Sashe 29
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Juhainah babba ta lallaɓa ta shiga bedroom ɗin tana rufo ƙofar ta murza key, ta shiga bathroom.
Tana barbaza gashin kanta ta buga kanta da bango ta ciro wayanta a cikin rigarta, ta danna kira idanunta na rikiɗewa.
Ana ɗaga kiran tace.
"Na rantse da girman Allah na fasa wannan kwangilar yanzu fansa zan ɗauka, idan dai Ni Raudah Sa'idu sunana sai naga bayan shegiyar yarinyar nan, Allah sai na hanata jin daɗin duniya, mayya Uwar jaraba mai naci wai Ni Raudah Sa'idu.
Alhaji Nuhu ka tuna tsawon wata uku nayi ana koya min yadda zan koyi haƙuri da juriya da iya magana kamar gaske na, ƙoƙarta har rayuwata na bada suka bugeni a mota, amma yaran gidan nan tsinannu sam ban masu ba, haka shima tsinannan baya sona baisan ba soyayyar gaskiya ta kawoni ba. Juhainah sai na bar mata babban tabo sai na addabeta na hanata jin daɗin duniya, ni zan tafi wlh na fasa wannan kwangilar..."
Tana gama magana ta kashe wayan baki ɗaya saboda bata buƙatar lallashi yanzu, wutar fansar Juhainah kecin zuciyarta na sharrin da ta mata da kiranta mayya, da wutar tsanar da ta hura mata tun ranan da ta fara ganinta, ba tare da tasan mugayen halayyarta ba..
Juhainah taƙi sakin Khairat tana manne jikinta a parlour, suna zaune akan lafiyayyun kujerun Royal Turkish Chairs ɗin.
Yana shigowa parlour ya kalli Juhainah tabi ta ƙamƙame Khairat, kana kallon Khairat kasan ta takura sosai yadda Juhainah baki ɗaya a jikinta take.
Yana kame fuska sosai a hankali.
Ya furta.
"Saketa karki jimata ciwo, munafukar banza, haka kika ƙarasa lalacewa Juhainah?"
Idanunta a rufe tana sake ƙamƙame Khairat tana hawaye a hankali tace.
"Kayi haƙuri Yayana bazan sake ba nayi alƙawari."
A hankali ya tako har Chair ɗin da suke zaune, ya tsaya.
Khairat kamar zata fashe da kuka ta zaci tare zai ɗauki hukuncin.
Ranƙwafowa yayi ya sanya tattausan hannunsa ya kamo kunnenta ya murɗa ta ɓare baki zatayi ihu ya buge bakin yana faɗin.
"Kina Min kuka ko hawayen munafurci jikinki ne zai yi bayani, kina son mayun su kamaki ne?"
Cikin sauri ta girgiza kanta tana kamo hannunsa da yake saman kunnenta tayi shiru jikin Khairat tana rarraba idanuwa.
Tsaki yaja yana janye hannunsa data riƙe ya miƙe yana faɗin.
"Khairat ba nace ki saketa ta zauna irin na kowa."
Ya ƙarasa maganar yana takunsa, ya nufi hanyar Stairs.
Khairat tace.
"Tom my brother"
Ai kuwa ta janye jikinta, Juhainah tayi kwanciyarta saman 3 seater royal turkish ɗin ta ɗauki
Cushions har 3 ta rungume gam tana shagwaɓe fuskarta, tana shafa jajayen laɓɓanta da sukayi launin pink, zafi suke mata bugewan da ya masu.
A hankali tace.
"I hate you Yah Boss, I hate you Yah Boss "
Khairat ta zaro idanunta tana dafe ƙirjinta tana kallon hanyar Stairs.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin yayi nisan da bazai jiba, takai mata duka tana faɗin.
"Juhainah kin me kike faɗa? Wlh idan yaji kasheki zaiyi fitsarariya kawai."
Juhainah ta ɓare baki tana faɗin.
"Wayyo Yah Sadeeq Aunty Khairat ta dakeni acikina Wayyo..."
Khairat cikin tashin hankali ta rufe mata baki kamar zata yi kuka tace.
"Don Allah ki rufe min asiri kiji tsoron Allah Juhainah"
Ta ƙarasa maganar tana kallon hanyar taga ba'a ma ganinsa, ta sauke ajiyar zuciya.
Cikin temakon Allah ya fara taka Steps an kirasa yana amsa baiji ba.
Juhainah tace.
"Toh ki sake dukana kiga idan banje na faɗa masa ba Allah"
Surayya ko tana shigowa parlours taga ana murɗa kunnen Juhainah ta laɓe taƙi shigowa har sai da ya tafi ganin Juhainah na ƙokarin ƙullawa Khairat sharri ta tsaya har suka gama, ta saɗaɗa tazo ta zauna tana ɗora hannunta agadon bayan Juhainah zatayi magana Khairat tace.
"Hattara zai iya gani daji, haɗiye maganar a ranki"
Surayya duk hankalinta a tashe ta miƙe tana faɗin.
"My sister gaskiya gida zani zan kiraki a wayar Aunty Khairat sai muyi magana"
Juhainah ta miƙe zaune tana gyara hular kanta tace.
"Muje na rakaki compound sai direba ya kaiki"
Ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Hannun Surayya ta kama suka fara tafiya.
Suna fitowa Juhainah taja hannunta tace.
"Dalla chan matsoraciya muje na baki labarin ko bakya so?"
Surayya tace.
"Inaso amma fa na bugo maki ruwa, da Yah Boss ya tsare ni"
Juhainah ta zaro idanunta tana faɗin.
"Me kika ce masa?"
Surayya ta faɗa mata yadda sukayi da Yah Boss.
Juhainah tace.
"Kira min yaya Jamal ɗin Please yi sauri."
Surayya ta ciro wayanta ta danna number Jamal.
Tanata ringing bai ɗauka ba, har suka isa ƙaton swimming pool ɗin suka zauna saman kujera.
Surayya tace.
"Wlh yaƙi ɗauka"
Juhainah ta taɓe baki tace.
"Nifa yanzu kawai ƙuna zanyi Wlh bazan tsaya bugun zuciya yamin yawa, Allah na haƙura duk wanda yaga dama ya aura min ɗin, idan aure dole ne zaman fa? Kawai ki share sa nagaji da shiga tashin hankali ina koke² a banza ke ko Jamal ɗin aura zanyi so what? Ni dai Wlh Ammar ne bansan me ya min ba, bana son aurensa Jamal kuma nasan ta ruwan sanyi zan lallaɓasa ya sakeni"
Surayya ta zaro ido tace.
"Wlh baki isa ba idan kin isa Allah ya tsinan, kaji ƴar rainin hankali..."
Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Yau fa na rainawa Yah Boss hankali dayawa, kuma duka kukan da nayi na ha'incine, ba ɗaya na gaskiya, yanzu dai bari na baki labarin.
Sunana Bilkisu Yakubu Abubakar Janfar amma gidanmu da duniya ma da Juhainah ta sanni, sbd shi iyayena da yan uwansa suke kirana.
Ni shagwaɓaɓɓiya ce ta bugawa a jarida, sangartata zan baka haushi idan baka saba daniba, zaka ga an sakeni kara zube ina abinda naga dama a gidanmu, Saboda ina Auta.
Mu 7 ne ya'yan baban mu, Yah Boss shine babba yaci sunan kakanmu mahaifin Papa Abubakar Sadiq.
Aunty Sumayya ke binsa,Yah Mustapha Yah Umar Yah Nasir sai Aunt Khairat nice Autar gidan.
Aunty Sumayya tanada aure kusan shekaru 14 da aurenta, ta riga Yah Boss aure, ƴaƴanta 4 mata biyu maza 2 Habibullah shekarunsa 12 sai Fatima shekaranta 9. kyawawane ajin farko saboda kyawun Aunty Sumy suka ɗauko duk da yaya Khabir mijin Aunty Sumy ba baya ba, suna kama da Yah Boss sosai tsananin kama tamkar shine ya haife su, shiyasa yake musu mugun so, duk da kuwa shi ɗin miskilin mutum ne.
Sai Fahad ɗan shekara 6 shi ke bin Fatima ,sai Abubakar Sadiq ɗan shekara 3 mai sunan Yah Boss saboda tsananin ƙaunar da take tsakanin Yah Boss da Aunty Sumy tai masa takwara ba dan yana sunan kakan mu ba.
Saboda idan ka cire Maah da Papa da Aunt Khadija matarsa da Suhaima and Al'amin, da yake musu mugun so da ƙauna ba kamar Maah ma, toh a duniya Aunty Sumy ce Abar ƙaunarsa, shiyasa ƴaƴanta ma suka sami wannan ƙaunar.
Mazan duka sunyi aure suna zaune da matansu lafiya.
Yah Boss tsakanin aurensa dana Aunty Sumy shekara biyu ne.
Yah Mustapha ya'yansa biyu Twins ne maza Shuraim da Shamsiddin, shekaran su 4 Ruwaida matarsa na ɗauke da ciki ta shiga wata 6 yanzu.
Sai Yah Umar ƴarsa ɗaya, an yayeta mai sunan Maah wato Zainab ana kiranta da Maah ɗinta.
Yah Nasir har yanzu shekara biyu da aurensa matarsa Hanifah bata samu ciki ba.
Nida Aunty Khairat ne bamu da aure.
Yah Boss yana kammala karatunsa bayan ya gama bautar ƙasa ya fara aiki, da kaɗan² yana samun ƙarin matsayi cikin shekara 11 da fara aikinsa na ɗan sanda har yazo matsayin commission, Sbd yawan karatunsa da yake zuwa, dole idan kaga yadda yake kyau cikin kayan da yadda yake kamewa da kula duk wani abinda ya dace a aikinsa, ba cin hanci ba rashawa sai dai bayan fage idan kuwa labari yazo masa kashinka ya bushe, kai dole ya burge ka ga shi matashi tunda bazaka ce yayi shekara arba'in ba, yanayinsa baya nuna hakan.
Kidnaping yayi sauƙi yawan faiɗe ya rage ƴan fashi sunyi sauƙi acikin garin mu da ma jahohin Adamawa baki ɗaya.
Aunt Khairat ita kam ta maida hankali akan karatunta, ni kam karatunta ma bai wani shamin kai ba, kinsan hakan dan ma Yah Boss ne baida sauƙi idan na shiga hannunsa baya tausaya min, duk rashin mutuncina acikin gidan nan sai idan baya gari ko baya gidanmu saboda har yanzu yafi yin rayuwa cikin gidanmu akan tamfatsetsen gidansa, dan wani lokacin idan yaje gidanmu sai yayi kwana biyu uku daga can yake wucewa aiki, kwana biyu ne ma naga ya daina zuwa bansan me ya saka ba.
Maganar samari ke kanki shedace akwai kala² na korasu ne, Sbd babu kalata ni babba nake so, Ammar kawai na bari, shima badan na auresa ba, amman yanzu kina gani bansan yadda ƙaddara zatayi daniba, tunda banida a hannu sai Ammar.
Matar Yah Boss Aunty Khadija larabawan Misira ne, Asalinsu amma a nan ƙasar Nigeria aka haife su a Abuja, gidansu yana Maitama, su uku ne iyayensu suka haifa, yayarta Iman da ƙaninta Suhaib.