← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 113

Sashe 106

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juhainah ta ƙarasa ta rungumeta tana faɗin.
"I'm sorry my Dijeh je ki cire uniform zanje na dawo, kizo kuyi fira da Maah"

Kai ta ɗaga tace.
"Aunty J ki dawo lafiya"

Juhainah ta amsa da.
"Ameen Amin Dijah"

Gun Maah ta iso tana faɗin.
"MAAH zanje na duba Aunty Surry Bazan daɗe ba"

Da mamaki Maah ta kalleta tace.
"Kece yau da kanki kike maganar zuwa gidan Surayya?"

Shagwaɓe fuska tayi tace.
"Toh ba matar Yayana bace?"

MAAH tace.
"Ba shakka kam matar yayanki ce, sai kin dawo karki kai Maghreb"
Kai Juhainah ta ɗaga ta tafi.
Tayi kyau sosai cikin Abayar da yake siririya ce, Abayar ta rufeta ruf.

Tana fita compound ɗin gidan taci karo da Hamza, suka gaisa tace ya kaita gun Yayanta police station.

Ba musu ta shiga motar yaja suka tafi.

Ammar kamar bazai je ba gidansu Amirah haka ya daure ya tafi.
Tarba ya samu gun mahaifinta bayan sun gama gaisawa a parlour baƙi ya turo masa Amirah.

Yana zaune fuska a haɗe ta shigo da sallama sanye da hijabi har ƙasa.
Tana da kyau ba laifi ita ba baƙa ba, ita ba fara ba.
Amsawa yayi ba yabo ba fallasa ya kalleta.
Dan diri tanada diri kamalarta ma ba laifi.
Rusunawa tayi ta gaishesa ta miƙe ta tsiyaya masa lemo ta zauna can nesa da shi.

A hankali yace.
"A tsarina babu auren haɗi amma kamun kanki da haɗuwar ki ba Mamaki nan gaba nayi Manage dake, sai dai ki sani ko na aure ki akwai tsohuwar budurwata ta fito daga gidanta da ciki tana haihuwa zan aureta ko ki jira na fara aurenta sai nayi ta biyu dake."

Amirah kanta a ƙasa tace.
"Shi kenan Allah zaɓa mana abinda yafi alkhairi, ai namiji mijin mace huɗu ne, Ance kuyi huɗu in zaku iya adalci idan Bazaku iya ba, kuyi ɗaya, ɗayar ma in Bazaku iya ba kuyi zaman ku haka, ina maka kyakkyawan zato baka daga cikinsu ko a ta huɗun zan iya aurenka Sbd biyayya iyaye."

Ammar jikinsa yayi sanyi tabbas ya samu nutsatsiyar mace, yaji daɗin zata zauna da Juhainah sa.
Hira suka taɓa ya miƙe ya ajiye mata rafar ƴan dubu² na dubu hamsin yace.
"Kinsa kati."

"A'a Wlh bana so kaje da abinka yaya Ammar"

Nan ya barmata ya tafi ta masa rakiya sai da ya shiga mota ya tafi ta dawo ciki.



Yah Boss

Zaune yake cikin ofishinsa ƙamshi da sanyin Ac na tashi.
Waya yake amsawa cikin kamewarsa Anutse yana juyi cikin lafiyayyar kujerasa.

Batayi knocking ba, ta murɗa ƙofar ta sayo kanta cikin ofishin, fuskarta a mugun haɗe.
Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke idanunsa.
A hankali cikin zazzaƙar muryansa lafazi mai shiga jini da jijiya, cikin kamewarsa yake faɗin.

"No, like how?
Kar muyi haka dake, Ai Ni nace zan zo gidan ku, just zan zo ɗin, because kin cancanta ne, miye na faɗin nabar tsokanarki?"
Ya ƙarasa maganar cikin izzarsa harshen sa taushi gun kalamai, yana ɗaukan Cup glass a ajiye kan table, yakai bakinsa.

Ko me aka ce masa a hankali anutse ya furta.

"I'm not a child, so why wouldn't I understand you? You deserve to come."
Ya ƙarasa maganar yana cire gilashin idanunsa da yake amsa wayan da shi
Ya saka wayan a Handsfree, ya fara danna System.

Daga can wacce suke wayan, ayi murmushi mai sanyi a hankali cikin class ɗinta na gogagiyar ƴar Boko tace.

"Honestly today I'm in good health and very happy, my man, you surprise me so much."

Juhainah da ta gama jin muryan matar, ta tako har gun Table ɗin, ta iso dab da shi kamar zata faɗa jikinsa, tana kafe wayan da dara-daran kyawawan idanunta.
Ƴar dariya tayi tana faɗin.
"Ga wayanka, nazo ka yanke duk wata alaƙa da yake tsakaninmu, idan zaka iya cire jininka a jikina Bismillah."

Ta ƙarasa maganar ta riƙe ƙungunta tana jijiiga cikinta na motsawa sosai.

Yah Boss kamar ba mutum bane a gabansa ko kallonta bai ba, hankalinsa a hankali ya furta.

"Thank you so much my dear ki jirani zan biyo in sha Allahu.
Because you deserve this kind of care.
Me kike buƙata na biya miki da shi...?"

Sansanyan ƙaramar dariya akayi ta cikin wayan, a hankali ta furta.
"Wow, thank you so much My Man"

Ai Juhainah idanunta har rufewa sukayi ta ɗauki wayan da take ajiye a gabansa ta bugata a ƙasa saman tayis, ta tarwatse screen ɗin ya fashe kaca-kaca...

Yah Boss bai ko kalleta ba, ya miƙe tsaye ya zuba hannayensa cikin aljihunsa, ya zagaya zai wuce tai wani kamosa ta fashe da kuka ta cakumesa da gaske tana dukansa ta ko ina tana faɗin.
"Natsaneka Yah Boss bana sonka bana sonka, I hate you, bana son ganinka. A yau da akwai inda zanje sai na Bar maka garin, because I hate you."

Wani irin rikici take tana dukansa ba da wasa ba.
Kafe lumsassun idanunsa yayi akanta.

Hannayenta ya riƙe a hankali ya furta.
"Alright tunda bakya ƙaunata, inada tarin masu ƙaunata, just dan na rasa naki bazai dameni ba, je akaiki gida, ki dinga kulawa saboda lafiyar ɗan cikinki"

Ƙoƙarin fizge hannunta take ta gaza.
Kujeru ya zaunar da ita ya juya yana takunsa Anutse.
Fridge ya buɗe ya ɗauki bottle ɗin water mai sanyi.
Buɗewa mirfin yayi ya iso gunta ya zauna kusanta ya beƙa mata bottle ɗin.
Kai ta kawar tana kuka wiwi.

Fuskarta ya riƙe ya tallafe kanta ya kafa mata bottle water ɗin a bakinta, a hankali kusan bayan kunnenta ya furta.
"Baby B ki Sha ruwan kaɗan ki kwantar da hankalin ki zan fita daga rayuwarki, kamar yadda kike so, amma sai kin haihu, Sbd bana son wani abu ya sameki da ciki"

A hankali ta dinga haɗe ruwan, haɗiya uku tayi ta kawar da kanta.
Bai sake magana ba ya miƙe.
Bottle ɗin ya ajiye.
Miƙewa tayi tsaye ta nufi ƙofar fita kamar zata tashi sama.
Wayar da ta fasa ya ɗauka, ya zuba aljihunsa, da sauri ya bita.
Hannunta ya riƙe ta zabga masa harara.

Handkerchief ya saka ya goge mata hawayen.
Yana riƙe da hannunta suka sauko.
Tunda suka fito ake kallonsu cike da burgewa.
Anata masa sannu da fitowa

Mota aka buɗe masa ya shiga ta shiga kusansa ta zauna fuska shafe da toka.
Da kansa yaja motar.

Hankali kwance yake driving ɗinsa.
Tunda ta shiga motar bata kallesa ba.
A hanya ya tsaya siya mata Orange dayawa.

Har ya iso bakin gate bai ce mata uffan ba.

Ƙofar ta fara kokowar buɗe wa.

Anutse ya ranƙwafo zai buɗe mata.

Juhainah sai taji zuciyarta ta karaya yadda yayi haƙuri da duk abinda ta masa, bai nuna mata ko a fuska ba, sai dai ya shareta baya mata fira tunda suka fito.

Ƙamshinsa da ɗumin numfashi sa ya saukar mata kasala rauninta ya ƙaru.
Waigowa tayi ta zuba masa dara-daran idanunta.
Dai-dai ya buɗe mata ya ɗago fuskarsu ta haɗe bakinsa ya manna hancinsu ya manne.

Da sauri ya janye fuskarsa, ya koma gun zamansa yana jira ta fice, ya tafi dan bazai ma shiga gidan ba ana wannan halin, bazata taɓa barinsa ya zauna lafiya ba.

Juhainah ta matso kusansa tana kafe dara-daran kyawawan idanunta akan kyakkyawar fuskarsa da baka gane wani yanayi yake ciki a dai-dai wannan lokacin.

A hankali tace.
"My brother Habiby I hate you."

Ta ƙarasa maganar tana sakin kuka ta sanya hannayenta ta ƙanƙame shi tana sake faɗin.

"I hate you My brother Habiby Yah Boss kaine rayuwata, natsaneka bana sonka"

Janyeta yayi a hankali yana gyara mata zamanta a kujerar, a hankali ya furta.
"Calm down Bilkisu, bazaki barni na huta da rikicin haka ba? Yanzu mi kike so ayi TOH?"

Kai ta ɗaga masa tana kuka.
Handkerchief ya ɗauka ya goge mata hawayen a hankali ya furta.
"Ai bakya son ganina ko?"
Da sauri tace.

"Yes, because i hate you"

Murmushi ya saki yana gyara mata mayafin abayar, ya ɗauki ledar Orange ɗin ya beƙa mata, a hankali ya furta.
"Amsa shiga gida, ko na ɓare miki ɗaya ki sha?"

Iska ta harara tace.
"Bana so, I hate you"
Amshe ledar tayi ta fice daga motar.

Tafiyarta tayi bata kulle motar ba.

Rufe motar yayi yaja ya tafi.
Kai tsaye gun Alhaji Usman Haja, ya nufa mai order Phones, a duba masa idan zata gyaru, Sbd kayansa na ciki, ga shi babbar Samsung ta ɗora a miliyan ɗaya harda kusan dubu ɗari uku a sama.
Duk da bata kai iPhone ɗinsa tsada ba, amma yafi sonta.
Kuma dole yanzu sai ya siya sabuwan wayan kafin gyaran, Sbd waya ɗaya bata masa, abubuwan sa sunyi yawa, business aiki jama'arsa, Familles nasa.


Washegari
Da misalin ƙarfe 5 na yamma
Surayya sanye da hijabi pastel peach colour, har ƙasa, tana riƙe da leda.
Tafiya take alamar gaggawa take Sbd Mamy ta aikata bakin titi.

Kamar daga sama ta hango Hanifah da Ummah, tasha uban gilashi takalmin ma gwara na Hanifah na Ummah mai tsinine.
Tafiya suke sun fito daga kwana da take tsallaken titin da Surayya take tafiya.
Basu ganta ba amma ita ta gansu.
Ai taji Ummah na faɗin.
"Ai kuwa a haukata tsinanna, ko a mata kurciya tabar garin, tun da wuri ayiwa abin tufƙar hanci."

Ai Surayya tsoro ya kamata tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!"
Ta ƙarasa faɗa tana sakin ledar ta tattara hijabinta ta kwasa aguje, hankalinta a tashe.

Kamar Ance su Ummah su kalli gun da Surayya take suka hangonta tana zabga gudu.....
[06/04 15:05] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 54*

Hanifah ta riƙe hannun Ummah Sadiya tana faɗin.
"Mun shiga uku! Ummah! Surayya Wlh nan anguwansu ne, taji me muka ce ne? Wlh kema Ummah bakya magana a hankali, sai ta faɗawa Juhainah tace taji muna maganar a haukata wata."

Ummah tace.
"Yo da uwar wa muke? Sun san ita budurwa da Malam ya gaza ganin fuskarta yace dai Nasir nada niyar aurenta? Zo muje gidansu dan ubanta mu tabbatar taji ne, ko kuma dai wani abun take yiwa gudun muka tsargu damu take."
Chapter 106 · 0% Book details