← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 113

Sashe 67

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai ɗago ba cikin nutsuwarsa hankali kwance, yana danna System hankali ya furta.
"Haka ne kam tunda nine na matsa kika aureni ba, toh kizo ki ƙwaci haƙƙin naki mana, ya muka yi dake kafin aure? Wlh bazan taɓa miki abinda kike so ba, Please kije karki sake shigo min ɓangare na tunda bana muradin ki, har cikin zuciyata ALLAH ya sani, shi yasa tun farko na faɗa maki gaskiya kika ce kinji kin gani, Wlh ban taɓa zaton ma zaki tunkaro Ni da wata magana da ta shafi wannan ba.
Duk randa kika sake min magana irin wannan zaki ga me zanyi, tunda ba'a zaman aure dole ba'a so dole, ke baki isa ki canza min ra'ayi na ba, fita don Allah..."

Ya ƙarasa maganar hankalinsa kwance yana danna System ɗin.
Zarah cikin kukan nadamar aurensa da ta tirsasa kanta, tunda ya faɗa mata gaskiya taƙi ji, amma bata taɓa zaton haka yake da kafiya ba, da bazata yi wannan gangancin ba na auresa, da ta haƙuri ta roƙi ALLAH mafi alkhairi.
"Shi kenan naji Allah ya baka haƙuri Abubakar, ni na jawa kaina ko mi ka min, da nabarwa Allah zaɓinsa da haka bata faru ba, zan zauna na wani lokaci Sbd bakin jama'a in sha Allahu da kaina zan nemi saki, amma ina so ka teka maka min na fara zuwa aiki takarduna na nan komai na gyara daga Jigawa."

Bai kalleta ba baice uffan ba.
A hankali cikin kukan takaicin sa kamar zata rufesa da duka dan babu halin hakan tace.
"Inason ka min haya na fara zuwa Court"
Dan ta tafi ta basa guri a hankali ya furta.

"Okay kije naji"

Kayan tea ɗin ta kwashe cike da haushi ta nufi hanyar barin parlour kamar zata tashi sama.
Bai masan tanayi ba.
Da ƙarfi ta buga ƙofar ta fice.
Tsaki Yaja a hankali ya furta.
"Bansan me yake damun wasu matan ba, basu da kamun kai da sanin darajar Kai..."

Khairat yau sun daɗe suna fira da Fu'adh tana can Down Stairs, sai kusan sha biyu ta hayo Stairs, lokacin da tazo ta iske Suhaima ta bacci suna manne da Juhainah.
Dariya tayi tunda ita bata san me ya faru ba, ta kashe masu fitala ta tafi gun Al'amin kar a barsa shi ɗaya.

Yah Boss yana gama abinda yake sai da ya kuma shan tea ɗin ya miƙe ya murzawa key ƙofar parlour ya kashe wayoyinsa ya nufi bedroom.
Brush yayi tare da alwala ya fito ya kunna Ac ya kashe fitilun ɗakin ya kunna ta gefen Bed ya haye yana shiga lallausan quilt, ya ɗauki hular Juhainah da ta manta ya ajiye gefe yana lumshe lumsassun fararen kyawawan idanunsa, a hankali yake karanto addu'o'in kwanciya bacci.
Sbd gajiyar da yake ciki yana gama addu'ar ko minti uku bai ƙarba sai bacci.

Ɓangaren Zarah tana sauka sai da taje ta zubar da tea ɗin kar wani ya sha a samu matsala, har zata je ɗakin Hajjah Mama ta fasa ganin me ma zata ce tunda masifarta ta janyo mata auren wanda baya muradin ta cikin rayuwarsa.
Kowa na bacci amma Zarah baƙin ciki da tunanin hanyar da zata bi ta saka Yah Boss yayi laushi, Sbd bazata bar gidan nan a banza ba, tana son ta mori aurenta koda sau ɗaya ne, ai dai tabar tarihi.

Toh wannan tunanin shi Zarah ta kwana tana yi har kusan asuba, kafin bacci ya sace ta.



Washegari
Ta kama yau laraba ɗaurin aure sauran kwana 2.
Misalin ƙarfe 8:20Am.
Nasir tsaye cikin shiri sanye da uniform ɗin Soja, sosai yayi kyau kakin Sojojin.
Tsaye gaban dressing mirror yana fesa turarensa mai sanyi ƙamshi da tsada.

Wayansa ta fara ringing.

Yayin da Hanifah take zaune gefen Bed tana kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi a hankali tace.
"Masoyi kayi kyau sosa, kullum idan ka saka uniform kamar an canza ka"
Turaren ya ajiye yana gyara hular ya kalleta ta jikin mirror ɗin ya kashe mata ido ɗaya tura mata kiss ta laɓɓansa.
Ƴar dariya tai tana faɗin.
"Kamar na biki gun aikin Wlh Masoyina"
Idanunsa masu lumshewa ya kafe Phone ɗinsa Samsung da take ringing.
Sunan
Hairat Yunus yake yawo saman screen ɗin wayar.
Hanifah ta miƙe ta matso jikinsa tana rungumeshi ta kalli Phone ɗin gabanta taji yana faɗuwa ganin sunan mace na yawo saman screen ɗin wayar mijinta.
Amman tsoronsa ya hanata magana taja wata rigimar kuma.
Kiran ya katse bai ɗauka ba ya ɗauki wayansa ya saka cikin aljihun wandonsa na kakin Soja.
Hanifah ya kalla yana ɗaga mata gira guda a hankali ya furta.
"Ni zan wuce sai dare in sha Allahu"

Ƙamƙame shi tai a hankali tana faɗin.
"Toh Allah ya kiyaye ya bada Sa'a"
Kanta ya shafa yana sumbatar kan nata a hankali ya amsa da.
"Ameen my wife ki kula da kanki"
Hannunsa ta riƙe ɗayan yana ɗaukan bindigarsa yana zurata gun zamanta a jikinsa.
Anutse suka fito parlour suna tafiya Hanifah hankalinta idan yayi dubu ya tashi number Hairat Yunus ta tsaya mata a ranta, tsoronsa ya hanata magana.
Suna fitowa farfajiyar gidan ana sake kiran bai ciro wayan ba ma bare yaga waye me kiran.
Ita ta buɗe masa ƙofar motar ya shiga ya zauna a hankali yana faɗin.
"My Hanifah akwai baƙi fa gidan Maah kije gaishesu, maybe ma ba'a rasa abinda za'ayi aiki gidan ba, can gidan su Ango masu Company kayan ɗakin da aka siya su za'a su saka komai yau, Kenan kije can gidan idan kin gama abinda kike anan ɗin, inda yaso sai kuje gidan Juhainah bazaku rasa aikin da zaku yi ba, na gyara"

A hankali ta amsa da.
"Ok my husband in sha Allahu zanje"
A hankali ya furta.
"Thank you my Hanifah bye"

Ya Ƙarasa maganar yana yiwa motar key yaja ya nufi gate yana horn.

Hanifah ta nufi ciki ranta a ɓace tana faɗin.
"Wlh ba uban da zai kaini gidan Maah, shegu tsinannun, inje ana yimin kallon banza ko, hummm! Sai naga dama zanje da yamma"

Tana shigowa parlour ta ɗauki wayar ta ta kira ummah.
Lokacin suna kan dinning har Baban su Hanifah, kyakkyawan dattijo suna kama da Hanifah.
Tana ganin kiran Hanifah ta miƙe tsaye tana ɗaukan wayan ta fice Babah Lamiɗo yace.
"Sweety don Allah ki zauna ki gama breakfast ɗinki kafin ki fara aikin naki na waya kamar mai aiki a kamfanin waya"
Harara ta zuba masa tana faɗin.
"Wai don Allah Lamiɗo me yasa kake son shiga rayuwata? Kai kaci abincinka mana kaida Ƴarka."

Ta ƙarasa maganar tana turo masa baki kamar wata yarinya.😂
Ta juya ta fice tana picking call ɗin.
Babah Lamiɗo ya girgiza kansa yana kallon Zara'u yarinya ƴar shekaru 4, yayanta Saanih yana school.
Mahmoud Hanifah Jawahir duk suna gidajen auren su.
A gaskiya Mahmoud mutum ne mai hankalin da nutsuwa, duk da shi wani lokacin maitar na motsa masa, sai dai yanada ƙarfin imani bai iya cin mutum sai dabbobi, suma shi yake kiwon abunsa idan maitar ta motsa yaci abunsa tunda babu yanda ya iya, abun kamar iskokai haka suke zuwar masa, sosai yake ibada da roƙon Ubangijinsa akan ya sassauta masa kuma kar Allah ya kawo ranan zai ci mutum bazai iya da zunubin ba.

Alhamdoulillah! Har zuwa yau ɗin bai taɓa kama kowane irin mutum ba a duniya, dan tun yana yaro mutum ne mai haƙuri da kawaici.
Yanada mace ɗaya da ya'ya biyu mace da namiji kyawawa, sunan iyayyensa ya saka.
Matarsa ba Mayya bace, haka ƴaƴansa Ubangiji bai sa suka gajesa ba, sbd duk wani abu da ake faɗa inda yaro yana jariri aka basa dan kar yaga maita TOH Mahmoud yana ƙoƙarin yinsa bare Daman mafi yawancin anfi samun maita mai ƙarfi idan ansha Nono uwa.

Jawahir ma tana zaune lafiya da mijinta da ƴarta ɗaya, itama dai irin na Hanifah ne bata ci saboda an nakasa ƙarfin maitarta tana jaririya, ita kam tafi Hanifah hali mai kyau, sanin halin mahaifiyarta bata taɓa faɗa mata abinda ya shafi gidan mijinta ko fira dangin mijinta, duk da kuwa wasu daga cikin ƴan uwan mijinta basa sonta suna tsangwamarta amma ta shanye abun a ranta tana ƙoƙarin zama da kowa lafiya.

Shiyasa Ummah tafi shiri da Hanifah akan Jawahir, Mahmoud kuwa daman duk da tana mahaifiyarsa bai bata wata fuskar da zata masa halin yarinta da ta saka a gaba.
Kuma har yau ba'a yi katari yaji daga waje tana bin maza ba.

Babah Lamiɗo yana kallon ƴarsa yace.

"Zara'u ! Ummanki aljannun yara ne a jikinta bata da hankali ko kaɗan, Wlh badan ina mugun sonta ba da na ƙara aure ko ta gyara halinta na rashin ganin girmana da yawan fita yawon biki"

Umma bedroom ɗinta ta nufa tana amsa wayan.

"My daughter ta wajena yarinyar albarka ya akwai labari ne?"

Hanifah ta zauna kamar zata fashe da kuka tace.
"Umma akwai gagarumar matsala Wlh, my Nas jiya ya shigo min gida da wani irin turaren mata mai shegen ƙamshi ajikinsa, ina magana ya fara min masifa sai hƙr na basa nabar abun a zuciyata.
Yanzu kuma naga number wata tsinanniya wai Hairat Yunus tana kiransa, amma bai ɗauka ba, Wlh nasan yana fita zai kirata bazata wuce budurwarsa ba, ummata ya zanyi?"

Umma tace.
"Wai Nasir kikaji ƙamshin mace a jikinsa? Kai jama'a, mutum baida tabbas ashe shima ƙwallon ɗan iska ne ban saniba? Toh ko itane take kirasa? Ai daman sojoji sai mai ƙarfin imani ne yake tsara kansa, ƴan iskan ciki sunfi yawa.."

Hanifah kamar tayi kuka tace.
"A'a gaskiya ummah bari ce masa ɗan iska, ya ina faɗa maki Abinda yake damuna kina son ƙaramin ɓacin rai, toh inda kuma cakumesa tai ta faɗo jikinsa fa?"

Umma tace.
"Hanifah ina rabaki da daurewa namiji ƙugu, zakici uwarki in dai namiji ne, ba'a ɗaure musu ƙugu, toh idan Kinsan haka ne uban me zan miki kika kirani?"

Hanifah tace.
"Umma Ni dai ki temakeni nagano wannan Hairat Yunus ɗin dan uwarta tabar min mijina"

Umma tace.
"Toh ni nasanta ne? Sai dai idan zuwa sanyi gidan malam Murtala ya bincika muga ko za'a dace, amma sai zuwa gobe daren juma'a yau baya duba"
Chapter 67 · 0% Book details