wayan da take hannunsa yakai kunnensa yana matsawa daga gun tare faɗin."Hello Sir yana ɗan uzuri ne bazai samu damar kammala wayan ba, amma zai maido kiran in sha Allahu da ya dawo normal." Yana gama faɗin haka ya katse kiran yana saka wayan cikin aljihunsa, ya dawo ya zauna. Juhainah tana hawa stairs ta shiga bedroom ɗinta, ta faɗa saman bed tana kecewa da wani irin kuka, harda shasheƙa. Duk duniya babu mai saka Juhainah kuka harda shasheƙa da hawaye bayan Yah Boss, saboda wani irin shegen taurin kai ne da ita, baka isa kaga kukanta ba komi zaka mata, sai dai idanunta su canza daga fari zuwa Ja, amma kuka kam Yah Boss kawai yake sakata shi. Sosai take kuka ta cusa kanta cikin pillow ta naɗe jikinta guri ɗaya ƙafarta na ciwo haka fuskarta na raɗaɗin marin da ya mata, har kanta ciwo yake saboda gashin da yaja mata. Zabura tayi cikin kukan saboda tuna abinda ya sakata yana can yana jiranta, ɓata lokacin zai sake sakawa ya mata wata azabar. Da rarrafe ta iso bakin bed ɗin ta zuro ƙafafuwanta ta sauko daƙyar saboda ƙafar na mata ciwo. Kayan jikinta ta cire baki ɗaya ta ɗaura towel tana ɗingisawa ta nufi bathroom. Ruwa mai zafi ta shiga tana hawaye. Bata jima ba ta fito ɗaure da towel, tana ƙamshin gel. Ƙatuwar wardrobe ɗinta ta buɗe ta kalli ɓangaren da manyan kayanta suke. Pink Turkish Abaya ta ciro sai kuma ta mayar tana jan tsaki ta ciro wata Dubai Abaya Brown colour mai masifar kyau da tsada wasu irin Stones farare akayi mata ado dasu, wanda suka fito da Abayar, kana kallonta kasan ba ƙananun ƙuɗaɗe bace. Ɗan mayafin ta ciro tana hawaye har yanzu dan bata taɓa sakata yaune zata fara sakawa ba, saboda Yah Boss ya kawo masu ita iri ɗaya ita da Aunt Khairat zuwansa Umarah azumin da ya wuce wata biyar baya. Jikinta ta goge ta ɗan shafa oil na jiki tana kallon bakinta inda ya fasa mata ya ɗan kumbura, idanunta masu wani irin kyau ta lumshe a gaban ƙaton madubin, hankali cikin muryan kuka ta furta. "Yah Boss me yasa duk azabar da kake min ban taɓa jin na tsaneka ba? That's why I want to be careful, Yah Boss, I want to be strong and overcome your fear. I hate you, dole sai na sakawa kaina tsanarka, ina baƙin cikin nonon da muka sha da kai, baka dace fitowa a jinina ba, saboda kakaf family's Janfar kai ɗaya ne mugu, daman kaine ka muuut..."Gaza ƙarasa kalamanta tayi tana sakin wani irin kuka tare da zama akan Stoll ɗin, tare da ƙanƙame jikinta cikin kuka take faɗin. "I hate you Yah Boss." Kusan minti uku tana kukan tana faɗin i hate you Yah Boss, kafin ta ciro tissue paper ta goge fuskrta da tayi Ja, idanunta masu kyau da haske suka fara kumbura. Juriyata ta dawo da ita ta ƙarasa shirya kanta, komi na jikinta Brown colour ta saka, ta fasa turarenta mai shegen ƙamshi, wanda ƙamshinsa ya isa ya sanar da kai tsadarsa. Kanta ta kalla a ƙaton haɗaɗɗan madubin nata taga wani irin kyau da tayi abunka da ramammiya Abayar nada ɗan faɗi dole ta rufe mata komai na jkinta ta yane fuskarta da ɗan ƙaramin mayafin Abayan, ta kalli Zara-zaran yatsun hannunta da ya cire mata false nails ɗin suke mata kyau a yatsun taja tsoki a hankali tace. "I hate you Yah Boss." Ta faɗa tana ɗingisa ƙafafuwanta ta nufo ƙofa dan saukowa. Umar yana kawo ruwan ya ɓalle mirfin ya beƙawa Maah, ta karɓa ta riƙe kansa ta kai masa bakinsa tana shafa kansa. Anutse ya fara shan ruwan, haɗiya uku yayi yana janye bakinsa tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, saboda bai ciki son duk abu mai sanyi ba bayan Ac, dan ko fanka baya son sanyinta. Umar ya zauna gefensa yana gaishesa tare da gaishe da Maah. Maah ta amsa cikin sakin fuska tana faɗin. "Ina Namesake da mamarta?" Umar ya amsa da"Suna gida tana gaisheku, Su My Babies an tafi school shiru gidan."