Sashe 124
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daula yai shiru yana tunanin maganar da Widad tazo masa da ita, yadda yaga suna nan nan da su Widad, da yadda suka sake dasu, suma hira ama wasa ana dariya, da yadda mutane keta shiga suna fita a gidan, ya tabattar masa da cewa sun riƙe su Yusuf da Amana, dan haka duk wanda ya shigo gidan seya fita da kuɗi ko Abinci, Daula ya dinga basu kyautar kuɗi da Abinci, da wannan ya shigo se Widad tace Daddy ga wane a bashi kaza, ko kuma ai masa kyautar kaza.
Widad sun sha hira da Gwaggo, seda aka tuƙa tuwon nan taci, suna ta faɗa ita Hari, Hari tace "Ohh ni Hari, wai Wudas ce sa ciki, ranar haihuwa akwai kallo"
Widad tace "me za'a kalla?"
"raki da rashin haƙuri mana"
"Hari kema fa Allah kaÉ—ai yasan abunda kika yi haihuwar fari"
Umma sunyi hira sosai da Gwaggo, ta dinga bata labarin yanayin zaman da suka yi dasu Yusuf a gidan, Hanne kam ta kasa yadda ace wannan ne mahaifin Widad, iya motocin da suka cika ƙofar gidansu ma 'yan rakiya kawai abun kallone, banda rakiyar motar' yan sanda, wai ashe dagaske dai Daula ne baban Widad, lallai yaci sunansa Daula.
Ɗaliban Widad suka dinga zarya suma, suma zuwa gaishe ta da ɗaliban Yusuf, magidantan da yai ta koyarwa, sedai dukda wannan tarin kaɓakin kayan Abincin da aka rarrabawa 'yan ƙauyen, wannan yazo ya bawa Widad kyautar kuka, wannan ya kawo tsintsiya, wannan ya kawo Nono, ƙwan zabi zuma, haka suka dinga kawo musu wai suyi tsaraba, Daddy yai farinciki da karamcin mutanen garin, da yadda suka riƙe' ya'yansa suka zauna lafiya, gefe guda kuma ya tausaya musu yadda suke rayuwa ba makaranta, ba wutar lantarki ba kwalta bare Asibiti.
Kafin su bar garin, Daddy ya sanar da me gari cewa za'azo a gina musu makaranta ta boko da islamiyya a saka gwamnati ta kawo musu malamai, Widad kuma tace zata gina musu Asibiti, a kawo musu ma'aikatan lafiya, Daddy yace "Alhaji Yusuf baka yi magana ba"
Yusuf yai murmushi yace "Aini tunda aka musu makaranta da Asibiti, an gama min komai, fatana kuma ai musu boreholes na ruwan sha, saboda babu ruwa a garin nan, a saka gwamnati ta samar musu da wutar lantarki, saboda Asibiti baze yuwu babu wuta ba.
Nan jama'ar suka dinga murna suna Allah ya Sanya alkhairi, suna saka musu albarka.
Hindu kam ta ƙuke a ɗaki, tana tunanin abunda Widad ke shirin yi, banda abun Widad ina ita ina wannan hamshaƙin attajiri, ɗan gayu me ilimi ga kyau da dukiya, ita kuwa ga ƙauyanci da rashin wayewa, amma ta dage seta aure shi, ita gani take kawai ze aureta ne saboda 'yarsa, amma tabbas ba sa' ar Aurensa bace.
Tana cikin tunanin taji ana guÉ—a da shela a tsakar gida
"Alhaji Daula, yaga 'yarmu yana so, kuma harya bada kuɗin Aurenta naira dubu ɗari biyar, mudai zaman Yusuf da matarsa a garin nan namu alkhairi ne, yace ya gani yana so, kuma me gari ya amsa, yace ya bashi, watan arzikinmu a ƙauyen nan ya tsaya,' yarmu zata auri attajiri, ko iya Asibiti da makarnta da akace za' a mana aimu am biyamu, 'yarmu Hindu Tayi goshi, zungureren goshima kuwa "
Gaban Hindu ya faɗi, kenan dagaske dai ta tabatta Widad za tayiwa Babanta Auren dole da' yar ƙauye?
Hanne kuwa gigicewa tayi, dan a ganinta tafi Hindu komai, dan meyasa ba'ace itaba se wata Hindu, Hindun daba wani kyaune da ita ba ga baƙin jimi, amma ace zata auri attajiri haka.
Da zasu tafi Widad ji tayi kamar karsu tafi, dan sosai takejin kewa da ƙaunar mutanen garin, saboda karamcinsu da girmamawa, Ta shiga ɗakin Gwaggo ta sami Hindu a ƙarshen gado tayi shiru tana tunani.
Widad tace "Hindu, karki ɗaga hankalin ki, babana bashi da matsala ko damuwa, mutumin kirki ne zaku zauna lafiya ƙalau dashi, sannan an saka wata biyu, saboda kafin ɗaurin Aure a kawo muku cigaba garin nan, saboda manyan mutane ne zasu garin nan, munyi magana za'a aiko da mota tun saura sati biyu biki a ɗauke ki a kaimin ke can kano, mu fara shirye shirye "
Hindu kawai jinjina mata kai tayi, daga nan suka yi sallama suka tafi, a hanya sunata jinjina karamci da mutuntawa na wannan al'ummar gari.
Gaba ɗaya ƙauyen nan ya ɗauka, Daula ze auri Hindu, ga kuma kaɓakin arzikin da aka sauke musj, sunata rawa da murna ga alƙawarurrukan da aka musu na kawo musu cigaba a garin.
Su Widad kuwa garin kanon dabo suka wuce kai tsaye, suka sauka a farmhouse, Bayan sun huta Alhaji Ahmad ya wuce gidansa, Umma tace ba zata zauna a nan gidan ba, gidanta zata tafi, shi kuma Yusuf nauyi yake ji, koba komai Daddy sirikinsa ne, ace suna gida ɗaya su kwana ɗaki ɗaya da Widad, haka ya basar Widad kuma ta dage se Umma ta kwana a gidan ba zata tafi can gidanta ba, da ƙyar Umma ta yadda ta amince.
Wasa2 Seda suka kwana biyu da dawowa, amma suna farmhouse tare da Umma, kullum se Alhaji Ahmad yazo, Umma ta takura akan cewa lallai seta bar gidan, dan ita gaba É—aya jinta take a takure.
Daddy yace zasu rakata gida, kafin nan ze kaisu gidan daya saiwa su Yusuf, kuma ranar nan da sati biyu Yusuf ze tafi Lagos, inda babban kamfanin shige da ficen ƙarafa yake, wanda yake mallakinsane, shi dai Yusuf jin abun yake banbarakwai, kamar bashi ba.
Koda suka fita seda suka fara zuwa ainihin gidansu da suke zaune, suna zuwa ma'aikatan nan suka dinga rige rige zuwa gurin Daula, ganin ya bayyana ashe yana raye, sedai gidan kamar kango, ba shige da ficen mutane, ba manyan motocim dake harabar gidan, abun duk se a hankali.
Nan su Murtalah, Nura da sauran ma'aikatan gidan suka dinga tururuwar zuwa gaban Daula, masu kuka nayi masu murna nayi, ai nan da nan labarin bayyanar Daula ya karaÉ—a gari, da jaridu Widad kam cikin gidan ta wuce, tana ganin gidan ya koma kamar wani kango.
Alhaji Daula yace "ina sauran mutanen gidan?"
Nura yace "ai ranka ya daÉ—e ai an kama Hajiyar"
Daula yace "nasani"
Nura yace "to yanzu dai, 'yan sanda sunzo sun kama Ramlah jiya, se Amal ce kawai a cikin gidan"
Daddy ya jinjina kai, ya shiga cikin gidan, yana shiga ya tarar Widad ta wuce ɗakinta, Amal tana zaune a falon tana ta kuka kamar an mata mutuwa, ta rame sosai kamar wadda aka zuƙewa jini, tayi baƙi sosai duk ta canza kamanni gwanin ban tausayi.
Maimakon Daddy yaji haushinta sema wani tausayinta daya kama shi, kafin yai magana Widad ta fito, Umma tace "Yusuf wannan kuma wacece?"
Yusuf yace "Umma wannan itace Amal, 'yar matar gidan nan ce"
"Amma ya naganta kamar mara lafiya?"
Yusuf yace "nima ban san abunda ya sameta ba"
Widad ta kalli Amal tace "Malama You have to leave this house, within some minutes, azzalumai kawai marasa tsoron Allah, masu butulci"
Amal ta shiga girgiza kai tana cigaba da kuka, dan idan ta fita bata san ina zata ba, dan bayan mamansu ta auri Daula, a dangima ba kowa take gani da gashi ba, yanzu idan ta fita ina zata?
Cikin tsawa Widad tace "Am talking to you"
Daddy yace "No Widad, É—an dakata tukuna"
Ya ƙarasa gaban Amal ya durƙusa, yace "Amal ɗin Daddy, baki da lafiya ne? Kikayi wannan ramar haka?"
Amal cikin kuka tace "Dan Allah kuyi haƙuri, kuyafemin, dan Allah, dan Allah kuyi haƙuri"
Tai maganar tana haÉ—a hannayenta alamar neman afuwa ðŸ™
"Daddy, waiya kake wani lallaɓatane? Do you want give them another chance to finish us?"
Daddy ya girgiza mata kai, ya sake kallon Amal yace "yanzu meke damunki kika rame haka?"
Nan ta gaya musu yadda akayi mata fyaɗe, Alhaji Haruna ya keta mata mutunci da abunda likita yace, a maganartata zaka fuskanci ta samu taɓin hankali.
Yusuf kansa seda tausayinta ya kama shi, duk rashin mutuncinsu, Amal ta ɗanfi sauƙin kai, dama Ramlah tafi zaƙewa da wulaƙanci.
Daddy yace "ki kwantar da hankalinki, nasan yanzu dole zaki shiga damuwa sosai, saboda gaba ɗaya 'yan uwanki da iyayenki suna hannu, ina fatan ze zame miki izina akan abunda ya faru, ban miki Alƙawarin saka baki akan taimakon mahaifiyarki da yayarki ba, saboda sun cutar dani a rayuwa, amma daga nan ko zuwa wace ƙasane, daga naira ɗaya zuwa miliyoyi, zan kashe a nema miki lafiya, kidena kuka kiyi musu fatan Allah ya shiryesu, sannan ki dimga musu Addu'a "
Aikuwa a hasale Widad tace " Daddy, why? Me yasa zakayi wannan hukuncin, dukda tarin laifukan da suka aikata mana? "
Yusuf ma cikin tsawa yace " Widad, Daddy kikewa magana fa, talk to him with respect "
" Haba Yoseef, a gabanka akace Mahaifimsu aka saka ya kashe min Ammina, yanzu meze sa Daddy ya temake ta? Bayan yadda suka so ganin bayana, da ganin ma zama mahaukaciya tuburan?"
Daula yace "Widad, ɗan halak baya manta alkhairi, ko bakomai ɗan uwanta yamin wahala, yayi ɗawainiya dani a Asibiti, yamin biyayya, kuma itama ba laifi tana girmamani, albarkacin Anwar nakeso Amal taci, ba ita tayi miki laifin ba, dan haka kiyi haƙuri, kiyi haƙuri ba danni ba dan Allah "
Daddy ya riga ya É—aureta da jijiyoyinta, dan haka dole tayi shiru.
Daga gidan suka wuce inda nan ne gidan da Daddy yace nasu Yusuf ne, a unguwar lamiÉ—o crescent, gida ne hargida ya haÉ—u ya tsaru iya tsaruwa, kamar ba'a Nigeria ba, Widad nata murna yayinda Yusuf ke jinjina abun, waishine da wannan gidan haka?
Amma Babban abunda Widad bata ji daÉ—insa ba, be wuce yadda Daddy yace " wai anyi bookin É—in jirgi shida Yusuf a ranar zasu tafi lagos da yamma, dan canne inda kamfanin Yusuf yake, zeje a nuna masa abubuwa tun yanzu, Widad taji haushi sosai, dan harga Allah tana kewar mijinta sosai, kusan watanni shida ana neman na bakwai basa tare, amma haryanzu sun kasa samun dama su kasance tare, shikansa Yusuf mazewa yake dan yana da kunya sosai amma yana kewar matarsa sosai, Widad ce dai wani lokacin se a hankali bata fiye jin kunya sosai ba, duna da yanayin rayuwarta.