Sashe 54
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yawwa haka nake son ji, yanzu wannan manyan filayen nasa nake so in sa a kasuwa na GRA, dan haka kiyi masa magana, kamar yadda akayiwa Gidajen layout É—in nan takadda, suma wannan ayi musu takaddu mu siyar, ke ni ko miliyan sha biyar biyar, a siye su"
Ramlah ta ɗan zaro ido tace "Mummy million sha biyar kima, a filayen miliyan kusan arba'in ɗin za" a siya a haka? "
" Eh to seme? Da gumunmu muka tara? Nifa sonake ayi yadda za'ayi mu É—an tara daga nan mu san nayi, dan haka ki masa magana, ke har gidan nan ma sena siyar dashi, ai in sun san wata basu san wata ba"
"hakane Mummy, amma gaskiya baza'a siyar da filayen nan a haka ba se an ƙafa, in ba haka ba mume zamu ci?"
"to koma dai yane, kiyi masa magana ayo takaddun daga nan musasu a kasuwa"
"Shikenan zamuyi waya dashi, kokuma inaga anjima ma zezo, se muyi maganar gaba É—aya"
Hajiya Halima tace "ainaji daɗin harkar nan da yaron nan, motocin nan na farmhouse ma ai duk shi yayi mana hanya aka siyar dasu, banda sauran abubuwa, aini wannan lamarin ma gaba ta kaimu"
"Wallahi kuwa Mummy, semunci rabon mu tukuna"
Anwar ji yayi kamar ƙasa ta buɗe ya nutse a ciki, dama kadarorin Daula mahaifiyar sa ke siyarwa yana wadaƙa da kuɗin? Lallai ɗan Adam butulu ne, idan ya tambayeta ina motocin gidan se tace tasa an kaisu Farm House, dama abunda take yi kenan? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un'
Jiki a sanyaye yaje ya ɗau motarsa ya tafi gidan gonar Alhaji Daula wanda aka riga aka mallakawa Widad, yaje da niyyar zagaye yake ya biya dan yaga gidan, ya tarar fiye da rabin motocin nan idan ya tambaya se ace Hajiya ta turo a ɗauka, hatta dabbobin Widad tana ta musu ɗuki ɗai ɗai, dan akwai da yawa wanda bana ƙasar nan ba a ciki, dan haka ana siyansu da tsada.
Abun ya bawa Anwar mamaki, ya tuna irin gwagwarmaya da É—awainiya da Daula yayi dasu, amma mahaifiyar su ta rasa dame zata saka masa se wannan zalunci da tsantsar butulci, lallai É—an Adam butulu.
Da ƙyar ya kai kansa gida, saboda azabar ɓacin ran da yake ciki, ta haɗa kai da 'ya' yanta suna ta wadaƙa da dukiyar marainiya data mahaifinta, se yanzu yake jin Widad bata da laifi da suke iƙrarin tana Wulaƙantasu.
Da yamma Widad taita zuba ido a hanya taga ta ina su Gwaggo zasu dawo, se bayan ƙarfe biyar se gasu sunyi sallama sun dawo, Widad ta dinga murna, tace "Sannunku da zuwa na zaci ma kum fasa dawowa yau"
Gwaggo tace "aiko kowa be dawo hau ba dole in dawo saboda ke, muna can amma hankalina yana nan"
Widad tace "Hindu 'yan biki, a huta azo a bani labarin abunda ya faru"
Hindu tace "ni wallahi muna gurin biki, hankalina yana kan makaranta"
"to aini tunda kuka tafi, nace a bari sekun dawo a cigaba'
Suka baje a tsakar gida, Yusuf ya fito yayi musu sannu da zuwa sannan ya fita.
Saboda É—aurin Aure, megari ma yaje gurin bikin, da shi da Sunusi Kasancewar Yayar megari ce ta aurar da 'ya, nan ma Yusuf ya shiga yayi musu sannu da zuwa, daga nan megari yaja shi da hira suka shantake a gurin.
Gwaggo ta baje kayan biki da suka zo dasu, ƙulli daban tayiwa Widad na kayan gara kuma fal da yawa, kayan zaƙin nan.
Gasu wainar masa da ƙuli, Widad tana son kayan zaƙi dama, ta zauna ta cicci abunta tana lashe baki.
Ana idar da sallar magariba ta tura yaro ya kira mata Yusuf a waje, Yusuf ya shigo gidan ya shiga É—aki ya sameta yace
"lafiya kika aika a kirani? Me zaki ban?"
"To ai kaine kaƙi dawowa tun ɗazu"
"to ai bamuyi sallar isha'i ba, kuma zamuyi karatu"
Ta miƙe ta ɗakko masa kayan da Gwaggo ta bata, Yusuf yace "masha Allah, 'yar gatan Gwaggo wannan duk namu ne?"
"Eh mana shiyasa nace kazo kaci naka, gashi nan kaci iya cinka, ni na tafi tsakar gida"
Tana gama maganar ta miƙe ta fita.
Yusuf ya zauna yana cin kayan gara, Widad tayi waje, Hindu tana ta bata labarin yadda bikin ya gudana, Hanne kuwa se cika take tana batsewa, ba wanda yabi ta kanta suka ƙyaleta da ƙuncin ran da take yi.
Bayan Yusuf ya gama ya fito tsakar gida yana alwala, Widad tace "Mama waiya mutum ze gane idan yana da cikine?"
Gwaggo tace "to babbar magana"
Jamila tace "karki damu, ni zan gaya miki in munfi haka yawa"
Widad tace "ai yanzu ma muna da yawa ki gayamin mana"
Hari tace "to bahaushiya, tana nufin se daga ke se ita tukuna"
Widad tace "koma yane, ni dai dan Allah Mama ki dingamin Addu'a, Allah yasa in samu ciki"
Hari tace "Ai himma kawai zaki ƙara, idan kika shiga ɗaki tun magariba, se wata magaribar"
Sam Widad bata gane me Hari ke nufi ba, Yusuf shi kunya cema duk ta kama shi, ya tashi ya fice waje.
Jamila tace "Widad zomu je ɓangarena, in baki tawa tsarabar"
Widad ta tashi ta bita, Jamila tace "Widad nace miki irin wannan tambayoyin, ni zaki dinga yiwa ba Gwaggo ba, kunyace dasu, kinga baki taɓa haihuwa ba balle ace kin san alamomin, dan haka ba lallai alamomin da zan gaya miki su zamana ciki bane, amma mafi akasari dai cikinne ke sawa, Alamomin da zaki gane kina da ciki sun haɗa da, ɗaukewar Jinin al'ada, zazzaɓi, ciwon kai, jiri, Mamanki zasu danyi miki nauyi, koma su dinga zafi, yawan tashin zuciya, koma amai, yawan san ki kasance da mijinki a shimfiɗar Aure, ko jin haushin hakan, yawan som cin wani abu ko ƙin wani kalar Abincin, da sauransu amma alamomin ba lallai kiji su duka ba"
Widad tace "wanne ne babban alama to?"
Jamila tace "ÆŠaukewar Al'ada, ko kuma laulayi idan cikin me laulayi ne"
Widad tace "shikenan nagode sosai"
Jamila tace "abubuwan duk da nake gayamiki, kina ganewa kuma kina aikatawa dai ko?"
Widad ta jinjina mata kai.
Suka cigaba da hirarsu, tana ci gaba dayi mata lectures akan Rayuwar Aure.
Da daddare Yusuf ya dawo Widad tayi masa sannu da zuwa, ya lura da ta canza akan abubuwa da dama, wanda da a baya ba tayi.
Ba zato Yusuf yaji Widad tace "Yayan Daddy dan Allah meye maganin mata?"
Yusuf ya kalle ta yace "ke a ina kikaji hakan?"
Tace "A gurin Jamila"
'Sha kika yi kenan? Ya tambaye ta
Widad tayi shiru ba tace komai ba, kawai taga Yusuf ya kwashe da dariya yace "lallai yarinya kina ruwa"
Kamar zata yi kuka tace "wani abu ne ze sameni?'"
"A'a ni bance wani abu ze same ki ba"
Gaba É—aya bata gane me Yusuf yake nufi ba, taga ya É—auki kayan shimfiÉ—arsa yayi wajen kwanan sa.
' Yusuf meye haka wai? "
Yusuf yace " A ina? "
" Naga ka É—auki kayan shimfiÉ—arka, yau bazaka kwana a gurina ba?'
"Eh yau a gurin kwanciyata zan kwanta"
Kamar zata yi kuka tace "Amma naga yaushe rabon daka kwana anan gurin, kawai se yau zaka wani ce a can zaka kwanta?'"
Kamar Yusuf zeyi dariya ya maze yace "A'a ni gaskiya sha'awar kwanan kam bargona nake, kowa ya kwanta a inda ya saba kwana"
Kawai ta zauna tana kuka, Yusuf ya sha dariya sosai, dan Widad ta iya gaɓunta wasu lokutan, seda yaga dagaske take sannan ya koma inda suke kwana yana mata dariya.
Da gari ya waye, idan Widad ta tuna abunda tayi jiya kawai se wani irin haushi yakamata taita tsaki, Yusuf yace "uwar kwaÉ—ayi, gobema kije a kuma baki abunda baki sani ba kici"
"Bazan ƙara ba har abada"
Yusuf yaita dariya yace "A'a gaskiya ki ƙara, ni zan bada kuɗi ma ki ƙara"
Ya dinga mata dariya, taga idan ta biyewa dariyar da Yusuf ke mata se tayi kuka, dan haka ta biye masa suka dinga dariyar tare.
Cam tace "Yoseef, dan Allah ka dinga min addu'a, Allah yasa in samu ciki, haihuwa nake so nayi nima"
Maimakon yayi magana, kawai seya janye ta daga jikinsa ya bar mata É—akin.
Mamaki ne ya cika Widad ta bishi da kallo, tana tunanin me yake nufi da wannan abunda yake yi, duk lokacin da tayi zancen tana son samu ciki, seya canza mata meye Nufinsa nayin haka?......
LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH ðŸ™ðŸ™ðŸ™
11/15/21, 4:52 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE

96_97
Widad taje ta samu guri tayi zamanta a tsakar gida tana kuka, saboda tayi mamakin abunda Yusuf yayi, idan wanine yace ze mata haka tabbas zata ƙaryata, amma se gashi Yusuf ke ƙyamar haihuwa ko meye dalilinsa oho, to koma dai wani daliline ai bashi da ƙarfin da zesa ace yana gudun haihuwa haka, idanma tunanin sa yadda zasu yi idan sun koma gida, ai suna da hujjar da zata nuna aure sukayi ba zaman kansu ba, kuma tasan Daddy zeyi farinciki da hakan, abun da yake ta buri yaga 'ya' yan Widad a rayuwarsa.
Kusan kwana biyu babu Anwar, an kai har gurin 'yan sanda amma babu Labari.
Hajiya Halima ta tafi gurin Alhaji Munir, yana ganinta ya ɗan ɓata rai yace "to uwar matsala, ke duk inda aka ganki ba alkhairi se tarin matsala da damuwa"