Sashe 81
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shagwaɓe fuska tayi tace.
"Allah yanzu naji ajikina idanunsa biyu, a gwada kiran, ai kashe wayoyinsa yake idan zaiyi bacci Please Maah"
Maah ta sumbaci goshinta tace.
"Da asuba zan kira maki shi."
Baki ta cinno gaba tana ƙamƙame Maah ta fara mata kukan shagwaɓa.
Maah ta shiga lallashinta, tana mata susa a kitson amaren da kunnenta, har ta samu tayi shiru, ɓarawo bacci mai daɗi ya sace ta.
Maah ta rungume ƴarta tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ta furta.
"Allah dai ya wadaranka Kamal Sanda, dalilinka nayi Allah wadai da Familles Taurari baki ɗaya na tsaneku.
ALLAH ya hanaka jin daɗin rayuwarka baki ɗaya, ka haramta mana abinda ALLAH ya hallasta, Sbd tsira da mutuncin mu, tsinanne, in sha Allahu sai ka mutu bakaga ƙwanka a duniya ba, sai ciwon zuciya ya kasheka..."
★
Washegari ta kama juma'a, ranan ɗaurin aure.
Gidansu yau tun safe jama'a sai dai muce ma sha Allahu.
Dangi dai kam nesa dana kusa, ma sha Allahu, ga abokan arziƙi, Maah bakinta baya rufuwa yau, tun safe ta gwangwaje da tsadaddun ɗinkunan da Yah Boss ya saka a mata kala Biyar aci gold wuya da hannaye ma sha Allahu.
A can gidan su Jamal ma jama'a ma sha Allahu, ba'a cewa komai.
Ta ƙarfin tsiya Mamy ta saka shi ya shirya ya fito gun yayunsa da suke farfajiyar gidan tare da abokansu, da nasa abokanan na makarantar su da dole ya gayyato su ba yadda ya iya.
★
Yah Boss yau bai zuwa gun aiki sbd yanada baƙi ga ɗaurin aure.
Ya dai gayyaci jama'a iya jama'a harda wanda suke wani gari, akan yau ana yiwa ƙanwarsa ɗaurin aure.
Abinka da babban mutum, kafin 11 na rana har waɗanda suke Kano Abuja Kaduna Katsina Kebbi Bauchi Gombe manyan dai ƙusoshi sun iso, daga mabanbantan garuruwan Nigeria, Sbd mutane mai kwarjini, kowa nason mu'amala da shi, shi ma sai ya tantance ya karanci mutum kafin ya yarda harkar kasuwanci ta gamasu, tunda Company Yah Boss yayi mugun fice a faɗin Nigeria da ma maƙota na nesa da kusa.
An kai kwana uku yanata shelar ɗaurin auren wa mutanen sa na business, dan Baida aboki, sai ƙwaya ɗaya tun yarinta Al'amin Hashim Bubah.
Yana ƙasar Australia shekaru 14 tunda ya gama karatunsa acan ya kama aiki har yau bai dawo ba, iyayensa sunyi nacin duniya yayi aure yaƙi, wai baiga wacce yake ƙauna ba har yanzun.
Shiyasa Yah Boss yake kiransa da Mai Aljana, wai aljana ta auresa shiyasa mata basa burgesa.
Duk idan kaji Yah Boss ya nustu yana waya da harshen Ingilishi ko fulatancin toh a kaso 10, 5 da Al'amin ne suke magana, Sbd shaƙuwar da take tsakaninsu tun yarinta, sunansa ne ya sakawa ɗansa Al'amin.
Fu'adh tun safe famar kai baƙi masauki yake masu rai da lafiya gidajen Yah Boss, daban daban ake ajiye baƙi, bai bari an kai ko mutum ɗaya hotel ba.
Tun ƙarfe 10 Yah Boss yayi wanka juma'a yayi Sallar (Duha,) yana idarwa ya yi shiga ta kece raini tabbas kana kallonsa kasan shi ɗin babban yaya ne ga Amarya Juhainah, ya shirya bayar da auren ta a yau ɗin. Sai da ya gama waya da dukkan baƙin sa kafin ya fara shirin saukowa yayi breakfast.
A nuste ya sauko down stairs yana bala'in ƙamshi, cikin ƙayatacciyar shigar alfarma, shadda mai mahaukacin kuɗi, ta bugu iya bugawa sai maiƙo take, an buga mata ɗinkin manya masu mahaukatan kuɗi, kalar da yake bala'in ƙauna, Brown (Pale).
Kai tsaye ya nufi kan dinning room yana duba tsadaddan agogon da yake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, sai walwal yake.
Dole idan ka kalli Yah Boss sai ka ƙara kallonsa a wannan lokacin, Sbd zaka rantse da Allah shi ne angon yayi bala'in haɗuwa, ya narka dukiya a jikinsa.
11:30Am. Ya gani.
Kujara yaja ya zauna yana ɗan lumshe lumsassun fararen kyawawan idanunsa, ganin lokacin yaja sosai.
Anutse ya ɗauki Cup ya haɗa lafiyayyan tea yaji komai, ya yi bismillah ya fara kurɓa.
Phone ɗinsa ta Familles ta ɗauki ringing.
Sunan Maah ya gani tana kiransa video Call.
Gilashin da yake manne a idanunsa ya taɓa gun ɗaga kiran da yatsarsa yayi picking call ɗin, yakai Cup ɗin tea bakinsa.
Juhainah zaune cikin wata irin kwalliyar kece raini tayi bala'in kyau, jikinta naɗe da Lafaya Pink colour, tana zaune saman bed ɗin Maah ta miƙe ƙafafuwanta Suhaima na gefenta zaune ta kwanto jikinta, yayin da Khairat na gefe Aunty Sumy tana leƙe.
Fuskarsa ya kame ya kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa akansu.
Suhaima ta ɗaga masa hannu tace.
"Hey My Dadd good morning?"
Cup ɗin ya ajiye yana ɗaga mata hannu a nutse cikin kamewarsa ya furta.
"Hey My daughter Babie how are you?"
Aunty Sumy tace.
"Yayana ina kwana? Breakfast kake yi? Gaskiya wanka yabi jiki kayi bala'in kyau sosai"
Hararenta yayi a hankali ya furta.
"Kema ai Kinyi kyau abunki, ina little Sadiq da sauran yarana?"
Khairat tace.
"My brother ina kwana? Ina Aunty Zarah har yanzu bata iso ba"
Wani mugun kallo ya watsa mata ai ba shiri ta diro daga bed ɗin ta fice daga bedroom ɗin.
Suhaima ta turo baki tana faɗin.
"Allah Momy Sumy Kice wa Aunty Khairat zan ɓata da ita"
Yah Boss ya kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa akan Juhainah da ta cika tayi fam, ƙiris take jira ta fashe da kuka.
A hankali ya furta.
"Bilkisu!"
Dara-daran kyawawan idanunta ta ɗago ta kallesa tana narke masa tai rau-rau da idanunta a hankali ta amsa.
"Na'am my brother Habiby please kace Aunty Sumy ta fice zanyi sirri da kai"
Aunty Sumy ta zaro lumsassun kyawawan idanunta tana faɗin.
"Ba sai an korani ba, bari naje daman Maah ta sakani tsaronki kafin Surayya ta iso. Yaya Sadeeq zan leƙo gidan naka zuwa gobe weekend kana gida ko?"
Kai ya jinjina mata.
Murmushi ta sakar masa ta sauka daga bed ɗin ta fice tana rufo masu ƙofar.
Juhainah ta shagwaɓe fuskarta tana kallonsa a hankali tace.
"My blood Habiby kayi kyau sosai i love you"
Ta ƙarasa maganar tana kallon Suhaima.
Suhaima tayi murmushi tana sumbatar goshin Juhainah tace.
"I love you too My Aunt J lovely"
Yah Boss cikin kamewarsa ya furta.
"Aunt Bilkisu! Please ki nutsu yau fa zaki girma, ki zama mace kema wacce igiyar aure zata hau kanta har guda uku, Please bana son kije gidan mijinki da shirme Ok?"
Ƙur ta masa da idanunta tana shagwaɓe fuskarta, a hankali tace.
"My blood Habiby ALLAH ina sonka, ko My Babie?"
Suhaima tana dariya ta rungume Juhainah tace.
"Yeah my Dadd muna sonka dayawa kace mana i love you mai wujijjiga Heart Please"
Anutse ya ɗauki croissant guda ɗaya, yayi wani irin gasuwa mai kyau sai ƙamshi yake, ya saka a plate yana kallonsu, ya saki ƙaramin murmushi a hankali ya furta.
"My Babie Suhaima ina My Amiin?"
Juhainah ta takarkare ta sakar masa kukan shagwaɓa tana faɗin.
"My blood Habiby kace min i love you Baby Juhainah please inason jin hakan kafin ɗaurin aurena"
Yah Boss ya furta.
"Aunt Bilkisu kukan shagwaɓa ne kike toh ba ruwana dake sai anjima, Karki sake kirana."
Yana ƙoƙarin katse kiran tace.
"Kayi haƙuri na fasa toh Please, zanci wannan abinda ka kake ci"
Kai ya girgiza a hankali ya furta.
"Is it croissant they're bringing you?"
A shagwaɓe ta ɗaga kanta tana kallon sa.
Fuska ya kame sosai ya furta.
"Buɗe bakinki ki amsa min"
Da sauri tace.
"I'm sorry Habiby eh a kawo min zanci"
Anutse ya amsa da.
"It's okay, za'a kawo miki"
A hankali ta nuna zoben ƙaramar yatsarsa tace.
"Da wannan zoben na gold Please Habiby"
A hankali ya furta.
"Alright za'a kawo duk abinda kike so mu rabu lafiya. Da me kuma kike so?"
Shagwaɓe fuska tayi a hankali tana nunasa da yatsarta tace.
"Da Kai nake so ka bani kanka Please My blood Habiby Nah, ko My Babie Suhaima tah?"
Suhaima ta rungume Juhainah tana tsadaddan murmushi irin Yah Boss, zatayi magana Yah Boss ya kame fuska a hankali ya furta.
"My Babie Suhaima! je kira min My Amiin naga fuskarsa, da lafiyarsa, fita zanyi yanzu, je kamosa"
Suhaima ta saki Juhainah ta sauka ta nufi ƙofar fita tana faɗin.
"Yana tare dasu su Fahad ɗin Aunty Sumy, my Dadd,bari na nemosa, Wlh yau yayi kyau Aunty Khairat ne ta shirya sa, bari kagansa"
Ta ƙarasa maganar tana fita.
Yah Boss ya bita da kallon ƙaunar ƴarsa.
Juhainah ta turo baki gaba tana rau-rau da idanunta.
A hankali ya maido idanunsa akanta, can ƙasa² ya furta.
"Do you want me to just talk without a reason?"
A hankali tace.
"I love you My blood Habiby, toh kayi haƙuri ai yanzu bance komai ba, Please ce min i love you Babe J, ko Bilkisu Mai gadon Zinari.
Ni dai don Allah ka haɗo min croissant ɗin, da sauran na bakinka kaji?"
A hankali ya furta.
"I love you fitinanniya, ki daina shirmen ki a gaban My Babies ɗinki"
Ƙyalƙyalewa tayi da dariya tana faɗin.
"Eh Ni mayya ce a soyayyarka, fitinata tashi take ako wani lokaci da mayen sonka, ina sonka ɗan uwana jinin jikina ALLAH zan iya mutuwa akanka, komai naka daban yake, kaga kyan da kayi yau? Kamar kaine ango.
Daman akwai ƙaddara da zata mallaka min kai, wlh zan amsheta da hannu bibbiyu idan zan sameka, ai nima Babe ɗinka ce, kuma Suhaima naso na, ai tana tayani dinka Habiby Nah"
Kafe lumsassun idanunsa yayi akanta yana cin abincinsa Anutse.
A hankali ƙasa² ya furta.
"You've gone crazy over love, Aunt Bilkisu.
Ki min shiru da shirmenki, kiyi istigfar, kuma ki kama min bakinki, kina kuma cewa wani abun akaina, daga nan har bayan azuhur a ɗaura auren ki, tsawon wata 1 nayi miki alƙawarin bazaki samu ko labarina ba, tunda shirme kika iya, idan baki da abin cewa dole sai kinyi surutu ne?"
Marairaice fuskarta tayi a hankali tace.
"Astagfirullah nayi shiru Habiby kayi haƙuri kaji? Amma ai kasan ina ƙaunarka ina sonka ko?"
Kai ya ɗaga mata, ya yagi tissus ya goge bakinsa, bai gama cinye croissant guda ɗayan ba, haka yake da wuya yake cinye guda.
Shagwaɓe fuska tayi tace.
"Please Habiby kace min kana sona"