← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 113

Sashe 70

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh munje gida zaka bani na sha, ya bakinki nake so ko mi zaka faɗa min idan dai zaka ɗora bakinka anawa ka jefa min sweet ɗin, Allah zan nutsu naji komai daman kuma Ni bana tsallake maganar ka"

Sosai yaji daɗin zata nutsun.
A hankali ya furta.

"Very good Aunty J, bari kici abinci sai muyi maganar, zan baki Sweet ɗin dayawa"

Da kansa ya zuba abinci ya ajiye da spoon biyu, ya zauna yana maida hankalinsa gun ta a hankali ya furta.

"Muci toh"

Ai kuwa Juhainah ta ɗauki spoon ta ciko da da abinci zata kai bakinta baiji tayi bismillah ba, ya kame fuska yana kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa a kanta ya furta.
"Kenan bakya bismillah idan zakici abinci?"

Ƙasa tayi da kanta Sbd mugun kwarjinin da ya mata, a hankali cikin zazzaƙar muryata a shagwaɓe tace.
"Na manta Habiby bazan ƙara ba"

Bismillah tayi ta fara cin abincin cikin farin ciki suna ci tare da Yah Boss.
Bai wani ci sosai ba tsakura yake dan ta samu taci dayawa sbd akwai alamar yunwa take ji.

Dafaffiyar madaran ya sha sosai ita ma ya bata ta sha.
Bayan sun kammala ta maida kayan cikin basket ya tattara hankalinsa gunta ya fara magana cikin kamewarsa.

"Bilkisu! Ki nutsu Karki kuskura koda wasa a gun wasu kice Ni kike so.
Kina son duniya ta zagemu tayi Allah wadai da Familles Janfar?"

Da sauri ta a girgiza kanta tana marairaice fuskarta.
A hankali ya furta.
Very good idan kin nutsu sosai zan baki Sweet a baki.

Cikin sauri tana riƙe hannunsa tace.
"Wlh zan nutsu ai Ni bana fatali da maganar ka"
A hankali ya furta.
"Jibi ɗaurin auren ki, ki nutsu ki rufa mana asiri ayi bikin nan lafiya, Karki kuskura wannan maganar taje gun Maah ko Sumy ko su Mustapha dasu Nasir Kice masu kina sona da aure..."

Da Wani irin sauri ta riƙe hannunsa tana sakin kukan tashin hankali tana faɗin.
"My brother Habiby da gaske ne Kenan? Don Allah me yasa aka matso auren? Wlh bana son natafi na Barka jibi fa me yasa ake ɓoye min...?"

A hankali ya furta.
"Calm down Bilkisu, ba dai kinason kiga ina farin ciki ba a rayuwata? Kuma bakya son nayi fushi dake?"

Kai ta ɗaga cikin kukan tace.
"Wlh ina so Habiby please karkayi fushi dani"
Hawaye ya goge mata da handkerchief a hankali ya furta.

"Ok ki dakatar da kukan, sannan ki amince da auren jibi Karki tayar wa da kowa hankali Ko da kinje gidan Maah kinyi min alƙawari?"

Kukan ta fasa ta jinjina kanta tace.
"Eh nayi tunda zakayi farin ciki, ai kuma zaka bani Sweet ɗin ko?"

Bai kalleta ba ya furta.
"Yeah Aunty J, idan naga kin nutsu kamar yadda nake burin ganinki..."

Lallashinta ya fara cike da hakima da wayo yana cusa mata son auren Jamal shi ne halilinta, shi uwa ɗaya uba ɗaya suke idan ma wani yaji daga waje zai mata Allah wadai.
A cikin kwantar da kansa da dabaru da hikima ya wa Juhainah wayo ta hƙr da auren Jamal, tare da mata gargaɗin karta kuskura ta taɓa ba kowa wannan labarin ta barsa a cikin zuciyarta daga ita sai shi su binne maganar.

Ta amince bayan ya sakata tayi masa alƙawari, shima ta saka ya mata alƙawarin zai bata Sweet ta ban kwana, yace Eh zai bata, dan bai san tsakaninta da Allah da gaske take sai ya saka mata ta bakinsa a bakinta ba.

Kasancewar ya daɗe yana lallaɓata har ta fahimta, Jamal shi ne halilinta basu tantance ba aka fara kiran sallar Maghreb.
Yah Boss yayi alwala ya fice masallaci, ya rufeta ta waje, yace tayi nafilar bayan Maghreb, raka biyu, tayi azkhar kuma.

Cikin farin cikin yau Juhainah take bata damuwa ko kaɗan, yadda yau Yah Boss ya zage yayi fira da ita sosai.
Room ɗin da yake hutawa taje ta shiga bathroom tayi alwala ta shimfiɗa darduma ta tayar da Sallah.

Surayya

Yau da aka tashi daga school gidan yayarta Wasila ta biya.
Tana sallar Maghreb ta mata sallama ta fito zuwa gida, Wasila ba yanda batayi ba ta tsaya idan mijinta yazo ya kaita gida taƙi ta tafi.
Kasancewar gidan can cikin ƙurya yake sai da ta tako kafin ta samu titi.

Tana tsaye sanye da Abaya Maroon ta yane kanta da ɗan kwalin abayar wayanta tana ringing a jakarta ta makaranta, bata ɗauka ba ta matsu ta samu keke napep.
Tun daga nesa take ɗagawa keke napep sabo ɗal da yake tahowa hannu.
Yana isowa gunta yaja burki ya tsaya da rawani akansa.
Ganin ba kawo bata tsaya ɓata lokaci ba ta shiga ta zauna tana faɗin.

"Karewa zanje dan Allah kayi sauri"

Harshe ya karya yana faɗin.

"Kuɗinki dubu ɗaya idan ya miki"
Tana ƙoƙarin ciro Wayarta daga handbag ɗinta tace.

"Ok muje yayi"

Jan Keke napep yayi ya kwasawa da gudu kamar yadda tace ɗin.

Mamy ce ta kirata ta ɗauka tana faɗin.
"Mamy ina hanya Aunty Wasila fa cewa tayi wai natsaya na ƙi ina keke napep mun kamo hanya"

Daga can Mamy tace.
"Allah ya kawoki lafiya Surayya, Wlh hankali na ne yaƙi kwanciya shiyasa na kiraki"

Surayya tayi dariya tana faɗin.
"Toh yanzu hankalin naki ya kwanta Mamy, baƙi har sun fara zuwa yau ko?"
Mamy tace.
"Eh wlh su Su Farida su Hajiya Rabi'ah duk sun iso kusan Maghreb harda Malam Kamalu dasu Dije rigama anzo sai ɓarna har ta fasa Flask ɗin ruwan zafin tea ɗin da aka kaiwa Malam"

Surayya ta taɓa baki tana faɗin.
"Ai mutanen Ruga fa sai haƙuri nagarin ma ya muka ƙare bare su suna can jeji, wai har yanzu bata kai shiga school bane?"

Mamy tace.
"Shekaranta 9 fa, gata da Manyan ƙashi zaki zaci tayi shekara goma 11.
Jikin marigayi mahaifiyarta ne, Asma'u, ta gado, Malam yaƙi sakata makaranta wai tana shiga makaranta akwai damuwa kullum zata iya fasa kan yara sama da biyu, islamiyyar ma kina ganin duk da gidansu ne sai a hankali, bye sai kin ƙaraso Surayya"

Mamy Ta faɗa tana yanke kiran.

Surry ɗagowa da zatayi taga Mai keke napep ya nufi wata hanya da ita wajan hanyar airport.
Da sauri tace.
"Bawan ALLAH ba nan bane hanyar..."
Bai saurari abinda tace ba ya ƙara gudu yabi wata kwana da ba Jama'a, ga duhu.

Ihu ta fasa tana ƙoƙarin faɗuwa daga keke napep ɗin, ya tsaya juyo yana watsa mata wani ruwa yana riƙe hannunta ya turata ta koma keke napep ɗin ta zauna, a take ta suma kanta larab ya jingina da allon kujeran keke napep ɗin.....
[16/02 17:25] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Masoyen Juhainah Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kaɗan-Kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books ɗina, A Channel ɗin.
Wanda Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku.💃🏻

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*_Allahumma Ballighna Ramadan Bil Iman_*

In Sha ALLAHU Sai Bayan Sallah idan muna cikin masu rai da lafiya.
Ubangiji kasa muna daga cikin ƴantattun bayi, kasa muyi ibada karɓaɓɓiya Ameen Rahman.

*Page 38*

Cikin farin ciki ya fito ya waiga babu kowa yayi sauri ya gyara mata zaman ya jingina kanta sosai kamar irin ta gaji ne ta dan kwanto jikin Keke napep ɗin.
Ya shiga keke napep ɗin ya tayar yaja ya tafi yana ɗaukan wayansa ya kira wata lamba yana washe baki.

Daga can aka ɗaga kiran cikin farin ciki yace.
"Mai gida yau fa dawa yayi nama an samo maka sabon jini fara tass zubin Fulanin asali, akwai abun duniya wallahi ko ina dam-dam alqur'an, dan haka sai ka ƙaramin dubu hamsin akan kuɗin da ka bani"

Alhaji yana washe baki yana gyara hular kansa, kamar na Allah yace.
"Yawwa Nahehe, ai yau naso na samu wata ƴar shila mai zubin larabawa siririya mai shegen kyau da baiwar da take ɓoye ba kowa zai gane ba sai irinmu masanaha mata,, amma Aradu ina kallon kyakkyawar fuskarta da yanayin ƙyallin goshinta faɗin laɓɓanta, nasan yarinyar duk wanda ya sameta duk bin matansa ya ƙare a kanta, nayi baƙin ciki sosai na rashinta, kasan kuma bana bin matar aure"

Nahe ya ƙyalƙyale da dariya yace.
"Ai wannan ma alqur'an mai gida sai ka yabamin, zaka kwashi gara sai na iso"

Ya ƙarasa maganar yana kashe kiran yana maida hankalinsa gun tuƙin yana washe baki zai yi aikin dubu ɗari da hamsin.
Yayi tafiya mai tsayi kafin ya kawo gun haske da tsirarun mutane, yana yi yana waigen Surayya.

Nasir driving yake cikin nutsuwarsa yana amsa waya.
"A'a my friend Hairat! gaskiya bazan samu dama ba zuwa gidanku yanzu, gobe zan leƙo commando ya aikeni fa nakai saƙo ina hanyar koma wa.
Wane irin shawara ne kike so dole sai na zo yanzu?"

Daga chan wata matashiyar budurwa bazata fi shekaru 22 ba, chocolate ce tana da ɗan tsayi kyakkyawa ce babu makosa a jikinta, komai daram yayi a hallitarta da Allah ya mata, tana da sanyin amma tana faɗa fa idan ka shiga hurinmuta aslin mahaifinta ɗan Niger ne, Hausawa ne, amma mahaifinta ma anan Yola aka haifeshi.

Mahaifinta shine commando sojoji, sosai yake ƙaunar Nasir komai nasa Nasir ne a gaba, harda muƙamin da Nasir yake samu da cigabansa a aiki commando Yunus ne yake temakon sa.

Hairat aminyar Nasir ce ta gaba Allah ya haɗa jininsu, koda ya auri Hanifah lokacin tana India karatu, can take university, kuma suna tsakiyar da jarabawa, ba halin zuwa, kowa yasan da Hairat Yunus agidansu Nasir kamar yadda agidansu Hairat kowa ya san Nasir tunda daman ba baƙo bane a gidan nasu. Hanifah dai ce bata santa ba, dan bai taɓa mata hirata, mafi yawa chatting ne suka Sai yana gun aiki bai taɓa magana da ita ba idan yana gidansa, Sbd shi mutum ne mai baiwa iyalinsa haƙƙin su, ko da safe ma Sbd haka yaƙi ɗaukan kiranta duk da ba budurwasa bane, mata nada juyayyen tunani Hanifah ba lallai ta yarda da hakan ba ko bata nuna masa ba.

Yau kwananta uku da dawowa daga ƙasar India sun samu hutu na wata ɗaya tunda ta tafi shekara biyu sai yanzu tazo.
Chapter 70 · 0% Book details