← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 127

Sashe 97

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mum Nurat taga sam bata ga gilmawar 'yarta ba, dan haka ta tafi É—akin Nurat É—in, tana zuwa ta tarar tayi wujuga wujuga saboda kuka, se rusa uban kuka take kamar ubanta ya mutu.

A É—an gigice tace "ke lafiya kuwa? Meye ya faru dake haka? Me akayi miki ne?"

Maimakon ta bata amsa, sema sake rushewa da kukada tayi, "ke bana son sakarci fa, menene haka? Meya sameki kike rusa wannan uban kukan haka?"

"Mummy baki ga hukuncin da aka yankewa Yusuf bane?"

"To idanma na gani me zanyi, ko kuma me zance? Allah ya bayyana gaskiya kawai, amma shine zakizo kina wannan uban kukan haka? Ai koni na mutu iyakar wannan kukan kenan"

"Mummy wai meyasa kike basarwa ne, baki san menene yake wakana ba? Kin san fa komai Mummy? Daga gidan nan fa ake shirya maƙarƙashiya fa kin sani fa"

Da sauri Mummy ta ƙarasa, ta tishe mata baki tace "dan ubanki yana cikin gidan nan, so kike ya jiyo yazo yai miki wani abun?"

Nurat ta fizge tace "Haba Mummy, meyasa zamu É—auke ido akan gaskiya Mummy? Wallahi ranar lahira muma harda mu a cikin wannan zaluncin da akayi, Mummy da saka hannun Daddy fa aka sace su Widad, Mummy da kunnena fa naji shi"

Maman Nurat na juyawa taga Alhaji Musa a ƙofar ɗakin, yana kallon su.

Nurat taƙi yin shiru tace "gaskiya Mummy idan mukayi shiru bamu da adalci, wallahi da saka hannun Daddy akan abunda ya faru, kuma kema kin sani, Wallahi da Daddy ake shirya komai, Mummy ya zakiji idan ɗankibaka yankewa hukuncin shekaru talatin da ɗaya a gidan yari? Kefa uwa ce Umma, bakya tunanin me mahaifiyarsa zataji a ranta a yanzu haka? Ancd shikaɗaine ɗanta amma an yanke masa hukuncin shekaru talatin da ɗaya a gidan yari "

Cikin tsawa Mummy tace " dan ubanki bazaki min shiru ba, seya miki wani abun tukuna? "

Nurat tace" Mummy nifa gaskiya nake faÉ—a, kuma ni zanje in bayar da shedar abunda ya faru, mahaifina yasan komai fa"

Alhaji Musa ya tako a hankali, yana zuwa bece komai ba ya danƙi hannun Nurat ya fara jan ta, a gigice Mummy tace "ya haka? Ina zaka kaimin 'yata? Ina zaka kaita? Karka cutarmin da ita dan Allah, ita kaɗaice' yata karka cutar da ita na gaya maka"

Be tankamata ba, ya dinga jan Nurat, Nurat tana faɗin "Daddy kaji tsoron Allah, a wannan shekarun naka me kakae nema a duniya haka, wanda zesa kasa hannu a zalunci wani, da Alhaji Nasir kake da matsala bada 'yarsa ko wanda beji ba be gani ba, dan Allah Daddy ku ƙyale Daula ya huta, da kunnena naji kana magana kune kuka saka aka sace Widad da direbanta, kuma yanzu kun sauya maganar kuna gabi aka kaishi kotu aka yanke masa hukunci akan abunda bejiba be gani ba"

Yana jan Nurat, tana biye dashi yayin da mahaifiyarta ke binsu tana masa magiya, wani ɗaki yaja Nurat can bayan ɗakinsa a ƙarshen bene, ya jefa ta ciki yasa mukulli ya kulle ta, ya juya ze tafi, Maman Nurat ta sha gabansa tace "meyasa zaka kullemin yarinya a wannan ɗakin ita kaɗai? Me yasa haka? Dan Allah ka buɗe mata ƙofar nan ta fito, karta cutu dan Allah"

Alhaji Musa yace "wallahi bazan buɗe ta ba, ashe kune manyan maƙiyanaba gidan nan? Dole ta bar ƙasar nan ko tana so ko bata so, kuma kema daga yau, bake ba fita ko ina, kuma duk sena karɓe wayoyin ki, munafukar banza da ta wofi"

"Niba munafuka bace, karka ƙara kirana da munafuka, halin rashin gaskiya 'yarka ce ta fara gano kana yi, dan haka babu laifina a cikin wannan batun? Dan Allah ka buɗemin' yata dan Allah ka barta ta fito, wallahi bazan bari tayi komai ba, dan Allah kayi haƙuri "

Tsaki yayi, ya raɓa ze wuce ta, amma ta sha gabansa tana kuka akan ya buɗe Nurat, aikuwa ya Tureta ze wuce bisa ga tsautsayi ta gangaro daga kan benen nan, ta ƙwala ihu da ƙarfin gaske, tun daga ƙafar farko har ƙasa, da sauri ya bita sedai kan ya ƙaraso tuni ta ƙarasa, ta faɗa da fuska aikuwa tuni jini ya wanke gurin, jikinsa yana rawa yazo ya ɗagota, fuskarta ta wanke tsaf da jini, gashi ko motsi ba tayi, akan idon me gadinsa ta faɗo daga kan benen.

Nurat ta jiyo ihun mahaifiyarta, amma bata san meyafaru ba, dan haka hankakinta ya tashi, ta shiga dukan ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske tans kuka, tana kiran sunan Mummy.

Aka ɗauki Maman Nurat, zuwa Asibiti cikin gaggawa, ana zuwa aka karɓeta a Asibitin, da gaggawa aka shiga da ita emergency.

Sabuwa ta dawo gidan da Widad take, ta shiga gurin Widad tace "Nifa naje na kai musu, amma basu bani komai ba, sun karɓi takardar sun karanta, sun bani wata takardar, sun karɓi ledar sunce in tafi kawai, hadda tambayata wai waye ya aikoni?"

Widad tayi murmushi tace "inaga basu da ita ne, bani takardar da suka baki"

Ta miƙawa Widad takardar da suka bata, ta karɓa ta karanta, tai ajiyar zuciya tace "nagode sosai Sabuwa, sunce basu da irin wadda nake so, se Allah ya kaimu jibi kije ki karɓa"

Sabuwa tace "to yanzu ya zakiyi? Ga jini na zuba?"

"no karki damu, zan iya maleji zuwa lokacin da zasu kawo É—in, bana iya amfani da kowacce se ita ne"

Sabuwa tace "to shikenan, Allah sarki ashe cikin ya fita dagaske?"

Widad tace "eh ya fita, ina son zan É—an kwanta"

Sabuwa tace "to shikenan, se anjima"

Fahad fa ya rasa inda zesa kansa, da yaga mamansa, se yaji tausayinta ya kama shi, se yaji ƙwalla ta tarar masa, maimakon yaji haushin kansa, haushin mahaifinsa ya dinga ji, dan dabe nemi mata ba da babu abunda zesa mahaifiyarsa ta samu, gashi ya rasa ta inda ze mata wannan baƙin bayanin mara daɗin ji.

Gidansu Amal ma gidan sam babu daÉ—i, idan Ramlah taga dama a falo, haka take zuwa ta kama shan shisharta, kota kunna sigari tana busawa, ta baje kayan coadine É—inta taita yiwa kanta caji, Hajiya Halima yanzu kam tsaro Ramlah take bata, sam bata iyayi mata magana, tana kallon ta, tana yi amma bazata iya cenata bari ba, Amal kuwa dama tuni ta fita daga harkar su.

Hajiya Halima na É—akinta, ko izininta bata tambaya ba ta fice ta tafi Asibiti dan a dubata, sedai ta razana da sakamako ya fito aka tabattar mata da tana É—auke da juna biyu, ta shiga É—imuwa da tashin hankali, tun a Asibitin ta lalubi lambar Alhaji Haruna ta sanar masa da tana É—auke da juna biyu, kuma ko yasan yadda zeyi da ita ko kuma tayiwa duniya Albishir da tana É—auke da cikinsa.

Abubuwa fa suka rincaɓe sosai, Wata Nurse inyamuda ta jata gefe tace mata tasan inda zata kaita a zubar da cikin, in dai bata son cikin, ba musu ko tunanin komai Amal ta amince da a zubar da cikin.

Yusuf yana cikin fursunoni, yana zaund shiru kamar yadda ya saba zama, akace yayi baƙi ya kalli gandiroban ya ɗauke kai kamar beji ba, "Malam da kaifa neka" gandiroban yai maganar a ɗan hasale"

Yusuf yace "bazani ba"

"Kamar yaya bazaka ba?"

'me zanje inyi? An riga an yanke min hukunci, burinku ya cika kuda iyayen gidanku, me kuke nema a gurina kuma? Ko waye bazani ba"

Gandiroban yace "koda mahaifiyarka ce kuwa?"

Da jin haka Yusuf ya miƙe da sauri, se kuma yaji bashi da karsashin tunkararta ya kalleta, dan yasan abune mawuyaci sukuma rayuwa da Ummansa kamar da.

Yusuf yabi bayan gandiroban jiki a saɓule, yana dogara ƙarafarsa da kyar saboda ciwo da take masa.

Yana zuwa yaga wasu mutane a zazzaune, wanda be sansu ba sam, aka bashi guri ya zauna yana ƙare musu kallo.

Ɗayan ya kalle shi yace "sannu Malam Yusuf, sunana Barrister Hafiz wannan abokan aikinane" yai maganar yana miƙawa Yusuf hannu.

Amma Yusuf ya ƙeƙashe ƙasa yaƙi bashi hannu, ya kalle shi yace "me kuke nema a gurina? Bayan shari'a tazo ƙarshe an yankemin hukunci, me yayi saura kuma me kuke so inyu muku"

Yai maganar cike da karaya, ƙwalla na taruwa a idon sa.

Hafiz jiya yi kamar yayi kuka shima, ya maze yace "haba Yusuf, ai ka tsaya kaji meke tafe damu ai, Barrister miƙo takaddar nan"

Barristern dake gefensa ya ɗakko takadda ya miƙawa Hafiz, Hafiz ya karɓa ya miƙa masa yace "ga saƙo inji matarka"

Jikin Yusuf na tsuma ya karɓi takaddar yana buɗewa yaga rubutun Widad "

_Bani da abunda zan iyayi maka a halin da nake ciki I love you My Yoseef, but I will do my best to see what I can do for you, please pray for me, is either we should meet again or the time you will be free i pass away_

Yusuf yace " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"

AMANA! AMANA!! AMANA!!!

AYSHERCOOL
07063065680
11/30/21, 8:20 AM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN  ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin  wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_)

IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _
Chapter 97 · 0% Book details