← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 113

Sashe 36

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yah Boss acikin sirri shi da Fu'adh sukayi bincike akan Jamal, yaron bashi da wani aibu fili da kuma ɓoye, hakan ba ƙaramin farin ciki ya saka shi ba, Ƙanwarsa zata auri kamilin Yaro mai hankalin manya....

Yah Boss da kansa ya maida Twins gidan Mahaifin su Mustapha, daga can suka wuce yaje ya kawo ma Khairat kayan zuwa makaranta da su Suhaima, saboda yana son Dukansu su dawo gidan nasa har sai auren Juhainah yazo sai koma can babban gidan.
Sai lokacin ya sanar wa Maah da Papa hira ran talata za'azo neman auren Juhainah daga gidan Abdallah Na kowa, yaron yanada hankali sosai ga nutsuwa.
Da Kuma hira auren Zarah da hajjah Bilkisu ta basa umarnin yayi.
Abin ya bawa su Maah da Papa mamaki basu dai ɗumaba, tunda sunsa Abbah bazai kawo mata mijin banza ba,ko kusa. Sai murna Abban nasu zaiyi aure ko wacece wannan sunsan tanada sa'a...

Washegari Khairat da Suhaima sun tafi Makaranta sai Juhainah kaɗai a gidan, ta sha baccinta son ranta, tunda Alhamdoulillah jikin nata yayi sauƙi.
Har Yah Boss ya fita aiki bata farka ba, bai kuma shiga ɓangaren nasu ba, yasan baccin take yi.


Washegari ta kama ran talata a yau iyayen Jamal zasu tafi neman auren Juhainah.
Da Yamma suka je gidan Yakubu Abubakar Janfar tambayar auren.
Sun samu tarba ta karamci, agun Papa da ƴan uwansa da ƴaƴan sa Yah Boss su Mustapha su Umar.
Sun zo tambaya sun bada kuɗin nagani inaso, aka basu rana gobe ma suna iya dawowo ba matsala sai a tsayar da magana ɗaya, hakan ba ƙaramin daɗi yayi wa Alhaji Abdallah ba, tabbas ya shaida ɗansa Jamal yaje inda ya kamata.

Ai kuwa washegari bayan sallar la'asar sun tafi an sanya rana aure tare da yin duk wata al'ada da akeyi a familles Janfar baki ɗaya, abun gwanin burgewa, su Aunty Sumy ba dama Yau bakinta yaƙi rufuwa.
Anyi Baiko tare da tsayar da ranan ɗaurin auren wata biyu masu zuwa in sha Allahu, tare da yarjejeniyar Juhainah zataci gaba da zuwa makaranta.
Duk wannan bidirin da ake Juhainah bata saniba, amma Khairat ta sani a bakin Fu'adh taji, tunda suna gidan Yah Boss, ba sani zasu yi ba, bata faɗa mata ba taja bakin tayi gum.
Surayya ko bata samun daman zuwa gun Juhainah ba, saboda jarabawar da suke yi, Abbanta ya amshe wayarta sai sun gama.
Ammar kuwa yana can yana murna an kusa kiransa ya tura neman auren Juhainah gidansu.

Washegarin Baiko.
Misalin ƙarfe 9 na safe
Jamal
Sanye yake da ƙananun shiga yayi masifar kyau, takalmin ƙafarsa da agogon Pakistan na hannunsa kawai sun isa shedar Yaron fa babban Yaro Ne.
Parlour iyayensa ya shigo bakin ɗauke da sallama.
Dattijo fari kyakkyawa, mai yanayi da Jamal ya amsa sallamar cikin sakin fuska yana faɗin.
"Babban mutum baka tafi Makaranta ba?"
Yanayin na nutsuwa ya tako cikin izzarsa, fuskarsa ba yabo ba fallasa ya iso gun Mahaifin nasa yana zama kusansa anutse cikin daddaɗar muryansa ya furta.
"Good morning Abba, eh yau bamayi zan fita ne wani taro yanzun"
Kansa Alhaji Abdallah ya shafa yana murmushi yace.
"Ma sha Allah, Ubangiji ya maka albarka ya albarkaci dukkan abinda ka sakawa hannu, ya jikin na Bilkisu ance batajin daɗi kwana biyu da suka wuce?"
Jamal dan kar ya ɓatawa kansa lokaci ya amsa da.
"Ameen Abba, a'a banje ba banida lokaci kwana biyu nan"
Mamy tace.
"Ai kuwa yanzu ka wuce kaje ka ganta, umarni nake baka, haba Jamaluddin! Matar da zaka aura kana burus da ita, wlh banajin daɗin shirun da kake mata"

Jamal ya zubawa Mamy manyan kyawawan idanunsa baice uffan ba ya jinjina kansa alamar zaije ɗin.
Abba murmushi yayi yace.
Yana miƙewa ya kamo hannun Jamal yana faɗin.
"Karki takura min yarona yace maki yana uzuri ne Yanzu in sha Allahu zai biya, muje ka tafi sha'anin gabanka"
Baice uffan ba yabi Abba suka fice yana riƙe da hannunsa.
Abba ya shiga motarsa yayin da Jamal ma ya shiga sabuwar Ferrari ɗinsa ya fizgeta ya nufi gate yana zuba wani Horn.
Aguje mai Gadi ya miƙe ya buɗe masa gate ya silala motar waje, ransa a mugun ɓace ya nufi gidan Yah Boss....
[18/01 16:16] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo
Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVELS. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U
👆🏽
_*Mutanen Kirki Kuci Gaba Danna Min Followers, Zan Dinga Antayo Muku Zafafan Tsofaffin littattafai Na, Kuna Chanawa Abinku😂💃🏻🫣*_

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 20*

Yau Yah Boss ya tashi da ciwon kai sosai shiyasa bayan sallar asuba da ya dawo daga masallaci ya koma bacci.
Har su Khairat suka tafi school bai farka ba.

Sai takwas da rabi ya farka ya ya kira Jamilu ya haɗo masa black Tea.
Sharp² ya haɗo ya kawo masa, a can bedroom ɗin ya sha, ya ɓalli Panadol yasha, ya miƙe ya shiga wanka ko zaiji daɗin jikinsa.

Juhainah yau yinwa ta hanata baccin kirki, takwas da arba'in da minti biyar ta farka ta shiga bathroom tayi brush ta fito hijabin Khairat dogo har ƙasa ta saka akan rigar baccin jikinta, ta sauka ƙasa.
Lokacin da ta sauko an gama gyara parlour ko ina tass sai ƙamshi yake tashi, ta nufi dinning room dan yin breakfast.

Jamal na isowa ba'a hanasa shiga ba, saboda Yah Boss ya sanar dasu, duk lokacin da yazo abarsa ya shiga.
Bayan ya shiga yayi parking, ya fito a nuste yana tunanin yadda ma zaiyi ya ganta, shi kam gani yake bai dace ya kira Yah Boss ba, haka shi baida numberta.
Fu'adh ne da ya shigo yanzu da mota.
Parking yayi ya fito ya isa gun Jamal yana basa hannu sukayi musabaha, Jamal yana gaishesa.
Fu'adh ya amsa yana faɗin.
"Baka samunta a waya ko?"
Jamal dan kar ya ɓatawa kansa lokaci ya amsa da.
"Eh kuma ina jin nauyin kiran brother"
Fu'adh yayi murmushi yace.
"Ok muje ka zauna parlour baƙi sai na turo maka ita"
A hankali Jamal ya furta.
"Thank you"
Lafiyayyan parlour baƙi na ɓangaren Yamma ya kaisa.
Juhainah sosai tayi lodi sai da taci tayi Haniƙan ta fito tazo ta kunna Tv tayi kwanciyarta saman 3 seater royal Turkish Chair ta fara kallon Tv tashar Zee Alwan ana series na India da larabci.
Jin hijibin ya takurata ta janye daga ƙasa tayi kwanciyarta yadda take so, dan a zatonta Yah Boss baya nan.
A nutse ya yake saukowa cikin takusan mai burgewa, sanye da uniform ɗin da ta masa wani irin kyau, sai fitinannan ƙamshi yake.
Tun daga nesa yake jin sautin Tv da larabci.
Yasan ba kowa a gidan sai Juhainah yasan itane.
A nuste yake takowa, yakai lumsassun fararen kyawawan idanunsa akan Tv'n.
Hanyar dinning room ya nufa yana amsa waya, cikin nutsuwarsa.
Sam bata ji ba, amma ta shaƙo ƙamshinsa.
Dara-daran kyawawan idanunta ta ɗago tana kallon hanyar Stairs, a hankali tace.
"Ƙamshi Yah Boss ya kama hancina Wlh, haba ni nayi mamaki me yake nema a gida yanzu"
Ta ƙarasa maganar tana gyara kwanciyarta.
Fu'adh ya shigo da sallama.
Juhainah tai saurin ta gyara hijabin tana miƙewa zaune, duk da Fu'adh baizo saitin da zai ganta ba.
Anutse ya iso yana murmushi yace.
"Amarya bakya laifi koda kin kashe ɗan masu gida"
Juhainah ta zuba masa dara-daran kyawawan idanunta tana Turo baki gaba tace.
"Ni dai a'a ba amarya bace, nida ban samu kalar Yah Boss irinsa nake so, bana son Ammar..."
Fu'adh ya zauna yana dariya saboda yasan Yah Boss yana dinning room, Juhainah bata saniba.
A hankali yace.
"Irin Sir kike so? Toh me ya saka kika kawo Jamal matsayin mijinki har aka saka maku ranan aure?"

Idanunta ta zaro tana faɗin.
"Innalillahi an saka ranan aure kenan? Toh me yasa ba'a faɗa min? Auren dole za'a min ne?"
Fu'adh yana dariya zaiyi Magana suka haɗa ido da Yah Boss yana goge bakinsa da tissus fuskarsa a haɗe.
Kansa ya kauda yana faɗin.

"Tashi kije Jamal yana parlour baƙi na ɓangaren Yamma yana jiranki."
Baki ta murguɗa tana kwanciya tace.
"Bazanje ba"
Yah Boss yana zuba hannenysa cikin aljihun wandonsa na uniform a hankali cikin zazzaƙar muryansa a kame ya furta.
"Tashi karki bari na iso gurin nan Wlh"

Dara-daran kyawawan idanunta ta zaro tana wuntsulawa daga kan Chair tana faɗin.
"Innalillahi."
A aguje ta kwasa ta nufi hanyar barin parlour.
Fu'adh ya dinga ƙyalƙyala dariya harda tafa hannayensa.
Yah Boss fuska a kame yana kallon Fu'adh ya furta.
"Kai kam kaji haushi Fu'adh, ka sakata gaba tana hauka kana dariya, Juhainah anya tanada hankali? Ita fa ta kawo yaron nan, yanzu kuma tana faɗin bata sonsa."

Ya ƙarasa maganar yana zama tare jingina bayansa allon Chiar, tare da zuba fararen kyawawan ƙafafunsa saman table.
Fu'adh dariya yake Sosai yace.
"Kasan me yafi bani dariya? Wai ita irinka take so, bata son Jamal bata son Ammar, gaskiya naso a bata zaɓin ranta"

Yah Boss ya taɓe lips ɗinsa mai kyau da sheƙi, idanunsa akan pictures ɗin Khadija ya furta.
"Toh ai bata da cikakken hankali, kaima da yake irinta ne ai ka biye mata kuna zuba haukan, ga shi nan har ciwon dariya ya kama ka"

Fu'adh dariya kawai yake.
Yah Boss ya miƙe yana faɗin.
"Ubangiji ya baka lafiya, tashi muje, zata iya masa ɗibar albarka, tunda bata da mutunci"

Jamal yana zaune yana duba saƙo cikin wayansa, Juhainah ta buɗe ƙofar parlour ta shigo, tana karairaya fuska a haɗe.
Jamal koda yaji ƙaran taɓa ƙofar parlon bai ɗago kansa ba.
Tsaye take riƙe da ƙugu tace.
"Jamal! Ni nace kakai kuɗin aurena gidanmu?"

Jamal kamar ma ba shi take yiwa magana ba, yaci gaba duba saƙon.
Matsowa tayi kusansa tana faɗin.
"Ko bakaji ina magana?"
Kansa ya ɗago ya mata kallon raini yana faɗin.
"Wa ya zaɓi hakan? Ko ance maki ina sonki ne? Ni bakya cikin kalar matan danake so, ina son mace mai tarbiyya da kamun kai, ba wacce zata roƙi na aureta ba, tsarin rayuwarki bata min ba, idan kin shiga gidana zan baki mamaki, nabarki lafiya."
Chapter 36 · 0% Book details