Sashe 95
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mamy ta amsa da Jamal.
Yah Boss ya gaishe da Mamy, ya nufi kujera dan zama.
Jamal ya gaishesa ya amsa yana tafiya.
Surayya da Faridah suka gaishesa.
Ya amsa can ƙasa
Dijeh ta murza idanunta tana zaro su ta washe baki tana kallon yadda Yah Boss yake tafiya tace.
"Alquraan ahe Larabawa ma suna kyau, cikin higar Hausa Fulani..."
Surayya ta fizgota tana buge mata baki tace.
"Wai ke bakinsa wacece aka kawo asibiti ba? Auntynki Junainah ce fa"
Ai kuwa Dijeh ta ɗora hannunta akai ta fashe da kuka ta zauna zaman ƴan bori tana faɗin.
"Wayyo Antiya Jihinah ki tashi karki mutu ki barni ina sonki..."
Yah Boss da Bai ma san me ake ba, dan hankalinsa baya gare su jin ihu ya saka shi kallon gefensu.
Fuska kame ya furta.
"Surayya! A fitar da wannan yarinya daga nan, nan ba gun ihu bane, wannan ai shirme ne"
Ai kafin Surayya ta kai ga kama Dijeh, Jamal ya shaƙota ya wanketa da mari yana jan hannunta.
Mamy ta riƙe shi tana faɗin.
"Kayi wa ALLAH ka rufa mana asiri Malam Kamilu da Abbanku ko wani lokaci zasu iya shigowa, idan yaga kana dukar masa ƴa mun shiga uku"
Mamy ta amshi Dijeh a hannunsa tajata suka fice.
Reception tajata suka zauna, tana goge mata hawayen fuskarta tace.
"Khadijah don Allah ki rage yawan surutun nan, kalli marin da Jamal ya miki, Matarsa babu lafiya kinata shime kinga yayanta ma yaji haushin ki, kuma shine zai biya miki makaranta idan kina shime zai fasa"
Dijeh tace.
"Mamy Bazan ƙara ba yayi haƙuri..."
Abba ne da Malam Kamilu da Naziru yayan Jamal suka shigo reception ɗin suka hango Mamy da Dijeh zaune.
Mamy tace.
"Kun iso?
Abba yace.
"Wai mi ya faru da ita? Jinnun ne ko zazzaɓin ne? Surayya ta kirani tana kuka tace, Jamal ya kawota asibiti a sume"
Naziru kyakkyawan ne da yake ba garin yake aiki ba, Kaduna yake jiya bai samu zuwa ba, yanzu zuwansu shi da matarsa da ƴarsa Aymana.
"Mamy ina Jamal ɗin?"
Mamy tace.
"Nazir saukar yaushe sannu da zuwa, Jamal yana can ƙofar emergency"
"Abban Abdul wlh bansan mi ya sameta ba, sai ta farfaɗo muji, muje yayanta ma yana can zaune."
Dukansu suka dunguma ciki.
Jamal sai hucin haushin Dijah yake, ya nufi ƙofar room emergency.
Ta ɗan Glass saman ƙofar yake leƙe.
Dr Majid nata ƙoƙarin ceton ran Juhainah.
Ji yayi hawaye sun silalo masa akan fuskarsa.
Yayi saurin gogewa a hankali yace.
"Astagfirullah in sha Allahu bazan sake mata wasan saki ba. Baby J ALLAH ya baki lafiya wallahi ina sonki Bazan sake ɓata miki rai ba."
Nasir cikin dabara ya fito da MAAH suka shiga Mota baice mata komai ba, har suka fito.
Sai da ya hau bakin titi Maah ta kalleshi tace.
"Abdulnasir! Autah ta wani abun ya sameta ne?"
Nasir yace.
"Maah Wlh Yah Sadiq ya kirani yace in kawoki Special Clinic Janfar, bansan waye baida lfy ba, kin san halinsa idan baiyi niyya bazai faɗa waye baida lfy ba, sai munje mugani."
Maah hankalinta taji ya tashi tace.
"Toh ko minene ya Ubangiji ka bamu ikon juriya, ko waye ba lfy Allah ka basa lfy Amin"
Nasir ya amsa da.
"Amin ya Allah Maah"
Yah Boss zaune yana waya su Abba suka shigo. Ganin sa suka nufi gunsa.
Yana ganinsu yayi sallama da wanda suke wayan ya miƙe dan basu girmansu.
Sallama sukayi wa juna suka yi musabaha, ya gaishesu ya koma ya zauna.
Abba da Naziru da Malam Kamilu suka isa gun Jamal da yake tsaye a bakin window.
Rungume Naziru Jamal yayi.
Nazir yace.
"Jamal! Kuka kake yau akan mace? Eh lallai so ya kama ka da tsauri, ya jikin nata?"
Jamal ya Gaza magana.
Abba ya kamo hannunsa suka zauna, ya shiga lallashinsa.
Mamy da kanta abun ya bata mamaki.
Papa da Mustapha and Umar suka shigo.
Papa suka gaisa dasu Abba da Malam Kamilu Naziru da Jamal suka gaishesu.
Bayan an gaggaisa su Papa suka tafi gun Yah Boss da yake zaune can gefe abinsa.
Mustapha da Umar suka gaishe da Yah Boss ya amsa.
Papa ya zaune yana kallon Yah Boss yace.
"Minene ya sameta haka Abbah?"
A hankali ya furta.
"Papa ina zan sani sai ta farfaɗo tunda ina zargin kamar lokacin da abin ya sameta mijinta baya gidan..."
MAAH ce da Nasir suka shigo.
Surayya idanunta bai sauka ko ina ba bisa tsautsayi sai a cikin na Nasir.
Gabanta ya yanke ya faɗi.
Ya zaro mata lumsassun kyawawan idanunsa, yana kame mata fuska ya juya mata idanun nasa.
Ba shiri tai ƙasa da kanta, tana jin jinin jikinta yana wani irin mugun gudu.
Tsaf ya janye idanunsa daman duk wannan abun a kaikaice ya mata shi, ba wanda zai gane sai ita da akayi wa.
Mamy ta tarbi MAAH suka gaisa tare da riƙe hannun juna.
Nasir ya gaishesu ya wuce gun yayunsa.
Surayya ta miƙe tazo ta gaishe da MAAH cikin girmamawa.
MAAH ta amsa tana faɗin.
"Zargina ya tabbata Juhainah babu lafiya har haka wannan jama'a?"
Surayya ta jinjina kanta.
Maah tace.
"TOH Ubangiji ya bata lafiya"
Jamal ya taso yazo ya rusuna ya gaishe da MAAH ta amsa fuska a sake tace.
"Ya me jikin Jamal? Allah ya bata lafiya"
Ya amsa da.
"Ameen ya Allah Maah"
Maah ta isa gunsu Abba ta gaishesu ta wuce gunsu Papa, tunda kowa yana zaune da jama'arsa ne.
Zama tayi tana kallon Yah Boss.
Ya kalleta a hankali ya furta.
"Sannu da zuwa Maah"
Murmushi ta sakar masa tana amsa tace.
"Ina alfahari dakai a matsayin ɗana yayan Bilkisu kuma, haƙiƙa ko yau na mutu Alhamdoulillah, ban bar baya da ƙura ba, akwai wanda zai tsaya mata a matsayin uwa uba yaya kuma garkuwa..."
Nasir yace.
"Yah Sadiq! Wai me ya sameta ne haka? Naga fa idanun mijinta jajir kamar kuka yayi."
Yah Boss ya kallesa baice uffan ba ya maida hankalinsa gun saƙon da yake shigowa iPhone ɗinsa.
Dr Majid ne ya buɗe ƙofar room emergency ya fito.
Ai baki ɗaya suka nufi gunsa daga su Mamy Abba jamal Nazir Surayya Dijeh da ta kama bakinta, da Farida.
Sai su MAAH su duka.
Dr Majid yana goge gumin goshinsa ya zuba masu idanu, kowa tambayar sa yake ya jikin nata banda Yah Boss da ya zuba hannayensa cikin aljihun rigarsa.
A hankali Dr Majid yace.
"TOH acikin ku wa zan amsawa kunfi ko goma sha? Alhamdoulillah ta farfaɗo, amma fa ɗakyar, bata ma cikin hayyacinta yanzu, Sbd fizge² take yi akwai alamar ma jinnunta na jikinta, Sbd na mata alluran bacci har yanzu bata yi bacci ba, amma waye take kira Yah Boss?"
Surayya da sauri tace.
"Yah Sadiq ne"
Dr Majid ya kalli Yah Boss yace.
"TOH a yanzu kai ɗaya zaka shiga gunta"
Jamal ya kamo hannun Dr Majid yace.
"Don girman ALLAH ka barni na shiga nima naga matata naga halin da take ciki"
Dr Majid zaiyi Magana Yah Boss cikin kamewarsa a hankali ya furta.
"Yes Dr Majid barsa muje tare idan addu'a ta kama zai riƙe min ita"
Dr Majid yace.
"Ok Sir muje"
Ya ba Yah Boss hanya ya wuce anutse, Jamal yabi bayansa.
Kwance Junainah take, ta fice daga hayyacinta, norses biyu tsaye a kanta sun riƙe hannayenta, sbd kar ta cire drip da aka saka mata.
Idanunta ma sha Allahu tar a buɗe sun ƙara girma.
Ana buɗe ƙofar ta kalli ƙofar.
Ido huɗu sukayi Yah Boss.
Wani irin kuka ta saki tana fizge hannunta daga hannun norses tayi watsi dasu sai gasu ƙasa kwance.
Tana ƙoƙarin fizge drip ɗin da wani irin sauri Yah Boss ya iso gunta ya riƙe hannayenta, a hankali ya furta.
"Calm down Bilkisu me yayi zafi haka TOH?"
Cakumesa tayi tana buga masa goshinta a nasa goshinta ta tofa masa yawo akan fuskarsa.
Yah Boss ya riƙeta sosai ya kalli Jamal yana faɗin.
"Jamal! Zo riƙeta"
Juhainah ta kalli wanda aka kira da Jamal, ta bari sai da yazo ya kamota jikinsa ta kamo wuyansa ta buga kansa da goshinta ta manna bakinta a wunyasa.
Yah Boss yayi saurin kamota ya ɗagata sama ya kwantar saman Bed ya, riƙeta da ƙarfin gaske, ta gaza ko motsin kirki yace wa Dr Majid.
"Dr zo cire mata drip ɗin har a samu su fita sai a maida idan ba haka ba ciwo zata jiwa kanta."
Dr Majid ya cire mata ƙarin ruwan dan norses ɗin sun fita, tsoronta ya kamasu.
Ana cire drip Yah Boss ya fara mata karatu cikin kunnuwanta, da wani irin sauti.
Ai kuwa wani irin ihu take tana kuka tana faɗin.
"Tsaya mu koma daman munzo tayata farin cikin sakinmu da akayi ne, ka tsaya mu koma tafiya zamuyi, tunda an barmana matar mu..."
Ai Yah Boss ko sauraronta baiba yaci gaba da karatunsa, ya mata wata irin riƙe wa ko motsi bata iyawa sosai.
Jamal ya zama ɗan kallo, yana jin shi jarumi ne ashe akwai maza gabansa...
Ai Jinnun nan ganin Yah Boss bazai saurara ba, ya buɗe musu wuta, azaba tayi azaba da gudun tsiya suka fice, ta hancinta.
Wata irin attishawa ta fara ajere har guda biyar.
Jikinta ya saki ta zube jikin Yah Boss tana ƙamƙameshi tare da sauke numfashi bacci take kamar tayi 1 hour tana baccin.
Yah Boss ya kwantar da ita ya gyara mata kanta saman pillow yana ƙoƙarin miƙewa ta damƙo tattausan hannunsa, tana ƙamƙamewa, tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ta kirasa.
"Yah Boss! My brother Habiby, i l..."
Yayi saurin ɗora tafin hannunsa wanda bata riƙe ba, akan lallausan laɓɓanta, ya rufe bakinta.
Ya kalli Jamal a hankali ya furta.
"Zauna kusanta kaci gaba da tofa mata addu'a.
Dr Majid mai da mata drip ɗin"
Jamal ya zauna kusan kan Juhainah, Yah Boss ya miƙe ya nufi ƙofar fita yana zuba hannunsa ɗaya cikin aljihunsa.
Jamal addu'a ya shiga tofa mata cike da tausayinta.
Dr Majid yabi Yah Boss.
Suna fitowa Yah Boss ya kalli Dr Majid a hankali cikin kamewarsa ya furta.