← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 113

Sashe 11

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rinannun idanunta ta buɗe a hankali tana kallonsa batace uffan ba, ta miƙe zaune, tana yamutsa fuska.
Jamilu ya juya ya tafi.
A hankali ta miƙe tana tafiya daƙyar ta nufi dining room ɗin, sosai take jin zazzaɓin.
Kujara taja ta zauna ta zubawa abubuwan da suke jera akan dinning idanunta masu kyau, Chips kawai taga zata iya ci.
Shi taci ta haɗa tea madara tafi komi yawa sai da yayi kauri ta ɗaga cup glass ɗin takai bakinta.
Sai da ta shanye tass ta ciro tissue ta goge bakinta ta miƙe tana hucin zazzaɓi ta dawo parlon.
Ko gama kwanciya akan Chair ɗin batayi ba, Fu'adh ya shigo parlon.
Anutse ya iso gunta yana faɗin.
"Kinci abincin?
Kai ta ɗaga ba tare da tayi magana ba.
"Ok ga maganin kisha kinsan kuma Sir duk inda yake yana ganin abinda yake faruwa gidansa ta wayoyinsa."
Jin hakan ya sakata miƙewa zaune batayi magana ba.
Da kansa ya ɓallo mata magungunan, dana ciwon kai zazzaɓi rage zogi kala uka ya bata masu tsada ne sosai.
Amsa tayi a hannunta tana kallonsu gabanta na tsananta faɗuwa ta tsani shan magani.
Gorar ruwa marar sanyi ya ɓalle mirfin ya beƙa mata, ta amsa kamar zata fashe da kuka.
Kai ta ɗaga sama ta zuba maganin cikin maƙoshinta ta ɗora gorar ruwan ta fara zubawa tana haɗiye ruwan, sai da ta tabbatar maganin ya shige cikinta ta janye gorar ruwan tana ajiyesa saman Centre table ɗin da ya gajiya da haɗuwa, komai nasa glass ne, ƙaton gaske.
Ta shiga maida numfashi.
Fu'adh ya beƙa mata Hempvana cream, yana faɗin.
"Ki tashi kije ki shafa a laɓɓanki da fuskar ki, da ƙafarki inda kikaji ciwo, sai ki kwanta ki samu hutu, in sha Allahu normal zaki farka.
Yace ace maki keys ɗin bedroom ɗin Babies na ɓangaresa a bedroom ɗinsa cikin drawer."
Bata ko kallesa ba kamar shine ya naɗa mata shegen dukan, dan duk haushin wanda suke tare ma da shi takeji.Kai ta saka ta tafi tabarsa gun a tsaye.
Murmushi yayi yana girgiza kansa yasan haushin kowa takeji yau ɗin.
Ƙofar fita ya nufa yana amsa waya.
A hankali Juhainah ta dinga taka Steps har ya haye saman benen.
Ɓangarensa ta nufa ta murɗa ƙofar falon ya buɗe wani sanyin ƙamshin daɗi ya daki hancinta.
Komai a tsare falon gwanin sha'awa.
Bata tsaya kalle² ba saboda tana cikin jinya, kuma babu wani abu baƙonta tunda ta sha gyara masa falon.
Bedroom ta nufa ta buɗe ƙofar.
Da picture ɗin Aunt Khadija ta fara cin karo, tana sanye cikin frame.
Tana dariya.
A hankali ta furta.
"Wa ya sani ko shi ya kashet..."
Da sauri ta rufe bakinta da tafin hannunta tana girgiza kanta ta lumshe idanunta tanajin wani iri.
Bata san me yasa ba duk lokacin da zata aibata Yah Boss, zuciyarta bata barinta yin hakan.
Drawer ta nufa ta buɗe ta ɗauki key ɗin na ɗakinsu Suhaima ta fice.
Tsaf alamun yau ma an gyara ɗakin sai ƙamshi yake, beds kowa wanne an gyarasa sabuwar shimfiɗa, kayan wasansu tili².
Bakin gadon Suhaima ta zauna ta cire mayafin kanta gashinta ya baje saboda headband ne ta saka ya tare gashin.
Cream ɗin ta shafa a duka fuskarta, ta shafa a lips ɗin ta shafa a ƙafarta inda takejin zafin.
A take sanyi ya fara ratsa duk gun da ta shafa.
Ac ta kunna ta cire Abayar jikanta tana jan tsaki tace.
"Wlh da nasan idan nayi shigar Brown colour Babu wani sassauci acin uwan da zai min da ban saka ba, na saka abinda naga dama aikin banza kawai."
Ta ƙarasa mgnar tana buɗe wardrobe ɗin Suhaima bata rasa rigar baccin da zata shigeta tunda ba wani abun kirki ne jikin nata ba.
Ai kuwa ta saka wata pink rigar bacci har ta mata yawa tsayin ne dai iya guiwarta.
Saman bed ta faɗa tana shigewa cikin quilt tana rufe idanunta, ko minti biyar bata cika ba sai bacci mai wani irin daɗi da nutsuwa, ga zazzaɓin ya fara sauka har ciwon kan, sai da basu gama sauka ba tayi baccin.


Fu'adh bai samu damar dawowa ɗaukan abincin da za akai ma marar lafiyar ba, saboda uzurin da ya riƙe shi, sai ya turo Walid ya amsa.
Ana sallar la'sar suka tafi Janfar Special Clinic.
Har lokacin da suka je bata farka ba, amma Dr Majid yace masa a kowane lokaci tana iya farkawar.
Zama sukayi saboda idan ya koma bazai samu time ba sbd wani busy na iya ɗaukan hankalinsa.
Ƙarfe biyar dai-dai ta farka bakinta ɗauke da salati, tana kallon room ko ba'a faɗa mata ba tasan asibiti ne tunda gata akan gadon marasa lafiya a kwance.

Zaune ta miƙe tana kallon jikinta tare da faɗin."Innalillahi wa'inna alaihir raji'un! Accident nayi? Allah yasa ba a hannun mugayen nan bane"
Ta ƙarasa mgnar tana duba jikinta tai saurin taɓa gabanta taji babu wata alamar anci fuskarta a gun.
Ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin.
"Alhamdoulillah!"
Norse ɗin da take yawan leƙowa ta leƙo cikin Sa'a ta ganta zaune.
Shigowa tai tana riƙo hannunta tace.
"Sannu baiwar Allah ya jikin?"A hankali ta ɗago kyawawan ƙananun idanunta masu wani irin haske ta kalli Norse tana faɗin.
"Don Allah suwa suka kawo Ni nan? Ya kamfannin su yake?"
Norse tace."Kije ki wanke fuskarki da bakinki ki kwantar da hankalin ki, masu hospital ɗin da kansu ne suka bugeki a mota, babu mai cutar dake anan sai dai kare lafiyar ki."
Jin abinda Norse tace ya sakata sauke ajiyar zuciya tana faɗin.
"Alhamdoulillah!"
Ta faɗa tana taɓa goshinta wanda da alama nan kaɗai taji ciwon.Toilet ɗin ta gwada mata ta shiga.
Ita kuma Norse ta fice dan kiran Dr Majid.

Fu'adh ya kalli Norse ɗin da ta fito daga room ɗin yana faɗin."Har yanzu bata farka ba?"
Norse ɗin tace"Alhamdoulillah ta farka cikin hayyacinta ma zaka iya shiga bari na kira Dr ko zai sake dubata."
Fu'adh yace."Ma sha Allah, thank you."Ya faɗa yana miƙewa ya ɗauki Basket ɗin abincin suka nufi cikin room ɗin shi da Walid.
A hankali suka murɗa ƙofar suka shigo da sallama bakinsu.
Bata fito daga toilet ba.
Kujera suka zauna suna jiranta.
Ƙofar toilet ta buɗe cikin nutsuwarta ta fito, sanye da hijabinta ta wanke gun da jinin ya taɓa.
Kallonsu Fu'adh tayi tana takowa bakin gadon.
A hankali tace."Assalamu alaikum ina yinin ku?"

Suka amsa sallamar da gaisuwan, Fu'adh yace."Ya ƙarfin jikin? Allah ya ƙara sauƙi ya kiyaye gaba."
Zama tayi gefen gadon tana ƙasa da kanta tana jinjina lamarin mutane haɗaɗɗu haka ga kyau ga kuɗi suka bigeta, amma suna nuna kulawa da ita har haka, ashe ba kowasu masu kuɗi bane suke da wulaƙanta talaka?Hawaye taji yana ƙoƙarin gangarowa akan fuskarta, ta ma gaza magana tayi ƙasa da kanta abinda, Hafiz ya mata ya shiga dawo mata, da irin ƙasƙancin da ta gani a gidan da tayi aikatau ɗin.
Fu'adh ganin ta shiga shock yayi gyaran murya yace."Baiwar Allah meye sunanki? Kiyi haƙuri da rayuwa a duk inda kika tsinci kanki, Allah kiyaye gaba."
A hankali cikin muryanta mai daɗi kanta a ƙasa tace.
"Sunana Juhainah, Ameen ya Allah Nagode Allah ya saka muku da alkhairi."

Fu'adh ya ɗan zaro kyawawan idanunsa jin sunanta Juhainah, Walid ma ya nuna mamakin ƙarara har yana faɗin."Juhainah! Allah ya baki lafiya sannu."
Da Amin ta amsa.
Fu'adh yana serving ɗinta Dr Majid ya shigo.Fuska sake yace.
"Ma sha Allah jiki ya warware yanzu me kike ji?"
Ya ƙarasa mgnar Yana isowa wajanta.
A hankali tace."Kasala sai goshina yana ɗan zafi kaɗan."
Dr Majid ya dubata sosai babu wata matsala, yace"Akwai magungunan da zaki sha shima zai warke."
Ya kalli Fu'adh yace
"Sai ka bata Hempvana cream ta dinga shafawa a goshin zai yi saurin warkewa, yanzu idan taci abincin zaku iya tafiya, maganin da na rubuta maka sai ka shiga nan pharmacy ka amsa."
Fu'adh ya ƙarasa haɗa mata tea ɗin ya beƙa mata yana zuba mata abincin yace."Ok thank you Dr Majid, bari na amso kafin ta gama cin abincin."
Ya ƙarasa mgnar yana ajiye mata plate akan ɗan ƙaramin table ɗin da yake gefenta yana faɗin
"Please kici abinci sosai saboda zaki sha magani."
Kanta a ƙasa tace"Nagode Allah ya saka da alheri."Da Amin ya amsa suka fice su duka suna rufe mata ƙofar.
Juhainah ta sauke ajiyar zuciya tana kallon cup ɗin tea ɗin da yake riƙe da hannunta, cup kaɗai abin kallo da birgewa ne, a hankali ta fara shan tea ɗin bata taɓa shan irinsa ba a rayuwarta, ga wata uwar yinwa da takeji, batayi aune ba ta shayen tea ɗin duka, sai kunya ta kamata na shanyewa da tayi.
Ƙananun fararen idanunta ta zuba akan wani irin plate mai kyau fari tass, an cika mata shi da Red beans and rice, sai wani irin ƙamshi yake tashi.
Yawunta taji na tsinkewa, bata ma san lokacin da ta beƙa ɓakin hannunta masu kyawun yatsu.
Spoon ɗin da yake ciki ta ɗauka ta ciko shi ta kai bakinta tare da Bismillah.
Idanunta ta lumshe tana taunawa.
Sosai taci abincin saboda daɗinsa gudun kar ta sake abun kunya ya saka da taci rabin plate ɗin ta ajiye ba dan ya ishe ta ba, saboda ita mutum ce da bata wasa da cikinta akwai cin abinci barin ma mai daɗi.
Tana shan ruwa Fu'adh ya buɗe ƙofar ya shigo da sallama ta amsa tana masa sannu da zuwa.
Fu'adh ya amsa ya beƙa mata maganin yace
"Juhainah! Amsa kisha sai mu tafi, can gida zuwa dare idan Sir ya dawo zai maki ƴan tambayoyi sai mu kaiki gidanku."
Idanunta suka ciko da hawaye takaici da baƙin cikin abubuwan da aka mata agidansu Hafiz ya taso mata, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba tana faɗin,
"Ba nan garin gidanmu yake ba, aikatau ne ya kawoni Yola, ni ƴar jahar Bauchi ne Misau, mahaifina ya rasu sai mamana tana halin jinya dole ne ya sakani fitowa nema ina aika masu kuɗin magani amma..."
Chapter 11 · 0% Book details