Sashe 58
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jidda ta kauda kai daga duk wani ƙalubale da take fuskanta, akan rainon Yusuf ta kowane ɓangare, Bashir yana iya ƙoƙrinsa akan Yusuf, daya isa shiga makaranta ya sashi a makarantar kuɗi, wanda a wannan lokacin se 'ya' yan wane da wani ake kaiwa private school, amma yasa shi a private school, yasa shi a makarantar islamiyya, ga tahfeez sannan aka ɗaukar masa malamin lesson, idan Bashir na gari shike kai Yusuf makaranta ya ɗakko shi, idan baya nan kuma Jidda ke kaishi, Yusuf ya taso cikin gata da kulawa, yayin da gefe guda dangin babansa suka sake ɗora masa karan tsana shida iyayensa, mussman Jidda waita asirce musu ɗan uwa tasa sun ɗakko shege yana masa bauta, ya taɓe a gindinta dana wannan shegen yaron.
Babban abun mamakin be wuce yadda suma yana wahalta musu dai dai gwargwado yadda ze iya amma basa gani.
Yusuf ya tashi da tarbiyya da ilimin addini dana zamani, gashi da matuƙar haƙuri, da wuya kaga yayi fushi, be fiye shiga faɗace faɗacen yara ba, karatunsa ya fiye masa komai.
A tsakanin maƙwabta ma ana samun hassada da ƙyashi, ganin kaf tsukinsu babu me gatan Yusuf, komai ana masa sam bashi da wata damuwa, hakan yasa maƙwabta suma suka fara jin haushinsa, abun wasa duk tsadarsa zakaga Yusuf dashi, shi kaɗai amma keken hawa uku ne dashi na hawa, shekararsa takwas a duniya, amma har system yake da ita saboda karatun Al'qur'ani da sauran litattafan addini dana zamani, dan haka Ƙwaƙwalwar Yusuf na kawo wuta sosai.
Nanma maƙota suka fara jin haushinsa, saboda wannan gata da tarairaya a cewarsu dama gashi shege kuma ana ƙara sangarta shi, Yusuf tunda ƙuruciyarsa yake jin kalmar shegen nandm daga bakin mutane, besan ma'anar kalmar ba, amma yasan kalmace me muni, da wasu lokutan maƙotan ko yaransu kan gaya masa, ko kuma dangin Abbansa, Yusuf yana da matuƙar haƙuri da kawaici, ko wasa ya fito cikin yara idan yaga za'ayi faɗa ko rigima, seya bar gurin ya koma gida, wasu lokutan har haushin haƙurinsa Bashir ya kanji, yaita masa faɗa ya dena yadda yara suna masa rashin mutunci yana ƙyalesu, se yace ai malaminsu yace "Allah yace yana son bayinsa masu haƙuri"
Katsam ranar suka yi faɗa da wani yaron maƙwabcinsu, akan kayan wasan Yusuf ɗin, yaron ya dinga zaginsa, uwar ɗan ta fito ta shigarwa Ɗanta, Yusuf ya juya ze koma gida, yaron ya biyo shi ya dake shi, Jidda ta fito jin Hayaniya, Jidda tace "Maman Salim bekamata ki dinga shiga faɗan yara ba, ɗa na kowane kamata yayi ki haɗasu ki musu nasiha, in da kara ɗana da ɗanki ai duk naki ne, idan zaman tsakani da Allah akeyi, Yusuf da Salim duk namune'
" Ke saurara karki ƙara haɗa ɗan sunna da shege, tsintacciyar mage wadda bata mage, akan me? Kedai da kika ɗakkoshi kikaga zaki iya se kije kiyi, kekaɗai ne ɗanki amma ni wannan yaron ba ɗana bane"
Nan da nan ran Jidda ya ɓaci, kawai ta durƙusa a gurin fashe da kuka, da yake ita bata da baki sosai, Yusuf yazo ya rungumeta yai shiru yana sake juya kalmar shege a ransa.
Salim ya ɗau dutse da nufin ya jefi Yusuf, amma ya samu Jidda a gadon baya, karo na farko da Yusuf ya harziƙa, beyi wata wata ba yai sama da Salim ya sake shi a kwata.
Nan babar Yusuf ta gigice ta biyo Yusuf zata daka, dai dai lokacin motar Bashir ta shigo layin, take yayi parking ya fito yace "ke lafiya zaki dakarmin ɗa? Ke kuma Umman Yusuf meya sameki haka kike kuka?"
Aikuwa ba tayi nauyin baki ba ta gaya masa komai, nan ya fara sirfa bala'i, yace "na lura mutanen nan bakwasan zaman lafiya, wallahi duk wanda ya kuma kiran ɗana da shege sena ɗaure mutum, kai kuma Yusuf duk yaran da ya kuma gayamaka haka, ko ya dakeka baka zanemin shi ba, ni zan zaneka da kaina, ba babarka zaka dinga shigarwa faɗa ba, duk wanda yayi maka ka masa duka ka lallasan mon yaro, in yaso akawomin ƙararaka zan bada haƙuri "
Tun daga nan Yara suka ɗan saurarawa Yusuf, saboda babansa mutum ne me raha da barkwanci amma be iya fushi ba da tashin hankali, Yusuf ya cigaba da tasowa, tun be gane kalmar da ake gaya masa ba harya gane ma'anarta, baze manta ranar wata Juma'a ba, wadda itace ranar da ya gane mariƙansa basu suja haife shi ba, ya ɗauka ana gayamasa shegene kawai dan a zageshi, amma ya gane basu suka haife shiba.
Ƙanwar Bashir, me suna Balaraba ta haihu, saboda gudun magana yasa Jidda ta shirya, ta shirya ɗanta tsaf dasu, kai kace wata matar hamshaƙin attajirice, saboda Bashir baya wasa gurin kula da gidansa, daga ci har sha da sutura, baya wasa gurin basu, shiyasa kullum iyalinsa suke tsaf dasu.
Suka shirya tun safe Bashir ya tafi kaisu gidan suna, a ƙofar gidan yayi parking ya kalli Jidda yace "kin san Allah, ba dan kin matsa ba da bazakuzo sunan nan ba, ke kin damu Yusuf yasan 'yan uwana, saboda halin Rayuwa ni kuma nasan babu wani amfani da hakan zeyi, dan haka idan kimga ba hali ki samu abun hawa kukoma gida, idan kinga zasuyi muku cin mutunci ki kirani a waya ko ku koma gida kinji ko? "
Jidda ta jinjina kai, Bashir yace "ki kularmin da kanki da Yarona, ya kalli Yusuf yace  " My boy, zaka shiga cikin yara, bance ka saurarawa duk wanda ya taɓamin kai ba kaji ko? "
Yusuf yayi murmushi ya sunkuyar da kai, Bashir ya sumbaci goshinsa, sannan suka shiga gidan, suna shiga basu samu wata karɓar arziki ba, sema bimta da aka dingayi da kallo a nayiwa zanin jikinta kuɗi, da kayan jikin Yusuf.
Suka dinga zage zagen su, suna faɗar baƙaƙen maganganu, Jidda ta tashi da nufin ta taya su aiki, suka dinga caccakarta kamar zasu cinye ta ɗanya, suna mata gori suna zaginta.
Ta tashi ta koma gefe, ta ɗau Yusuf ta ɗora akan cinyarta, tana share hawaye, Yusuf ya kwanta a jikinta yayi lamo yana jin yadda take kuka, har kusan ƙarfe ɗaya ana ta rabon Abinci, amma aka hanata ita da Yusuf, ga lokacin da shabiyu na rana tayi, take bawa Yusuf abinci, se can wata mata daga maƙotan Balaraba ce ta kawo musu Abinci, dambun shinkafa aka kawo musu, sedai Yusuf baya cin dambu, se Jidda ta aiki wani yaro tace
"Dan Allah jeka gurin da ake rabon Abinci, kace a baka waina zan bawa yarone, in basu baka ba kazo ka karɓi kuɗi ka siyomin wani abun in bashi"
Yaron yana zuwa yace a bashi waina, wata ta kalle shi tace "waye yace a baka"?
Ya nuno Umman Yusuf yace "gata can, ita ce tace a bata zata bawa yaronta, wai baya cin dambu"
Asma'u tace "iyeee ina abun yake inji Mayya, saboda samun guri har wani zaɓen Abinci yaron yake yi, lallai abunda mamaki samun guri, dama ɗan uwanmu ne ya haife shi da sauƙi, amma kin sashi a gaba anje gidan marayu an ɗakko shege se wahala yake akanku, ke gaki juya shi gashi shege ba dangin iya babu na baba an samu guri se iskanci ake, kina ci kina ƙiba kina narka kashi, gefe shegen daba'a san asalinsa ba ma yana cin nasa rabon, kin kanainaye mana ɗan uwa kin hanashi yayi mana komai "
Balaraba tace " wai lafiya kike wannan kwarmaton haka? "
" inafa lafiya, za'amin iyayi da feleƙe wai wannan shegen yaron sun samun an basu Abinci, hadda turowa wai a canza masa bayacin dambu, saboda samun guri wai Abincin ma seya zaɓa, dan ubanka da a gidan Marayun ka taso, naga uban da zakawa sanaben baka cin kaza, kai kaza kake ci"
Jidda ta toshe baki ta fashe da kuka, a nan Yusuf ya fara fuskantar ashe ba Babansa ne ya haifeshi ba, idan be manta ba a makarantar su sun taɓa zuwa gidan marayu, akace musu wanda iyayensu suka yadda sune, kokuma wanda iyayen suka rasu, wato kenan shima yadda shi akayi, ko iyayensa na asali sun mutu.
Jidda ta tashi, ta kama hannun Yusuf ta baro gidan nan, kafin ta fito ma shaddarta milk ta sha aiki, suka watsa mata dagwalon kayan miya, haka suka tafi tana tafe a hanya tana kuka,
Yusuf yace "Umman Yusuf kiyi haƙuri, kidena kuka Allah yana son masu haƙuri, haka ya sayyadina yake gayamin"
Amma ta kasa dena kukan nan, ta rasa wani abu tayiwa dangin Bashir suka tsaneta haka, banda hauka ina laifin Yusuf a wannan al'amarin? Me yayi musu? Shida yake yaro ƙarami, take tayi wani tunani ita yanzu daba cikakkiyar lafiya ba, idan ta mutu waye ze kular mata dashi, ita dai Allah ya jarrabeta da son Yaron nan, tasan babu matar da zata kulamata da ɗanta tsakani da Allah haka.
Gaba É—aya wunin ranar haka suka yi shi babu daÉ—i.
Bashir na dawowa ta dake ta maze, ta ɓoye duk wata damuwa da take ciki, ta saki fuskarta, suka ci Abinci ya rungume Yusuf yana faɗin
"É—an Babansa, meyafaru ne? You look somehow disturbed, meyafaru ne gayamin"
Yusuf yace "am ko Abba, ba abunda yake damuna, munje gurin suna amma ba'ani Babyn na É—auka ba"
Bashir yace "Subhanallah, to shikenan rabu dasu, da kaina zan kaika a baka ka É—auka tunda kana so"
Yusuf yace "to Abba nagode, nima Allah yasa Ummana ta haifi Baby, in dinga kular mata da ita ina goya ta"
Bashir yace "Ameen ya Allah yarona, waini idan ka girma me kake son ka zama ne?"
"Daddy doctor nake son zama, surgeon doctor"
"Wow that's good my Boy, Allah ya bani rai da lafiya inga burinka ya cika Yusufana, kenan baza'abi sahun Abba ba a kare dukiya da rayukan al'umma ba?"
"Ina so Daddy, amma bana son in dinga cin hanci, ustaz ya cemin ba kyau"
Bashir yayi murmushi yace "babu aikin daba'a cin hanci Mu Son, nima na gashi police bane, kaga ina irin wannan?"
Yusuf yace "A'a".