← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 127

Sashe 2

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf yace "Hmm Allah ya shiryeki to, aini ban san haka kika iya neman magana ba, ganin cewar a baya ko maganar ma bakya son yi, idan anga fara'arki to da magenki ne roux ko kuma Daddy"

"Allah sarki, harka tunamin da sister roux É—ina, nasan tana missing É—ina, maybe ma yanzu sun barta ta mutu saboda yunwa, nasan bame kulamin da ita, nima haushina suke ji balle magena"

Yusuf yace "Eyya Sorry, Insha Allah bata mutu ba zamu koma ki tarar da ita tana nan"

"Hmm is very hard gaskiya, am missing Home Yoseef, ina tunanin dabbobina gaba É—aya nasan suna missing É—ina"

"wai me yasa kikafi son dabbobinki akan mutane, kina ƙaunar dabbobi sosai"

Widad tayi ajiyar zuciya tace "labarin yana da tsayi sosai, Amma tabbas dabbobi sun fiyemin mutane, except in some circumstances, duk abu indai dabba ta shaƙu da kai, ba zata yadda a haɗa kai da ita a cutar da kai ba, amma dan adam fa yana iya manta dukkan alkhairinka a hada kai dashi a cuceka, shiyasa na zabi rayuwata a cikin dabbobi”

Yusuf yace “hakane maganarki amma sedai ba duka aka zama daya ba, Amma na Allah  ai basa karewa sannan ba yadda zaai ace mutum yayi rayuwa ba mutane"

Widad tace "kai ka ga haka, nikam nayi, kuma yafi kwanciyar hankali"

Yusuf yace "Ai ba ƙaramin mamaki nayi ba, ranar dana ga kina sukuwa akan doki"

Widad tayi murmushi tace "i miss that Moment, ko a England ina wasan polo, ina son tseren dokuna sosai"

Yusuf yai murmushi yace "ko tsoro ba kya ji"

Daga nan  be kuma cewa komai ba ya maida kai yayi shiru yana da  cin abincin a hankali, widad ta kalleshi tace kamar
" akwai Magana abakinka da kake so ka gayamin,naga jiya tun jiya kana ta yawan kallona"

Yusuf yace aini kullum cikin kallonki nake, babu wani abu da nake son gayamiki

"shikenan tunda kace haka,amma gara inda akwai ka gaggauta gayamin, bazan takuraka seka gayamun ba amma nasan akwai abunda yake damunka”

“kinfara samun ido kenan?”

“ba ido nake samka ba, yanayinka ne ya nuna min, amma shikenan ba ina kokarin matsa maka bane, ko son sanin me kake ciki ba, ni bari in tashi in fita in dan sha iska”

Yususf ya kalleta yace “bana son kifita ki barni,ina jin daɗin hirar nan da muke”

Yamutsa fuska tayi tace  "ni kuma na gaji da zaman dakin, dan haka waje zan fita”

Yusuf yace “shikenan tunda haka kike so,your wish is mine my queen”

“ka ji dashi dai, inka gama karka manta da shan maganinka" daga nan tai waje abunta

Alhaji Haruna ne shida Alhaji Munir suke cigaba da tattaunawa akan al amuransu.

Alhaji Munir yace "‘anya baka ganin ayi kokari a sakarwa matar nan danta, da yasan inda Daula yake iya azabar da aka gana masa ya isa ya fadi inda yake, amma tunda be faɗa ba to tabbas besan inda yake ba, gashi ana batun tafiya kotu, karfa matar nan ta tona mana asiri”

Alhaji Haruna yace “ka kwantar da hankalin ka, hakan ma duk shirine, idan sun tafi kotu, za a dauke hankalin mutane daga wasu abubuwan, da zarar hankali ya dauke ya karkata can, mukuma semu cigaba da barnar mu, kafin a farga mun kwashi abunda muka kwasa koda wancan abubuwan basu samu ba”

“banƙi ta taka ba, amma ka gane wani abu guda daya, mudinga yi muna ankarewa da abunda ze biyo baya, yanzun idan aka shiga kotun nan slide mistake ze iya sakawa asrinmu ya tonu, sannan maganar  da muke har yanzu fa babu wanda yasan inda yaran nan suka shiga, tunda suka gudu har yanzu shiru babu labarinsu, babu labarin inda suka tafi, kuma har yanzu basu dawo garin nan ba, gaba daya a tsorace nake, kuma yakamta ace zuwa yanzu shi wannan yaran da muka sa su sace su me adda yake kowa?, yakamata ace basa raye bekamata abarsu suci bulus ba,suma fa hatsarine as garemu”

Alhaji Haruna yayi murmushi yace “Alhaji Munir ikon Allah, kaikam wasu lokutan akwaika da tsoro, munefa masu kasar nan, ko yaya muka ga wani abu na shirin kawo mana tangarda zamuyi maganinsa, mukeda hukumar tsaro kudi da masu mulki, kai a tunnainka har akwai wani wanda ze kawo mana tarnaki ne? ka sha kuruminka, komai a tsare yake, shekara nawa mukayi ana tafiyar nan, ba tare da an samu mtsala ba? Karka manta Alhaji Bukar ma fa namune, kadai mubi komai sannu”

Alhaji Munir yace “ duk nasan da wanan, amma abunda nake so ka sani shine,wannan mahaukaciyar matar fa zata iya komai idan taji za a kaimata danta prison,bafa zata zuba mana ido tana kallo danta ya tafi prison ba”

“karka damu za a san yadda za ayi da ita”

“shikenan, amma nifa kwanan nan na fuskanci wasu halaye da Musa yake yi, sam na kasa gane kansa fa”

“ba kai kadai ba, nima kallonsa kawai nake, kar ace na fiye matsawa ne ko neman rigima shiyasa kawai nake kyleshi”

Alhaji Munir yace “Banda shi mahaukaci ne, wai takara ze fito, ubanwa ze zabeshi bayan bakin tabon da Daula ya goga masa, ai mutane ba mahaukata bane”

Alhaji Haruna yace “kyaleshi ai ya zata mutane basu da hamnkali, a da alokacin da yayi siyasar ma ai farin jinin Daula ne yasa aka zabeshi, ba wai dann ya cancanta ba, mu zuba masa ido ya cigaba da haukansa tunda bashi da hnakali”

“aikam babu alamar hnakli, gara yaje mutane su cinye ɗan abunda ya tara ɗin ai, se sun talauta shi sannan yazo ya fadi zaben, mutum se taurin kan tsiya, baya ɗaukar shawara sam, indai 'yan siysa ne zasu ziga shine, su cinye komai idan ya fadi su gudu su barshi”

Alhaji Musa yace “:ai shiyasa ban damu da in bashi shawara ba gara yaje suma suci rabon su, daga baya yayi hankali ai”

‘shikenan, ni bari in wuce se munyi waya”

“shikenan,semunyi waya”

Daga na sukayi sallama.

Ganin wucewar Hajiya Halima ne yasa Ramlah bin bayanta zuwa dakinta, tana zuwa tace “Mummylafiya kuwa?”

Zama hajiya Halima tayi tace “ina fa lafiya, wai kotu za akai Anwar kotu fa Ranlah”

“mummy wane irin kotu kuma? Ba za bada belin nas ba ?”

“sun hana , sunce ba zasu bada belinsa ba, kuma wadan nan banzayen sunki suyimin komai akai, sun barni se wahala nake nikadai, nikadai na haifeshi nikadai nake wahala ta, dan san abunda ze biyo baya kenan da ban barin Anwar yaje yana wannan wahalar ba, idan yaso ba zagi ba ko tsinewa ce duniiya sumun baze dameni ba,amma ina kallo akaimin da na prison baze yuwu ba, niba abun  in tona asiri ba, nima zan kwana a ciki, da sedai ayi duk wadda za ayi”

Ramla tace ” mummy kiyi hakuri, ki kwantar da hankalinki, idan kika fallasa ba iya asirinsu ba hatta namu muma ze tonu ne, dan haka kiyi hakuri mubi a hankali”

“wani irin mubi a hankali komai yana lalacewa, in zuba ido akaimin ɗana prison sam baze yuwu ba wallahi, ana shiga kotu nasan prion ne zasuce zasu kaimin shi”

“babu me kaishi prison, kidena damun kanki, Anwar ze fito”

Haka taita kwantar mata da hankali.

Tunda widad ta fice tsakar gida bata sake komawa ɗaki ba, tana maƙale da Gwaggo da Hindu tana koyo aikin gida, yayinda gefe guda sunayi suna faɗa da Hari, yayinda Hanne keta jifanta da bakaken maganganu, wani abun Widad ta gane wani ba zata gane ba, dan wata hussar ina tayi tsauri bata ganewa sam, ita dai tafi maida hankali akan ta koyi aikin,Gwaggo bata hantarar ta idan tayi ba daidai ba seta gyara mata cikin ruwan sanyi.

Saleh ne ya shigo gidan, ya tarar Widad zatayi tatar gasara, tanata kokowa da abun tatar Gwaggo tana gyara mata, gashi ta maida duk hankalinta so take ta koya, gwanin ban dariya da tausayi.

Saleh yace "Ina kwana ranki ya dade?”
Dagowa widad tayi ta kalleshi cikin basarwa tace “lafiya kalau”

Saleh yace  “aiki kike ne?’

Gwaggo tace “aikam aiki muke tayi”

”madallah sannu da kokari Gwaggo, ya me jiki kuma?”

Gwaggo tace “jiki da sauki Alhamdilillah”

“mashaallah, bari inshiga in duba shi”

Widad na jinsu tayi masa banza taki kula shi.

Da sallama Saleh ya shiga dakinsu Widad, ya tarar da Yusuf a zaune yayi shiru yayi zurfi a duniyar tunani, Yusuf ya dago ya amsa.

Saleh yace “ya dai ko jikin ne?”

Yusuf yace “ jiki ai naji sauki Alhamdilillah”

“madallah ai haka ake fata, ai can naga mutuniyar taka a tsakar gida tana ta kokawar yin tatar gasara, se barna take”

Yusuf yayi dariya yace “danma baka ga yadda take tankaɗe ba, bakaga asarar garin da tayiwa Gwaggo ba, ai Gwaggo ba karamin mutunci take man aba, se fatan Allah ya sakamata da alkairi”

Saleh yace “ai abunma da takaici ace yarinya kamar wanna bata iya aikin gida ba,abun da kunya ai”

“yakamata kiyi mata uzuri da an koya mata da zata iya ai”

Saleh yace “waye ze koya mata, ta dinga hantarar mutum tana masa wulakanci”

Yusu yace “adinga kara mana matata ce fa Saleh”

Sale yai murmushi yace “masu mata manya,to Allah ya bada hakuri, na manta ne, Allah yasa in an tashi komawa a tafiwa da Daula jika”

Shiru Yusuf yayi bece komai ba yana tunani, Saleh yace “lafiya kuwa?”

Yusuf yace “Saleh akwai matsala ina cikn damuwa sosai, har yanzu bata san waye niba, bana son taji a wani gurin tayimin kallon makaryaci, yanzu ban san ta in zan faraba bansa n ya zata kalli abunba, zata iyayimin bore ina tsoron darunta”

Saleh yace “hakane amma ai kai namijine, kuma zuwa yanzu duk ta rage wasu abubuwan ai, ba lallai ta maka wulakanci tunda yanzu ba wanda ta sani se kai”

“Saleh anya ba ka manta wacece Widad ba? Jiya ta gama jadaddamin bata yafiya ga wanda yayi mata karya ko yaci amanarta”
Chapter 2 · 0% Book details