Sashe 57
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hayaniyar da su Aziza sukaji da sakin kukan hajjah Mama ta saka suka fito a guje su dukansu, tsaye sukayi daga can ƙofar parlour suna kallon ikon ALLAH.
Yah Boss ya kalli Hajjah Mama baice uffan ba, haka fuskarsa baka gane mi yake ciki.
Juhainah hankalinta ya tashi ta saki wayar tana miƙewa tsaye tana kallon Yah Boss.
Baka gane wani hali yake ciki a yanzun, abinda yafi ɗaga mata hankali kenan, ita tafi gane ya nuna ɓacin rai akan abu zata fi samun sassauci.
Ido suka haɗa da Yah Boss ta farin Glass ɗin da yake manne akan kyakkyawar fuskarsa.
Hannunsa ɗaya cikin aljihunsa, fuskarsa babu wani alamar damuwa, ko tashin hankali.
Suhaima ta saki hannun Yah Boss tana bin su Zarah da mugun kallon ƙyama.
Ta isa gun Juhainah tana rungumeta tana faɗin.
"Yo mi Aunty J tayi da za'a ce ta lalace, Allah ya rabata da lalacewa. Please My Dadd kace wani abu mana, ko bakaji me hajjah Mama take faɗi akan Aunty J ba"
Suhaima ta ƙarasa maganar tana sakin kuka....
🤣Kai jama'a nace Zarah tana ganin jalala, ga hajjah Mama na neman nuna Juhainah ta iskance a gaban su Zarah, da suka kirata karuwa, ko wani matakin Yah Boss zai ɗauka akan Juhainah, da sakin zancen da tai, gefe kuma da su Zarah da suka lafta mata mari har 2.😂
Juhainah Fan's Gobe muna biki bazaku jini ba, kuma idan bakuyi comments da Sharhi ba, Wlh a Monday ma bazaku jini ba, amma idan kunyi in sha Allahu ran Lahadi ma zan ƙoƙarta na baku ko ba yawa. Sbd inason mu gama Book One kafin azumi.💃🏻🥰
[08/02 17:15] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo
Masoyen Juhainah Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kaɗan-Kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books ɗina, A Channel ɗin.
Wanda Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku.💃🏻
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx
*Page 31*
Jamal
A lokacin da ya fito daga part ɗinsu Mamy Allah ne ya kawosa part ɗinsa lafiya.
Yana shigowa parlour sa ya zube saman Sofa yana dafe kansa da tafukan hannayensa, ya runtse manyan kyawawan idanunsa a hankali yake faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Wannan wata iriyan ƙaddara ce take bibiyata? Daga yin recording dan suji a fasa auren sai kuma a ƙara wa abun armashi. Allah ya isa tsakanina da Surayya, wannan yarinya ta ceceni Wlh, duka² nawa nake zasu ƙaƙaba min aure. Auren ma Juhainah fanɗararriya"
Wlh ko kare bazan gayyata ba, babu wani abu da zanyi na biki, zasu ga yadda ake auren ƙiyayya, tazo ta zauna taci uwar da zataci a gidan..."
Ya ƙarasa maganar yana miƙewa ya nufi bedroom yana tangaɗin takaicin da aka kumsa masa yau...
★
Khairat ta zaun daɓas akan Chair a tana dafe kanta, tare da faɗin.
"Ya ALLAH! Wannan fitina da ta kunno kai duk laifin Juhainah ne"
Ta ƙarasa maganar a hankali yadda Yah Boss bazai ji ba.
Kiran Fu'adh na shigowa wayarta bata ɗaga ba, saboda bata da nutsuwar ɗaga kiran a Yanzu.
Al'amin shima yaje ya rungume Juhainah da Suhaima, yana kallon su Zarah.
Yah Boss ya kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa akan Suhaima da Juhainah da Al'amin.
A hankali ya furta.
"Ok alright My Babies zanyi magana, kibar kukan Ok?"
Kai Suhaima ta ɗaga.
Hajjah Mama tana salallami tace.
"Yanzu Zainab haka kika ƙullace ni a ranki? Ai ke idan baki gane abinda Bilkisu take nufi ba ni na gane, wane irin sake ne wannan saboda Allah, yaushe Bilkisu duk ta san wannan al'amari...!"
Yah Boss yay saurin tare maganar hajjah Mama ganin su Zarah sun fito, sun ƙura masu ido, su na son jin me ke faruwa.
Cikin wata irin kamewa ya furta.
"Please calm down hajjah Mama."
Ya Ƙarasa maganar ya
kamata ya zaunar da ita a hankali cikin kwantar da murya, yadda babu wanda zaiji sai ita da yake yiwa magana ya furta.
"Kiyi haƙuri hajjah Mama, yarinta ne ita kanta, Bilkisu bata san me take faɗi ba shirme take just.
But zanyi maganinta duk da hakan, kibar maganar akwai baƙi kar a ɗauke mu mana Mamana ki yi hakuri ya isa zanyi maganinta, Karki damu"
Hajjah Mama tana fato majina a gefen mayafinta tace.
"Shi kenan Abbana, na fasa tafiya ko ina sai naga matakin da zaka ɗauka akanta dan ina nan na fasa tafiya goben lamarin Bilkisu akwai tsoro, idan aljanun ne ma ayi maganin su"
Yah Boss a hankali ya furta.
"It's okay Mamana anan zaki zauna ko can gidan Papa?"
Duka ta kai masa a hannunsa tana faɗin.
"Anan gidan zan zauna bana iya hawa Beni a share min ɗaki anan ƙasa"
Yah Boss ya furta.
"Ok alright Hajjah Mama, amma yanzu ki tashi na kamaki mu hau Benin ki kwana zuwa gobe sai ki dawo down stairs ɗin."
Da ƙyar ta amince ya kamata ya shagalar da ita dasu Zarah na tsaye yana mata hira suka tafi da yake ba hanyar da suke hanyar Stairs take ba, shi yasa bata ma lura dasu ba.
Inna Laure Ramlah Azizah Yaganah sun sha mamakin Yah Boss da Bai ko kallesu ba, suka tafi.
Jiki a sanyaye suka koma parlour suka zauna suna jiran suji me zai biyo baya.
Juhainah ta kamo hannun Suhaima dana Al'amin suka nufi hanyar Stairs.
Khairat ta miƙe ta nufi parlour Zarah.
Sunyi cirko-cirko ta buɗe ƙofar ta shigo da sallama bakinta.
Kallo ɗaya suka mata bayan wanda suka mata a parlour suka gane ita ƙanwar Yah Boss ne akwai kama duk da bata da ƙarfi kamar ta Aunty Sumy ba.
Amsa sallamar sukayi.
Ta ƙaraso tana zama kusan Aunty Zarah tace.
"Barkanku da zuwa fatan anzo lafiya?"
Suka amsa da.
"Lafiya lau"
Inna Laure tace.
"Ƙanwar mai gidan ce ko?"
Khairat tana murmushi tace.
"Eh don Allah kuyi haƙuri da shimen Juhainah, yarinta ke damunta, ina Auntyn namu?"
Azizah ta nuna Zarah tana faɗin.
"Ai amarya ta fita daban itane kusan ki"
Zarah ta danne damuwarta ta saki fuska tace.
"Kenan itane Juhainah? Ke mi sunanki?"
Khairat tace.
"Eh itace, sunana Khairat"
Zarah tace.
"Wlh bansan ita bane, ma sha Allahu sunan ya dace dake, ya karatu?"
Zatayi magana kiran Fu'adh ya sake shigowa wayarta, ta kalli Zarah tace.
"Aunty sai anjima zanje na amsa waya"
Ta ƙarasa maganar tana picking call ɗin ta nufi ƙofa a hankali tana shagwaɓe murya tace.
"Assalamu alaikum Heart"
Zarah tace.
"Yarinya me kirki Wlh"
Duk ba wanda ya tankata, dan duk su na shaƙe da takaicin Yah Boss da ya dizga su babu ko kallon arziƙi bare sannu da zuwa.
Daga can Fu'adh da yake ɓangarensa na gidan Yah Boss, zuwansa kenan daga gidansu, ya amsa sallamar yana kwaikwayon maganarta, hankali ya furta.
"My heart I miss you, wai kin damu dani kuwa? Ina kikaje ina kira har kusan sau 4 baki ɗaga ba?"
Khairat tana ƙoƙarin zama a parlour take faɗin.
"Miss you too heart, Wlh kana raina exam muka fara jiya, ai na faɗa maka, Yanzu kuma ina wani ɗan uzuri ne shiyasa ban ɗaga ba, ya gajiyar yanzu ta fita ko?"
Fu'adh yayi murmushi yana faɗin.
"Toh Alhamdoulillah dai, ki fara shiri dasu Abbu ya sake min magana akan ki, ki temakeni Heart mu shige daga ciki Please."
Khairat tayi murmushi tace.
"Heart yanzu ya kake so ayi kenan?"
A hankali ya mata raɗa.
"Ki bamu dama su Abbu suzo neman auren na saki daga ciki, wlh hankali na bazai kwanta ba, idan ba an rataya miki igiyata uku akanki ba, inafa sane da duk Mazan da suke kawo miki wawa a AUN American University, har ɗan anacin wannan na sani acikin malamanku wai shi Sheikh Jibril ko?"
Khairat tai ƴar dariya tana faɗin.
Amma dai kasan kai nake so ko?"
Fu'adh yana murmushi cikin farin ciki yace.
"Yeah Heart Amma sharrin maza nada yawa, kar naje ayi min wata iri, nidai gaskiya ki faɗa za'a zo neman min auren ki"
A hankali tana narke murya tace.
"Ok shi kenan zan faɗawa Aunty Sumy sai ta faɗawa Maah, Maah ta faɗawa Papa da Ƴah Sadeeq, dasu Yah Mustapha Umar Nasir, sai muji me zasu ce ko? Wlh ni kunya nakeji bazan iya faɗa masu ba"
Fu'adh ya marairaice yana faɗin.
"Please gobe ina son mu zauna muyi magana sosai, na daɗe banji ƙamshinki kusana ba, da daddaɗar muryanki da kyakkyawar fuskarki ba, gobe juma'a da wuri kuke sauka idan anyi sallar juma'a gunki zan shigo ba lunch zai kawoni ba, Heart please, kuma ki sanar da Aunty Sumy fa"
Khairat tace.
"Toh shi kenan heart naji, zan faɗa mata sai kazo, gobe ai da wuri zan dawo..."
Hira sosai suke cike da so da ƙaunar juna...
Yah Boss bedroom ɗin su Suhaima yakai Hajjah Mama, ya shimfiɗa mata katifa sabuwa mai daɗin kwanciya batada tudu.
Lallausan Duvet ya shimfiɗa mata.
Yana kallonta tana zaune saman gadon Al'amin ya kamo hannunta yana faɗin.
"Hajiya Mama kwanciyar zakiyi ko kallon TV?"
Hajjah Mama tace.
"A'a kwanciya zanyi dare yayi ni dai don Allah ka ɗauki mataki, a rage auren Bilkisu ayi kwana nan"
A hankali ya furta.
"Ok alright Hajjah Mama ki kwanta karki saka komai a ranki"
Hajiya Mama ta kwanta tana washe baki tace.
"Yawwa Nagode Allah ya maka albarka Abbah"
A hankali ya amsa da.
"Ameen ya Rabbi Mamana, sai da safe"
Ya ƙarasa maganar yana ɗaukan remote ya kunna mata A'c ya fice yana rufe ƙofar, a ransa yana shirya yadda zai yi maganin Juhainah ko fitinar ta zata rage.
A ƙofar falo suka haɗu.
Juhainah ta saki hannunsu Suhaima ta nufi gunsa.
Yah Boss ya kame fuskarsa sosai yana ƙoƙarin wuce su, ko kallon Juhainah bai ba.
Cikin tashin hankali tai saurin kamo hannunsa tana sakar masa kukan shagwaɓa.
Suhaima ma kukan ta saki tana kamo hannunsa ɗayan.
Kuka suka saka shi gaba suna masa kuka tsakaninsu da Allah.
Juhainah
Cikin kuka take faɗin.
"Yah Sadeeq ai ni ba Ƴar iska bace ko?"
Jan hannunsu yayi suka fice daga parlourn, yana faɗin.
"Ku kama min bakin ku yanzu"
Shiru sukayi suna binsa.