Sashe 47
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Page 26* Zuby Rashin sanin waye akan layin, taci gaba da rashin mutunci. "Yarinya Ni ba'a shiga gonata, na kai sati ina nemanki bana samun ki na sanar dake ba'a shiga gonata. Ammar nawane ni kaɗai babu wata shegiya, jiya yana tare dani amma Juhainah ce a bakinsa, toh Wlh bari kiji ko waye ubanki a ƙasar nan, sai na ɗauki mataki a kanki. Tun ranan da na samu labarin kece yake haukan SO, na tsaneki nake nemanki ido rufe ban sameki ba, sai jiya na tabbatar da kin mallake min shi. Ki fita daga sabgar Ammar, shi ɗin nawane ni ɗaya babu rabon kowace shegiya, ki kama kanki, idan kuma kika yi kuskuren aurensa Wlh kin Banu... Kuma bari kiji..." Yah Boss ya katse kiran, yana cin fankansun sa hankali kwance. Yana gamawa ya yagi tissus ya goge bakinsa, ya miƙe ya wanko hannunsa ya dawo ya ɗauki wayoyinsa ya zura ɗaya aljihunsa, ya ɗauki wayan Juhainah akwai password ciki. Sunanta ya saka Juhainah bai buɗe ba, ya saka Bilkisu shi ma bai ba, ya saka Suhaima bai ba, ya saka MAAH bai buɗe ba, ya saka Al'amin bai buɗe ba, ya saka sunansa bai buɗe ba. A nuste yabar dinning room ɗin, hankalin da kwance. ★ Ammar Jiya dolensa Abuja raod ya kwana saboda ya bugu dayawa bazai kuskuren zuwa gidansu ba. Tunda sassafe ya koma gida kasancewar Dady Najib baya gari ajiyan, bai da fargaba saboda Haj Maimuna bazata san bai kwana a gida ba, Hisham kuma baida kulawa tunda kowa da ɓangaren sa yanzu. Koda ya dawo gida kwanciya yayi yana saƙa yadda zai ɓullowa al'amarin cikin sauƙi, ya rama cin amanar da Juhainah tai masa, tunda yasan bazai taɓa samun aurenta ba, tunda ta furta wa ƴan gidansu bata son sa, toh Tabbas baza su aura mata shi ba. Ƴar dariya Ammar yayi yana sake gyara kwanciyarsa, ya ɗora hannunsa akan mazakuntarsa yana faɗin. "Juhainah tunda bazan sameki ta hanyar da naso ba tsakanina da Allah ba, so zan sameki ta hanyar da bai dace ba, Wlh idan wannan abar bata shiga cikin jikin ki ba, bazan taɓa samun kwanciyar hankali da nutsuwa tare da sassaucin zuciyata ba, ina sonki ina sha'awar ƙaramin jikinki, ina sha'awar baiwar albarkatun ƙirjinki da Ubangiji ya baki tamkar ke ɗaya ake so, Wlh idan ba shasu na kamasu ba naji ki acikin jikina ba mutuwa zanyi sha'awarki da sonki son hallitarki sun yiwa zuciyata babbar illa. Wlh da nasan haka zaki min da nayi anfani da damar dana samu a baya na lallaɓaki nacinma burina..." Ya ƙarasa maganar hawayen baƙin ciki suna gangarowa saman fuskarsa. Wayarsa ya ɗauka yana shiga gallery ya fito da hoton Juhainah, tana sanye da abaya Pink colour ƙirjinta dam ko ta abayar ma sha Allahu. Tana murmushi wushiryata ta bayyana, dimples ɗinta ya loɓa. Ji yayi hallitarsa na motsawa cikin shauƙin Juhainah, ya sumbaci laɓɓanta masu kauri, ya ɗora bakinsa akan saitin ƙirjinta yayi kissing ɗinta. Contacts ya shiga ya ciro number ta. Kwata-kwata bai samunta yana danna kiran, kiran yake katse wa, Na'ura bata ce masa wayan a rufe ba, bata ce masa tana amsa waya ba. Tsaki Yaja yana kida da wayar ya miƙe ya diro daga kan bed, dan yau babu tsiyar da taɓuka... ★ Maah tana gama wayan ta ɗago kan Juhainah da ta manna da ƙirjinta tana shafa goshin nata tana faɗin. "Autah Juhainah kin taɓo Abbah ko? Shi ne kika zo nan kika manne jikina, zan iya hanasa ya dakeki ne? Mi ya ji miki ciwo a goshi, jiya na manta ban tambaye ki ba?" Shagwaɓe wa tayi jikin Maah tana Turo laɓɓanta masu kauri tace. "A saman bed ɗin Babie Suhaima na faɗo, Maah Allah na tsani matar da Yah Sadeeq ya auro tun ban ganta ba..." Shiru tayi jin ƙamshinsa ya ratso kofofin hancinta. Tayi lamo jikin MAAH. Anutse ya zauna kusan Maah ɓangaren dama, yayin da Juhainah take ɓangaren hagu, yana faɗin. "Ke! Zo nan" Maah tace. "Nagode Allah da kaji da kunnenka abinda take faɗi, karka mata da wasa, ta raina maka mata, tun bata shigo gidan ba.." Siririn kuka ta saki tana ƙamƙame Maah. A hankali cikin kamewarsa ya furta. "Toh Maah bata sonta dole sai ta sota ne? ai nasani bata sonta, saboda damuwar har zazzaɓi tayi jiya, a banza tana son cutar da kanta akan macen da bata da wani daraja ko kima a waje na. Ta so kizo nan, ko sai na kamo ki da ƙarfina? Kuma ki kama min bakin ki da kukan munafurci" Maah ta saki baki da ido tana kallon ikon Allah, Abbah yana ji yana ganin Juhainah tana faɗin ta tsani matar da ya auro amma ya ɗaure mata gindi, shi da ya kamata ya kamata ya naɗa mata duka, dan kar taje can gidan nasa ta saki zance. Juhainah tayi shiru tana maida hawayen ƙaryan ganin ya gano ta. A hankali ta miƙe ta dawo kusansa ta zauna a ƙasa saman Carpet kusan ƙafafuwansa, tana ɗora tattausan hannunta akan rufaffen takalmin ƙafarsa mai kyau da tsada, ƙoƙarin kwance ɗaurin takalmin take, tana son zura hannunta cikin takalmin, dan kamo ƙafarsa. Hannunsa ya ɗora kan hannunta ya buge hannunta a hankali ya furta. "Ɗauke min hannunki a ƙafata. Maah Bilkisu da mayya ce ƙafafuwana zata fara cinye wa a jikina" Da sauri Juhainah ta janye hannayenta tana shagwaɓe fuskarta. Maah tayi dariya tana faɗin. "A'a Abbah bana bayan ka bana bayan Autatah, koda ita mayya ce baza taci Yayanta ba, ko Juhainah Babyn yayanta?" Ai kuwa Juhainah ta narke fuskarta kamar zata yi kuka cikin wata irin kalar shagwaɓa tace. "Eh Maah ni ina sonsa dayawa bazan iya cinyesa ba, sai dai naci wasu a waje, Allah My brother Habiby I love you, bazan cinyeka ba, amma da nasan inda zan samo maitar siya na siyo na cinye amaryarka da na si..." Hannunsa ya ɗora kan laɓɓanta ya buge a hankali, yana zabga mata harara cikin zazzaƙar muryansa a hankali ya furta. "Kama min bakinki, na kuma jin zancen siyan maita, wlh da ke mayyane sai kin cinye ƙafata zaki huta na sani ai." Maah dariya take tana faɗin. "Abbah bari danganta min ƴata da mayu, Ni dai nasan ko mayya ce bazata iya cin naman Abbah ba Autah." Yah Boss, a hankali ya furta. "Maah! Kibar ɗaure mata gindi." Ya ƙarasa maganar ya saka hannunsa ya ɗago kanta ya nuna wayanta da kyakkyawar fuskarta, sai ga wayan ta buɗe. A hankali tace. "Yah Sadeeq sunanka ne fa na saka." A hankali ya kamo kunnenta ya murɗa ya furta. "Ƙarya kike munafuka" Kanta ta sadda ƙasa tunawa ashe Yah Boss ne ta saka password ɗin, idan ya gane zaici ƙaniyarta ne. Cikin mutuna ƙalilan ya bincike wayan Juhainah babu wani aibu acikinta ko maganar batsa ɗaya, dukkan hirasu da Ammar ta soyayya ce, kuma shine mai zuba kalaman, tana amsawa jifa² ko ta tura masa heart. Sai group na ƴan school ɗinsu, da wasu lambobi guda uku da suke tura mata saƙon soyayya, ba ɗaya da ta amsa sai dai tana tura masu emojis na dariya ko harara. Ajiyar zuciya ya sauke yana sake bincika wayan ciki da wajanta. Number Zuby ya ɗauka ya loda a a wayarsa yayi blocking ɗin number ya go kiran da tai, ya goge number Ammar yayi blocking ɗinsa, ya beƙa mata wayan, cikin kamewarsa yana faɗin. "Amshi duk number da ta kira ki idan ba suna ba kuma Jamal bane ki tura min ita ta message" Kallonsa tayi cike da shagwaɓa zatayi magana ya kafe lumsassun idanunsa a kanta, yana hararenta ta lumshe dara-daran kyawawan idanunta tana ƙoƙarin kwantar da kanta akan guiwowinsa ya riƙe kan nata yana faɗin. "Ta shi kije ki kwanta, kinsha maganinki ?" A hankali kanta ƙasa tana shaƙar ƙamshinsa tace. "A'a yanzu zan sha" Miƙar da ita yayi tsaye cikin kamewarsa ya furta. "Oya karki ƙara ko minti biyu baki sha ba wuce, zuwa dare zan zo mu wuce, ki saka hula a kanki yanzu². Kai ta ɗaga masa tana amsawa da. "Toh" Ta sa kai ta tafiyarta. Maah dai kallonsu take cike da farin cikin ƙaunar da Abbah yake yiwa Autarsu. Bayan Juhainah ta nufi Stairs Yah Boss ya zauna kusan Maah fuskarsa a kame sosai ya riƙe hannayen Maah kamar ƙaramin yaro ya furta. "Wlh bana sonta ko kaɗan Maah, ƙarfa² Hajiya Mama ta min dan babu yadda sanyi da ita..." Dai-dai lokacin Hanifah ta sauko daga Stairs tana isowa gunsu, da sallama. Suka amsa Maah tana kame fuska sosai. Hanifah jikinta har rawa-rawa ya fara saboda tsoron Maah take sosai tunda ta fara sauya mata. A diririce ta gaishe da Yah Boss, tunda ta gaishe da Maah ɗazun. Amsawa yayi a nuste ba tare da ya kalleta ba, tunda haka halinsa ne hakan. Juyawa tayi da sauri ta koma hanyar Stairs. Maah taja tsaki fuskarta shafe da toka tace. "Allah ya kyauta, nifa bana son naci Allah ya sani, yanzu da ban ɗaure fuska ba, Wlh haka zata sakani a gaba nida Ɗana taji me zamu faɗa akai mu gaba." Yah Boss ya kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa akan Maah cike da mamaki, dan bai taɓa ganin inda mahaifiyarsa taci mutuncin wani mutum mai rai ba, idan aka cire Familles ɗin (Taurari). A hankali yana sake riƙe hannunta ya furta. "Maah bakya ƙyamar mutum sai da dalili, me ta miki?" Maah ta sauke ajiyar zuciya, dara-daran kyawawan idanunta irin na Juhainah suna son kawo ruwa. Da wani irin sauri ya furta. "No! Maah abar maganar Please karki ɗaga min hankali, Ya Rabbi! Me yayi zafi haka kuma? Bana son jin komai saboda bansan irin matakin da zan ɗauka ba daga ita har wanda yake aure da itan" Maah ta jinjina kanta tana damƙe hannunsa a hankali tace. "Abbah! Cigaba ina sauraren ka, me yasa baka son matar da aka ɗauro maka aurenta jiya, amma ka bari aka ɗaura? Shin duk biyayyar Aunty Bilkisu ne? Me yasa ka amince? Nasan halinka fa yarinyar nan bazata taɓa jin daɗin zama dakai ba, bana son Allah yayi fushi dakai a kanta, me yasa kayi hakan?" Yah Boss ya girgiza kansa a hankali ya furta. "Wlh Maah na faɗa mata gaskiya tace taji ta gani, kuma