Sashe 87
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma bari inaje in tuɓe inyi wanka zafi nake ji, mayi magana gobe"
Ta faɗa tana katse kiran ta ajiye wayar ta miƙe ta nufi bedroom dan ta cire Ankon...
★
Surayya lokacin da ta shiga ɓangaren Jamal kowa ya watse, har Wasila mijinta yazo ya ɗauketa sun tafi gida, sai Khairat kaɗai da akace ta zauna.
Surayya tana shiga bedroom ɗin Juhainah da aka narkawa dukiya, sai wani irin bala'in ƙamshi yake tashi ciki.
Da gudu ta ƙaraso tana jifa da mayafinta ta zauna gefen ƙaton Bed tana rungume Juhainah tace.
"Oyoyo Aunty J ɗita, I'm sorry naje karɓo saƙo ne. Aunt Khairat sannu se ke ɗaya?"
Juhainah tace.
"Ayyah! Ba damuwa sister Surry"
Khairat tace.
"Wlh kuwa Surry amma tunda kinzo bari natafi, Fu'adh yana hanya zaizo ɗauka na"
Juhainah ta buɗe mayafin da yake rufe da fuskarta, tana kallon Khairat ta kamo hannunta a hankali kalar tausayi tace.
"Don Allah Aunty Khairat karki tafi"
Khairat tace.
"Gobe zanzo da wuri sai mu wuni shi kenan ko? Ga Surayya yanzu"
Juhainah batace komai ba sai hawaye.
Khairat tana ganin haka ta zare hannunta ta miƙe tace.
"Surry sai nazo da safen ku kwana da Juhainah Please"
Surayya ta zaro idanunta tana kallon Khairat zatayi magana Khairat ta ƙifta mata ido.
Surayya ta rungume Juhainah tace.
"Toh Aunty Khairat shi kenan zan kwana sai da safe"
Khairat da sauri ta nufi ƙofar karma Juhainah ta saka mata kuka.
Khairat tana zama parlour Juhainah, kiran Fu'adh yana shigowa wayarta.
Picking call ɗin tai tana masa sallama.
Fu'ada ya amsa yana faɗin.
"My heart na iso ina bakin gate"
Khairat ta amsa da.
"Ok Heart gani nan"
Ta faɗa tana miƙe wa ta gyara gyalen jikinta ta fice...
Yana cikin mota zaune cikin shigar alfarma.
Da kansa ya buɗe mata ƙofar ta shigo da sallama ta zauna tana rufe ƙofar tare da faɗin.
"Washhh! Heart na gaji sosai Wlh, yau ban zauna ba"
Fu'adh ya kalleta cike da soyayya yana murmushi a hankali ya furta.
"Ga shi babu damar na maki massaging na fitar da gajiyar."
Hararensa tai tana Turo baki gaba.
Dariya yayi yana yiwa motar key yaja yabar ƙofar gidan su Jamal.
A hankali yake driving cike da ƙwarewa yace.
"My heart ni kaina yau nagaji Sir bai barni na huta ba, kusan dukkan hidimar baƙinsa nine bai yarda da kowa ya kula dasu sai Ni har suka tafi, ga zirga-zirga kafin ɗaurin auren.
Yanzu dai Alhamdoulillah tunda anyi biki lfy an gama lfy.
Ya Juhainah? Ya akayi tabarki kika fito salin-alin?"
Khairat ta kalleshi cikin ƙaunarsa a hankali tace.
"Heart kayi kyau sosai mata nawa suka kalle min kai yau? Tsakani da Allah zaka faɗa min?"
Ido ya zaro yana murmushi yace.
"Mata kusan dubu inaga"
Baki ta turo tana ɓata fuska tace.
"Sai na faɗawa Yah Sadeeq"
Dariya yayi.
A hankali tace.
"Autah tayi ɗan hankali wayo na mata nace da safe zan zo mu wuni ta yarda kuma"
Fu'adh yace.
"Shi ne hankalin? Shi kenan na fasa kallon drama ita da Sir, Allah Sarki rayuwa hummm!"
Khairat ta kalleshi tana faɗin.
"Me ya faru Heart?"
Fu'adh yace.
"Ba komai Heart, yanzu kina lissafin kwanakin ragowar auren mu?"
Murmushi tayi tace.
"A'a banayi karatuna ya sha min kai"
Hannunsa ya beƙo ya zunguri kanta yace.
"Ƙarya kike Babayna"
Dariya tayi tana basa labarin jarabawar da suka kammala shekaran jiya...
Surayya bayan Khairat ta fita ta janyo masu ƙofar, ta gyara zamanta tana kallon Juhainah tace.
"Aunty J kin me Wlh Yah Nasir..."
Juhainah ta kalleta zata yi magana aka buɗe ƙofar bedroom ɗin aka shigo da sallama.
Juhainah ta ɗago kanta, ta kalli Jamal cikin shigar alfarma yayi masifar kyau, fuskarsa ba yabo ba fallasa.
Ta amsa sallamar tana janye idanunta akansa, ita sam bai burgeta ba, bata jin koda ɗigon sonsa a cikin zuciyarta.
Ai Surayya kaɗan ya rage ta wuntsulo ta kai Sbd tsoron ganin Jamal a gadon matarsa ɗare² a zaune, jikinta har rawa yake ta diro tana neman gun laɓewa.
Hararenta yayi anci Sa'a bai tankata ba, ya iso har bakin Bed ya zauna yana kallon Juhainah a hankali yace.
"Amarya Barka da zuwa ya gajiyar bikin?"
Ai Surayya tana ganin haka bata tsaya ɗaukan takalmi ko mayafinta ba, tattara skirt ɗin jikinta na Anko ta kwasa guje ta buɗe ƙofar ta fice.
Tsaki Yaja a hankali ya furta.
"Mahaukaciyar banza, amarya ya gajiya?"
Juhainah Allah ya sani zaman da Jamal yayi dab da ita ma bata ƙauna, amma kuma alƙawarin da tai wa iyayenta in sha Allahu sai ta cika sa, a hankali ta amsa da.
"Alhamdoulillah!"
Tana kallon Surayya tana ƙoƙarin ficewa ta fara hawaye tace.
"Don ALLAH Surayya ki dawo mu kwana"
Ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin sauka daga bed ɗin.
Jamal ya sanya tattausan hannayensa ya kamota jikinsa ya rungumeta gam ya manna bakinsa akan kunnenta a hankali ya raɗa mata.
"Ina kika taɓa jin amarya ta kwana da wani ba mijinta ba? Kiyi haƙuri mu amshi ƙaddara mu haka Ubangiji yake ikonsa, na amsheki matsayin matata, fatan zaki amsheni a matsayin mijinki?"
Juhainah ji take kamar ya runguma mata garwashin wuta, haɗuwar jikinsu, sai dai ba yadda ta iya, kamar yadda ya faɗa ƙaddara ta haɗa su zaman aure dole zata haƙura ta amshe sa.
Shiru tayi batace masa Komai ba, shima miskilin kansa bai sake magana ba, ya sumbaci kunnenta ya ɗago kanta ya kalli kyakkyawar fuskarta da take hawaye ya hura mata iska cikin dara-daran fararen kyawawan idanunta.
A hankali ya saketa ya miƙe ya kamo hannunta ta sauko yana riƙe da hannunta har parlour.
Zaunar da ita yayi, ya zauna kusanta ya buɗe ƙatuwar leda fruits ne sai yogourt.
Wani ƙaton zabo ya buɗe ya ajiye saman plate yace mata.
"Bismillah ci ki ƙoshi ga juice ga yogourt ga fruits, sai kin darje bari na watsa ruwa"
Kallonsa tai a hankali tace.
"Toh kai bazaka ci ba?"
A hankali yace.
"Zanci ke dai Kici ki rago nakine fanshewa zakiyi, kinga dole sai abinda mai abu ya rago zanci"
Sam JUHAINAH bata gane abinda Jamal yake nufi ba, dan haka yana nufar bedroom ɗin da take mallakinsa, ta gyara zamanta ta ɓarke zabon nan, ta samun gun ciyar ta dinga ci tana korawa da yogourt, tana gutsira Apple.
Abun mamaki ashe Juhainah yunwa fal cikinta, ƙatuwar cinyar zabo guda da fin rabi ta cinye kaɗan ta bari a cinyar ta biyu, kunsan mutuniyar da ci, ta shanye robar yogourt guda taci Apple ɗaya da Banana guda, tsabar ta ƙoshi bata iya shan sauran fruits ɗin ba, da juice ɗin, ko ruwa gaza sha tayi, sai numfashi take maida wa.
Tana idarwa bata jirasa ba, ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta, ta shiga bathroom tayi brush ta fito, ta cire kayan jikinta ta saka rigar bacci, daman Ac'n a kunne, ta kashe wutar ɗakin, ta haye bed ɗin ta kwanta.
Tsabar gajiya da baccin da take ji, ga ta ƙoshi bata yi minta biyar cikakku ba tayi bacci.
Jamal wanka yayi ya ɗauro alwala ya saka kayan bacci ya ɗora jallabiya akai, ya fito.
Wayam bata nan.
Da mamaki yake kallon yadda ta baje taci ta ƙoshi wanda ko za'a yankasa bai isa yaci duk wannan abubuwan da ta lodawa cikinta ba, a hankali yace.
"Ma sha Allahu taci Abunta daman nata ne"
Zama yayi yaci iya abinda zai iya, ya tattara sauran ya kai fridge ya ajiye ya dawo ya yaje ya rufe ƙofar shigowa parlour'n ya nufi bedroom ɗin Juhainah.
Fitilar ɗakin ya kunna dan bata kunna ta gefen Bed ba.
Da mamaki yake kallonta yadda ta baje tayi ɗai-ɗaya saman katafaren gadon nata tana bacci harda minshari. Abun da ya basa mamaki, duk wannan ramar tata Ubangiji ya bata Lafiyayyun dukiyar Fulani masu wani irin cika da kyau, Sbd rigar jikin nata ƙirjinta kusan rabi a waje, sbd ba wata rigar arziƙi bace.
Haka fararen siraran cinyoyinta sunada matuƙar kyau, ƙirata asalin Coca-Cola ce, sirintarta ke sakawa acikin kaya ba'a ganin hakan.
Kansa ya kauda daga kallonta.
Dariya sosai abun ya basa, dan dai ba mutum bane mai saurin dariya, da sai ya dara, amma duk da haka ya ɗan saki murmushi iya lisp ɗinsa, ganin minsharin da Juhainah take, hankalinta kwance kamar babu yaƙi a gabanta.
Jamal
A hankali ya fara magana.
"Tabdijam! Ki cinye min ƙaton Zabo kizo kina baccinki hankali kwance ƴan mata? Duk da ma umarnin mahaifiyata zanbi da saka min albarka, da yafiyar da ta min, amma ai sai kin ramo garaɓasar da kika kwasa."
Bakin Bed ɗin ya ƙarasa ya sanya hannayensa ya kamota yana ɗan girgizata ya kirata.
"Juhainah! Ta shi babu kyau bacci randa aka kawo gidan miji ba tare da kayi sallah ba"
Idanunta ta buɗe tarrr ta kalleshi ta shagwaɓe fuskarta tace.
"Kai Yah Jamal nayi sallah Allah kuwa"
Laɓɓanta masu kauri ya tsinci kansa da ranƙwafowa ya lasa a hankali ya mata raɗa cikin kunnenta.
"Na sani wannan sallar ɗakin mijine ta nafila, tashi kiyi alwala idan munyi Sallah sai kici gaba da baccin"
Shagwaɓe fuska tayi sosai tana riƙe hannunsa ta sauko daga bed ɗin.
Ta nufi bathroom ɗin.
Zama yayi gefen gadon.
Bata jima ba ta fito, zani ta ɗaura akan rigar baccin ta saka hijabi.
Darduma ya shimfiɗa yace.
"Bismillah"
Isowa tai yajasu sallah raka'a biyu.
Koda suka gama ya daɗe yana addu'a.
Yana gamawa ta miƙe ta cire kayan ta linke ta maida Wardrobe ta haye bed tana faɗin.
"Good night Yah Jamal ka rufo min ƙofar"
Bai amsa ba yaje ya kashe fitilar ya rufe ƙofar ya cire jallabiyar jikinsa ya haye Bed ɗin, ba ɓata lokaci ya rungumeta cikin jikinsa, yadda ya mata rungumar zaka rantse da Allah su ɗin masoya ne masu tsananin ƙaunar junansu.