Sashe 16
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Danna number Aunty Sumy yayi.
Bugu ɗaya ta ɗaga tare da sallama tana gaishesa.
A nuste Yah Boss ya amsa cikin kulawa, saboda yana bawa ƙanwarsa lokaci sosai, saboda ƙaunar da take tsakaninsu.
A hankali yake taka Steps cikin nutsuwarsa.
Ya furta.
"Sumy! Yarinyar nan zan mata aure in sha Allahu, kinada labarin duk abinda tayi, ba sai na tsaya miki dalla-dalla-ba.
Ɗazu da safe shi saurayin nata ya kira wayan baisan nine akan layin ba, ya yi ta surutu, so abinda na fahimta yana sonta sosai, but bazan tsaya ɓatawa kaina lokaci ba, zan kirasa na bincike shi, idan tarbiyyarsa da nutsuwarsa sun kai, naji ko ɗan waye babu gurɓacewar tarbiyya gidansu zan basa aurenta.
Because yarinyar tana son lalacewa bata son karatu auren shi yafi,
sai dai bazan bari ta auri shuga dady da take so ba, shi dai wannan ɗin zata aura in har baida wani aibu.
Idan kuma yanada bazan rasa wanda zan aura mata ba, inada jama'a nagartatu.
"Ya ƙarasa mgnar yana ƙarasa saukowa tare da jan dogon numfashi, ya nufo gun Fu'adh, da yake tsaka da waya da Khairat cikin soyayya mai tsafta.
Zama Yah Boss yayi yana sauraron abinda Aunty Sumy take faɗa masa.
Fu'adh kuwa miƙewa yayi ya gusa dan yaji daɗin soyewarsa.
Aunty Sumy daɗin bayanin ɗan uwanta taji sosai, hakan ya saka ta dinga zuga shi.
"Ai Wlh Yah Sadiq hakan yayi min daɗi Maah da ba son laifin Juhainah take ba, idan aka barsu da ita babu wani mataki da zasu ɗauka akanta..."
Hira sukayi sosai kafin ya yanke kiran, ya miƙe ya nufi dining room ko zai iya cin wani abun.
Sama-sama ya ɗan ci kaɗan ya sha Black tea, ya dawo parlon.
Fu'adh ya iske zaune yana jiransa.
Yana ƙoƙarin zama ya furta.
"Fu'adh a kirata muji inason kwanciya na huta, kaina na ciwo."
Fu'adh yace
"Subhanallahi Allah kawo sauƙi Sir."
Ya faɗa yana miƙewa.
Juhainah tana kwance ba bacci take ba, ta shiga duniyar tunanin rayuwa ne.
Ƙaran ƙwanƙwasa ƙofar ne ya dawo da ita daga tunaninta.
Miƙewa tai tana addu'ar Allah yasa ba Juhainah bace.
Saukowa tai daga kan bed ɗin tana gyara mayafin abayar jikinta, ta nufi ƙofar, ido huɗu suka yi da Fu'adh.
Kanta ta sadda tana gaishesa cikin girmamawa.
Fu'adh ya amsa yana faɗin."
Kizo Sir nason magana dake, ki nutsu ki faɗa masa gaskiyar komai a cikin rayuwarki, ba mamaki zai iya taimakawa rayuwar taki."
Cikin ladabi tace
"Toh Nagode in sha Allahu."
Juyawa yayi tabi bayansa kanta a ƙasa.
Tana sanya kanta cikin parlon taji ƙamshin ya canza ba irin wanda ta bari bane da yamma.
Hancinta ta buɗe tana shaƙo daddaɗan ƙamshin da irinsa ta shaƙa a cikin motar da aka kawota gidan nan.
A hankali take takowa ta ɗan ɗago kanta, akansa idanunta suka sauka akan kyakkyawan mai gidan wanda samu namiji cikin Hausa mai kyau da cikar hallita fari ƙira mai kyau kuɗi, irin su suna wahala a zamanin nan, sai dai ka samu mai kuɗin baƙi kuma marar kyau, ko ka samu farin ne amma sai munin tsiya babu fasali.
Laptop yake danna wa cikin nutsuwarsa.
Wani irin faɗuwar gaba taji har sai da ta dafe ƙirjinta a hankali tana faɗin.
"Hasbunallahu Wa Ni'iaml Wakil"
Ashe a jikin pictures bata ga haɗuwa ba, kamar yanzu da take ganinsa a fili, sai taji gudun zuciyarta ya ƙaru sosai.
Har ta shiga shock ɗin da ta manta batayi sallama ba, tasa kai sai tafiya take, ƙananun idanunta masu kyau, akansa ta shagala sosai, wanda idan ka an kare kallo ɗaya zaka gane tana cikin shaukin kallonsu.
Fu'adh da tun tuni ya an kare, bata tantance ba taji muryan Fu'adh ƙasa² yan faɗin.
"Ki nutsu kiyi sallama karki ƙarasa babu sallama za'a samu matsala, dan Wlh uffan bazai ce dake ba, sai dai ki gaji ki tafi."
Ai take hankalinta ya dawo, ta tattaro jarumta, hankali tace.
"Assalamu alaikum."
Ba tare da ya ɗago ba a nutse cikin kamewarsa ya furta.
"Wa'alaikumoun Salam."
Ya faɗa yana ci gaba da danna laptop ɗinsa.
Zata zauna ƙasa can nesa da shi ƙasan Carpet, fu'adh yace.
"Bismillah ga guri ki zauna."
Kanta ta girgiza tana ƙarasa zaman akan lallausan Carpet ɗin, da takejin daɗin zamansa saboda taushinsa.
Tana ƙarasa zaman a hankali tace.
"Nagode nan ma yayi, Yallaɓai ina yini?"
Yah Boss ba tare da ya ɗago ba ya amsa da
"Lafiya, ya jikin?"
Daga haka yaci gaba da duba laptop ɗin.
A hankali ta amsa da
"Alhamdoulillah da sauƙi, Nagode da taimako Allah ya saka da alheri"
Fu'adh yace" Ameen, Sir yana son sanin minene ya fito dake a wannan lokacin kina ruɗe har kika shiga gaban mota aka bugeki, kuma Dr Majid ya faɗa mana irin sambatun da kika yi har kina kalaman da suka nuna anso yin raped ɗinki?"
Kanta a ƙasa hawaye har sun ciko idanunta, a hankali tace.
"Sunana Juhainah Abubakar mai Kanwa,mu yan jahar Bauchi ne, Misau iyayena basu da ƙarfi,mu huɗu ne ya'yansa. Babbar yayarmu ta ɓata tun tana ƙarama, lokacin ko ni ba'a haifa ba, anyi nema har an gaji akayi haƙuri da ikon Allah, yanzu mu uku ne, nice ƙarama.Yaya Musbah yanada matsalar taɓin hankali, wanda hakan bai barsa yayi karatun Boko ba, gwara ma na islamiyya shima ba sosai ba, saboda baya yin ko an koya masa, haka akayi haƙuri aka rungumi ƙaddara, saboda ba wata magana ba yake sosai.
Wani lokacin ma idan ciwon ya tashi a yaci baya sha sai ya kwashi kwanaki haka.
Sai Aunty Hibbah yayata tanada aure da yara biyar mijinta bayada ƙarfi haka iyayensa rabin gidan itane take kamawa da ƴan sana'o'in ta, kuma malamar makarantar primary ce, ta temakawa gidanta ta taimaka mana, tunda bamu da wani ɗan uwan na kusa da zai temaka mana, kowa yanzu kansa ya sani.
Lokacin da na gama secondary school nayi jamb, daƙyar cikin azaba ina murna zan shiga jami'a, daga nan ƙaddarata ta fara, na haɗu da wani ɗan mai kuɗi Mansoor ɗan cikin garin Bauchi ne, iyayensa nada hali sosai, ganin yafi ƙarfina nace masa yayi haƙuri ruwa ba sa'an kwando bane, kowace ƙwarya akwai abokin burminta, amma sam yaƙi ya nace shi dai aurena yake son yi, ni kuma inajin tsoron ba lallai iyayensa su yarda ba, hakan ya saka naƙi amince masa, shi kuma ya nace min koda yaushe yana hanyar Misau, babu abinda baya yi wa mahaifiyata na kyautatawa, haka yana son yaya Musbah sosai har ya saba da shi, ciwon da Mama take fama da shi na zuciya tun ƙuruciya na ɓatan ƴarta, shigowar Mansoor rayuwarmu sai komai, ya canza Mama ta warke ta kama ƙarfinta, har Aunty Hibbah yake temakawa sosai, wannan halayyar tasa da ƙaunar ƴan gidanmu da yake,sai naji matsananciyar ƙaunarsa ta kamani, har Bansan lokacin da na amincewa soyayyarsa ba.
Da yake komai rubutaccene daga Rabbil'samawati, sai ga shi iyayen nasa sun amince da aurenmu, saboda suna son ɗansu sosai babu damar suƙi abinda yake so.
Cikin watannin da basu fi biyar da fara soyayyar mu ba, iyayensa suka zo neman aurena, gun ƙanin mahaifina wanda yayi watsi da rayuwarmu, amma ganin masu arziƙi ne suka zo neman aurena, lokacin ya nuna shi uban mu ne, duk da shima sai ya fita yake samo abinda zai bawa iyalinsa.
Kafin watannin da aka saka na auren mu yazo Mansoor ya gyara mana gidanmu an shafesa da siminti har tsakar gidan da yake ƙarami ne.
Komi da ake yiwa ƴar gata haka Mansoor ya min lefe na kece raini, ya ba wa Aunty Hibbah kuɗaɗe masu yawa yace tayi min sayayyar komi na kayan aure, nida ita da Mama mun sha kukan farin ciki.
Kwance tashi har rana ta zo aka ɗaura aurena da Mansoor, aka sha biki, aka kwasheni zuwa Bauchi ina kukan rabuwa da mahaifiyata da ƴan uwana.
Haƙiƙa nayi alfahari da auren Mansoor saboda ya bani dukkan wata kulawa da so da ƙauna da mace take fatan samun irin mijina.
Cikin watanni uku da auren mu ya cike min komai na samu admission nan Bauchi na fara karatu a jami'a, cikin gata da kulawa tare da soyayyar mijina.
Shekarar mu ɗaya da aure Allah ya bamu ƙaruwa ta juna biyu, Allah ya temakeni bai zo min da laulayi ba, hakan ya saka naci gaba da karatuna cikin nutsuwa.
Sai da cikina ya shaga watan haihu ne na daina zuwa makaranta.
Banfi sati biyu da fasa zuwa ba na haifi kyakkyawar ɗiyata wacce tazo da ƙoshin lafiya, ranan sunah taci sunan mahaifiyar Mansoor Rahama muna kiranta da Nadrah.
Ranan da Nadrah ta cika shekaru biyu a ranan na shiga gararin rayuwa ƙaddara rabuwa da Mansoor ya sameni wanda nafi shekara ko maganar kirki banayi saboda tashin hankali da masifar da iyayensa suka jefani acikinta.
Ina makaranta nake sauri na dawo domin zamu haɗawa Nadrah birthday dan ayi komai har cake nayi an gyara wajan da za'ayi birthday.
Ina hanyar zuwa daga makaranta da kaina nake driving, wayana ta fara ɗaukan ruri,
ganin number babu suna ya sani ban ɗauka ba, amman ganin kiran yayi yawa na gangara bakin titi na tsaya na ɗauki kiran, abinda naji ne ya kusa dakatar da numfashina.
Wani irin kuka ne ya kuɓuce wa Juhainah babba a dai-dai wannan lokacin, wanda sosai ne take yinsa ta haɗa kai da guiwa.
Sai a lokacin Yah Boss ya ɗago kansa ya zuba mata lumsassun fararen idanunsa, bai dai ce uffan ba, kallon seconds 5 ya mata ya janye idanunsa, dan baya yiwa mace da ba ta gidansu ba kallon da yafi seconds biyar.
Fu'adh ya yi gyaran murya zai mata magana, Yah Boss ya dakatar da shi, ta hanyar ɗaga masa hannu yana girgiza masa kansa.
Tafi minti biyar tana kuka kafin tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ta furta.
"Ya Ubangiji bazan gaji da kai kukana wajanka ba, idan wani ne yayi sanadin mutuwar Mansoor ya jefa rayuwata cikin ƙunci da baƙin ciki aka Rabani da Ƴata Allah ka sakamin ka toni asirin koma waye kafin nima na bisa inda ya tafi."