Sashe 96
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dr Majid! Me ke damun Bilkisu har tayi irin wannan sumar? Har abubuwanta suka motsa?"
Dr Majid yace.
"Muje office sai na maka bayani"
Yah Boss baice uffan ba ya bisa.
Yanzu ma dukkansu suka nufo Yah Boss da Dr Majid.
MAAH tace.
"Abbah! Naji ihunta mutanan ne?"
Dr Majid yace.
"Maah Papa muje office sai na muku bayani"
Mamy tace.
"Dr muma iyayenta ne yanzu muje muji damuwar ƴarmu"
Dr Majid yace.
"Ok muje sauran su tsaya mu fito"
Nasir yace.
"Dr Majid muna iya shiga wajanta yanzu ko?"
Dr Majid yace.
"Eh zaku iya amma karku yi yawan magana"
Nasir yace.
"Thank you"
MAAH Papa Yah Boss Mamy Abba malam Kamilu, suka bi Dr Majid office, yayin da Nasir da Mustapha Umar Naziru Farida Dijeh Surayya suka shiga room da Juhainah take.
Jamal zaune kusanta yana tofa mata addu'a har yanzu, ya ƙura mata ido, tayi wani irin fari laɓɓanta masu kauri sai sheƙi suke yi.
Da sallama suka shigo.
Ya amsa yana kallonsu.
Nasir yace.
"Jamal ya me jikin?"
A hankali yace.
"Alhamdoulillah! Yah Nasir"
Nasir ya iso bakin gadon ya tsugunna, ya kamo hannunta marar drip, yana kallon ta ya shiga tofa mata addu'a.
Mustapha ma ya duƙa ya kama kanta yana addu'a.
Sai da suka gama Umar yazo ya zauna kusanta ya rike kanta ya mata addu'a.
Yana miƙewa Surayya tazo wucewa dan ta zauna idan ya miƙewa, kusan Nasir ne inda yake tsaye.
Ya faki idon jama'ar ya beƙa fararen dogayen ƙafafuwansa irin na Yah Boss, ya taɓeta ta tafi zata faɗi, har ta rufe idanunta tana ƙoƙarin fasa ihu.
Naziru yayi saurin riƙota jikinsa, yana kamo kunnenta yace.
"My Surry har yanzu babu hankali, kika rufe ido zaki mana ihu gun marar lafiya."
Ashe Dijeh taga Nasir.
Ai kuwa ta tace.
"Alquraan yaya Nazihi wancan mai kama da balaraben ne ya taketa na ganhi, mutanan binni sai hegen mugunta suka iya..."
Wani mugun kallo Nasir ya watsa mata, taja bakinta tana rarraba ido ta juya masa baya, Sbd taji tsoronsa har zuciyarta.
Naziru yace.
"Dijeh waye ya taɓe Surayya? Wa kika gani kusanta?"
Dijeh ta murguɗa baki tana faɗin.
"Hine dai ya zaro min idanu yaya Nazihi"
Nazir yace.
"Ke nifa bana son shirmen banza Nazihin ƙaniyarki, sakara banza komai baki iya faɗa ba..."
Baki ta turo ta ƙara gaba tace.
"He na gayawa Baba Malam an zageni, yo mi na maku ba yanda na iya faɗa ba zan faɗa he inyi abinda ban iya ba."
Jamal ya miƙe a fuskance zai bita Nazir ya riƙesa yana faɗin.
"Ka rabu da ita mahaukaciya ce fa.
Ke kuma my Surry ki dinga kulawa da kanki."
Kallon Nasir tayi tana rau-rau da idanunta.
Cikin Sa'a ya kalleta.
Harara ya zuba mata yana zaro mata lumsassun kyawawan idanunsa.
Kanta ta kauda tana riƙe Naziru a hankali tace.
"Yah Nazir Wlh bansan me ya takaleni ba zan faɗi"
Nasir ya zuba hannayensa cikin aljihu ya fice daga room.
Bazai iya cewa yayun nasa su fito ba ya wuce abinsa.
Mustapha ya girgiza kansa yana kamo hannun Umar yace.
"Mufita, wancan fa Yah Sadiq ya ɓata mana shi"
Umar yayi murmushi suka fito.
Surayya tabi Nasir da Harara.
Zama tayi tana kamo hannun Juhainah ta riƙe gam.
Jamal ya kalli Naziru yace.
"Yah Nazir kaga amaryata babu lafiya, manyan iskokai suke bata wahala, ina son Juhainah Sosai"
Surayya ta zaro idanunta tana kallonsa da mamaki, wai Juhainah kuma Yah Jamal yake so yanzun?
Gum tayi.
Naziru ya riƙe hannun Jamal yana kwantar masa da hankali.
A can kuma office ɗin Dr Majid bayan sun zauna, ya kallesu yace.
"Alhamdoulillah! Yanzu dai mun saita komai. Amma akwai abinda ta gani ko taji da ya firgitata har ta razana da jin abun ko ganinsa, Allah ya kiyaye dan abun yaso taɓa mata zuciya, amma hakan bai faru ba, sai dai fa a kiyaye, zuciyarta bata ɗaukan mummunan jin abu ko gani"
Yah Boss ya Tuno lokacin da yake mata Ruƙiyya yaji Jinnun yace sunzo mata nurnan sakin da aka mata.
Da wani irin sauri acikin zuciyarsa ya furta.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ya Allah karka saka abun nan ya zama gaske"
Amma a zahiri cikin kamewarsa ya furta.
"Ok Dr Majid in sha Allahu, bari na turo maka mijinta sai ka faɗa masa"
Godiya suka masa suka fito.
Room suka zo MAAH tayi wa ƴarta addu'a Papa ma Mamy ma da Abba da Malam Kamilu.
Yah Boss ya tura Jamal gun Dr Majid.
Mamy da Abba da Malam suka fita ya rage daga Yah Boss sai MAAH da Papa Surayya an kirata a waya Farida ma ta fita.
Mustapha da Umar and Nasir sun tafi sun ce sai zuwa dare zasu zo da matansu.
Jamal yana fita Juhainah ta fara motsi, amma idanunta a rufe.
Dai-dai drip ya ƙare.
Yah Boss ya cire mata.
Maah ta zauna kusanta, tana riƙe hannun da aka cire mata drip ɗin.
A hankali ta fara buɗe dara-daran kyawawan idanunta.
Kallon slin room take.
Maah tace.
"Alhamdoulillah! Autah kin tashi?"
Idanunta ta maido ta kalli MAAH, batayi magana ba.
Papa yace.
"Sannu Aunty Bilkisu ya jikin naki?"
Kallon sa tayi a hankali tace.
"Yaushe aka kawoni asibiti? Wa ya kawoni? Ina Yah Sadiq?"
A hankali ya ƙaraso ya tsaya gabanta ya furta.
"Gani Bilkisu ya jikin?"
Kallon sa tayi ta beƙa masa hannunta hawaye na silalo mata akan fuskarta.
A hankali ya tsugunna gaban gadon bai bata hannunsa ba, ya kama ƙarfen gadon ya riƙe, a hankali ya furta.
"Hajjah Mama akwai damuwa ne...?"
[31/03 19:56] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx
*Page 49*
Kai Juhainah ta ɗaga masa tana kuka.
A hankali ya furta.
"Ok faɗa mana menene?"
Cikin kuka tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil La Haula Wala Quwwata Illah Billah."
Numfashi taja ta shiga karaton addu'a.
"Allahumma inni abduka, ibnu abdika, ibnu amatika, nasiyati biyadika, maḍin fiyya ḥukmuka, adlun fiyya qaḍā’uka, as’aluka bi kulli ismin huwa laka sammayta bihi nafsaka aw anzaltahu fi kitabika aw ‘allamtahu aḥadan min khalqika aw ista’tharta bihi fi ‘ilmil-ghaybi ‘indaka an taj‘alal-Qur’āna rabi‘a qalbi wa nura ṣadri wa jalā’a ḥuzni wa dhahāba hammi.
لَا إِلَهَ إِلَّا أَنتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ الظَّالِمِينَ"
Yah Boss ya miƙe ya zauna gefen gadon yana faɗin.
"Idan kin gama addu'ar muna sauraron ki, kalleni Yah Boss ɗinki ne a gabanki, faɗi maganar ki kai tsaye mi ya faru?"
Jikinsa ta faɗa ta ƙanƙameshi tana faɗin.
"Wallahi tallahi ban zubar da mutuncin gidan mu ba, shi ya sani Aunty Sumy ma sheda ce, kawai yayi niyar cimin mutunci ne, don Allah my brother ka yarda dani, wlh yanzu haka bani da lafiya juriya nake da baƙin cikin wannan abinda ya min, ba ina takaicin rabuwar mu bane, inajin zafin darajata da na rasa daga gun wanda bai san darajar ɗan Adam ba..."
Yah Boss ya janyeta daga jikinsa yana riƙe kafaɗunta ya furta.
"Bilkisu Karki harzuƙani akansa dayawa faɗa min me ya miki? Mun yarda dake mun yarda da tarbiyyar da muka baki, me ya faru?"
Cikin kuka ta sanar dasu dukkan abinda ya faru.
Ta sake ƙamƙame Yah Boss tana kuka.
Hannayensa ya saka bayanta ya zagaye yana buga bayanta a hankali, Sbd yasan tana buƙatar nutsuwa a yanzun ba ma kamar gunsa.
Ya manna bakinsa akan kunnenta ya furta.
"Ya isa Karki sake kuka akan dukkan abinda ya miki, ALLAH zai baki mafi alkhairi in sha Allahu. Ki yafe min Ni na matsa kika aure sa Aunty J na maki alƙawarin da zaran kin gama iddah zan kawo maki shuga Daddy ɗin da kike son aure shi kenan damuwa ta ƙare kiyi shiru..."
Sake riƙe shi tayi gam kamar zata koma cikinsa, tana girgiza masa kanta alamar bata so.
Shiru tayi da kukan tana sauke ajiyar zuciya, nutsuwa na kawo mata farmaki ta ko ina nutsuwa take jin na zuwa kaɗan² cikin zuciyarta.
Yah Boss ya zubawa iyayyensa idanu.
Tsabar shock Maah ta kusa faɗowa daga bed, sai da Papa ya tare ta ta faɗo jikinsa yana goge mata hawayen.
MAAH tace.
"Bilkisu kenan kema irin wannan ƙaddara zaki fara gani tun yanzu...."
Papa ya rufe mata baki yana faɗin.
"In sha Allahu daga wannan sakin an gama sakin Aunty Bilkisu, mu ba jahilai bane bazamu maidata ba, sun rabu kenan Sbd muna buƙatar ƴarmu tayi zama tsarkakake."
MAAH tace.
"Abbah! Bakace komai ba"
Numfashi Juhainah yaji ƙasan wuyansa yana sauka, alamar tayi bacci.
Kwantar da ita yayi ya rufe ta da sabon zanin rufar.
Ya fuskanci iyayensa a hankali ya furta.
"Shirun ba yana nufin nayi shiru bane, zan samu iyayensa yanzu, karku bari ya shigo room ɗin nan"
Ya ƙarasa maganar yana ficewa.
Yana fitowa suka haɗu da Jamal.
Kallon da Yah Boss ya masa ne ya saka shi ƙasa da kansa Tabbas asirinsa ya toni Juhainah ta farka.
Yah Boss ya furta.
"Mun gode, daman abinda kake nema a gunta kenan? Kana samu ka saketa! Ka sani haƙƙinta bazai Barka ba, kashedin da zan maka karka kuskure ka shiga ɗakin da take, idan kuma ka shiga zaka san waye Abubakar Yakubu Abubakar Janfar."
Ya juya zai tafi Jamal ya zube gabansa ya kamo ƙafarsa.
Yah Boss dan kar jama'a su ankare abinda baya ƙauna kenan, da sauri ya fizge ƙafarsa yasa kai ya wuce.
Kai tsaye gun Abba da Mamy ya nufi.
Sallama ya masu ya zauna kusan Abba yana faɗin.
"Abba zamu tafi gida da Bilkisu zuwa dare ko gobe sai kuzo a duba lamarin, yanzu hospital muke bai dace ayi wata maganar ba, babu daraja."
Abba yace.
"Shi kenan ina sha Allahu mai girma commissioner zamuzo ALLAH ya bata lafiya"
. Yah ya amsa da.
"Ameen"
Tafiya yayi kai tsaye gun Dr Majid ya tafi ya kirasa ya duba Juhainah, yace da zaran ta farka zasu iya tafiya.
Ya rubuta magunguna Yah Boss yaje pharmacy ya amso.
Abba yana kallon Mamy yace.
"Akwai babbar matsala kuma kallonsa kinsan yana cikin ɓacin rai, muje gida mu tisa Jamal gaba muji me ya yi mata.."
Ɗakyar suka lallaɓa Jamal suka tafi gida.