← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 113

Sashe 100

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fu'adh kansa yayi mamakin yadda Yah Boss ya sake haskawa ya ƙara fresh, kwarjinin sa ya ƙare kyansa cikarsa.
Wata irin kamewa ya ƙaro, ai dole idan ka kalli Yah Boss a yanzu ka ƙara baki ɗaya ya ƙara canzawa cikin wata 4, ya sake zama mai tsare gida komai nasa ya ƙaru.
Kai tsaye gidansa yace su wuce.
Sbd yadda hadarin ya ƙara gangamowa

Suna zuwa da wanka ya fara yayi sallah, ya saka Suit mai masifar tsada da kyau, Brown colour (chestnut)
Iya haɗuwa dai Yah Boss yayi cikin Suit ɗin.
Ƙamshinsa kawai ya ishe ka.

Lokacin da ya sauko down Stairs dinning room ya nufa, ya ɗan sha Madara mai zafi suka fita da Fu'adh.

Misalin ƙarfe 9 Su Suhaima suna Stairs karatu suke, har Khairat da Dijeh.
Tunda Maah tace masu Dadd ɗinsu ya fasa zuwa yau sai gobe, idan an kirasa ba'a samu.
A she da gangan yayi masu haka yana son yayi surprise ɗinsu, ya hana Fu'adh ma ya faɗa masu gaskiya.

Juhainah ce a parlour gun Maah sai Papa.
Sanye take da jeans sai riga baƙa rigar ta ɗan sauka zuwa guiwa ta mata masifar kyau, ɗan cikinta ya fara fitowa.
Dogon gashinta ta masa kamun gefe.
Book ɗin da yake hannunta ta ajiye akan ciyar Maah ta miƙe.
Maah tace.
"Ina zaki Autah?"
A hankali tace.
"Maah zan fita compound na shaƙo ƙamshin iskar Damina tunda ruwan yaƙi zuwa Wlh daɗi take min"

Maah tace.
"Kanki ba hula Autah?"
Bedroom taje ta ɗauko hula Ja mai kyau ta saka ta ɗaura igiyar rigarta tsaf ta fice.

A hankali take tafiya tana taɓa cikinta tana faɗin.
"Ni wannan ƙibar da taƙi fitowa a jiki sai aciki haushin da take bani, Surayya har dariya take min, wai nayi kyau"

Yah Boss ya hangota lokacin da yake fitowa daga cikin mota.

Rumfar hutawa ta shiga iska na kaɗawa ga ƙamshin furannin da yake kaɗawa.

Zama tayi ta buɗe wayan Maah da ta ɗauko ta ɗora ƙafafuwanta akan Table ɗin gabanta ta fara Game, na tseren motoci.

Sosai ta shagala da Game ɗin taji fitinannan ƙamshin Yah Boss ya daki hancinta.
Cak ta tsayar da Game ɗin, tana lumshe idanunta sai hawaye, dan ta san ƙamshin ne da ta haddace a hancinta yake mata gizo.
Bayan haka ma fushi take da shi ko yazo ba ruwanta da shi.
Yah Boss a hankali ya tako a hankali har cikin rumfar a hankali ya furta.
"Assalamu alaikum Aunty Bilkisu?"

Juhainah ta buɗe dara-daran idanunta tana sauke idanunta akansa.
Wani irin abu taji ya daki zuciyarta, wani fitinannan kyau yayi ya ƙara canzawa, komai na yayanta ya ƙara hawa, darajar sa ta hauhawa.

Idanunta ta rufe ta saki siririn kuka.
Da mamaki yake kallonta.

A hankali cikin zazzaƙar muryansa ya furta.

"You're not happy that I'm here?"

Banza ta masa, tana kukan a hankali ta miƙe tsaye bata yarda ta kallesa ba, ta fara takawa zata bar masa rumfar.

Ƙurawa cikinta ido yayi da ya fara fitowa, kallo ɗaya zaka mata kasan tanada cikin haihuwar ɗan mutum.

Zama yayi a anutse akan kujerar da ta tashi.
A hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Bilkisu! Zo zauna Karki kuskura ki tafi"

Ƙin sauraron sa tayi ta saka kai ta tafi ko waiwaye.
Miƙewa yayi cikin zafi nama ya bita taku uku ya sha gabanta.
Kanta ta kawar tana kuka ta raɓa ta jikinsa zata wuce, Sbd flowers sun tare hanyar.

Da sauri ya riƙe hannunta ya janyota jikinsa a hankali yadda cikinta bazai takura ba. A hankali cikin zazzaƙar muryansa cike da izzar da ya ƙaro can ƙasa ya furta.

"Calm down, Aunty J. I realize I wronged you. Alright, the crying is enough I'm sorry, my sister. Look at me, let's talk."

Ya ƙarasa maganar da wani irin sauti mai tayar da tsikar jiki.

Ya riƙe kyakkyawar fuskarta da tafukan hannunsa.
Ai kamar zata sume masa taji, Sbd wani irin fitinannan kyau da kwarjini da ya ƙaro da sauri ta rufe idanunta.
Wani irin kuka ta sakar masa tana dukan ƙirjinsa tace.
"Ni ka sakeni ba ruwana dakai da gaske nake na fita a sabgarka, babu wata magana kuma."
Numfashi taja cikin tsiwa tace

"Four months ago, I didn’t die.

Ai da mutuwar zan yi da na mutu, ko Ni ba jinin ka bace ka tuna dani cikin wata 4 harda kwanaki.
Ka sakeni ko nayita kuka har zuciyata ta ƙarasa bugawa, kowa ya huta tunda daman ba ƙaunata ake ba.."

Yah Boss ya Saketa a hankali bai ce komai ba, ya bata hanya ta wuce.
Da gudu ta bar gun tana kuka mai cin zuciya, kamar ta koma ta shiga jikinsa takeji amma haushin sa take ji ba kaɗan ba, da wani ne yau wani irin dukan huce takaici zata masa.

Hannayensa ya zuba cikin aljihun Suit ɗinsa, anutse yana takunsa.

Tana shigowa parlour bata tsaya ba ta wuce bedroom ɗin Maah.
Maah da Papa suka bita da kallo suna mata magana tayi banza da su.
Tana shiga bedroom ɗin Maah ta murza key....
[02/04 14:43] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

_💃🏻Masoyan JUHAINAH Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kadan-kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books Ɗina, A Channel Ɗin. Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku._

*Page 51*

Cikin nutsuwarsa ya shigo parlour bakinsa ɗauka da sallama.
Maah da Papa suka amsa cike da mamaki Maah tace.
"Abbah! Saukar yaushe? Muda akace mana sai gobe? Wai daman kaine Autah take wa wannan gudun?"
Anutse ya zauna kusan Papa yana gaishe su cike da girmamawa.
Suka amsa Papa yace.
"Abbah! Ya gajiya? Sannu da zuwa ai mun ɗauka sai gobe? Ma sha Allahu sannu tafiya ta amshe ka an ƙaro kyau"

MAAH tayi dariya tace.
"Wa ma ya sani ko tsoro yaba Autatah"
A hankali ya furta.
"Alhamdoulillah! Papa MAAH fatan na sameku lafiya?"

Suka amsa da.
"Lafiya lau Abbah"
Maah tace.
"Bari na kira yaran nan"

Yah Boss yana kallonta ya furta.
"A'a Maah ki barsu zanje da kaina.
Bilkisu rigima takeji kuka ba dalili daga ganina"
MAAH tace.
Ai fa ta canza ba kaɗan ba, laifinka ka san shi ma, tunda ka tafi baka neme ta ba Abbah."
Ɗan ƙaramin murmushi ya saki a hankali ya furta.
"Maah a barta ta nutsu yanzu bata son ganina. Bari na dubo my Babies."
Ya ƙarasa maganar yana miƙewa anutse ya nufi hanyar Stairs.

Juhainah kuwa tana shiga bedroom ɗin bayan ta rufe ta haye bed tayi kwanciyarta.
Tasha alwashin yau bazata buɗe masa ƙofar ba, sai dai ya gaji ya tafiyarsa.



Surayya dai-dai wannan lokacin tana gidansu kwance a bedroom ɗinta, bacci sama-sama Ya fara satarta saboda gajiyar da tayi, gidan Wasila yayarta ta wuni.

Cikin bacci taji ringing ɗin wayarta.
A hankali ta buɗe idanunta tana jan tsaki, ganin number babu suna.
Kamar bazata ɗauka ba, sai dai ta ɗauka tana dab da yanke wa.

A Handsfreeta ta sakata tana komawa ta kwanta, batayi magana ba.
A hankali cikin zazzaƙar muryansa yayi sallama.

Surayya da mamaki ta miƙe zaune tana murza idanunta, kamar a mafarki take jin muryan Yah Nasir.
Tsabar ta gigice ta manta bata amsa Sallamar ba, take famar murza idanunta.
Cikin masifa yace.

"Ke ƙanwar marar mutunci kin samu an kira ki ma kike rainawa mutane hankali? Ke kafirace da ana miki sallama bazaki amsa ba?"

Surayya cikin tsiwa tace.
"Dalla Malam dakata! Nafa gaji da cin fuska, idan yayana yayi cin mutunci Ni nayi? Ko yanzu an isa a ƙanƙare jinin da suka haɗa?
Allah gaban nan idan kamin sai na rama tunda baka garin, in ka dawo ka kasheni, haba dan Allah meye haɗina dakai, bayan kai yayan Aminiyata ne, kuma wadda zamu haɗa zuri'a dasu, kabi ka tsangwami rayuwata, wata kusan biyar hankalina kwance ba wanda ya dameni sai yau zaka ɗaga min hankali"

Nasir yace.
"Ni zaki yiwa rashin kunya dan bana kusa ko? Zan baki mamaki wallahi Surayya zaki san Abdulnasir ba sa'anki bane."

Baki turo gaba tace.
"Anje anyi rashin kunyar naci bulus kafin kazo nayi aure, baka isa ka taɓa matar mutane ba, idan ka sake kirana sai na faɗawa Aunty Hanifah ince kace kana sona..."

Lumsassun idanunsa ya zaro, yana ciro handkerchief daga aljihunsa yana goge hancinsa Sbd mura yake.

A hankali yace.
"Kin haukace a soyayyatah shiyasa zaki faɗa mata hakan, ai nine mijin ita matar"

Surayya ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Oho muku dai, kana sake kirana sai na faɗa mata"

Nasir yace.
"Ranan da kika faɗa sai kin zama matata da izinin ALLAH, na koya maki hankali, azabar Hanifah ma kaɗai ta isheki, ƙwaila kawai, baki fita daga fitsarinki ba amma kina son maza ko?"

Takaici ya saka Surayya ta fashe masa da kuka tana faɗin.
"Wlh nafi ƙarfin ka kirani da ƙwaila, aka yiwa Aunty J aure ma tayi ciki bare Ni..."

Sai tayi sauri ta canza maganar sam ta manta ta saki layi.

"Ai dai Wlh Ni ba ƙwaila bace kafin ka dawo zan baka mamaki aure zanyi"

Tsaki yaja a hankali ya furta.

"Wlh kina aure kafin inzo ya tabbata ke ƙaramar cikin ƙwailaye ce, kuma kin bada mata, mace cikakkiya itane ta tsaya tayi ilimi mai zurfi kafin aure"

Shiru tayi tana sauraron sa har ya gama bayanin.
A hankali tace.
"Ni dai sai nayi auren nafison nayi Ɗa da wuri irin na Aunty J"

Nasir ya ciza lips ɗinsa na ƙasa a hankali yace.
"Oh! Toh zo ayi kwangila mana, idan kin amince, amma ki bari sai na dawo"

Surayya tace.
"Wace irin kwangila kuma Yah Nasir?"

Nasir yace.
"Au ashe ni yayanki amma kika min rashin kunya yanzu?"

Baki ta turo tace.
"TOH bakai ba ne"

A hankali yace.
"Ni me?"

A hankali tace.
"Ka matsa min mana, ko tausayi na bakaji. Wace kwangilar zamuyi?"

Ɓoyayyen murmushi yayi a hankali yace.
"A'a ki daina auren da zakiyi idan nazo zan faɗa maki kwangilar"

Cikin shagwaɓa tace.
"A'a ni dai gaskiya ka faɗa min yanzu inda da rabi sai ayi"

A hankali can ƙasan maƙoshi yace.
"Akwai riba mana, ɗan da kike so zan baki"

Idanunta ta zaro tace.

"A'a gaskiya nafi son na haifa da kaina"
Chapter 100 · 0% Book details