← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 113

Sashe 55

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yah Boss yana ƙoƙarin cire uniform yaji ihun Juhainah tana kiransa, cikin kuka.
A hankali ya furta.

"Oh! My God! Yarinyar nan me ke damunta ne? Dole dai sun saka ni barin ƙasar baki ɗaya"
Tana shigowa parlours taga baya nan ta nufi bedroom ɗin.
Tsaye yake yana jiranta ya fasa cire kayan.

Tana buɗe ƙofar ta hangosa tsaye harɗe da hannayensa akan faffaɗan ƙirjinsa.
Da gudu ta nufi gunsa.
Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya zaro hango shatin mari akan farar kyakkyawar fuskarta.
Da wani irin sauti ya furta.
"Bilkisu! Mari? Waye ya mareki har cikin gidana...?"
[06/02 15:08] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Masoyen Juhainah Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kaɗan-Kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books ɗina, A Channel ɗin.
Wanda Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku.💃🏻

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 30*

Zarah ko lokacin da taji kukan Juhainah ta kalli Ramlah tana faɗin.
"Banso ku ka daketa ba, duk da naji zafin abinda ta min, tunda bamu san wacece ita ba, hankalina ya kasa kwanciya, kunjita can tana ihu. Ku a ganinku wata daga wace ta shigo ta mana iskanci har haka?"
Aziza cikin takaicin yayar Tata tace.

"Dalla Aunty Zara ki rufe mana bakinki idan ke bakiji zafin cin mutumcin da aka miki ba, mu munji.
Ko ma ɗiyar uban waye wannan tazo da rainin hankali, ni wallahi ba dan inna Laure kin hanaba naso mu mata mugun dukan da gobe bazata sake yiwa wasu ma ba mu ba, yarinya ƙarama sabon balaga a bushe kamar karan hatsi sai masifa, da baki kamar ƴar maroƙa"

Ramlah cikin takaicin Zarah tace.

"Ke yanzu saboda Allah duk wannan iskancin da ta mana bakiji zafi ba, laifin mu ma kike gani? Wai ke Zarah wani irin zuciya ne dake kamar ba jinin Kanuri ba?"
Zarah
Jikinta yayi sanyi tace.

"Toh kuyi haƙuri daman na bari kun naɗa mata najakin, tazo da raini sosai toh tsoron da naji kar aje Familles nasu ce, nayi baƙin jini"

Yaganah tace.
"Hummm! Wlh ko yanzu banga alamar karɓuwa ba, duba kowa fa danginsa ya tafi, Hajiya Mama kaɗai ta wuni damu, akwai karɓuwa anan kenan? Ko ya'yansa da ake faɗa da ƙannensa da suke hannunsa wa kika gani? Wai Aunty Zarah bawan ALLAH nan ya amincewa auren ki kuwa ko takurasa kika yi?"

Inna Laure ta tari numfashin Yaganah tana faɗin.
"Haba kuko ya da haka? Idan bai amince ba ta ya zai aureta? Kawai ba ruwan ta da kowa tunda dai ya amince da auren macace fa! Ita bata san yadda zata dawo da mijinta hannunta ba, sai kace ba jinin Kanuri ba"

Zarah
Tayi murmushi tana faɗin.

"Inna Laure barsu dai, Allah ya bamu rai da lafiya kawai, mahaƙuri mawadaci"

Ramlah jikinta yayi sanyi bata iya magana ba, saboda har ga Allah bata san haka auren ƙawarta yake ba, da bazata zo ba, saboda bata ƙaunar dizgi a rayuwarta Sam....

Juhainah
Ai kuwa mutuniyar kamar ya zaguta ta ƙara sautin kukan tana isowa gunsa tana ƙoƙarin ƙamƙameshi ya riƙe hannayenta yana kallon shatin marin a zafafe ya furta.
"Na ce waye ya mareki?"

Cikin kukan shagwaɓa tace.
"Su biyu ne harda amarya sunata zagini wai nice mai kama da sandar takanɗa, wai ni bana kama da da familles namu, kuma wai da karuwar Turawa nake kama...."
Cikin tsananin ɓacin rai ya furta.

"What? Tabbas Zarah zata gane bata da wayo, sani take zancen, jinin nawa suke kira da karuwar Turawa? Wlh zata biya in sha Allahu.
Hannunta yaja tana kuka tana kiran Maah.

Zaunar da ita yayi yana zama ya ciro handkerchief yana goge mata hawaye.
A hankali ya furta.
"Ya isa kije kiyi shirin sallar Maghreb, bana son sake ganin hawayen kuma"

Kanta ta ɗaga tana riƙe gefen handkerchief ɗin hannunsa a shagwaɓe tace.
"Yah Sadeeq ai ni bana kama da karuwai ko?"
Hararenta yay cikin kamewarsa ya furta.

"Karki kuskura na sake jin wannan maganar a bakinki, bare har taje kunnen Maah taji, tashi kije ki fara shirin sallar Maghreb"

Miƙe wa tayi tana marairaice fuskarta, ta zare handkerchief ɗin hannunsa a hankali tace.
"Allah da yaya yana auren ƙanwarsa sai na aureka na nuna mata karuwancin agun mijina..."
Wani irin kallo ya mata a hankali ya furta.

"Please come here Bilkisu"

Kwaɓe fuska tayi tana haɗe hannayenta tana hawaye ya ƙara matsawa nesa sosai da shi, a hankali tace.
"Astagfirullah, I'm sorry my brother Habiby kawai ina faɗin abinda yake cikin raina ne, duk da nasa na saɓawa ALLAH gurin faɗin abinda bazai yiyuwa ba, kayi haƙuri ka barni na faɗa ko na rage jin zafin kalaman matarka..."

A nuste ya fara takowa ya nufo gunta.
Da gudu ta kwasa tana faɗin.
"Don Allah kayi haƙuri Wlh bazan sake ba Yah Sadeeq"

Kansa ya dafe da tafin hannunsa yana juyawa.
Ƙofar bedroom ɗin ya rufe ya murza key, yana lumshe kaifafan lumsassun idanunsa a hankali ya furta.
"Astagfirullah Wa'atubu ilaikh, Juhainah zata kasheni baki ɗaya, bataji Sam, bansan me taje ta saki zance ba a can
har suka mare min ita."

A hankali cikin nutsuwarsa ya fara cire uniform ɗin jikinsa.
Yana gama cire kayan ana fara kiran sallah, jallabiya sabuwa ɗal ya zaro Brown Rosy ya saka, ya fesa lafiyayyan turarensa mai sanyaya zuciya.
A gaggauce ya shiga bathroom yayi alwala ya fito ya wuce masallaci.

Juhainah ma wanka ta sake ta saka riga da skirt na atamfa mai shegen tsada sosai.
Sallah tayi anci Sa'a yau ta tsaya tayi azkhar.
Tana gamawa ta cire hijjab ɗin ta kamo ɗogon gashinta baƙi siɗik kamun gefe tai masa ta murza oil na jiki ta shafawa bakinta lipstick ta fesa turare ta saka flat shoes, tsaf tayi kyau kalar atamfar ta mata kyau sosai.
A haka ta fito ta nufi down Stairs...


Nasir

Lokacin da suke isa gida ruwan wanka ta haɗa masa.
Bayan yayi wanka yayi sallah, ya cire kayansa ya saka gajeren wando iya guiwa da rigar sa,yana baza ƙamshi ya kunna Tv.
Kallon Hanifah yayi wacce har yanzu bata yi wanka bare canza kaya.
A hankali ya furta.
"My Hanifah! Zo nan."

Jiki sake ta miƙe ta dawo gunsa.
Masauki ya mata akan cinyarsa yana shafa mazaunanta ya mata raɗa a kunnenta a hankali ya fara magana.
"Wai mi a kayi ne? Ba haka na sanki ba?

My Hanifah! What's wrong with you?"

Hawayen da take dannewa ta fara tana rungumeshi sosai ta fashe da kuka.
Bayanta yake shafawa a hankali.
Idanunsa akan Tv.
"Nasan daman akwai matsala, wa ya taɓa ki? Me akayi?"

A hankali ta fara rage kukan tana faɗin.
"My husband Maah bansan me na mata ba, fushi take dani banajin daɗin rayuwata Wlh, sbd Allah ya jarabeni da ƙaunarta bana son ɓata mata rai Sam.

Nasir kyawawan idanunsa ya zuba mata tunda ta fara magana bai katse ta ba, har sai da ta gama.

Fuskarta ya riƙe da tafin hannunsa.
A hankali ya fara magana.
"My Hanifah wife anya Maah ɗina na fushi da mutum haka kawai? Gaskiya ban yarda ba, ki binciko kanki ki nutsu sosai"

Kallon sa tayi gabanta na tsananta bugawa tana sake ke cewa da kuka tace.
"Allah Nasir ban mata komai ba, amma ka tambayo min ita ko na mata wani abun cikin rashin sani, sai na bata haƙuri..."

Kallonta yake ba ƙiftawa, ya ɗan kame fuska a hankali yana faɗin.
"Ok Kina nufin bata isa ke ki tambayeta da kanki ba, sai dai ni ɗanta da ta haifa ko? "

Hanifah ta sake rikicewa tana ƙamƙameshi tana kallon sa, cike da sonsa tace.
"No masoyina I'm sorry, ba haka nake nufi ba, kayi haƙuri ka yafe min baka fahimce Ni ba ne, shi kenan zanje na tambayeta kayi haƙuri"

Kiss ya manna mata akan idanunta masu zubar da hawayen, ya fara goge mata hawayen yana faɗin.

"Alright But karki sake min hakan, ni maganar Maah karki sake idan wani abun ya gifta tsakanin ku, saboda ai uwata ce ba faɗa zan mata ba, ba fushi zanyi da ita saboda ke, so kenan hakan bai da anfani.

Ke ya kamata ki sameta saboda ruwa baya tsami banza, nasan wacece Mahaifiyata, But ni bance ita bazata iya kuskure ba, Sbd ɗan adam ajazi ne.
Lamo tayi ajikinsa tana faɗin.
"Zanje na sameta"

Nasir ya shafo ƙirjinta yana faɗin.
"Ki ɗan haɗa min wani abu mai sauƙin dafuwa yunwa nake ji sosai"
Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana faɗin.
"Ok Masoyi... "

A hankali ya furta.
"My Hanifah ki kawo min ruwan zafi nasha Lipton kafin ki gama girkin"
Da sauri ta amsa da TOH tana nufar hanyar kitchen.
System ya kunna ya jona wayansa ya fara ƙoƙarin isar da saƙon gun rukunin da suke ƙarƙashinsa...



Jamal
Ana sallar Maghreb ya nufo gida.
Mamy zaune kusan Abba suna magana, ya shigo da sallama.
Abba ya amsa yana faɗin.
"Wai Surayya sake kwana zata yi ne can?"
Mamy zatayi magana sai ga Surayya ta shigo da Sallama.
Kusan Abba ya zauna tana shagwaɓe fuskarta a hankali tace.
"Abba I miss you Mamy I miss you.
Yaya Jamal i miss you."
Jamal ya zabga mata harara a hankali ya furta.

"Tsohuwar munafuka kawai"

Mamy zatayi magana Abba yace.
"Don Allah karki matsa masa Sadiya, Jamaluddin! Ya gajiya?"

Jamal ya matso kusan Abba yana kallon Mamy a hankali ya amsa da.
"Alhamdoulillah! Abba, Mamy na kirata na bata haƙurin, ga abinda ya saka ma wuci guda ban samunta"
Ya ƙarasa maganar yana danna masu recording ɗin da yayi.
Mamy ta amshi wayan tana faɗin.
"Allah Sarki Bilkisu Allah ya bata lafiya, ai ana auren zamu dage da addu'a harda neman maganin ma"
Jamal ya ƙura mata idanunsa masu kyau, a ransa yana faɗin.
"Kenan aikin banza nayi ƙara sonta ma take hummm!"

Abba yace.
"Akwai wani aminina aikinsa kenan yana fitar da iskokai duk taurin kansu, bayan auren sai muje gunsa Allah ya bata lafiya.
Amma zan kira Alhj Yakubu na nemi alfarma a matso da bikin kusa, ko nan da sati biyu a rage wata ɗaya, Sbd ba'a wasa da lamarin iska basuda mutunci.

Jamal ya zaro cike da mamaki yana faɗin.
Abba! Sati biyu kuma? A barsa kamar yadda aka saka mana..."
Chapter 55 · 0% Book details