Sashe 13
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aunty Sumy kyakkyawar gaske suna tsananin kama da Yah Boss, har dimple ɗinsa irin natane, kana kallonta kasan ƙanwarsa ce.
Idanunta ta zaro tana dafe ƙirjinta tana faɗin.
"Ya Allah! Oh! Ni Sumayya Yakubu Abubakar Janfar, Wlh yau dai kam da na iske ta gidan nan sai na mata tsinanan duka, wanda Yah Sadeeq bai taɓa mata irinsa ba, saboda iskancin Juhainah ya yi yawa, duka² nawa take har take maganar aure take so bata son karatu, wai auren ma shuga daddy innalillahi.
Shi kenan yanzu auren zai mata ko ya? Bari na kira Yah Sadiq naji."
Ta ƙarasa mgnar tana amsar wayanta a gun Sadiq ƙarami yana Game.
Kukan shagwaɓa zai fara mata ta zaro masa ido tana faɗin."Dadynka mai sunanka fa zan kira."
Ai kuwa cikin murna ya haye kan cinyarta yana jin daɗi.Number Yah Boss danna wa kira wadda take special tasan garantie tana hannunsa.
Lokacin yana tare da baƙi har mutum 3 a ofishin sa, ganin sunan Sumayya ya saka shi ɗaukan wayan wayar tare da picking Call ɗin, yakai kunnensa, lokacin ta masa sallama.
A nutse cikin kamewarsa ya amsa sallamar yana furta.
"Yes Sumy inaji."
Sumy tace.
"Yah Sadiq ina wuni? Ya haƙuri ashe Juhainah ciwon kai ta saka ma yau? Don Allah Yah Sadiq karka sassauta mata, Wlh kai kaɗai zaka mana maganinta, shegiyar yarinya mai taurin kan tsiya, don Allah karta dawo nan ta zauna can hannunka har ta zama mutum..."
Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya ɗan lumshe na Seconds biyar ya buɗe, a hankali ya furta.
"Sumy! Ina tare da baƙi zan kira zuwa dare, ki shafamin kan Sadiq bye."
Yana ƙarasa mgna ya katse kiran, yana maida hankalinsa Wajan baƙin nasa.
Sumy tana masifa tace.
"Ina dalili ta sakamin ɗan uwa cikin damuwa, Wlh har yanzu bai sauka daga fushin da ta saka shi ba, Allah yasa ya haɗa ta da tsoho ma auren ƙarshen shuga daddy.
Maah anya Yah Sadiq bazai mata hukunci mai tsauri ba, kinji yadda muryansa take."
Maah ta ɗaga kafaɗarta tana faɗin.
"Ina na sani Sumayya wannan yarinya tafi ƙarfina sai addu'a Autah batajin magana."
Khairat ta gyara zamanta tana faɗin.
"Wlh Aunty Sumy na taɓa kamata tana irin wannan mgnar, ita da Surayya ƙawarta, basu aiki sai hira maza kuma manyan maza suke so, dan Surayya Yah Sadiq ne take mutuwar so, nace aiki ya sameta ta nemo mijinta tun dare bai mata ba, mai zai yi da ƙaramar yarinya."
Maah ta watsa mata hannu tana faɗin
"Ungo nan Khairat! Nace ungo nan, me yasa kinsan tana irin wannan hirar baki taɓa faɗa min ba ko ki faɗawa yayan naku?"
Khairat tace
"Haba Maah ko na faɗa ma ƙaryatani zakiyi, da safe ma ba na faɗa maki ƙaryar rashin lafiya take ba kika ce na mata ƙarya, sai ga shi Allah ya tona mata asiri ko wuni ba'ayi ba."
Maah tace
"Wlh nazata batada lafiyar ne Khairat! Amma ai yanzu kam shi kenan dan nasan da wuya ya barta ta dawo gidan nan, ni Allah yasa ma sanadi hakan yayi aure ya riƙe ta a can ɗin.
Ita yanzu Surayya ganin da nake mata sintirin da take gidan nan wajan Autah, Abbah take so? Ta ɗauko ruwan dafa kanta, manyan matan ma yaƙi bare wannan ƴar cikin tasa."
Aunty Sumy ta taɓe baki tace
"Ai kam Ni bata min ba, bana son macen da bata ɓoye maitar namiji, ita yarinya ƙarama tace sai babba, babban ma da aka san yanada masu gidan rana."
Maah tace
"Allah ya kyauta, ai Papa Ku nake jira ya dawo nayi masa bayani a nuste kamar yace zai takura Abbah ya maido Juhainah tunda bata jin magana"
Aunty Sumy tace
"Ai kuwa Maah haka yafi, nima zan kira Papa."
Al'amin ne ya shigo falon da sallama yana jifa da school bag ɗinsa ya nufo gun Aunty Sumy yana washe baki yana faɗin.
"Oyoyo Mom."
Aunty Sumy ta janye Sadiq daga jikanta tana ware masa hannayenta tana faɗin.
"Oyoyo my son har kun taso ina Babyna Suhaima?"
Da gudu ya faɗa jikinta yana dariya harda kiss a kumatu.
Itama rungumeshi tayi tana sumbatar goshinsa.
Suhaima ta shigo falon goye da school bag ɗinta tana sallama a hankali.
Kallonsu tayi tana faɗin.
"Momy ina yini, Maah sannu Aunt Khairat sannu."
Tana gama faɗin haka ta nufi hanyar stairs.
Aunty Sumy ta washe mata baki tana faɗin"
Lafiya lau my love zo mana naji dominki, kin gaji ko?"
Juyowa tai tana zubawa Aunty Sumy fararen lumsassun idanunta irin mahaifinta sak, ta tako a hankali tana isowa gun Aunty Sumyn ta zauna tana kwantowa jikinta kaɗan batace uffan ba.
Aunty Sumy tayi murmushi tana shafa kanta sumbaci goshinta tace.
"Jini ba ƙarya ba my love."
Maah tayi ƴar dariya tace
"Suhaima ai kam haka Allah yayi su ita da mahaifinta, Suhaima zakuci abinci? Ko Madara za'a dafa?"
Suhaima ta ɗaga kanta tana faɗin.
"Sai da zamu shiga ajin islamiyya ne ma nayi lunch zan sha madara dai.
Momy zanje nayi wanka sai na fito."
Ta faɗa tana miƙewa ta shafa fuskar Sadiq tace.
"i love you My Dad."
Sadiq yayi murmushi yana kama hannunta yace."
Aunty Suhaima zanje ɗakinku nayi wasa."
Bata ce masa uffan ba ta kama hannunsa suka fara tafiya.
Aunty Sumy kamar zata yi kuka tace.
"Ya Allah ka haɗa Yah Sadiq da mace ta gari wadda zata so ya'yansa tsakani da Allah."
Da sauri Suhaima ta juyo fuskarta haɗe tana zuba wa Aunty Sumy idanunta.
Aunty Sumy tace
"Kiyi haƙuri Suhaima Aunty Khadija ta samu mutuwar shahada, kinason Dad ɗinku yayi ta zama babu mace?"
Hawaye ya ciko a idanun Suhaima ta juya ta nufi stairs.
Yarinya ce Suhaima amma Allah ya saka mata kishin mahaifinta, gani take duk wadda ta auri mahaifinta zata rabata da shi, kuma ma sanadin auren nata ne suka rasa mahaifiyarsu, dan da mahaifiyarsu na raye zai yi wuya Dad ɗinsu ya ƙara wani auren.
Maah tace
"Ameen ya Allah Sumayya, kullum addu'ar da nake masa a matsayina na mahaifiyarsa, da safe Harɗo sunyi fira da Haj Bilkisu, shi kuma alamun nasa bayada niya, Allah ya jiƙan Khadija, Suhaima yarinta take damunta, da zaran ta samu macen kirki tana kula dasu zata fasa ƙiyayyar."
Aunty Sumy tace
"Ameen ya Allah, Maah! Wlh matan ne na yanzu kafin ka samu masu sonka tsakani da Allah idan dai Kanada dukiya kamar Yah Sadiq sai ansha wuya kake samun mace tagari, ga shi Suhaima za'ayi fama da ita kafin taso matar da Yah Sadiq zai aura.
Bari na sameta na lallaɓata, banson ganin hawayenta."
Khairat ta miƙe ta bita tana faɗin.
"Bari na sameta Aunty yanzu ta warware in sha Allahu."
Aunty Sumy ta bi bayanta dan su lallaɓata tabar kukan, da basa son ganinsa a idanunta...
★
Unguwar
Dou Girei Ammar tun bayan da ya katse kiran da yayi wa Juhainah, ya faɗa albarkacin bakinsa, ya fito parlon su Mom ɗinsa da Dady ɗinsa suna zaune, kasancewar daga tafiya Dady ya fito, akwai gajiya a tare da shi, shiyasa yake hutawa.
Kana kallon Dady Najib kasan cikakken bafulatani ne, fari ne mai kyau ga nutsuwa ga addini, mutum ne mai faran-faran da jama'a, ƴaƴansa huɗu ne Ammar shine babba sai Hisham Zara'u Nabila ce Auta, Ammar yanada shekaru 28 Hisham 25 Zara 20 Nabila 15, suna son junansu ma sha Allah.
Dady Najib nada arziƙi ma sha Allah dai-dai gwargwado, babban ɗan kasuwa ne, yana fita ƙasashen waje sosai, Alhj Najib yayi suna ba laifi, duk da ko rabin ƙafar commissioner Abubakar Y A Janfar bai kama ba, amma shima yanada kuɗi sosai.
Kasancewar sa ɗan kasuwa Shiyasa ya zaɓi Ammar ya ƙaranci ɓangaren business, a University yana kammalawa ya ɗorasa a harakar kasuwanci, mafi yawa tare suke fita ƙasar waje, ko watarana Ammar ya tafi shi ya tsaya, wataran kuma Dady ya tafi Ammar ya tsaya, haka suke yi.
Ammar kyakkyawane fari mai matsakaicin tsayi, yanada ɗan kauri, ma sha Allah tsaye yake namiji sosai.
Sai dai Ammar yanada wani hali a ɓoye da giyar kuɗi take ɗaukansa da kuma farin jinin da yake da gun ƴan mata, sai hakan yayi tasiri da kuma ƙuruciya, wanda har yau iyayensa ko ƴan uwansa basu san yanada wannan halayyar ba, tabin mata, da ɗan taɓa shaye². Yana taka tsantsan saboda Dady Najib yanada mugun zafi, baya yarda da shashanci ko gurɓacewar tarbiyya ya'yansa, saboda ya tsaya masu sosai.
Ammar ya fara haɗuwa da Juhainah ne agun auren Lawisa yayar Surayya ƙawarta, shine babban abokin ango, awajan dinner suka haɗu shekara ɗaya yanzun.
Da farko bata kulasa ba baya fasa fuska, amma kyan halinsa da ya nuna mata da bata wata irin kulawa da soyayya mai tsafta da yake nuna mata hakan ya saka taji ya ɗan kwanta mata, sai dai ta faɗa masa gidansu ba'a barinta fira, zasu dinga chatting da kuma waya, lokaci-zuwa-lokaci sai su dinga haɗuwa gidan Lawisa da yake gidan abokinsa ne, haka kuwa aka yi ta haka ne soyayya mai ƙarfi ya shiga tsakaninsu, Juhainah ma babu wanda ya sani gidansu dan tasan Yah Boss na kamata kashinta ya bushe.
Ammar yana sonta son aure, saboda ita duk ya watsar da ƴan matansa, sai masu naci da suka ƙi rabuwa da shi saboda yadda ya iya kwanciya da mace da iya romance na fitar hankali.
Tunda Ammar ya samu Juhainah yake jin babu wata mace da zai kuma so a rayuwarsa, sai dai idan jarabarsa ta motsa zai je gun marasa kamun kan ya kashe wutarsa ya ƙara gaba, shaye² man ya rage sosai, duk da daman a ɓoye yake yi, mafi yawa ma idan baya ƙasar yafi shan abinda yake shan.
Kamar an jefo mutum daga sama suka ga Ammar hannunsa ko ina jini yake fitarwa.
Cikin tashin hankali Haj Maimuna ta miƙe tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna alaihir raji'un! Me zan gani Ni Maimuna? Kai Ammar? Mi nake gani haka?"