Sashe 8
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ɗan jinjina kai tace " lallai biri yayi kama da mutum, ranar ba yadda banyi da kai ka gayamin meyafaru ba, amma kaƙi ka gayamin, nima nasan nayi ganganci a wannan ranar, na zuwa gidan Alhaji Musa, sedai ina ƙoƙarin cire kaina a cikin rigimarsa da mahaifina, shine dalilina na zuwa gidans, amma shima ka ɓoyemin baka gayamin meyafaru ba ranar, meyasa? "
Yusuf yace " saboda muddin na gaya miki zakiyi yunƙurin ɗaukar mataki ne, da kinyi yinƙurin yin haka nikuma Asiri naa ze iya tonuwa, kuma zaki ɓata komai ne, Amma dan Allah ya akayi kika sani? "
Cikin isa tace "Lallai ka raina Wacece Widad da kuma AƘIDARTA, in dai nice har yanzu bakaga komai ba, Tunda kazo gidanmu, jikina ya bani akwai something different with you, either good or bad, na kasa nutsuwa, na dinga ɓullo da abubuwa daban daban amma na kasa gane komai na cutarwa a tare da kai, ranar da 'yan sanda suka kama ka da bindiga, ni na fara ganin bindigar a jikinka kafin mu fita daga gida, kazo shiga mota ka ɗaga rigarka naga bindigar, nai shiru ban nuna na gani ba, dan ina son sanin da wacce kazo, sannan inga wani hukunci ne ya dace da kai, bayan mun fita a ranar aka kamaka da bindiga ka bawa 'yan sanda id card, sukayi ƙoƙarin saluting ɗinka amma ka hanasu, tun daga nan nabi diddigi da ƙwaƙƙwafinka na gane waye kai, har headquarter ɗinku naje aka bincikomin waye kai, sedai abu ɗaya ne ban gano ba har yanzu, waye yasa a baka aikin nan?!"
Yusuf yayi ajiyar zuciya, cikin damuwa yace " Nima ban sani ba, da bani za'a bawa aikin ba, amma abokin aikina yace a bani na fishi haƙuri, ban san waye ya bada aikinba nima"
Widad tace "Abokin aikinka Sani me zuwa gurin Isa megadi ko? Wato Abbas"
Gaba É—aya Yusuf ya rasa meze ce saboda tsananin mamaki.
"Ni na saka aka É—auke shi daga kano, aka kai shi kudancin Nigeria saboda ban yadda dashi ba, yayi ruwan Azzalumai da yawa"
Yusuf yace "Dama kece kika saka aka É—auke shi? Ba mugu bane aminina ne, bani da aboki sama dashi"
"Yana É—aya daga abunda yake cutar da mutane, shine saurin yadda, waye ya gaya maka duk memaka dariya sonka yake yi? Kayi kuskure ni bemin ba, shiyasa nasa aka rabashi da garin nan, sannan ina cike da son sanin waye ya bada wannan aikin"
Yusuf kam rasa bakin magana yayi, se kallonta kawai da yake yi.
Widad tace "shikenan" ta miƙe tsaye ta ɗau kwanukanta, yaji taja sumar kansa tace "matsoraci kawai, ashe haka kake da tsoro, i wish kaga idonka yadda suka sauya, kaine mutum na farko da na yafewa wanda yai min laifi mafi muni, saboda kaima hanyar da akabi aka baka aikin dan a cutar da kaine"
Yusuf yace "kamar yaya?"
"Bazan faÉ—a ba, ban yadda da kai ba" tai waje abunta tana dariya.
Mamaki ya cika Yusuf tatil, yanzu dama kallon biri yake mata take masa na Ayaba, tasan waye shi tsawon lokacin nan, be taɓa zaton zata gane ba yadda ya dinga taka tsan tsan, lallai Widad ba ƙaramin wayone da ita ba, amma kuma yana da tarin tambayoyi daze mata, amma taƙi bashi damar yin hakan.
Anwar ne ya shigo falon mahaifiyarsa yace "Mummy zanje kiran da Babansu Fahad yake min ne"
Ta kalle shi tace "Naji amma tare da Amal zaku tafi"
Anwar yace "Amma Mummy meyasa?"
"Saboda haka naga dama" ta bashi amsa, ta É—au wayarta ta kira Amal tace tazo.
Befi mintuna biyar ba sega Amal ta shigo tace "Mummy gani"
"Jeki shirya maza kizo kuje gidan Bulsma keda yayanku"
Amal tace to, Hajiya Halima ta kalle shi tace "jeka mota ka jira ta"
Anwar ya fita kamar yadda aka bashi umarni, Amal ta shirya ta koma ɗakin mahaifiyarta, tace "Mummy gani na shirya"
"Yawwa ki buÉ—e kunnenki ki jini, wannan yayan naku wani lokacin sakaraine, ba hankali ya cika ba, ina son ki saka min ido akansa, duk abunda ya faru ko abunda Bulama yace idan kun dawo ki gayamin"
Amal tace "shikenan Mummy, Insha Allah zan gaya miki"
Ta juya ta fita, ta samu Anwar a mota suka tafi.
Suna zuwa gidan Bulama, Ramadan da Iman suka shiga murna Ramadan yace "Sannu Anwar, barka da Arziki Allah ya kiyaye gaba ya bayyana Daddy"
Anwar yace "Ameen Ramadan"
Iman tace "Sannu Yaya Anwar, Allah ya tsare"
Nan suka tsaya suna hira, Hajiya Sarah ta fito daga ɓangaren ta, itama tana ganin Anwar ta faɗaɗa murmushinta tace "Anwar, sannu Anwar ashe ka fito da yau naso inzo har gida in maka jaje, Amma naji alamun hawan jinina ya tashi, shiyasa na fasa fitar"
"Allah sarki, bakomai Mummy Allah ya baki lafiya"
"Ameen Anwar, Amal sarkin zumunci ya Maman naku? '
Amal tayi murmushi tace " Mummy kenan tana lafiya "
Bulama ne ya sakko daga kan benensa, bayan ya sakko Anwar cikin girmamawa ya rusina yace " barka da Yamma Daddy "
Bulama yace " Yawwa barka Anwar, ya kake ashe ka fito?"
"Eh Daddy Alhamdilillah, Allah yayi na fito"
Amal cike da basarwa tace "Ina wuni"
Bulama yace "lafiya ƙalau Autar mamanta, ya gidan naku?"
"Lafiya ƙalau" ta bashi amsa.
Yazo ya zauna a kan É—aya daga cikin kujerun falon.
Ya kalli Anwar yace "barka da Arziki Anwar, ba irin sintiri da shiga ficen da ba'ayi ba akan aga an samu ka kuɓuta amma Allah be nufa ba, amma ya akayi suka sakoka ne suka bar Sufyan?"
Anwar yace "to nima dai wani mutum ne yazo ya taho dani, bemin wani gamshashen bayani akai ba, ya cemin shima wanine ya turoshi"
"Allah sarki, haka lamarin ubangiji yake ai, kaga mu ba yadda bamuyi ba amma abu ya gagara, mahaifiyarka ta ɗaga hankalinta ta dinga ganin kamar bama wani ƙoƙari akai, se gashi Allah yayi an sako ka, to ubangiji Allah ya kiyaye gaba"
"Ameen ya Allah Daddy, Daddy nace to har yanzu babu wani labari akan ɓatan Daddy, har yanzu ba'a san inda yake ba?"
Bulama cikin damuwa yace "Anwar da akwai wani labari ai da kaji, babu wani labari har yanzu, binciken ake amma kamar ba'ayi"
"ubangiji Allah ya bayyana shi, ni fatana Allah yasa yana hannu nagari, tunda bashi da lafiya"
Hajiya Sarah tace "sha'anin ƙasarmu ai se Addu'a, banda haka ace an sace mutum kamar Alhaji Daula, abun da mamaki kuma har yanzu ko a jita jita babu wanda yaji inda yake, bawan Allah nan ba lafiya ba, yana fama da kansa ga tashin hankalin an sace masa 'ya, Amma a bishi har gadon Asibiti a sace, ga' yar tasa har yanzu babu wanda yasan inda take, abun akwai ban tausayi, Daula yana ganin Jarrabawa "
Bulama yace " tabbas, yana ganin jarrabawa, na rasa wani irin abune wannan ita kanta Widad wata na biyu zuwa uku kenan da ɓatan tal, amma babu labarin inda take, ni abun har tsoro yake bani"
Anwar yace "gaskiya ne, abun da tsoro kam, kamar Widad tasan meze faru ranar da zasu tafi farm house, tana kuka tacemin ga Amanar Daddy nan in kula dashi, nace mata zanyi iya ƙoƙarina, Amma ga abunda ya faru, i don't even know how to explain this incident to her when she's back "
Ramadan dake gefe yace " Allah sarki, karka damu ai duk wanda yaji abunda ya faru yasan ƙaddara ce, Amma ni wani lokacin har mamakin Widad nake, yarinyar nan 'yar baiwace akwai ta da kai"
Anwar yace "sosai makuwa, ina fatan Allah ya bayyana mana su gaba ɗaya"
Suka amsa da Ameen.
Haka suka cigaba da hira, sannan suka fito zasu tafi.
A harabar gidan suka haɗu da Fahad, Fahad yana ganinsa cike da borin kumya ya rungume Anwar yana faɗin "Ohh God, so you are free now, Alhamdilillah na ta yaka murna, Allah ya kiyaye gaba, nace zanje in duba ka akace ba'a bari a ganku"
Anwar yace "Haba kamar kai kaje inda nake ace bazaka ganni ba, da kazo da zamu iya haÉ—uwa ai"
Fahad yace "kasan bana son disgracing, and those people are good in that, but da naji ance court za'a kaiku ya akayi ka fito?"
Anwar yace "Al'amarin ubangiji ne kawai, shiya dubeni ya fitar dani"
Fahad yace "hakane, that's good ubangiji Allah ya ƙara karewa" ya kalli Amal yace "ke bakya kula mutane ne?"
Tsaki tayi tai masa wani irin kallon banza, ta buÉ—e mota ta shige.
Anwar ya girgiza kai yace "Fahad bari inje, akwai inda nake son zuwa daga nan".
"Ok, shikenan my regards to Mummy and lovely Ramla please"
Anwar yayi murmushin yaƙe yace "Fahad kenan, za suji insha Allah"
Daga nan shima ya juya ya shiga motar.
Suna cikin tafiya Anwar yace "wai Amal meyasa kuke yawan faɗa da Fahad ne? Banji daɗin abun kikayi masa ba, ya yanki ne fa"
Amal ta kwaɓe baki tace "nifa wallahi Yaya Anwar na tsani Fahad ɗin nan, nifa tun asali bemin ba, mugun maƙaryaci ne munafuki duk yadda kuke dashi ya kasa zuwa ya jajanta maka abunda ya same ka"
Anwar yace "to meye a ciki? Koma menene ba gashi Allah ya fito dani ba, idan kace zaka dinga biye wa mutane ranka ne kawai ze ta ɓaci"
Amal tace "taɓ ai kai zuciyar ka daban Yaya, ba kowa ze iya wannan abun naka ba"
Da suka je gida a waje yayi parking, ya kalli Amal yace "sauka ki shiga gida, ina son zani wani guri ne"
Ba musu ta sauka daga motar ta shige gida, shi kuma Anwar ya tafi.
Shiru shiru Yusuf be fito daga ɗaki ba, har Widad taje tayi wanke wanke ta dawo yana zaune a inda ta barshi, ta kalle shi tace "wai yau bazaka fitan bane?"
Jiki a sanyaye yace "zan fita mana"
"to ai naga ko wanka ba kayi ba, ko har yanzu tunanin kake ne?"
Ɗan murmushin yaƙe yayi, yana sake mamakin Widad, ya miƙe yaje yayi wanka ya shirya, yana yi yana kallonta yaga ko zata canza masa, amma yaga babu wata alama ta damuwa a tare da ita.
"zan tafi"
"Wai naga se wani sunkuyar da kai kake, kana komai a sanyaye meyafaru ne"
Cikin damuwa ya kalleta yace "bakomai"