← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 113

Sashe 94

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin Aunty Sumy ta shiga kitchen tana gyara kayan miyar girkin dare.
Wayan tana saman fridge a ajiye taji ringing ɗinta.
Hannunta ta wanke ta nufi fridge ɗin.
Sunan yayanta ta gani, ta ɗaga kiran tare da sallama.
Anutse ya amsa yana zuba ƙafafunsa akan Center Table, a hankali ya furta.
"Sumy ykk? Kina gidan Bilkisu ko kin tafi gidanki?"

Aunty Sumy tace.
"My brother ai tun sha biyu na rana da ƴan mintoci na dawo, magana kake so da ita?"

Cikin kamewarsa ya furta.

"Yes Sumy, here is her phone with me."

Aunty Sumy tace.
"Toh ka kira Jamal ɗin ko Surayya, shi lokacin da nazo baya gidan, bari na tura maka number Surayya suna tare"

A hankali ya furta.

"Okay, send it to me."

Aunty Sumy tace.
"Ok My brother"
Sanin halinsa baka kashe masa kira idan ya kiraka sai shi ya katse ta jira ya kashe ɗin.
Yana katse
Kiran ta shiga Contacts ta tura masa number Surayya.

Yana ganin message ɗin Sumy ya shiga ya ɗauki number ya kira Surayya.

Lokacin tana parlour a zaune ita da Farida da Dijeh suna kallon TV.
Dijeh na zuba masu iyayi, Surayya na hantarata.
Kira ne ya shigo wayanta ta kalli screen ɗin wayar ba su.
Tsaki taja tace.
"Ni fa na tsani kira daga number da ban saniba"

Farida tace.
"Haba ke kuwa sister Surry ki ɗaga mana"

Kiran yana dab da katsewa ta ɗaga da sallama.

Yah Boss yaji daɗin Sallamar da tayi ya amsa a nuste yana faɗin.
"Surayya! Kina tare da Bilkisu ne? Hope tana lafiya?"

Ai Surayya jin kamilar muryan Yah Boss cike da izza da nagarta tayi saurin cewa.
"Yah Sadiq ina wuni? A'a bama tare, Yah Jamal yazo ɗazu na dawo part ɗinmu."

A hankali ya furta.
"Ok, hope tana lafiya ba damuwa?"

Surayya tayi kiskirin tana son faɗa masa gaskiyar abinda ya faru tanajin tsoron kar ace a ɗauki Juhainah a maida ta gida sai ta warware, dan wani lokaci jinnun basa sakinta da wuri.

Yah Boss tuni ya fahimci akwai matsala.
Da wani irin sauti a hankali ya furta.

"Surayya! I'm talking to you and you're being quiet, is there a problem?"

Cikin inda-inda tace.
"Wlh daman Yah Sadiq Aunty Juhainah batada lafiya, ɗazu iskokanta suka tashi, bakaga yadda suka naɗawa Yah Jamal mugun duka ba, harda dressing bandage aka masa a wuyansa. Amma an samu sun sauka tayi bacci maybe yanzu ta farka ma"

Yah Boss ya lumshe lumsassun fararen kyawawan idanunsa, a hankali ya furta.
"Ya Salam! Ya Mujeeb! Je kiga ta farka idan ta farka ki bata wayan"

Surayya ta miƙe tana amsawa da.
"TOH bari naje na kashe kiran?"

A hankali ya furta.

"Did you call me, or did I call you? Just go."

Surayya bata yarda ta sake magana ba ta fito.

Jamal lokacin ya gaji da jiran fitowar Juhainah shiru, ya miƙe ya shiga bedroom ɗinsa ya ɗan miƙe a Bed Dan har yanzu jikinsa na masa ciwo ya daku sosai.

Surayya da sallama ta shigo parlourn shiru ba kowa, taji tsoron kar aje Jamal yana tare da ita, yaci mata mutunci.
Cikin dauriya ta nufi bedroom ɗin Juhainah.
Ƙofar a buɗe ta ɗan leƙa zatayi sallama ta hango Juhainah kasa kwance.
Da gudu ta isa tana faɗin.
"Aunty J lafiya kika kwanta ƙasa?"

Taɓata tayi taji bata motsi tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yah Sadiq Juhainah bata numfashi..."

Da wani irin sauti yana sauke ƙafafunsa daga Center Table ya furta.

"What? Ina Jamal ɗin? Maza kirasa a waya a kawota hospital ɗinmu yanzu², ganinan zuwa."
Surayya ta fashe da kuka tace.
"Baya nan, maybe ya fita bari naje na kira Mamy..."

[31/03 12:33] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

_Masoyan JUHAINAH Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kadan-kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books Ɗina, A Channel Ɗin. Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku._

*Page 48*

Bata rufe bakinta ba, sai ga
Jamal ya shigo ɗakin a guje yana zubewa a gaban Juhainah.
Saboda yaji kukan Surayya tunda ba bacci yake ba, tunanin furucin da yayi wa Juhainah ya addabi zuciyarsa kamar wasa.

Cikin damuwar da bai san ma ya shiga ba, ya ɗago Juhainah ya rungumeta yana girgizata tare da faɗin.
"Juhainah! Ki tashin don girman ALLAH wallahi ina sonki nayi alƙawarin zama dake har abadan..."

Yah Boss daga can cikin tsawa ya furta.
"Ke! Surayya bani Jamal ɗin wani shirmen banza yake, ya sakata gaba bazai ɗauketa zuwa mota aje asibiti ba? Duk yana ina ma har ta suma bai sani ba?"

Surayya kanta taji mugun tsoron jin muryan Yah Boss a wannan lokacin.
Ai har ta miƙe tsaye bata saniba, zuwa kira Mamy ta beƙawa Jamal wayan tana kuka tace.
"Amsa Yah Jamal Yah Sadiq ne yake magana"

Jamal jiki yana rawa ya amshi wayar, kafin yayi wata magana Yah Boss ya furta.

"Jamal! Yarinyar a sume ka zauna kake shirme? Me ka mata ne? ka tashi ka ɗaukar min ƙanwata zuwa hospital, tamu zaka kaita yanzu gamunan zuwa, wannan shi ne amanar da aka baka...?"

Kittt ya katse kiran bai jira Jamal yayi magana ba.
Jamal ya ba Surayya wayan ya cicciɓi Junainah da wani irin sauri ya fice da gudu, har cikin zuciyarsa mugun sonta da ƙaunarta yaji marar algus ganinta cikin wannan halin, daga yi mata wasan saki har ta fita hayyacinta.

Surayya da gudu da ta nufi part ɗinsu Mamy.

Mamy shigowar ta parlour kenan Surayya ta shigo aguje ta firgice ta zube gaban Mamy tana sakin kuka.
Mamy cikin tashin hankali ta riƙe Surayya tace.
"Surayya! Me ya faru? Lafiya?"

Dijeh ta washe baki tana faɗin.
"Kawai shugubace irin ta matan binni Antiya Suraiya ko kumya bakyaji gototo hekizo kina kuka?"

Mamy tace.
"Don ALLAH Dijeh rabani da shirmenki naji me aka mata. Surayya Jamal ya dakeki da ya ganki da Farid ko?"

Surayya tace.
"A'a Aunty Juhainah ce babu lafiya ta suma Yah Jamal ga shi can ya ɗaukota zuwa asibiti..."

Mamy ta miƙe tsaye tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Zama bai ganmu ba, maza kira Abbanku gaya masa bari na ɗauko mayafi"

Mamy da gudu ta janyo hijabin sallah ta saka suka fito ita Surayya da Faridah.
Koda suka fito Jamal ya tafi.

Dijeh harda kuka ta bisu dole suka tafi da ita.
Mamy da kanta take driving ɗin motar, bazata jira direba ko Abba ba.

Yah Boss yana katse kiran ya ajiye Phone ɗin ya miƙe dan hawa Stairs ya shirya.

Zarah tsautsayi tayi dariya tunda inda suke akwai nisa bata san me yake cewa ba, sosai akwai ƙaran Tv, ta dai ga ransa ya ɓaci abinda baka gani.

"Abubakar akan wace ƴar Gold ne kake tayar da hankalin naji kamar kana kiran asibiti...? Ko dai amarya Juhainah ce?"

Ko kallonta bai ba, ya nufi hanyar Stairs yana zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa.
Miƙewa tayi ta sha gabansa, tana faɗin.
"Magana nake maka, kai wani irin mutum ne?"

A hankali ya furta.
"Don ALLAH ki shafa min lafiya"

Ya raɓeta ya wuce.
Tayi dariya tace.
"In sha Allahu sai ka soni so mai girma munyi rayuwa tare na haifa maka ya'ya, mai girma commissioner of police, Abubakar Janfar"

Da sauri ya juyo yana faɗin.
"Zarah kije na sake ki saki ɗaya..."

Ya ƙarasa maganar yana juyawa ya tafi cikin kamewarsa.

Zubewa tayi akan guiwowinta ta ɗora hannunta akai tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un "
Fashewa tayi da kuka tana faɗin.
"Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil La Haula Wala Quwwata Illah Billah, me nakeji Ni Zarah? Sakina da gaske? Wlh Bazan tafi ba, ai saki ɗaya ne."

Kuka ta dasa a gun har Yah Boss ya shirya ya fito, cikin wani fitinannan Yadi Brown night, ɗinkin kawai abin kallo ne yana baza ƙamshi, hular kansa ta ƙara masa kyau, da kwarjini.
Ko kallonta bai ba, ya ɗauki wayoyinsa ya nufi hanyar fita, yana kiran Walid da yake Fu'ada kaɗai ya fita da yaran Shopping.

Yah Boss sai da Walid ya fita daga gidan yace masa Special Clinic Janfar zai su tafi.

Jamal kai tsaye
*Janfar Special Clinic*
Ya nufa da Juhainah, gudu yake Sosai yana yi yana riƙe hannunta.
Mamy na biye da shi.
Jamal yana isa Janfar Clinic yana shiga da motar yaga norses tsaye da gadon ɗaukan marasa lafiya, Sbd Yah Boss ya kira Dr Majid ya sanar da shi ana kawo Bilkisu tana hanya.

Kafin ma ya gama parking har sun iso.
Yana buɗe motar suka fito da ita da kansu
Suka kwantar da ita saman gadon, aka nufi ciki da ita yabisu da gudu.
A bakin room ɗin emergency Dr Majid ya dakatar da Jamal yace.
"Ai bazai yiyu ba ka shiga ka jira anan ko ka tafi reception ka zauna."
Jamal ya gaza magana yana jinjina kansa, idanunsa sunyi jajir yanaji yana gani aka rufe ƙofar.

Gefe ya koma ya yayi tsaye dan baya jin zai iya zama ma, dan masifar son Juhainah ya kamasa lokaci ɗaya bazato ba tsammani.

Mamy suna shiga asibitin bayan tayi parking sun fito emergency suka nufa.

Jamal yana tsaye kamar gumki sai kai komo yake, idanunsa jajir kamar garwashin wuta.
Mamy tun basu iso gunsa tace.
"Jamaluddin! Ya jikin nata? Sun shiga da ita? Wai me ya faru da ita?"

Jamal gun Mamy ya nufa ya faɗa jikinta yana faɗin.
"Mamy wallahi ina sonta ina ƙaunarta, bansan ƙiyayyar da nake nuna mata soyayya bace sai yau"

Mamy ta buga bayansa tace.
"Me ya sameta Jamal har ta suma? Ko Jinnu ne?"

Jamal yace.
"Mamy wasa na mata wallahi bansan abun zai sakata shiga wannan halin ba"

Mamy tace.
"Wani irin wasa Jamal? Ko kuma bari har naga farkawar tata zanfi nutsuwa"

Wani irin ƙamshi suka shaƙo, kafin su waiwaya sukaji daddaɗar muryan Yah Boss, yana faɗin.

"Yes Nasir kaje ka ɗauko Maah yanzu, kuzo Special Clinic Janfar ina jiran ku, Mustapha da Umar suna tare da Papa suna hanyar zuwa."

Yana gama faɗin haka ya katse kiran.
Cikin kamewarsa Anutse ya ƙaraso yana masu sallama, amma fuskarsa a kame.
Chapter 94 · 0% Book details