← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 113

Sashe 18

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fu'adh bai daddara ba duk yadda Yah Boss yayi kicin² da fuska, ya matsa nesa da shi sosai yana shafa inda ya kai masa duka yace.

"Allah Sir a cire maganar wasa Juhainah babba, ina maka kwaɗayin aurenta, saboda tana da dabi'u masu kyau, wanda ban sake ganinsu agun kowace mace ba tun bayan rasuwar Madam Khadija.
Hakan ya saka nake maka sha'awar Juhaina babba nan, saboda samun mace marar son abin duniya kamar ta a yanzu yanada wahala.
Please karka bari ta kuɓuce maka, watarana idan kuna zaune inuwa ɗaya zaka sota zaka ƙaunace ta saboda kyawun ɗabi'unta."

Ya ƙarasa maganan yana haɗe hannayensa alamar ya amince da roƙonsa.
Wani irin mugun kallo Yah Boss ya watsama Fu'adh, idanunsa na ƙara Ja baya jin zai iya yiwa marigayi Hubby Khadija kishiya, duk da bata raye, ita yaso ita ya ƙaunata, ita ta zame masa komai a cikin rayuwarsa, irin rayuwar da suka gina tare a yau a wayi gari ta Rasu kawai sai ya mata kishiya? Kishiyar ma ba kalarta ba, ƙasan² ƙasanta? Ina No! Sam bazai iya ba, shi a yanzu samun macen da zai so, sai ankai ruwa rana, a cikin rayuwarsa, duk class ɗinta da gogewarta da ilimin ta da kyawunta, Toh fa Khadijah na gabanta, dan baya jin akwai kamar matarsa cikin sauƙi.

Iska ya furzar daga bakinsa yana ƙoƙarin rufe laptop a hankali cikin kamewarsa ba tare da ya ko kalli wajan da Fu'adh yake ba, ya furta.
"Koda irin kalata ne ita ɗin bazan aureta ba, bare akwai banbanci mai tarin yawa a tsakanin mu da ita, so hanyar jirgi daban hanyar mota daban, but karka sake wannan maganar Wlh Fu'adh zamu samu matsala ni da kai, ka kama bakinki karka bari su Maah suji wani shirmen kan nan, because ranka zai ɓaci abinda ban taɓa maka ba, ban kuma saka ran har mu koma ga Allah zan ɓata maka ba, so amma akan maganar nan..."
Bai ƙarasa ba, ya yi shiru yana sake ɗaure fuskarsa.
Fu'adh yace.
"I'm sorry Sir Allah ya jiƙan Madam Khadijah"
A cikin zuciyarsa ya amsa da Ameen Amin.
A zahiri ya sake haɗe face.

Tsam ya miƙe tsaye baice masa uffan ba beƙa masa tattausan farin hannunsa yayi, ya basa wayoyinsa biyu na business.
Beƙa masa yayi yana sake faɗin.
"I'm sorry Sir, zanyi bayani kaɗan don Allah karka kaimin duka.
Amma kayi tunani Please, ka aureta ko dan kyawun halaiyarta, kamar yadda mazan Allah S.A.W, yace ka auri mace ko dan iliminta ko kyawunta da kyawun ɗabi'unta ko asalinta ko dukiyarta, mafi kyawu shi ne ka auri mai ilimin addini.
Toh Sir kaga kenan ita da halayya uku zaka aureta ko huɗu duk da bansan asalinta ba, asalinta ya nuna a zahiri gidansu ta samu tarbiyyar nan, kaga tanada kyawu duk da tana ɓaka kalata, tanada nutsuwa ga hali mai kyau ga addini, Toh me kake so a tattare da mace saboda Allah?"

Fu'adh ya ƙarasa maganan yana kallon Yah Boss wanda ya fara ƙoƙarin barin gurin saboda baya son yayi wa Fu'adh abinda zai dawo yaji babu daɗi.

Laptop ɗin yake ƙoƙarin ɗauka, Fu'adh yayi saurin ƙarasawa ya ɗauko yana faɗin.
"Muje na kaima waya 3 a hannunka Sir ina zaka iya da laptop, salon wata ta suɓuce ta faɗi ƙasa."
Yah Boss dai baice masa uffan ba ya nufi hanyar upstairs, so yake ya lissafo wa Fu'adh manyan mata masu class da ilimi da kyau da asalin da ko kallon arziƙi basu ishesa ba, amma baida lokacin magana da shi yanzun.

Fu'adh murmushi yake ƙasa² saboda yasan halin mutumin sa akan maganar yayi aure iyayen sa kawai yake wa zuru saboda ba yadda zai yi da su.

A parlon sa ya ajiye masa laptop ɗin, ya kallesa ya zauna yana danna wayarsa, ta iya family's Janfar, ko kallon inda Fu'adh yake bai ba, number Nasir ya danna wa kira yana ajiye wayan ya saka gilashinsa wanda zai iya maganarsa da shi.

Nasir
Haɗaɗɗan matashi ɗan kimanin shekaru 27 fari dogo kyakkyawan gaske, sosai yake tsananin kama da Yah Boss duk da kamar Yah Boss da Aunty Sumy yafi na Nasir amma idan babu Aunty Sumy a kusa, sak zaka ga Nasir babu mai kama da Yah Boss kamar sa.
Yana parlon gidansa zaune sanye da wasu kayan bacci masu taushi, milk colour yana kallon Tv tashar CNN news saboda Allah ya masa son kallon labarai na ƙasashe dan sanin abinda yake faruwa a duniya.
Ƙaran sautin wayarsa ne da take ajiye akan Center table ya saka shi janye idanunsa daga kan Tv'n ya maida akan wayan.

*My Big brother*
Yaga sunan yana yawo akan screen ɗin wayan.
A cikin rawa jiki ya ɗauki wayan yana picking call yakai wayan kunnensa yana sallama tare da faɗin.
"Allah yaja da ran Babban yaya ina wuni? Yayana nayi kewarka kwana biyu."

Yah Boss ya amsa sallamar, cikin kamewarsa a nuste ya furta.
"Nasir! Hope kana lafiya? Ina son ganinka gobe zuwa dare, because akwai abinda yake damun Maah akanka, but bana son na takura ka babu hujja, I want to see you come and talk face to face, don't you dare call me again."

Nasir ya marairaice fuska cikin kalar tausayi yace.
"Ok my brother zanzo kace Maah tayi haƙuri duk da bansan me nayi mata ba"
Ya ƙarasa maganar yana waigowa ɓangaren da yake jin tafiyar takalmi ƙwas².

Wata matashiya ce ƴar kimanin shekaru 25 kalarta chocolate tana da kyau da diri ba laifi akwai class, wanka iya wanka ta san kanta sosai.
Sanye take da doguwar riga ta atamfa ta dameta sosai kamar zasu yage kayan.
Cikin ƙwalisa take takowa gun mijin nata, da ya kafeta da manyan kyawawan idanunsa irin na Yah Boss.
Tana isowa ta haye kan cinyarsa ta rungumeshi tana sumbatar lips ɗinsa tana murmushi zatayi magana ya girgiza kansa.
A take ta sha jinin jikinta Yah Sadeeq ne suke waya.
Daga can Yah Boss yace.
"Ok ina jiran ka goben"
Diff ya katse kiran saboda yajin ƙaran kiss yasan Matarsa ce mai wannan ɗayan aikin.

Nasir kallonta yayi yana shafo mazaunanta ya ɗan bugi gurin yace.
"My Hanifah Kina ganin ina waya zaki kawo min aiki, babban yaya ne fa"
Ido ta zaro tana dafa ƙirjinta tace
"Innalillahi wlh my One I'm sorry Wlh ban sani ba, naga kunyi waya da Maah da papa ɗazu banyi tunanin babban yaya zai kira ka a daren nan ba, lafiya dai ko?"
Kallonta yayi yana sumbatar kumatunta yace.
"Lafiya lau my Hanifah kawai yayi kewar ƙaninsa ne autan Mazan gidanmu"

Dariya tai tana dukan ƙirjinsa tace.
"Allah dai ya bamu Baby ka fasa kiran kanka Auta kana tunzara Autah Juhainah dan bata ƙaunar wani a gidanku yace shi Autah ne sai ita"

Dariya sukayi yana maida idanunsa akan Tv hannayensa na yawo a jikinta...

Yah Boss yana katse kiran Nasir ya danna number Jamilu.
A hankali ya furta.
"Jamilu! Bring me some black tea now"

Yana gama faɗin haka ya katse kiran ya ajiye wayan akan table ya miƙe ya nufi bedroom, ko kallon Fu'adh baiba.

Murmushi Fu'adh yayi, yana faɗin.
"Good night sweet dreams Sir."
Yana gama faɗa ya juya ya fice yana rufe masa ƙofar parlon, dan yasan ko zai kwana agun bazai masa magana ba, haka bazai kallesa ba.

Kayan bacci ya saka ya fito parlon yana jiran Jamilu.
Baifi minti biyar da fitowa Jamilu ya kawo Black tea ya sha ya kashe wayoyinsa ya murza key a parlon ya nufi bedroom.
Da Bismillah ya kwanta ya rufe rabin jikinsa da lallausan Duvet ya lumshe lumsassun fararen idanunsa, yana karanto addu'o'in bacci.
Bayan ya idar da Addu'o'in ko minti biyar ba'ayi ba bacci mai nauyi ya ɗaukesa.
Ƙarfe uku na dare ya farka kamar kullum, ya fara ibada ba shi ya koma kwanciya ba, sai bayan ya dawo daga Masallaci sallar asuba, kafin ya tafi masallaci sai da ya shiga har parlon su Suhaima ya buga ƙofar bedroom tashin Juhainah, sai da yaji ta motsa yace mata.

Bilkisu! Maza tashi kiyi sallah, idan kika kuskura kikayi sallah baki zauna kika azkhar ba, kika kwanta zaki sani, you hypocrite, I will arrest you and hear what you have to say."

Cikin abun bacci tana rawar murya tace.
"Yayana kayi haƙuri Wlh Babu abinda nace maka, zanyi in sha Allahu..."
Toh fa ai dole yau sai da ta tsaya tayi azkhar kafin ta koma bacci tana turo baki tana gunguni cikin ranta.

Yah Boss bayan ya kwanta ya samu bacci kafin ya wuce aiki, kasancewar yau juma'a ne.



A can ɓangaren Ammar ya shiga cikin damuwa, saboda baya samun wayan Juhainah, ya rasa yaya zai yi da ransa, ga shi baya son ya sake ɓatawa mahaifinsa rai.

Misalin ƙarfe 9 na safe, gidansu Ammar kowa yana kan dining area, banda shi.
Dady ya kalli Hisham yace.

"Ammar bai farka bane? Bayan nace masa akwai meeting ɗin da zamuyi na ƴan kasuwa aciki kuwa harda shugaban tafiyar Abubakar Y.A Janfar, ƙarfe 10 zamu fara, amma shi ne bai fito ba."

Hisham yace"Dady brother idanunsa biyu inaga baya jin daɗin jikinsa ne, yadda naga idanunsa sunyi, ɗazu na leƙa ɗakin nasa ai."
Haj Maimuna tace"Subhanallahi nayi mamakin yau bai shigo da asuba ya gaisheni ba"
Ta ƙarasa mgnar tana kallon Nabila wacce take tsananin kama da Ammar tace
"Nabila! Je kice yazo."
Dady yace
"A'a zauna Nabila bari naje naga, Ammar yarinya nan ce a ransa, ba wani ciwo."
Ya ƙarasa maganar yana miƙe wa ya nufi hanyar ɗakin nasa.
Ammar kwance saman bed ya laɓe cikin Duvet idanunsa lumshe, da yake fuskarsa a waje take.
Dady ya buɗe ƙofar ya shigo yana faɗin.
"Ammar! Bakada lafiya?"
Ya ƙaraso bakin bed ɗin yana zama akan gefen bed ɗin, yana faɗin.
"Ammar! Har ka saka damuwa akan yarinyar nan ko? Shin wani irin so kake mata ne haka?"
Ammar jin abinda Dady Najib yace ya saka shi yin ƙurin miƙewa zaune, yana ƙoƙarin ɓoye damuwarsa, cikin juriya ya zauna yana cire Duvet ɗin da take lulluɓe jikinsa, yana faɗin.
"A'a Dady banajin daɗi ne, ciwona bayada nasaba da wannan maganar."
Ya ƙarasa maganan ya zama sosai akan bed ɗin.
Chapter 18 · 0% Book details