← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 113

Sashe 30

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da inada karanci shekaru shekarata bakwai akayi auren Yah Boss da Aunty Khadija, amma aurene na soyayya ni ma ina shaida hakan, ita Dr ne a babbar asibitin gwamnatin Abuja, tasan kanta gurin aikinta ga tausayin talakawa, kowa sonta yake asibitin bayada ƙyanƙyanmi, ga sakin fuska, Aunty Khadijah, Allah dai ya jiƙanta da rahama.
Wannan halayyar ya saka Yah Boss yake mata wani Irin so da ƙauna kowa ya sani cikin familles Janfar, ga ta bata raina danginsa ba, har na ƙauye fa ziyarta take, komi nisan waje idan dai ya shafi jinin Janfar da Maah sai taje ga kyauta, Wlh inason Auntyn Khadijah sosai da halayyarta, kamar fa ba Balarabiya ba, halinta ba kowa Allah yake ba irinsa ba, shiyasa nake tausayin Yah Boss, dan Wlh da wuya ya kuma samun mace irin Aunty Khadija, ki kalli Al'amin da yake kamarsu ɗaya da ita wlh halinta Yaron garesa, baida ƙyamar kowa ga fara'a da son mutane, amma Suhaima sai a hankali Yah Boss ya ɓata min ɗiyah"
Ta ƙarasa maganar tana turo jajayen laɓɓanta da suke launin pink masu kauri.
Kafin taci gaba da cewa.
"Wlh my Surry bamu taɓa tunanin Yah Boss zai dawo normal ba, duk da har yanzu sai haƙuri, amma lokacin da ta rasu ita da jaririn da ta haifa, kai wlh mun shiga tashin hankali, saboda kwata² baya cikin hayyacinsa, duk juriya irin tashi da basar da abu rasuwar Aunty Khadijah da babynta ya girgiza shi tare da kowa a familles Janfar, iyayenta su suka da dawo suna lallashinsa"

Surayya tace.
"Allah Sarki! Allah ya jiƙanta ai tanada kirki jifa idan na biyaki gidansu wancan idan ta rasu, nima kamar ta goyani dan kirki bare kouƙannen mijinta, Allah yasa ta huta, wlh da zai aureni zan kwatanta koyi da halayyarta"

Juhainah ta kalleta tana sheƙewa da dariya tace.
"A'a na rabaki Wlh ki kiciresa a ranki, zaifi dan Wlh kina aurensa ciwon zuciya ne zai karki.
Kinsan me ya saka nake son na auri babban mutum my Surry?"
Surry tace.
"Eh mana dan ki samu soyayya mai tsafta"

Juhainah tace.
"Toh bari kiji akwai wata rana lokacin inada shekara 13 an bamu hutun makaranta Aunty Khadija taje da kanta ta kawoni, sbd ni tsoronsa baya barina yawan zuwa gidansa ita take zuwa tazo dani sbd tana tsananin ƙaunata.
Toh a wannan zuwane lokacin Al'amin yanada shekara biyu a haifa, Suhaima nada shekara 6.
Watarana cikin dare ƙishirwa ta tasheni a bacci fridge ɗin ɗaƙin mu nida su Suhaima babu ruwa sai juice na fito na sauko downstairs dan na ɗauki ruwa na kowa.
Kin san me nagani My Surry?"

Surrayya ta girgiza kanta tana faɗin.
"Muguwa ina zan sani tunda baki taɓa faɗa min ba, kina baƙin ciki"
Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tana faɗin.....
[14/01 15:20] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVELS. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

_*Mutanen Kirki Kuci Gaba Danna Min Followers, Zan Dinga Antayo Muku Zafafan Tsofaffin littattafai Na, Kuna Chanawa Abinku😂💃🏻🫣*_

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 17*

"Dalla chan ƙaramar ƙwaila.
Ai ina Steps na ƙarshe da zan sauko, na hango Yah Boss tsaye sanye da kayan bacci wandon iya guiwa sai rigar ta ɗan wuce guiwa amma batada buttons sai abin ɗaurawa, shima bai ɗaure ba, gashin ƙirjinsa a waje gargasan da suke ƙwabrinsa luf kwance.
Aunty Khadija na bayansa ta rungumeshi ta baya, tana dariya Saboda irin kalaman da yake zazzaga mata na soyayya Wlh harda batsa naji yana mata, wai tanata dariya tana shafa gashin ƙirjinsa, yana lumshe wannan shegun idanunsa irin na kwartaye, ai shi yasa bana jure kallon ƙwayar idanunsa."
Surayya cikin zaƙuwa tace.

"Ni don Allah ki ƙarasa bani labarin mi sukayi a tsayen Please?"

Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Hummm! Ke kam kin Banu wlh,Wata kalma naji ya faɗa mata yana juyo da ita ta dawo gabansa wata irin runguma naga ya mata, yana kamo mazaunanta, daman rigata ita da babu duk ɗaya, naga ya manna lips ɗinsa a kunnenta ko mi yace mata oho ta ƙyalƙyale da dariya tana faɗin, i love you Hubby my husband....
Ai kawai sai naga yana lasar ƙasan haɓarta zuwa wuyanta yana sakar mata wata irin sumbata yana mata magana ƙasa² yana gangarawa tsakiyar ƙirjinta ya fincike saman rigar sai ga rigar a ƙasa buttons sun watse ƙasa suma, daga ita sai pant da bra, yana tura fuskarsa ƙirjinta, tare da ƙamƙameta yana faɗin.
I love you too Hubby my wife,... Sai kuma ya faɗi wata kalma tamin tsauri a wancan lokacin, Amma ina nayi nisa cikin shaukin abinda suke ban gama tsuma ba sai da naga ya ɗagota sama da hannayensa saboda ya fita tsayi sosai.
Laɓɓansa masu kyau da sheƙi naga ya ɗora akan nata...
Ya Allah! Surayya! Idan na faɗa Duk abinda naga a ranan Yah Boss yana yiwa Aunty Khadija cike da soyayya mai tarin yawa wlh sai kin linka soyayyar da kike masa sau Goma sha biyu.
Ke samun kamar Yah Boss a fannin baje kolin ƙauna wlh sai an tona akwaisu amma basuda yawa adai ƙasarmu ta Hausa, Ban ce India da Larabawa ba, duk da zai goga da su ɗin.
Ai ina faɗa maki Allah kawai ya maidani ɗaki lafiya da dafe², tun daga shi ban ƙara yarda na rasa ruwan sha ba, jerasu nake gorar ruwan can kamar ba siya su ake ba, dan a ranan wlh na dinga ciwon mara wannan shine mafarin da na fara period.

Ke wannan Yah Boss hummm! Allah dai yasa munada rabon auren maza irinsa mu shoshale abinmu"
Surayya tace.
"Allah har na ƙara sonshi sai dai ba halin samunsa, nifa gaskiya tafiya zanyi naga ke hankalinki kwance yake baki damu da ruwan da na bugo ba, kuma Wlh zai iya cinyemu dagani har ke, idan hankalina ya kwanta zan sake tariyo labarin ni kinga tafiyata, zan shiga keke napep idan na fita daga layin."
Juhainah ta miƙe ta riƙe hannunta tana ƙyalƙyale dariya tace.
"Ni dai gani ga Allah, ɓarawo a hannun mata, idan kinje yadda kukayi ki kirani a number Aunty Khairat. Don Allah ki masa dabara ya yarda, kuma ki turo min number sa a wayan Aunty Khairat"

Har bakin gate ta rakata ta dawo tayi kwanciyarta a parlour.
Tana kwanciya Yah Boss na fitowa cikin wani irin shiri mai ƙayatarwa yana baza ƙamshi.
Juhainah mayen ƙamshinsa ta shaƙo ta ƙamƙame Cushion ta zabura ta miƙe zaune tana ɗago kanta ta buɗe dara-daran kyawawan idanunta tana kalli hanyar Stairs.
Karaf suka haɗa ido, yana wani irin takunsa, mai burgewa.
Fuskarshi a kame sosai, hakan ya saka tayi ƙasa da kanta kamar zata yi kuka cike da tsantsar shagwaɓar da bata jure ƙin yi masa tace.
"Yah Sadeeq kaina yake ciwo."

A nutse ya wuce yana amsa waya ta Glass ɗin idanunsa, yaƙi ce mata uffan.
Da kallo ta bisa tana turo baki gaba, ta koma ta kwanta tana rungume Cushion ɗin.

Khairat cike da ladabi tace.
"My brother a dawo lafiya"
A nutse ya amsa da.

"Allahumma Ameen, Ke Juhainah! Karki kuskura kiyiwa mutane bacci da yamma nan. Tashi kije bedroom ɗina akwai maganin ciwon kan ki sha.."

Ai kuwa ta miƙe zaune tana murza dara-daran kyawawan idanunta, tana shagwaɓe fuska, ta miƙe tsaye ta fara tafiya.
Khairat tace.
"Allah ya shirya ki Wlh ƙarya kike nasani dan kar ki barsa ya zauna lfy bai ce uffan ne"
Baki ta murguɗa wa Khairat tana tafiyar fitsara tana kaɗa ƙugunta kamar ɗan kwanko.

Yana fitowa suna jiransa saboda yaso yin latti gun meetings ɗin, ya shiga suka tafi, Yana bawa Walid umarnin yayi driving da ɗan gudu saboda ya makara.....


Anguwan
Dou girel

Jamal zaune farin Glass manne a kyawawan idanunsa yana danna System.
Surayya ta faɗo masa parlour kamar an jefota babu sallama.

Da mamaki ya ɗago yana kallonta yana haɗe fuska cikin izzarsa ya fara magana.
"Ke! Miye haka lafiya? Uban me zan maki kike famar dokamin kira, naƙi ɗauka shi ne kika baro inda kika je ɗin ki faɗo min parlour babu sallama? Gat out, ko na tsintsinka maki mari, ni zaku rainawa hankali, ashe auren bogi kuke so nayi da ita, Ni ɗan iska ko? Haka kawai ina zaune cikin kwanciyar hankali na ina karatuna da aikina, zaku sakani a chakwakiya, yanzu ba daɗe wa commissioner ya kirani wai nine Jamal Abdallah nake son ƙanwarsa yana nemana zuwa dare, naje gidansa zamuyi magana, ni Wlh tsabar shock ɗin dana shiga har ya gama magana bance uffan sai Ok kawai nace saboda abin ya girmi tunani, ku ƴan iska ko?"

Surayya ta zube akan guiwowinta tana riƙe ƙafafunsa tace.
"Don Allah Yaya Jamal kayi ceton rai, ka temakeni ka rufa mana asiri, ashe har ya kira ka ya faɗa maka? Wlh auren dole ne za'a mata, Kacece mu Wlh cewa tayi tana sonka zata zauna da kai, ai kai abun alfahari ne wannan haɗaɗɗiyar tana sonka, Kuma sabon jini irinka Please ka amince ko don son da take maka..."
Harbata yayi da ƙafar da ta riƙe yana shirin tsinka mata mari tai saurin wuntsulawa ta miƙe ta koma bayan Chair ɗin da yake zaune ta laɓe tana faɗin.
"Don Allah yaya Jamal kayi haƙuri ayi auren nan, wlh tana sonka..."
Miƙewa yay cikin fushi ya nufota ta fasa ihu aguje ta nufi hanyar fita daga parlourn tana kiran Mamy.

Mamy tana zaune suna magana da Abdulkarim yayan Jamal wanda yazo yanzu dan gaishesu, yanada aure harda ya'ya uku.
Ma sha Allahu suma Ubangiji ya basu kyau da farin ga rufin asiri, suma asalin Fulani ne.

Kamar an jefota haka ta shigo parlour tana famar ihu, ta faɗo jikin Mamy tana laɓewa.
Abdulkarim yace.
"Wai ke Surayya! Yaushe zakiyi hankali ne? Meye haka? Keda wa?"
Tana haƙi tana kallon kofar shigowa parlour tace.
"Yaya Abdul ba yaya Jamal ne ya biyo NI dan naje na kai masa labari mai daɗi, Juhainah ƙawata ta fito da shi tana sonsa suyi aure shi ne ya biyo NI zai dakeni"

Mamy tace.
"Ikon Allah! Itane ma take son nasa ba shi ba? Ni Ban gane ba?"
Chapter 30 · 0% Book details