← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 113

Sashe 109

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khairat anata samun kulawa tun Jiya gun Fu'adh kamar ya maidata cikinsa, wani irin love yake nuna mata, ai mutuniyar ta saki jikinta ganin mijin nata na musamman ne.
Cikin kwana biyun kawai da sukayi sunyi wata irin shaƙuwa, Fu'adh jira yake ta warke yayi maimaici.💃🏻

Yah Boss yana zuwa gidansa Sai me yana isa gida ya iske abun mamaki.
Shi kansa tsaye yayi bayan ya fito daga motar sa, tunda labarin ya ruskesa daga gate ɗin farko.....
[07/04 16:02] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 55*

Fuskarsa a kame sosai, a hankali yake takawa cikin nutsuwarsa, ya nufi gun security's ɗinsa.

Tun kafin ya ƙarasa suka tarbe sa hankalin su a tashe, duk da basu ga ɓacin ransa ya fito akan fuskarsa ba.

Da wani irin sauti da bazaka gane halin da yake ciki ba, ya furta.

"The last warning I'm giving you,
Idan mutum yazo nemana bana nan, Just ya tafi, laifin ku ne ba na Baba Garba ba.
Why would you let her gate be opened so she can come into my house?"

Shahid yace.
"I'm sorry Sir.
God willing, we won't let anyone come into this house again without your permission.
Abinda ya saka ma muka barta dan munga abokiyar aikin ce, tazo da uniform kuma wani lokacin muka iske ta a office ɗinka, zamu kiyaye ayi Haƙuri."

Fuska a kame ya juya yana zuba hannayensa cikin aljihun wandon uniform ɗinsa a hankali ya furta.
"If you want to keep your job."

Ya ƙarasa maganar ya nufi gunta.

Zaune take cikin lafiyayyar Motar ta sabuwa, ƙira Toyota (Highlander).
Motar fara ce tass.

Sanye take da Uniform ɗin police ajikinta, zatayi shekaru 30 a haife, wankan tarwaɗa ce, kalar chocolate, mai dirarran jiki, kyakkyawa ce, kana kallonta kaga ƴar Boko, akawai wayewa sosai a tare da ita.
Sosai uniform ɗin ta mata kyau.

Yah Boss ya ƙaraso gun motar hannayensa cikin aljihu, bakinsa ɗauke da sallama.
Ta buɗe ƙofar ta fito tana amsa sallamar fuskarta a sake tana kallonsa, a hankali cike da kissa tace.

"Good evening Sir.
I'm sorry I startled you, right?"

Yah Boss ba yabo ba fallasa yana rage kaifin idanunsa a kanta, a hankali ya furta

"Honestly, you really surprise me.
Is DSP Hidayah working? Amma mi yasa baki kirani ba?"

Murmushi tayi cikin farin ciki tace.
"Bana son takuraka Sir, zan iya ɓata lokaci ina jiranka ban damu ba"

A hankali ya furta.

"Thank you Hidayah, Bismillah"

Ya faɗa yana wucewa.
Bayansa take bi bakinta yaƙi rufewa sai murmushi take, tana kallon ingarman jikinsa wanda yake murɗe gym ya kamasa sosai, yadda yake takunsa abun akwai burgewa.

Anata zaton katafareren parlourn sa zai kaita, sai taga ya nufi rumfar hutawa.
Fararen kujeru ne masu mutuƙar kyau, a jere cikin rumfar.
Ya zauna anutse yana lalubo number Jamilu ya kirasa.

Hidayah ta zauna tana fuskantar shi.
Jamilu yana ɗaukan kiran bayan yayi sallama.
Yah Boss a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Jamilu! bring to the resting pavilion everything appropriate for receiving a guest."

Cikin girmamawa Jamilu ya amsa da.

"Okay Sir, it will be brought now, God willing."

Kiran ya katse yana ajiye wayar akan table ɗin gabansa, fuskarsa ba yabo ba fallasa, ya fuskanci Hidayah bai kai yin magana ba, tai saurin tarar numfashinsa.

"Sir na huta she ka, kawai na biyu ni na gaishe ka ne, tunda kamin alƙawari baka samu dama ba jiya, nayi ta zuba ido shiru, na saka hakan a raina, because ina son zuwan naka, bansan me ya hanaka zuwa ba Sir?"

Kallon seconds 5 ya mata ya janye idanunsa a hankali, Sbd bai fiye kallon mutum ya wuce wannan sakannin ba, mace idan ba muharamasa bace.
A hankali ya furta.

"Hidayah! I didn't have time. Work overwhelmed me, the office, the company, and the guests that keep coming to me."

But Nagode ke da kika zo, ya gajiyar aiki?"

Hidayah zatayi magana Jamilu ya shigo da sallama.
Suka amsa ya ajiye ƙaton tray'n mai kyau Fruits a yanka sai juice na coconut ya buɗe ya tsiyaya mata, a Cup glass mai kyau, ya ajiye mata gabanta, ya tsiyaya mata ruwan gora mai sanyi ya ajiye.
Hidayah tana murmushi tace.
"Thank you"

Jamilu ya tsiyaya wa Yah Boss juice ɗin coconut ɗin ya ajiye masa ya fice.
Hidayah ta ɗauki Cup takai bakinta tana murmushi.
Yah ɗauki Cup yakai bakinsa ya kurɓa ya ajiye.

A hankali ya furta.
"Hidayah da gaske lokacin kina cikin karatu kafin ki zama ƴar sanda kin taɓa aure harda yaranki biyu kika rabu? Me yasa kika rabu? Rayuwa haƙuri ake"

Hidayah ta dafe ƙirjinta ta zaro idanunta tana faɗin.
"Innalillahi Sir inji wa? Wlh ban taɓa aure ba, budurwa ce Ni, Auntynah ce tayi aure tana tsakiyar karatu, kuma ai har yanzu tana tare da mijinta basu rabu ba"

Bai kalleta ba a hankali ya furta.

"Maybe mai bani labarin yayi shirme ne, but bansan ko dan bana buƙatar labarin mutane, ne ya saka banji me yace ba.
Kema ALLAH ya baki miji na gari, mutuncin mace ɗakin mijinta.

Duk arziƙin ki nasaba asali kyau ilimi, idan baki da aure wannan banza ne, ba kowa yake maku kallon mutunci ba, banyi maki gori ba, ya dace a yanzu ace kina gidan auren ki koda aikin ki Zakiyi TOH ya kasance kina gidan aurenki Hidayah.
Rayuwar nan duka guda nawace kinada shekaru talatin bakiyi auren ba, bare ki haihu, lokacin mace ƙalilan ne na haihuwa, bare yanzu a zamanin da muke ciki wata kafin ta rufe arba'in ma haihuwa ta tsaya mata, ba dan wai ta wuce ba, a'a komai na iya canza wa da ikon Allah, wata tana kai arba'in zuwa arba'in da biyar, amman yanzu ba sosai ba, Sbd komai ya canza, ga abincin da wasu suke ci yanzu sai a hankali, daga cimar abinci ma yana canzawa mace rayuwa, wata kuma bakin abinda ALLAH ya bata ne sai ya dakatar.

But na fara janki a jiki ne Sbd na yarda da nutsuwarki da addinin ki, ilimin ki na addini.

Please ki daure kiyi aure duk da nasan lokaci ne, amma sai ka riƙe mutuncin ka da darajarki data gidanku, kana ki saka niyar auren acikin zuciyarka sai ALLAH ya taimake ki, ki daure ki ƙanƙarowa kanki mutunci da gidanku a idanun jama'a da wajan ALLAH ma."

Hidayah jikinta yayi sanyi a hankali tace.
"Thank you Sir wallahi na daɗe banyi farin ciki ba irin na Yau, ko ƴan uwana da muke ciki ɗaya basu tsaya suka tunasar dani ba kamar yadda yau ka tunasar dani, ALLAH ya saka maka da alkhairi"

Yah Boss a hankali ya furta.
"Ameen Amin babu komai, fatan akwai dai wanda za'a fitar a hannu?"

Hidayah tayi murmushi tace.
"Akwai a da baya bansan adadin su ba, yanzu ɗaya ne, sai dai bai min ba, Zuciyata ta ginu da son waninsa, ina sonsa dayawa bansan ya zan fuskancin al'amarin ba"

Yah Boss sai lokacin ya ɗago lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya mata kallon sakanni biyar ya janye idanunsa a hankali ya furta.

"Waye na sansa ne?"

Hidayah tayi murmushi tana rufe fuskarta da tafin hannunta.
A hankali tace.
"Eh, amma yanzu bazan faɗa maka sunansa ba, kuma kana ganin ba damuwa na sanar da shi nan gaba?"

Kai tsaye ya furta.
"A'a gaskiya karki yi abinda zai cutar dake, ki tsaya kiyi tunani ki auri namijin da yake sonki ba wanda kike so ba."

Hidayah tana murmushi tace.
"Kamar yana sona fa!"
A hankali ya furta.
"Kibi dai a sannu"

Hidayah tace.
"In sha Allahu Sir Nagode bari natafi dare ya fara"

Ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Yah Boss ya miƙe yana saka hannayensa cikin aljihu.
Suka fara takawa bai ce mata uffan ba.

Har gun motarta ya rakata, ta shiga mota a hankali ya furta.

"Thank you so much for visiting me.
Ubangiji ya kawo miki miji nagari."

Hidayah tayi murmushi tana faɗin.

"You deserve that Sir.
Thank you too for your care. Amin Ya Allah Sir bye"

Yah Boss ya ɗaga mata hannu baice uffan ba.
Taja motar ta nufi gate na 2.

Ciki ya nufa anutse yana takunsa, ya kira Jamilu a waya akan yazo ya ɗauko tray'n



Wasa² su Hanifah sai da suka yi kwana biyar a Special Clinic Janfar, babu wanda yazo ganinsu daga dangin Nasir, sai danginsu.
Ana Sallamar su Hanifah ta koma gidanta cike da takaicin dangin Nasir, ga shi ba'a samunsa a waya bare ta faɗa masa ko ta rage takaicin Abinda aka mata.
Ummah akaci gaba da jinyar ƙafa a gida, Hanifah kuma babu haƙori guda, tasan kuma dole sai lokacin da Nasir ya dawo za'a saka mata, tunda danginsa sunyi watsi da ita.


Yau Khairat kwananta 8 gidan Fu'adh ya gama goge mata hadda, babu kalar soyayyar da bai gwada mata ba.
Tana kwana 6 yayi maimaici taci wuya sosai amma ya ta iya ta jure Sbd ba ƙaramar soyayya yake nuna mata ba.
Yanzu kwance take jikinsa babu kaya a jikinsu, ya gama tishi na uku duk tsawon kwana 9 gidansa yau yayi tishi na 3.
Wanda ya gama juyar mata da ƙwaƙwalwa, bata taɓa zaton Fu'adh mayen love ba, sai bayan aurensu, koda wasa bai taɓa koda kama hannunta ba kafin auren su.

Kallonsa take cike da soyayyar sa.
Murmushi ya sakar mata yana sumbatar lips ɗinta, a hankali ya mata raɗa.
"Nagode matar aljanna, Wlh da ban sameki ba, na gama yin asara a duniya"

Khairat ta narke a jikinsa tana shafa ƙirjinsa a hankali ta sumbaci lips ɗinsa ta masa raɗa a cikin kunnensa.
"My heart baki ɗaya ka gama haukata zuciyata da tsantsar ƙaunarka, Nagode wa ALLAH da ya bani miji nagari mai ƙaunata"

Bakinta ya wawura yana mata wata irin sumbata.
Ta lumshe idanunta tana ƙamƙame shi.
Can ta zare bakinta tana marairaice fuska.
Dariya Fu'adh yayi yana sakinta ya miƙe zaune ya sauka daga bed ɗin ya beƙa mata hannunsa ta kama ya janyota jikinsa ya ɗaga sama ya nufi bathroom da ita domin su tsarkake jikinsu su kwanta dare ya fara...
Chapter 109 · 0% Book details