Sashe 39
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
★
Misalin ƙarfe biyu na rana
A can gidansu Maah ma kuwa kamar sabon auren fari, an taru Aunty Sumy tare sukazo da mijinta yaran kuma suna school sai Sadeeq kaɗai tazo da shi.
Ruwaida matar Mustapha tazo Rumaisa matar Umar sai Hanifah matar Nasir.
Hanifah yau ta kasa sakin jikinta irin nada saboda yadda Maah take ɗan ɗaure mata fuska bata san me tayi mata ba, tana magana da Ruwaida sai nan nan take da ita kodan tana ɗauke da abinda take so ciki.
Ko Rumaisa da bata da ciki sai tarairayarta Maah take tana sakata aiki tana kiranta Sbd tana son Rumaisa sosai har zuciyarta tinda ta haifo Little Zainab mai kamar su da Autarta Juhainah.
Sai aiki take saka Rumaisa ta bata wancan tace kai gu kaza, amman ita ko kallonta batayi, kuma ko ta taɓa aikin sai tace ta bari Rumaisa dasu Sumayya su Halima sayi.
Hakan ya sakata tayi sanyi ta rasa me ke mata daɗi. Gashi anata aikin abincin saboda gidan akwai jama'a sosai.
Sauƙin ta ɗaya Sumayya nata sakata ajikinta tana mata fira, lura da kamar bata cikin jin daɗi.
Dan
Yanzun ma
Duk suna zazzaune a parlour Maah bakinta yaƙi rufuwa, Cikin shigar alfarma take, anci gwala-gwalai wuya da kunne da hannaye.
Aunty Sumy sai kai kawo take saboda farin ciki. Ruwaida tana kusan Maah zaune yayin da Rumaisa ko tana dannawa Maah ƙafafuwanta tana saka mata albarka yayin
Little Maah ɗiyar Umar ƴar shekara biyu da watanni, an mata gayu kamar diyyar Larabawa, sosai take tsananin kama da Juhainah, sak tamkar anyi copy ɗinta.
Shiyasa Maah take masifar son little Maah Zainab. Saboda ba sunan ba kamar ma sak nata ta ɗauko, tunda Juhainah babu abinda ta bari na Maah, shiyasa take da wani irin kyau mai tsayawa a zuciyar mutum.
Little Maah zaune take akan cinyar Maah tana wasanta, Rumaisa ba ƙara min daɗi take ji ba yadda ake son little a gidan gata kamarta ɗaya da zuciyar gidan wato Juhainah.
Maah ta kalli Rumaisa tana faɗin.
"Rumaisa! Ki bari ki huta mana, ai ƙafar naji sauƙi sosai ga gajiyar aikin abinci kun sha."
Ta ƙarasa maganar tana kallon little Maah da take jan dogon hancinta tana gwarancin maganarta.
Aunty Sumy da take shirin zama kusan Ruwaida tana tsokanarta.
"Hajiya R tsohowa ya gajiya"
Ruwaida tayi murmushi batace komai ba, saboda kunyar Maah, ga ƙawayenta Hajiya Karimah da Jamila. Gasu Haj Lubnah ƙanwar Maah, abin dai gwanin burgewa tamkar auren farko ake ɗaurawa.
Maah tace.
"Sumayya! Su Khairat idan sun taso daga makaranta suma su biyo ta nan a dama dasu, ya kamata Autata ma tazo na ganta yau, kusan sati biyu ban sakata a idona ba"
Aunty Sumy tayi dariya tace.
"Bari naje gidan da kaina yanzu sai nazo da ita munyi waya yace yana gida bai zuwa ko ina Yau.
Maah tace.
"Yawwa Sumayya ƴar albarka tashi don Allah, kece kaɗai Kai tsaye zai bar ki kizo da ita"
Haj Lubnah tace.
"Kai Aunty Zainab wannan ƙauna ta Autah, yanzu ji kike kamar kije ki kawota, Ni kuma nayi² a bani ko aro anƙi har na hƙr sai yayanta aka ba, koda yake ma auren nata yazo kwana hamsin da ƴan kai"
Ta ƙarasa maganar tana murmushi.
Hajiya Karimah ƙawar Maah tace.
"Daga auren ya rage sauran wata ɗaya zata koma gidana na gyara ƴata da hannuna"
Haj Jamila tace.
"Kaji son Kai mu haɗu mu gyara Autarmu dai"
Rumaisa matar Yah Umar tana dannawa Maah ƙafafuwanta tayi murmushi tace.
"Momy zan kai gudun muwata can, Autah ai ƙawata ce dan ma iskar ta ƙini kwana biyu ba'a zuwa yanzun gidan Ruwaida ake zuwa, da gidan Nasir..."
Ruwaida tana gyara zamanta saboda kumburin da ƙafafuwanta suka fara cikin ya shiga wata na bakwai kenan.
A hankali tace.
"Lah Rumaisa sanin Da kikayi, Autah Juhainah yanzu kam bata yina nida taje har gida tace min sai ta aurawa Mustapha ƙawarta Surayya idan banyi wasa ba, babu laifin zaune babu na tsaye fa"
Kowa na cikin parlour dariya yayi Hajiya Jamila tace.
"Autah ai ja'ira ce, wai kamar itane Zainab kinaji sai ta saka Mustapha yayi aure, Uwar Biyu mi kika cemata kekuwa?"
Ruwaida tayi murmushi wushiryata na bayyana tace.
"Momy mi zance mata ai yi nayi kamar banji ba, dan Wlh idan na nuna naji haushi tana iya sakani tashin hankalin rana tsakiya"
Aunty Sumy ta kece da dariya tana miƙe wa tace.
"Ai kuwa yanzu idan naje gidan yaya Sadeeq zan haɗaku ince kina nan kina gulmar ta..."
Ruwaida ta zaro idanunta tana faɗin.
"Haba Aunty Sumy nah Bama haka dake fa"
Hanifah tayi murmushi tana faɗin.
"Kai Aunty Ruwaida kin sare sosai fa"
Ruwaida tace.
"Hanifah! Autah Juhainah fa kinsan halinta kema"
Aunty Sumy tana dariya tace.
"Matsoraciya kawai, Hanifah! Muje kiyi min rakiya gidan Yaya Sadeeq..."
Maah har zatayi magana ta fasa.
Hanifah ta miƙe Aunty Sumy ta ɗauki jakarta da key ɗin motarta yake acikin suka fita.
Maah ta taɓe baki tana yiwa Hajiya Karimah magana.
★
Jamal yana zaune a parlour sa Surayya ta shigo da Sallama tana laɓe².
Amsawa yayi ba tare da ya ɗago ya kalleta ba.
Ƙaraso wa tayi ta gaishesa yaƙi amsawa yaci gaba danna System ɗinsa.
A hankali cikin ladabi ta duƙa dan ta samu biyan buƙata tace.
"Yaya Jamal daman Mamy ce tace nace maka, don Allah ka kaini gidansu Juhainah motarmu tana wajan gyara tun safe, ita kuma ta tafi gidansu Juhainah yanzu yayanta yake aure..."
Wani malalacin kallo ya watsa mata ya maida kansa ƙasa.
Wayarta ta fara ringing.
Ɗagawa tayi tana faɗin.
"Hello Mamy"
Mamy daga can tace.
"Kibani Jamaluddin, ko baki isa part ɗin nasa ba?"
Surayya tace.
"Gani a gabansa Mamy yayi banza dani"
Mamy tace.
"Saka wayan speaker ai ba kurma bane zaiji ni"
Surayya ta saka wayan a speaker.
Mamy tace.
"Jamaluddin! Kana jina?"
A nutse ya amsa da.
"Eh Mamy"
Mamy tace.
"Toh madallah! Ka tashi kakai Surayya gun Juhainah, Sannan ka tabbatar ka kirata kun gaisa, kafin ka baro gidan, kuma idan bakada number ta yau inason ka amsa, Allah akan yarinyar nan zan ɓata maka rai Jamal"
Manyan idanunsa masu kyau da haske ya lumshe zuciyarsa na ƙuna, a hankali ya furta.
"Kiyi haƙuri Mamy zanyi duk abinda kike so, Please karki riƙe Ni a ranki hakan babu alkhairi a gareni"
Dan kar ma yaga ta sassauta ta katse kiran.
Ai yana miƙewa ya ɗauke Surayya da mari cikin fushi yake faɗin.
"Allah ya tsinewa halinki albarka, Wlh yadda kika saka na ɗanɗani zafin ɓacin rai sai na miki abinda baki zata ba, munafukar banza, wuce muje"
Surayya hannunta dafe da fuskarta tana kuka ta wuce da gudu acikin zuciyarta tana Allah ya isa.
Ai ko yadda ya fizgi motar ya nufi gate ya saka Surayya tsorata da lamarin Jamal da gaske baya don ƙawarta.
★
Juhainah wasa² tun safe zazzaɓi take tunda ta haye Stairs bata kuma sauka ba, tana kwance saman bed ta lulluɓa da lallausan Duvet, har akayi Sallar azuhur batayi ba, saboda zazzaɓin da ƙarfi ya kamata, ko jikinta bata son motsawa.
Ƙarfe biyu da mintina 39 Yah Boss ya fito cikin shirin zuwa gun baƙin da yayi wani irin fitinannan ƙamshi yake tashi a cikin jikinsa.
Shiga yayi ta alfarma tasu ta manyan mutane.
Yana zuwa dai-dai ƙofar parlour su Suhaima ya kalli gun da yake ƙofar a buɗe.
Wayam bata nan, ya ɗan gifta kaɗan yana shirin taka Steps na farko yaji yinƙurin amai da ƙarfi.
Ja yayi ya tsaya yana saurarawa, saboda Allah yayi masa ji sosai.
Da wanine tabbas daga bedroom ɗin su Suhaima ko kusa bazaiji wannan yinƙurin aman ba.
Sosai yaji ana kelaya aman.
Sanin Khairat da su Suhaima basu dawo daga school ba, yasan Juhainah ce.
Dan rabonsa da ita tun da safe a dinning room da ya Koreta.
Da sauri ya juyo yana nufar parlour.
Kai tsaye bedroom ɗin ya nufa ya kama handle ɗin ƙofar ya murɗa ya sa kai.
Kwance take ƙasa alamar ma faɗuwa tayi daga bed ɗin, gurin sauka ƙasa tayi aman, dan ga goshinta nan ya kumbura harda jini kaɗan.
Ya girgiza da ganinta a halin da ya ganta yanzun.
Da wani irin sauri ya isa gabanta ganin matsanancin halin da take ciki...
[21/01 15:44] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo
Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVEL. sur WhatsApp : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx
*Page 22*
Sumayya tana isowa bakin ƙaton gate ɗin gidan Yah Boss, ta danna Horn ba ɓata lokaci sanin wacece ita, aka buɗe mata gate, ta shige cikin gidan kai tsaye.
Tana isa parking spaces .
Tai parking ta fito, Hanifah ma ta fito ma'aikatan gidan da security's na gaisheta, ta amsa cikin mutun taka suka nufi ciki.
Jamal yana zuwa bakin gate yana horn aka buɗe masa ƙofar shi ma ya shige cikin gidan da lafiyayyar motarsa.
Bayan yayi parking ya kalleta ransa a ɓace yana faɗin.
"Munafukar banza, fita ki kirata Ni banida number ta"
Surayya ta buɗe motar da sauri tana ficewa, tana turo baki a ranta tana masa Allah ya isa.