← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 127

Sashe 60

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abunda bata taɓayi ba, ta shiga ɗibar zannunwanta tana siyarwa, dan a lokacin Yusuf kansa bashi da lafiya, dauriya kawai yake yi, tun yana daurewa harta koma ta kwanta babu lafiya, shima ya kwanta ba lafiya, dan komai se tayi masa saboda zafin ciwo.

Haka ta kwashi flasanta da Bashir ne mafi akasari yake sauya mata, ta kai kasuwa akayi musu sayen wulaƙanci, ta karɓo kuɗin ta ɗau Yusuf zuwa Asibiti, suna zuwa aka basu gado, Ulcer ta masa mummunan kamu, ga typhoid da malaria, ita bata ta kanta ta lafiyar Yusuf take, Bill ɗinsu kusan dubu goma sha huɗu dukda Asibitin gwamnati ne, haka ta zare ta biya, taje pharmacy ta karɓo magani zata koma ward, 'yan sanda suka kawo wasu sunyi accident.

Wani ya kalleta yace  "wannan kamar matar Bashir"

Ta kalle shi tace  "eh nice"

Yace  "Ai na sanki, ai tare mukayi aiki da Bashir, baki ganeni ba? Isyaku ne fa, amma yana ganki haka, baki da lafiya ne?"

Tace  "A' a Ɗanmu ne ba lafiya, na kawo shi nan aka bamu gado, an kaantar dashi"

Mutumin yace  "A'a, naga da kamar private Hospital kuke zuwa? Ya zaki kawo yaranku nan gurin? Ke kanki kamar baki da lafiya fa"

Haɗe rai tayi, dan mutumin nan ya fara isarta tace  "lafiyata ƙalau ni"

Yace "yi haƙuri, naga kamar kin fara hasala, amma ai naga kuɗinsa ya fito wata biyu baya, amma ya zan ganku haka, kuma kuɗin nasa dayawa"

Ta kalle shi da sauri tace   "Yaushe kuɗin nasa suka fito?"

"Kina nufin baki sani ba? To 'yan uwansa da wasu' yan sanda sun haɗa kai sun karɓi kuɗinsu, ai na zata an baku naku?"

Da gudu ta wuce ɗakin da Yusuf yake kwance, tana kuka yanzu kuɗin mijinta sun fito amma sun karɓa sun cinye, tasan babu yadda za'ayi ko ficika su bata, ga tarin wahala da suke ciki, amma ba imani suka hanata kowani kasone a ciki, haka taje ta zaunatayi kuka kamar ba gobe.

Kwanansu takwas a Asibiti aka sallami Yusuf suka koma gida, ta ƙarasa jinyarsa a gida ya koma makaranta, tayi tayi makarantar nan da take Nanny su maida ta bakin aikinta amma suka ƙi, haka ta haƙura duk yadda ta kai ga danne zuciyarta, seda tayiwa dangin mijinta Allah ya isa, akan haƙƙin mijinta da suka danne suka cinye sukaɗai.

A ɓoye wani maƙocin su yaga yadda taketa wahala, yai mata hanya gurin wani ɗan siyasa a temaka mata, amma mutumin nan ya nuna mata halin bunsurai, dan haka bata kuma zuwa ba, itace wankau, itace aikatau na biki kona taro, Yusuf yana Sss1 aka tafi da shi Quiz Abuja na akan harkar lissafi, aikuwa Yusuf yazo na ɗaya aka  bashi kyautar dubu ɗari biyar, malamansu suma suka cicciri nasu dana babu gaira ba dalili, ƙarshe dubu ɗari biyu aka bashi.

Umma tayi murna da samun kuɗin nan, Yusuf yace  "Umma duk an kwashe fiye da rabin kuɗin, kinga da mun samu da yawa, dubu ɗari biyar fa aka bani"

Umma tace  "Yusuf ina lefi, da ina muka samu wannan ɗinma? Ai Alhamdilillah mai dai Allah yayi maka albarka, ya ƙara hasken makaranta ya jiƙan Abbanka'

Yusuf yace  " Ameen Umma, ga kuɗin nan, wace sana'a kike ganin zamu fara ne? "

Umma tace " Yusuf ka maida hankali a karatunka, sannan kuÉ—in nan ka É—au abunda zaka É—auka, semu yi tunanin abunyi"

"haba Umma, na girma fa ki bari in fara sana'a mana, kuma ni ba abunda zan É—auka a kuÉ—in nan, muyi tunanin abunyi"

"A'a Yusuf, dole ka sai sutura, zan shiga kasuwa in samo maka yaduka, da takalama, dako É—an agogone, ka fara zama saurayi, ina kallo kayanka duk sun mutu, ba yadda zanyi ne kawai"

Yusuf yace "Umma karkice zaki kashemin kuɗi dayawa, ina sa ran zamu kuma zuwa wani competition ɗin, kema ki sai wani abu a ciki, nace ko injin markaɗe zamu siya, se a ajiye shi a ƙofar gida idan na dawo in dinga zama"

Aikuwa Umma ta yadda da shawarar Yusuf, suka ajiye kuɗi basu taɓa ba tukuna, suna shirin siyan injin markaɗe.

Yusuf ya dawo daga makaranta sukaje kasuwa suja siyo inji, akazo aka saita komai suka sai kayan Abinci da sauran buƙatu.

Da safe idan Yusuf ya tafi makaranta, Ummace take markaɗen a cikin gida, idan ya dawo ya fito dashi waje yayi zuwa magariba, se maƙota suka fara surtu wai ana cika musu kunne, bayan a ƙarshen kayanma akwai babbn gurin niƙa, da suke wuni guda niƙa, amma suka zo sukace wai suna takura musu da ƙarar inji.

Duk shiru na Yusuf ya dinga faɗa, yace "wallahi babu wanda ya isa ya hanamu sana'a, me kuke so muyi ƙasa zamu ci kome, yanzu da wani fitinannen na zama sekunfi kowa tsinemin, ba irin wahalar da bamu shaba, kuma mun kafa sana'a kuce semun ɗauke baze yuwuwa ba"

Maƙwabcinsu Na jikin gidansu yace  "kai dalla har kana da bakin magana, banza tsintacce wanda ba'asan asalinsa ba, karuwa tayi ciki ta haife ta yar, an tsintoka an rufa maka Asiri, amma kazo kanawa mutane Iskanci a gari"

Maganar nan tayiwa Yusuf ciwo, yaji haushin maganar nan, yaji kamar ya soka masa mashi a zuciyarsa, amma ya dake yace  "idanma hakan akayi, inma ba hakan bane, ba a kaina aka fara ba, kuma ba kaina za'a ƙare ba"

Umma dake cikin gida, tazo ta janye hannun Yusuf tana kuka suka koma cikin gida  tace   "Yusuf mi haƙura da markaɗen nan kawai, bazan iya jure ana cimim zarafinka ba, bazan iya ba"

Ya goge mata hawaye yace  "Umma idan mun dena Meza muci, kidena damuwa ni baya damuna, saboda nasan bani da wasu iyaye inba Ummana ba, da Abbana Allah ya jiƙansa, ki rabu dasu kawai, komai lokacine wataran in ance suyi min ba zasuyi ba"

Haka yaita rarrashinta yana bata haƙuri, washegari ya tafi makaranta, bayan ya dawo tun daga soro ya fara jiyo kukan ummansa tana   "da ikon Allah se Allah yasakamin abunda kukayi min, yadda kukayi nufin tozartani Allah yasakamin, wallahi ɗanlami da kai da Ballo da 'yan uwanka bazan yafe muku zaluncin da kukamin ba, wallahi Allah ya isa"

Yusuf ya shigavda sauri, yaje ya sameta a dirƙushe tana kuka, ga su Yaya ɗanlami da wasu mutane.

Yusuf yace "Umman Yusuf, lafiya kuwa me suke mana a gida? Me kuma mukayi musu?"

Yaya Bello yace  "kai dalla tafi can banza, meye naka a ciki wani wai me muke muku a gida, inane gidan naku meye haɗakinka da Bashir,? Ɗan tsintuwane fa kawai amma ko taku baka dashi a abunda ya bari, seka bazama neman karuwar da ta haifeka ta yasarka ta nuna maka ubanka"

Cikin kuka Umma tace "Wallahi karka ƙara shegantamin ɗa, Yusuf ba karuwa ce ta haife shi ba, ɗana ne, kuma ɗan sunnane duk Wanda ya kuma shegantashi ban yafe ba"

Yusuf bece komai ba, yaje ya durƙusa ya ɗago Umman dake kuka yace  "Umma meyafaru ne wai?"

"Yusuf kaga, bayan sunje sun karɓe haƙƙin Babanka sun cinye, babu wanda ya waiwaye mu, sun saida gidan da muke ciki, an bamu notice, wai bazasu bamu gadon komai na Bashir ba, Yusuf an mana adalci kenan? Yanzu sun kyauta kenan? Yusuf ynzu kana ganin da Bashir ne a raye ze musu haka? "

Yusuf ya rumgumeta ganin yadda jikinta har rawa yake tana kuka, gata ba cikakkiyar lafiya ba yace "Ummana kiyi haƙuri, ai Allah baya bacci ni idan bani da gadonsa aike matarsa ce yakamata su baki"

"Yusuf gidan nanfa nawane nida kai, har rubutu Bashir yayi ya bari kafin ya rasu, kuma Bello ya sani amma shine suka saida gidan, idan na tashi daga nan mu koma ina? Me nake dashi idan na bar nan?"

Ɗanlami yace "koma gidan ubanwa zaki ki tafi, ai dama ba gidan ubanki baane, seki koma gidan ƙasar da ubanki ya mutu ya bari, shi kuma ya koma gidan ajiye shegu da kuka ɗakko shi"

"Wallahi se nayi shari'a daku, se an ƙwatar mana haƙƙinmu"

"Haba Umman Yusuf, aishi Allah baya bacci, kuma Allah na kowane baya barin zalunci, menene gida idan sunyi haka dansu wulaƙantamu Allah baze basu dama ba, ki kwantar da hankalinki mun rasa Abba ma, kuma dangana mukayi mukai haƙuri, dan haka gida ɗazune, in da rai da lafiya insha Allah sena gina miki gida na ban mamaki, gidan a wanke hannu kafin a taɓa "

Yai maganar yana goge mata hawayen fuskarta, yana murmushi dukda Shima fuskarsa sharkaf take da hawaye.

Murmushi tayi na ƙarfin hali tace " na dena Yusuf, na barwa Allah nasam baze wulaƙantamu ba"

Saboda keta haddi da cin mutunci, tana zaune wai za'a wuce da masu siuen gida har ɗakin baccinta a duba, Yusuf ya miƙe ya tare ƙofar yace "dul abunda zakumin zan iya jurewa, amma wallahi duk garin nan babu mecin mutuncin uwata in ƙyaleshi, ɗakin baccinta gurin sirrinta ne, dan haka babu me shiga, jibi in Allah ya kaimu zamu tashi mu bar muku gidan, ba zamuyi shari'a daku ba, amma Allah ya biwa Ummana haƙƙinta"

Bello yace "kaikuma kai a wa? Gayyar tsiya arna a idi? Kama je kayi shari'ar damu mana, dalla gafara nan a duba É—aki sirrin banza sirrin wofi"

"Wallahi taku ɗaya ka ƙara daga inda kake, kai yunƙurin shiga ɗakin nan idan na ɗaga ka se nayi jifa da kai ta katangar nan wallahi"

Tabbas yadda ƙirar jikin Yusuf take, dukda ba wani girma yayi ba tsaf ze iya aikatawa, haka suka haƙura suka tafi suka ƙyalesu.

Umman Yusuf ta cigaba tana cewa "Yusuf Allah yasaka mana, kana gani ana cewa an kashe Abbanka, aka dawo da motarsa suka ɗauka suka siyar, banyi magana ba, kuɗinsa suka fito suka wuce gaba suka karɓe suka cinye, se a bakin jama'a naji labarin kuɗin sun fito, duk 'yan kadarorin daya bari sun siyar, kuma suna kallon wahalar da nake yi, babu tausayi babu imani a tare da su, ya suke so muyi da ranmu Yusuf, sun cutar damu"

Tai maganar cikin kuka da sheshsheƙa, Yusuf yace "Umma kidena kukan nan, zanje a samo me siyan injin markaɗen nan, da ɗan cinikin da mukayi mu samu gida ko ƙaramine mu kama"
Chapter 60 · 0% Book details