← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 113

Sashe 89

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ta ɗaga tana ƙamƙame shi.
Janye ta yayi ya kama hannunta yana faɗin.
"Muje ki tayani wanka ki bani abinci naci, yunwa nake ji sosai Wlh..."

Da temakon ta yayi wanka suka fito ya shirya cikin kayan bacci suka fito parlour suka nufi dinning Table.

Sosai yaci abinci, suna hirasu ta soyayya, suna idarwa suka nufi bedroom suka kwanta rungume da juna.

Nasir bai daɗe da kwanciya ba daddaɗan bacci ya kwashe sa Sbd gajiya, Hanifah ba haka taso ba, taso sai sunyi romance har ma uban gayyar, amma shi ina sam baya ma ta wannan, dan yanada gajiya sosai, kuma tasan halinsa shi Baida haɗama akan mace wani lokacin har sai yayi kwana biyu uku kafin suyi kwanciyar aure, idan ya tada kuma sai ya jera kwana 4 yana tarayya da ita. Komai na Nasir irin na Yah Boss ne.
Dan shi ma haka halinsa yake, Baida haɗama akan mace bai zaƙewa, duk haɗamarki Yah Boss in yayi 1 zai gamsar dake.


Washegari

Yah Boss
Bayan ya dawo daga masallaci, bai hau Stairs ba, ɗakin gyam ɗinsa ya tafi, ya cire jallabiyar jikinsa haɗaɗɗun fararen kayan jikinsa da yake gyam dasu, suka bayyana sunyi matuƙar masa kyau sosai sun kama murɗaɗɗan jikinsa.
A cikin nutsuwarsa ya fara motsa jikin nasa.

Tsawon mintina 30 yayi, ya ɗauki jallabiyarsa ya riƙe jikinsa na tsatsafo da gumi ya fito yana goge fuskarsa da wuyansa da ƙaramin towel.

Ƙaton parlour shiru, a hankali ya fara takawa zuwa kitchen.

Jamilu har ya iso ya fara ƙoƙarin girka abinda za'ayi breakfast.

Ƙofar ya buɗe ya shigo da sallama.
Jamilu ya amsa yana faɗin.
"Yallaɓai Good morning"

Yah Boss anutse ya furta.
"Morning Jamilu! Ina buƙatar coffee yanzu, ka kai min Stairs, breakfast kuma ina buƙatar Sushi, yaran ka masu cookie, ka ɗan soya masu kaza ko ɗaya ne, da tea mai kyau.

Idan yaso kai sai kuyi duk irin girkin da zai muku daɗi, fatan aikin bazai maka yawa ba? Nace a ƙaro mutum ka ƙi mutum biyu yanzu ya kamata a ƙaro ayi komai cikin ƙaramin lokaci."

Jamilu yace.
"Wlh zan iya Yallaɓai in sha Allahu, bari na dafa maka coffeen"

Yah Boss ya furta.
"Thank you, Amma zan ƙaro mai temaka maka"

Ya ƙarasa maganar yana fitowa daga kitchen ɗin.
Kai tsaye ya nufi ɓangaren Zarah.

Juhainah ɗakyar tayi sallar asuba, zazzaɓin ya dawo, Jamal ya lallaɓata ta sake shan magani bayan ya saci jiki yaje ɓangaren su Mamy ya dafo mata tea mai kauri.

Tana shan maganin sai bacci sbd akwai mai saka bacci.
Ƙarfe tara tana farkawa ta fara rigima sai ya kira mata Maah.
Dole ya bata wayar ta saka number Maah ya kira, lokacin Maah suna kan dinning tare da baƙi da suka zo biki harda Hajjah Mama, suna breakfast, kiran ya shigo.

Tana ɗauka ta saki kuka.
Maah hankalinta ya ɗan tashi, dan kar ta tayar wa da Papa hankali da sauran jama'a ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta, tana faɗin.
"Ina zuwa zan amsa waya"

Tana shiga ta rufe ƙofar tace.
"Autar mata me ya faru? Kiyi shiru kimin bayani"

Juhainah sai taji bazata iya faɗa ba cikin kuka tace.
"Ni ba komai amma don Allah Maah ki kira min Aunty Sumy ni ko na kirata bazata zo ba, Ni dai Inason inga ɗan uwana kusa dani, tunda kinga Yah Boss bazai zo ba"

Maah ta sauke ajiyar zuciya tana Hamdalla ga Allah, dan ta gane ƴarta ta girma tabbas.

Cikin farin ciki tace.
"Ubangiji ya albarkaci rayuwar ki Autatah, Allah yasa ki gama da duniya lafiya, ya sanya miki albarka, in sha Allahu Sumayya zata zo kiyi haƙuri kinji?"

Juhainah ta fasa kukan sai hawaye cikin rauni ta amsa da.
"Ameen Maah Nagode sai anjima"

Ta katse kiran ta ajiye masa wayar tana kwanciya.
A hankali yace.
"Tashi muje parlour ga kayan breakfast Mamy ta bada an kawo muje ki daure kiyi Please"

Idanunta ta rufe tayi masa banza.
Jikinta ya taɓa akwai zafi, hannayensa ya saka cikin jikin nata yana tausawa a hankali yace.
"Jikinki ciwo yake ko?"

Kamar jira take ta sakar masa kuka tana faɗin.
"Ai kafi kowa sani miye na tambayar"

Jamal yace.
"Ok Allah ya baki haƙuri Juhainah shi kenan na fasa, ki daure muje kici wani abun..."

A hankali ya samu ya lallaɓata suka tafi parlour ya haɗa mata tea mai kauri, ya zuba mata farfesun Kajin da Mamy tayi tun da asuba.

Ba laifi taci sosai tasha tea ya lallaɓata ya maidata bedroom ya shafa mata cream ɗin tanata rigima.

Shi kansa al'amarin na basa mamaki yadda ya ƙasƙantar da kansa gun Juhainah, samunta a cikakkiyar budurwa ba ƙaramin daɗi ya masa ba.

Fitowa yayi ya zauna yayi breakfast, yana gama wa, ya shiga bedroom ɗinsa yayi wanka ya yi shiga ta alfarma yana baza ƙamshi ya fito ya nufi bedroom ɗin Juhainah ya isko ta fara bacci.

A hankali ya fice ya janyo mata ƙofar, ya nufi part ɗinsu Mamy.

Zarah ta baje saman bed tana rama baccin da bata samu tayi jiya ba Yah Boss ya shigo.
Har bakin bed ya isa.
Har zai tasheta ko me ya tuna oho ya juya ya fice, fuskarsa a mugun kame.

Maah
Juhainah tana katse kiran ta kira Aunty Sumy, lokacin suna kan dinning da Khabir da ƴaƴanta Habibullah Fatima Fahad little Sadiq, sosai ƴaƴan Sumy suke jinin Yah Boss, duk da sun ɗebo kamannin Khabir.
A nutse suna breakfast ɗin.

Kallon Khabir tayi tana faɗin.
"Honey karku jirani Maah take kirana ina zuwa"
Murmushi yayi yana faɗin.
"Ok Honey"
Fatima tace.
"Momy zanje gidan Daddy police"

Aunty Sumy ta ɗaga mata hannu ta tafi.

Keɓewa tayi tana ɗaga kiran tare da sallama.
Maah ta amsa tana faɗin.
"Sumayya! Don Allah idan babu damuwa ki faɗawa Khabir Autah batajin daɗi zakije ki duba min ita yanzu Please"

Aunty Sumy tace.
"Ok Maah Muna breakfast zan faɗa masa idan mun gama, dan kasuwa ma zai fita ajima, yaran kuma zasu tafi islamiyya, sun makara ma, sbd gajiyar jiya"
Maah tace.
"Yawwa Allah ya miki albarka Sumayya, idan kin isa gidan nata ki kirani naji lafiyarta don Allah, dan babu halin zuwa Wlh da da kaina zan tafi"

Aunty Sumy tace.
"Toh Maah in sha Allahu"

Bayan sunyi sallama ta dawo kan dinning ɗin, ta zauna tana kallon Khabir tace.

"My Honey anjima idan ka fita zanje gidan Juhainah na dubata batada lafiya"

Kallon ƙauna ya mata yana murmushi a hankali ƙasa² ya furta.
"Ok Honey, ai ku duk gidanku matan tarbiyya ne"

Murmushi tayi tana masa nuna da idanunta ƴaƴansa na nan...

Ƙarfe 10 na safe Yah Boss shi da ƴaƴansa bayan sun cika tumbin su da daddaɗan girkin Jamilu, sukayi wanka suka bar gidan, kayansu iri ɗaya bugagga shadda Brown (cinnamon)

Shi da Al'amin ɗinkinsu iri ɗaya, yayin da Suhaima an mata ɗinki doguwar riga an samo ɗinkin ba kaɗan ba, ko dan telan nasu telen manyan mutane ne, an samu ɗinkin nasu, idan ka kalli Yah Boss da ƴaƴansa a wannan lokacin sai ka sake kallonsu, tamkar Larabawa, shi farin bafulatani, ƴaƴansa jinin larabawa.
Aunty Sumy ƙarfe goma saura minti 7 ta isa gidan Juhainah......🖊️
[29/03 11:42] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

_Masoyan JUHAINAH Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kadan-kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books Ɗina, A Channel Ɗin. Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku._

*Page 46*

Surayya tana zaune a parlour da Dijeh sai Farida ɗiyar Yayar Mamy, Jamal ne ya turo Surayya tazo ta zauna da Juhainah kafin Aunty Sumy ta iso.
Mamy sai washe baki take zuciyarta fara ƙal, tasan ɗanta ya cika alƙawari, yarinya kuma ta kawo mutuncinta gidan aure.

Jamal fita yayi ya tafi duba wata kwangila da aka basa ta ginin wani ƙaton masallacin juma'a, ya saka har an fara kwanaki biyar da suka wuce.
Surayya cikin girmamawa ta tarbi Aunty Sumy ta gaisheta ta amsa.
Farida ma ta gaisheta, Dijeh kuwa baki ta washe tana bin Aunty Sumy da kallo tana faɗin.
"Alquraan binni cike take da angayu, hekace su sukayi kansu, ba ma ƴa gidansu Antiya amarya..."
Surayya ta buge bakinta tana faɗin.
"Sakara Aunty Sumy baki ganta a can gidansu Juhainah ba? Auntynta ce, Aunty Sumy ki shiga tana ciki bacci take"
Aunty Sumy tace.

"Haba Surry meye na dukanta muma ba mumada ƴan uwa a can ƙauye ba, Ok bari na dubata"
Ta faɗa tana nufar bedroom ɗin.

Kwance take tana lulluɓe cikin Duvet Jamal ya rufe ta da zai fita.
Janye Duvet Aunty Sumy tayi taga Juhainah har ta sake faɗawa abinka da dama ba wani naman kirki ba.
Hannunta ta sanya ta taɓa jikin nata akwai zafi.
Tashinta tayi tana ɗagota.
"Juhainah! Buɗe idanunki gani nazo"

Ai Juhainah tana jin muryar Aunty Sumy ta faɗa jikinta tana ƙamƙameta, sai hawaye.
Aunty Sumy ta zauna tana rungume ƙanwar tata, cikin lallashi tace.
"Autar Maah kiyi haƙuri kowa ce mace da kika gani, in dai ƴar mutunci ce, toh da haka ta faro, wannan ita ce daraja da kimar mace waccen da ta san mutuncin kanta, ta kuma kawo darajata ɗakin mijinta, kinyi wanka da ruwan zafi yau?"
Juhainah ta sake mannewa jikin Aunty Sumy kamar zata gudu, ta girgiza kanta.
Aunty ta janyeta ta miƙe ta buɗe jakarta ta ɗauki ledar garin bagaruwa da sauran magungunan gargajiya, ta shiga bathroom ɗin.
Ruwa mai zafi ta haɗa cikin bathtub, sai da takai rabi ta zuzzuba maganin ta fito.
Kamo hannunta tai ta sauko a hankali, suka nufi bathroom ɗin.

Cikin bathtub ɗin ta saka ta, ta fasa ihu.
Aunty Sumy ta riƙeta tana faɗin.
"Kiyi haƙuri zakiji daɗi Juhainah ki daure"

TOH a haka tana mata dabaru na manya har ta samu ta gazata sosai, ta barta tace tayi wanka.
Ai kuwa sosai Juhainah taji daɗin gashin da Aunty Sumy ta mata, babu wannan raɗaɗin da take ji na ƙasanta sai kaɗan.
Haka jikinta ya rage ciwo sosai.
Chapter 89 · 0% Book details