← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 113

Sashe 59

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya furta.
"My Suhaima! Zaki koma ɗakinku ki kwana da hajjah Mama da My Amiin"
Kamar zatayi kuka tace.
"Please My Dadd zan kwana da Aunty J"

Yah Boss ya girgiza kansa yana sanya tattausan hannayensa ya ɗauki Suhaima cak ya sauketa yana kama hannunta yana faɗin.
"Please ki barta ta huta ita da Khairat zasu kwana."

Ba yadda Suhaima ta iya ta amsa da.
"Toh Allah ya bata lafiya."

A hankali ya furta.
"Ameen My Babie"
Hajjah Mama ta biyosu.
A bakin ƙofa suka haɗu da Khairat zata shigo.
Yah Boss ya kalleta yana faɗin.
"Kin sha maganin?"
A hankali ta amsa da.
"Eh"
Wucewa yayi yana faɗin.
"Ki nutsu Khairat babu abinda zata miki in sha Allahu"

Kai ta jinjina tana shiga tana ɗagawa Suhaima hannu alamar bye-bye.
Itama Suhaima ta ɗaga mata hannunta.

Sai da safe Yah Boss ya sake yiwa Hajjah Mama ya shiga parloursa ya rufe ƙofar.
Suhaima ma rufewa tayi zuciyarta agun Aunty J, haka ta kwanta tayi wa Al'amin addu'a itama tayi ta kashe ƙwayayen ɗakin masu wani irin kyau kala² ta kunna ƙwan gefen Bed ɗinta ta kwanta.
Hajjah Mama ta kwanta tana addu'a.

Yah Boss dole shi ya gyara gun da Juhainah tai amai tsaf kamar mace, Sbd ganin Khairat kamar sosai take jin bugun da Juhainah tai mata.
Yana idarwa ya saka turaren wuta a parlour ya wuce bedroom ɗinsa, wanka yayi ya fito ya murza body lotion ya saka kayan bacci masu taushi ya fesa turare ya kashe duka wayoyinsa Sbd yana son bacci da wuri, kansa ciwo yake Sosai.
Anutse haye faffaɗan Italian bed ɗinsa yaja lallausan quilt ya rufe lafiyayyan jikinsa zuwa ƙugunsa yana lumshe lumsassun fararen kyawawan idanunsa.
Anutse a hankali ya fara karanta addu'o'in bacci...
[09/02 14:15] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Masoyen Juhainah Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kaɗan-Kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books ɗina, A Channel ɗin.
Wanda Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku.💃🏻

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 32*

Su Zarah su na baza ido wai ko Yah Boss ya shigo inda suke ko dan darajar Inna Laure, amma shiru babu labarinsa. Dan shi har ga Allah ma bai san akwai dattijuwa acikin su ba, tunda bai wani kallesu ba.

Har kusan 11 na dare suka ga ba Sarki sai ALLAH, suka miƙe su ka shiga ciki domin kwanciya.
Bayan kowa yayi shirin kwanciya, Zarah na kwance saman bed ta kalli Ramlah tana faɗin.
"Don Allah Ramlah kiyi haƙuri nasan ranki ya ɓaci sosai da abinda akai maku a cikin gidan nan, Wlh wlh bansan lamarin zaiyi zafi har haka ba, nazaci zan samu karramawa, koda daga dangi na ne, ya basu girma ya nunawa duniya ni ɗin matarsa ne koda baya sona amma Kashhh! Sai ya shayar dani giyar mamaki.
Matsalar yanzu bazai yiyuwa ba na kashe auren nan zan haƙura na zauna koda watanni ne ko shekara har na kawar da hankulan mutane Sbd bakin duniya..."
Ta ƙarasa maganar tana zubar da hawayen takaici da baƙin ciki.

Yaganah tace.
"Hummm! Ai Wlh koda ace duniya zata kalleni da abin kunyar da bata yi ba a duniya ba, Nidai Wlh da nice yau sai bar masa gidansa, Allah ya sani koda shugaban ƙasane a yau ni bazan ɗauki wannan cin fuskar da ya miki ba, duk da nima an dizga ni"

Azizah ta taɓe baki batace komai ba Sbd takaicin Zarah da yake cikinta.
Ramlah tana kallon Zarah tace.
"Ok daman ya faɗa maki baya sonki bazai iya zama dake ba, kika bari akayi auren? Ba Matsala tunda kina sane sai kici haƙurin iya yadda zaki iya, Ni dai Wlh gobe idan rana ta fito ina gidan nan TOH fa ba zatayi zafi ina cikinsa ba, aganina mutunci da daraja sunfi ƙyale-ƙyalin banza, kalli kallon tsana da ƙyama da ƴarsa tai mana ɗazu..."

Inna Laure tace.
"Yanzu dai don Allah duk mubar maganar nan tunda abinda zai faru ya rigada ya faru, idan karatu ne ma yanzu ai zatayi ta gane ba kowane namiji bane yake iya jure tunkaro abinda baya so"

Zarah dai ba wanda ta sake yi wa magana sai hawaye take yi, Tabbas sai ta san yadda tayi kafin tabar gidan tayi duk abinda zatayi sai commissioner of police A.Y.A Janfar ya kwanta a ruwan cikinta, ta nuna masa duk yadda kake mace ta fika shu'umanci, dan auren ya fice a ranta, amma bazata fita a One Zero ba...


Washegari
Har gari ya waye Juhainah bata farka ba.
Amma Khairat ta sha cakuma Sbd kusan ajikin Khairat ta kwana, Sbd yadda ta ƙamƙame Khairat tana baccinta.
Haka Khairat ta jure tunda ba shegun bane.

Yah Boss
Yana fitowa daga sallar asuba ya nufi ɗakin gyam ɗinsa, ya cire jallabiyar wasu haɗaɗɗun kaya na motsa jiki farare kala² yake dasu, dasu yake gyam.
Sanye jikinsa sunyi masa kyau, cikin nutsuwarsa ya fara motsa jikin nasa hankali kwance.

Tsawon mintina talatin kafin ya gama ya sauka ya ɗauki towel ya goge gumin da ya sauka a dukkan jikinsa ya ɗauki jallabiyarsa, ya maida jikinsa, ya fito yana ƙoƙarin nufar Stairs.
Ido 4 sukayi da Zarah bisa tsautsayi ta fito zata nufi kitchen, tana son dafa tea Sbd jiya bata iya cin Komai ba.

Idanunsa ya kawar yana takunsa a nutse, ya nufi hanyar Stairs.
Wani yawu mai zafi Zarah ta haɗiye.
Wani kyau ya mata yadda yake takunsa, da tsayinsa da zubinsa ba kowane namiji yake samu ba, ga jikin mazantaka.
Ƙamshin sa ya mamaye hancinta.

Kasa jurewa tai ta bisa da gudu bata tsaya ɓata lokaci ba ta faɗa jikinsa faffaɗan bayansa ta rungumeshi tana zagaye hannayenta saman faffaɗan ƙirjinsa.

Ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanunta, ta saki sirirn kuka tana sake ƙamƙameshi, hannayenta saitin nipples ɗinsa.
Yah Boss wani irin takaici ya kamasa da wani irin sauti ya furta.

"I don't want, Wlh na tsani irin wannan turaren naki.
Ke! Lafiyarki kuwa? Sakeni kar na jefar dake, ashe lokacin ma da wuri zai zo, amma kika taɓa min lafiyar ƙanwata.

Marin nan hukuncin ki shi ne zaki tsani zaman gidan nan da kanki ki nemi saki, duk da dama na faɗa maki kika nace, banda alhaki, bayan haka bazan ko kalli waɗanda suka kawoki ba, bare su saka ran zan masu magana bare sannu, tunda har suna da izzar iya ɗaga hannu su mari ƴar masu gida, basa tunanin me zai biyo baya, hakan ya nuna basuda mutunci da kawaici, ina baƙo ina faɗa daga zuwa guri."

Ya ƙarasa maganar yana sanya hannunsa ya finciketa daga bayansa, yana tsayar da ita da ƙafafuwanta, baice uffan ba ya juya yana taku biyu ta sha gabansa tana tare masa hanya.
Baki ta buɗe cikin tsananin ɓacin rai take ƙoƙarin magana, amma suna haɗa ido yanayinsa ya faɗar mata da gaba, yayi mata mugun ƙwarjini, sai guiwarta tayi sanyi, ta gaza aiwatar da ƙudirinta, sai hawaye ta kamo tattausan tafin hannunta tana riƙewa cikin nata, kanta ƙasa ta siɗaɗa ta shige jikinsa tana kwantar da kanta lafiayyan ƙirjinsa, mai fitar da wani irin ƙamshi, ta sakar masa kukan takaicin gaza masa tijara da tayi niyyar yi.

Yah Boss baƙin cikin mannawa jikinsa da take ya kawo masa wuya amma Sam shi baya son nuna fushinsa a gun da bai dace ba, halinsa ne ɓoye fushi, ko magana zai gatsa maka ba cikin faɗa yake gatsa maka ba.

Janyeta yayi daga jikinsa bai ce uffan ba yay hanzarin barin gun yadda bazata ma iya cinmasa ba, ya fara taka Steps Anutse.
Da kallo ta bisa jin sonsa take kamar zata haɗiye zuciya a yau bata sani ba, ko ɗan ta rungumeshi ne abin ya ƙaru.
A hankali ta nufi kitchen kamar ƙwai ya fashe mata cikinta, tana saka aranta zata bawa Juhainah hƙr ko zai rage fushin da ita.🤔

Ƙofar su Khairat ya ƙwanƙwasa.
Khairat tana zaune tana duba Books ɗin, makaranta tunda tayi sallah bata kwanta ba.
A hankali ta miƙe ta fito tazo ta buɗe masa.
Ganin Yah Boss ne ta matsa ta basa hanya tana gaishesa.

Anutse ya amsa yana zuba hannenysa cikin aljihun jallabiyar jikinsa.
Fuska a kame a hankali cikin zazzaƙar muryansa ya furta.
"Khairat! Ya jiya an samu damuwa ne?"

Khairat tace.
"A'a my brother normal tayi bacci amma sai dai ni ko motsin kirki banyi ba, jikina ta kwana tana juyi"

Kallonta yay ba wasa yana sake kame fuskarsa ya furta.
"Ok ƙanwarki bata da lafiya jikin wa kike son ta kwana idan ba jikin ki ba? Kenan ta takura ki jiya Khairat?"

Khairat ta girgiza kanta tana ɗaga hannuta tana faɗin.
"A'a kayi haƙuri ba haka nake nufi ba my brother, kamar ina gaya maka iya abinda tai kenan a daren jiya."

Yana tafiya ya nufi bed ɗin ya furta.
"Tayi sallah?"

Khairat tace.
"A'a Wlh nayi ta tayar da ita taƙi tashi"

Bai ce mata uffan ba ya isa bakin bed ɗin ya zaro hannayensa, ya ranƙwafo yana bugun pillow'n da kanta yake sama ya buga a hankali ya fara kiranta.

"Bilkisu! Ta shi maza kiyi sallah"

Shiru bata motsa ba, quilt ɗin da take rufe yaja kaɗan ya bugi saitin hannunta yana ɗan ɗaga muryansa kaɗan yana faɗin.
"Hey Juhainah tashi"

Firgigit tai tana zabura ta buɗe dara-daran kyawawan idanunta, da suke cike da gajiya, a hankali ta sauke su akan kyakkyawar fuskarsa.

Ido huɗu sukayi ya kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa a kanta.

Da sauri ta lumshe dara-daran kyawawan idanunta.
A hankali yanayi na musamman wanda ya kawo mata farmaki ba tare da ta shirya ba tace.
"My brother Habiby, I'm sorry"
A hankali ya furta.

"Look at my eyes Juhainah"

A hankali kamar zatayi kuka tace.

"Yah Sadeeq bana iyawa idona zafi suke"

A hankali ya furta.

"Juhainah! How are you feeling now? Miƙe ki zauna kuma ki buɗe idanunki ni maye ne cinyeki zanyi."

Da sauri ta miƙe zaune tana janye quilt ɗin jikinta, tana girgiza kanta tace.

"A'a ai bana jin komai yanzu sai yafiyar ka nake so.
My Brother, please forgive me,
Wlh na fasa rashin ji daga yau, zan riƙe bakina"
Chapter 59 · 0% Book details