← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 127

Sashe 127

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Daddy ya rasa inda ze saka ransa da murna, a ranar Umma ta dawo kano, Umma kamar ita akayiwa haihuwar, ta dinga murna tana farinciki ta É—au jika.

Saura kwana biyu Suna su Hari suka zo daga ƙauye, da abun arzikinsu, megari yabada raguna biyu manya yace a yankawa jaririn nan, Yusuf yai masa huɗuba da Muhammad Bashir sunan mariƙinsa, anyi shagali sosai a sunan nan, jariri ya samu kyaututtuka daban daban daga gurin mutane.

Ana zaune a falon Widad, bayan an dawo daga event É—in da akayi sunan, ba zato ba tsammani Widad tace "wai yaushe ne bikin Hanne"

Hari tace "to ai mijin natane har ynzu be shirya ba, lega yake tafiya neman kuɗi, amma dai abun dai duk se a hankali ba wata Ƙwaƙwaƙwarar sana'a da yake yi"

Widad tace "aiga 'yar uwatta nan Hindu, ta tambayar mata mijinta a sama masa abunyi shima"

Hindu ta kalli Widad, dan ita harga Allah bata iya tambayar Daula komai, to mema zata tambayeshi bayan komai ya ajiye mata.

Hindu tayi fuska ba tace komai ba, da daddare Daddy da kansa yaje ya É—akko Hindu, bayan sunje gida har sun kwanta yace "Hindatu Widad tacemin zakiyi magana dani ko?"

Hindu ta girgiza kai tace "A'a"

"gayamin, nasan bazata miki ƙarya ba"

"Bafa nice ba, cewa tai wai ince maka a samawa wanda ze auri Hanne aiki"

Yai murmushi yace 'ta gayamin, ina son ji daga bakinki ne, daga yau kome kike buƙata kowa kike so ayiwa alfarma ki faɗa kanki tsaye zan masa, ance ya iya tuƙin mota, zamu bashi jan manyan motocinmu, sannan zan basu gida a nan garin, itama ta dawo ta zauna a nan ta shiga makaranta "

Hindu harda kukan murna, ta durƙusa har ƙasa tana masa godiya, ya girgiza kai yace" meye abun damuwa haka kuma? Karki damu kinji"

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, lokaci É—aya akayi bikin Nurat da kuma Amal, kuma duk Daulane yayi musu walicci, da kayan É—aki da manyan kyautuka ga kowaccensu.

Muhammad Bashir wanda suke cewa Aryan yayi wayo, kusan koda yaushe Daula ya kan je gidan Widad saboda Aryan, yana matuƙar ƙaunar Yaron.

Wataran da daddare Daula ya shigo yace "Hindatu, kisa hijjabinki zamuje muyiwa su Widad sallama, gobe in Allah ya kaimu zamuje Abuja, daga nan zamuje Dubai ki rakani taron kasuwanci"

Hindu tace "sekaje dani taron kasuwanci har wata ƙasar, abokanka za suyi maka dariya ka auri 'yar ƙauye"

"Ni matata ba' yar ƙauye bace, kuma ba inda zanji shakkar shiga da ita, in nunata ince wannan matata ce, saboda ina sonta a haka"

Hindu ta rufe fuska tana murmushi.

A daren suka tafi gidansu Widad, Hindu ta kama Aryan ta rungume tana ta masa wasa, Widad ta karɓi Aryan ta bawa Daddy, taja Hindu ɗakinta, ta bata wata riga tace ta gwada, Hindu ta cire hijjabinta ta gwada rigar, abun da Widad ke son gani, kuma ta gani ciki ne a jikin Hindu.

Widad tai kamar bata gani ba, ta bata kyautar riga, a ranta tace "shine Daddy bemin Albishir ba.

Widad tana jin daɗin yadda mahaifinta ya samu nutsuwa, Dan ita kanta ta lura da yadda Daddy ya samu nutsuwa, da biyayya da take masa, daga ita har Daddy sunyi tsaf dasu sunyi ƙiba, watan Aryan biyar Widad tabi Yusuf Lagos, ya kama harkar kasuwancinsa sosai.

Watannin cikin Hindu tara ta haihu, amma seda aka mata CS aka cire yaron daga cikinta, saboda yai girma da yawa, kwana biyu tana labor, sannan aka mata cs É—in aka cire yaron.

Widad kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murna, an yi mata ƙani, yaron kamarsa ɗaya da Yusuf sak, kamar shiya haife shi, kuma kusan duk kamaninsu ɗayane dai da Daula.

Daula be taɓa saka ran ze sake haihuwa ba, lokacin da aka gayamasa Hindu na da ciki ma, shiru yayi da bakinsa yaita Addu'a, da cikin ya fara girma kuma ya dena zuwa ko ina da ita, saboda kar itama ayi mata yadda akayiwa Huda, se yanzu data haihu sannan kowa yaji, an taya Daula murna sosai, da kyautar da Allah ya bashi na ɗa namiji.

Widad anyi ƙani, ga kuma ɗa da miji, murna ba kama hannun yaro, se bayan sati biyu akayi gagarumin shagalin suna, a garin kano, har Nurat da 'yan gidsnsu sunje barka, sedai Widad sam bata shiga sabgar Nurat sosai, seda Daddy ya zauna ya sata a gaba, yaita mata faɗa da Nasiha, sannan take ɗan sakin jiki da ita kaɗan.

Duniya ta dawo sabuwa ga wannan ahali, suka dinga tara zuriya, dukda Daddy ya manyanta amma seda Hindu ta haifi yara huÉ—u dashi, Widad ma ya haifawa Yusuf yara uku.

Bulama kuwa bayan shekara shida a haka ya mutu a gidan yari, yana wannan tsutsar da zubar da ruwan, babu wanda yake iya zuwa inda yake saboda wari da ɗoyi, haka aka yasar dashi a gadon Asibiti, harya mutu babu wata cikakkiyar kulawa haka ya mutu a wulaƙance.

Lokaci lokaci Amal ta kanje ta kaiwa mahaifiyarta ziyara a gidan yari, sannan tana zuwa gidan masu rangwamen hankali, Ramlah ta zama mahaukaciya tuburan, se an É—aÉ—É—aureta haka zatai ta ihu tana fizgar gashin kanta, idan bayan gidane a nan za tayi, komai a gurin take yi, ta zama mahaukaciya tuburan, abun da Hajiya Halima taso Widad tayi, shine ya faru a kanta.

Duk wanda ya zamana da sa hannunsa a badaƙalar da Bulama yayi, seda aka masa hukunci daidai da shi, daya mutu ma ds ƙyar aka samu masu masa jana'iza, sedai kowa yana toshe hanci saboda yadda jikinsa ya dinga ruɓewa tun yana raye, ga kowa baya faɗan alkhairi akansa, sedai sharrinsa da Allah wadaran.

Daula baya ƙasar lokacin daya samu labarin rasuwar Bulama, amma seda ya zubda hawaye jin irin mutuwar da Abokin nasa yayi, tabbas da yana Nigeria dashi za'a sallaci Bulama, ya dinga kuka yana "Allah ya jiƙanka Abubakar, Allah ya maka rahama ya yafe maka, yasa jinyar da kayi kaffara ce, ni dai na yafe maka abubuwan da kamin, Allah ya yafe maka"

Seda Widad taji haushin yadda Daddy ya damu saboda mutuwar Bulama.

Daula a haka ya  dinga sawa ana kai kayan Abinci gidan yari, da gidan mahaukata, Arziki ya cigaba da bunƙasa, Hindu ta zama hamshaƙiyar mace itama, Daula ya ɗau nauyinta taita karatu na addini dana zamani.

Umma dai Allah be bata haihuwa ba, amma bata sa hakan a ranta, saboda tana da Yusuf ga sirikata ta ɗaiketa uwa, ga yara sun haifa suna da jikoki, gashi tana zaune da mijinta da matarsa lafiya, yaransa suna matuƙar girmama ta.

Yusuf ma suka samu kyakkyawar rayuwa, suna zaune abunsu a garin Lagos da yaransu, ƙauyen su Hindu kuwa, banda wanda yasan ƙauyen ƙayaune a baya ba zakace shine a yanzu ba, saboda cigaban da suka samu ta kowane fanni, bazasu taɓa mantawa dasu Widad ba, saboda a sanadinsu ne Allah yasa suka samu wannan cigaban wanda basu samu ba a baya.

TAMMAT BI HAMDILLAH

9/12/2021

ALHAMDILILLAH ALA KULLI HALIN, ALLAH YA NUFA NA KAMMALA WANNAN LITTAFIN NA AƘIDATA, INA FATAN DARUSSAN DAKE CIKI ALLAH YA BAMU LADA, AKASIN HAKA UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA.

A TARA NAN GABA KAƊAN DOMIN JIM LITTAFIN DA ZANZO MUKU DASHI, AKWAI LITATTAAFAI JINGIM A TASKAR COOL, WASU NA KUƊI WASU NA KYAUTA, INA FATAN DUK WANDA NAZO MUKU DASHI, ZAKU KARƁA HANNU BIYU, NAGODE SOSAI DA KULAWARKU DA KUMA ƘAUNARKU A GARENI

SANNAN INA SON JIN RA'AYOYINKU AKAN WANNAN LABARIN DA KUKA KARANTA

NAGODE SOSAI, A KODA YAUSHE INA MATUKAR ALFAHARI DAKU MASOYA.

ƘOFATA A BUƊE TAKE, DAN GYARA, SHARHI KOKUMA SHAWARA

AYSHERCOOL
07063065680
Chapter 127 · 0% Book details