Sashe 108
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɓangaren Surayya a rikice ta shigo parlour Mamy tana zaune shigowar Abbah kenan.
Da mamaki suke kallonta.
Mamy tace.
"Ina aiken dana miki? Ina cabbage ɗin?"
Surayya tana zaro idanunta tace.
"Mamy wallahi su Hanifah ne naji suna cewa a haukata ta ko a mata kurciya.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Mamy! Abba! Ku ceceni daga hannunsu wallahi kasheni suke so suyi Sbd Nasir, a maida masa sadakinsa na fasa auren..."
Mamy ta riƙeta tana faɗin.
"Ke! Surayya! Bana son hauka da shirme, ina kika ga Hanifah da Ummanta?"
Surayya tace.
"Na rantse da Allah Mamy sun fito da kwana nan ta bakin tsallaken titi, na gansu ganin idanuna, nagudu nayi jifa da cabbage ɗin"
Mamy ta shiga salallami tana faɗin.
"Kika jefar da ledar cabbagen? Ai kuwa sai kin koma kin siyo min wani, akwai abinda suka isa su miki ba tare da amincewa Ubangiji ba? In sha Allahu babu abinda suka isa su miki, aure kuwa keda Nasir har Aljanna in sha Allahu tunda kina son Mijin ki"
Abba yace.
"Surayya akwai tsoro ba mamaki ma bada ita suke ba, kin tsorata ne kin aure mata miji.
Ai kam cabbage bazata sake fita ba, bakiga yadda ta firgice ba, barta zan saka a kawo yanzu"
Mamy tace.
"Kenan da gaske ne yawon bin malamai suke da uwarta? Allah ya shirye su ya tsare mana imanin mu, ya karemu daga sharrinsu Ameen..."
Surayya dai ta tsorata sai raba ido take ta shiga tsakanin iyayenta ta zauna ta riƙe hannayesu kamar zasu zo su kamata yanzu...
★
Ko da aka kai su Hanifah Special Clinic Janfar, Dr Majid ya kira Yah Boss ya sanar da shi matar Nasir da mahaifiyarta an kawosu a buge maybe accident sukayi.. Yah Boss yace a basu kulawa, ayi duk abinda ya dace babu damuwa.
Sam ya manta sai bayan da dawo gidansa anyi sallar Maghreb ya tuna bai kira Maah ya sanar da ita ba.
Dole ya fito daga masallaci ya koma gida, ya sanar da Maah.
Maah sai da ta gama sauraronsa tsaf tace.
"Abbah! Wlh Nida ƴaƴana babu mai zuwa, kaima ban amince kaje ba, idan kaje Wlh zan ɓata maka rai, da kaji irin abinda sukayi wa Autah tsnarsu zakayi..."
Tsaf ta basa labarin abinda ya faru, Jinnun Juhainah ne suka lafta masu tsinannan duka.
Ta ɗora da cewa.
"Nasir ina nan zai dawo Wlh sai ya Saketa wannan fa zuri'a zasu ɓata mana, mu masu tarin Familles, a dinga kallon mu a duniya wasu irin Familles"
Yah Boss a hankali ya furta.
"Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil La Haula Wala Quwwata Illah Billah, I'm sorry Maah bansan haka abun yake ba, yau kaɗai naji daɗin abinda Jinnun Bilkisu sukayi.
Ko baki faɗa ba ma, yana zuwa sai ya rabu da ita, ko yanzu ma ta zauna gidansu har ya dawo, idan matan biyun yake sha'awar yi ya ƙaro ɗaya daga baya."
Maah tace.
"A'a ta dai zauna gidan nasa har ya dawo, so nake ta dinga shiga sabga cikin familles Janfar tana shiga ana ƙyamarta, ta taɓa taji kafin mijin nata ya dawo"
A hankali Yah Boss ya furta.
"it's okay MAAH, ya jikin na Bilkisu?"
MAAH tace.
"Ta farka ana kiran sallah, tayi wanka tayi sallah amma taƙi fitowa tana ɗaki tana lazimi"
A hankali ya furta.
"Idan na fito daga masallaci zan leƙo tambayeta mi take son ci na siyo"
Maah tayi murmushi tace.
"Kawo mata Orange da lemon"
Yah Boss ya amsa.
"Ok Maah bye"
Ya ƙarasa maganar yana katse kiran, ya ajiye sabuwar Phone Samsung ɗin da ya siya jiya, Sbd waccan sai taje Kano ko za'a samu ta gyaru.
Masallacin ya koma.
Hanifah ana can cikin wani hali babu haƙurin gaba guda, baki ya kumbura.
Ummah Hanifah kuwa ta daku kamar sakwara.
Hanifah tun tana saka ran Maah da iyalinta zasu zo, shiru babu wanda yazo.
Dama Umar da Mustapha da aka faɗa masu sun ce basa zuwa haka matansu ma bazasu ba.
★
Misalin ƙarfe 9 su Maah zaune a parlour Suhaima tana dannawa Maah ƙarfafawa, Dijeh tana danna mata cinyoyinta.
Al'amin yana zaune kusan Papa suna fira, yana Game da wayan Papa.
Papa yace.
"Zainabu matar gado kuje kuyi lesson mana, dare ya fara."
Suhaima tace.
"Papa muna yiwa Maah massage ne, kadin da tasha agun Aunty J"
Maah tace.
"Kiyi shiru kar aje ta fito taji kuyi Shiru da bakinku, koda yake ke Bama surutun kike ba, Khadijah dai ƴarta.
Tashi kuje kuyi lesson ɗin."
Suhaima ta miƙe tace.
"Amiin tashi muje"
Maah ta kalli Dijeh tace.
"Kuje Khadijah sannu"
Tafiya sukayi Papa ya kalli MAAH yace.
"Fatan dai bakiji ciwo ba?"
Kusansa ta matso tana riƙe hannunsa tace.
"Don ALLAH Harɗo karkaje hospital ɗin nan, ka rabu da matsiyata"
Murmushi yayi yana faɗin.
"Ni faɗa min bakiji ciwo ba? Ko sai munje ciki na duba?"
Murmushi tayi zatayi magana suka tsinci sallamar Yah Boss wanda har ya kawo tsakiyar parlour.
Maah tayi saurin sakin hannun Papa, ta matsa kaɗan.
Sai dai ta makara har ya gansun da Shegun Lumsassun idanunsa.
Ledar ya ajiye saman Centre table yana zama kusan Papa ya gaishe su.
Suka amsa cikin kulawa.
Ya kalli MAAH yana faɗin.
"Maah bakiji ciwo ba dai ko?"
Maah tace.
"Eh Abbah, ya gidan da aiki?"
Anutse ya amsa da.
"Alhamdoulillah! Ina yaran da Bilkisu?"
Papa yace.
"Tana ɗaki su kuma yanzu suka hau Upstairs, ka barsu suyi lesson ɗinsu."
Maah tace.
"Zakaci wani abun?"
Yah Boss yana miƙewa a hankali ya furta.
"Nayi dinner gida sama², banajin yunwa, bari na dubata"
Ya ƙarasa maganar yana duƙawa ya ɗauki ledar ya wuce hanya bedroom ɗin Maah.
Kwance take saman Sofa, sanye da kayan bacci riga da wandon, masu buɗewa Sbd cikinta.
Pink colour masu taushi sun mata kyau.
Kanta sanye da hula baƙa.
Idanunta lumshe ba bacci take ba, kawai dai batajin daɗi zuciyarta ne, dan ma tana ta addu'a tun ɗazu abun da take ji ya lafa.
A hankali ya murɗa ƙofar ya shigo da sallama a hankali.
Tun kafin yayi sallama taji fitinannan ƙamshin sa.
Sai zazzaƙar muryansa mai cike a nutsuwa da kamewa ta daki dodon kunnenta.
Ƙin buɗe idanunta tayi ta dai buɗe baki a hankali cikin mutuwar jiki ta amsa sallamar.
Ledar ya ajiye saman ɗan teburin mai kyau na Glass, da yake cikin bedroom ɗin.
Hannayensa ya zuba cikin aljihunsa.
A hankali ya furta.
"Bilkisu!"
Baki ta turo gaba, bata amsa ba.
Tsugunne yayi gaban Sofan da take kwance, a hankali ya furta.
"Tashi ki zauna, zakici pizza? Ga lemon na kawo miki harda orange"
A hankali ta buɗe dara-daran kyawawan idanunta, ta sauke su akan shi.
Idanunta ta janye daga kallonsa, Sbd kwarjinin da ya mata, da kyau, matuƙar tana kallon shi bazata iya masa rashin kunya ba.
Idanunta lumshe cikin tsiwa tace.
"Ka kaiwa dear ɗinka bana so, kuma ina dubu hamsin ɗina?"
Dogon hancinta yaja, Yana sakin ƙaramin murmushi ya duƙo fuskarsa dab tata, a hankali ya furta.
"Ai ke Ƙanwata ce, ita kuma wacce zan aura, kinfita kusa dani, tashi kici pizza"
Zabura tayi da ƙarfi tana ƙoƙarin miƙewa, ta gaza, ta riƙe cikinta tana runtse idanunta.
Hannunta ya kamo ya miƙar da ita zaune a hankali.
Can ƙasa ya furta.
"Ki dinga bin komai a hankali karki cutar min da Baby"
Dukansa ta fara tana sakin kuka tace.
"Wai kai dole ne sai ka shiga sabgata? Ba nace kowa yayi rayuwarsa ba? Kuma Babyna ba Babynka bane, nawane ni ɗaya, kaje can wannan marar ajin ta..."
Saurin ɗora hannunsa yayi saman laɓɓanta, yana matso da fuskarsa sosai dab tata, a hankali ya furta.
"Shiiittt! Aunty Bilkisu, karkace komai, Yi shiru bana sonta, kwantar da hankalin ki, zan baki zaɓin mata keda Babie Suhaima ku zabo duk wacce ta muku, shi kenan nabar kulata zaki kawo min matar?"
Ai sai taji ɓacin ranta ya kau.
Cikin farin ciki ta ɗaga masa kanta, tana kamo fuskarsa da tafukan hannunta, tana kallonsa zuciyarta na neman tarwatsa wa Sbd ƙaunarsa, ta rasa ma me zatayi dan farin cikin ya fasa auren wacce taji suna waya.
A hankali take ƙoƙarin kai bakinta akan nasa.
Yayi saurin janye wa, yana murmusawa ya kamato ta miƙe tsaye, ya riƙe kafaɗunta yana kallonta yana mata wani Irin murmushin da bai taɓa mata ba.
A hankali ta furta.
"Ya ALLAH! Yah Boss Kasheni zakayi ka daina min murmushin nan"
Ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin zubewa a jikinsa.
Da sauri ya riƙe hannunta a hankali cikin zazzaƙar muryansa yana faɗin.
"Albishirin ki Aunty Bilkisu?"
Ya ƙarasa maganar yana zaunar da ita ya zauna kusanta yana buɗe kwalin pizza.
Yawu ta haɗiye a hankali tana hararensa tace.
"Goro miye kuma?"
Yanko pizza yayi yakai mata bakinta, a hankali ya furta.
"Haaa"
Kai ta kawar tace.
"Ba'a ci, sai ka faɗa min albishirin"
Bakinsa yakai pizzar har ya saka bakinsa bai kai rufe bakin ba, yaji yatsun hannunta cikin bakinsa, ta wani gama rai.
Idanunsa masu figirtata ya ɗan buɗe yana mata kashedin karta ciro pizza.
Zaro pizza tayi ta bakinsa ta kai bakinta, tana jefawa harda abun yawunsa.
Wata ya yanko yana kallon ta a hankali ya furta.
"Zaki sha Orange?"
Kai ta ɗaga masa, tana tauna pizza à bakinta.
Hannunta ya saka mata wacce ya yanko.
Orange ya ɓare mata guda da lemon guda.
Da dabara ya samu taci pizza dayawa, ta sha Orange ɗaya, sai lemon shima ɗaya ko tsamin bataji.
Ai fa tana ƙoshi ta shiga bathroom tayi brush tazo tahaye bed, tayi kwanciyarta tayi banza da shi, tunda baya son tana taɓa shi, haushi yake bata.
Tanaji yana magana tayi banza da shi.
Yana zaune yana duba saƙon email a iPhone ɗinsa ta business, koda ya ɗago tayi bacci har ta fara minsharin nata na gado.
Miƙewa yayi yazo ya mata addu'a ya tofa mata ya daɗe yana addu'ar ya ɗan rufeta kaɗan Sbd sanyin Ac'n ya fara yawa.
Nan yabar mata kayanta a leda ba mamaki ajima ta farka tana so.
Papa da Maah suna zaune suna fira ya fito ya zauna suka taɓa hira ya masu sallama ya tafi gidansa.