Sashe 111
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Widad bata da gurin wanda zata ta zauna, Akace a kaita gidan gwamnati fa zauna, kafin Allah ya bayyana mahaifinta, tace ita gidan gonar nan zata je ta zauna, akace baze yuwu ta zauna ita kaÉ—ai ba, Amma Widad ta dage ita babu gidan wanda zata ta zauna, aka ajiye jami'an tsaro a layi da kuma cikin gidan dan tsaron lafiyarta aka barta ta zauna É—i .
Widad Ta dinga tunanin ya akayi Yusuf be nemeta ba, dukda yayi free yanzu, sedai tayi tunani babu lallai Yusuf ya sake karɓarta, bayan ta gaza taimakonsa a lokacin da yake buƙatar hakan.
Gaba É—aya gidan ya canza, babu manyan dawakan nan nata, da wasu daga dabbobinta duk babu su, haka manyan motocin dake gidan duk babu, an kwakwance wasu abubuwan masu mahimmanci daga gidan, taga gidan ya mata faÉ—i, babu Daddy babu kowa a tare da ita yanzu.
Ta zauna tai shiru tana tunani, ta fito harabar gidan tana zagaye, ma'aikatan se zuwa suke suna mata fadanci, suna mata jaje tare da barka da Arziki, ta kira wani daga cikin ma'aikatan gidan Imrana, yazo gabanta ya durƙusa tace "naga gaba ɗaya gidan nan ya canza, ina wasu daga cikin dabbobina da motocin duk da suke cikin gidan nan?"
Imrana yace "ranki ya daɗe, Hajiya ce take turowa a ɗiba a fita dasu, kuma bamu da ta cewa"
Widad ta jinjina kai tace "shikenan jeka"
Haka ta dinga zaga gidan, tana tuna abubuwa da suke shuɗe, da abubuwan da suka faru daren da akayi garkuwa dasu, ta shiga ɗakin data kwanta a ranar, tana dube dube, can ta hango wayarta guda ɗaya a ƙasan gado, Da daddy yazo ya azalzaleta ta tashi ta fito wayar ta faɗa ƙasan gado, ta ɗau waya ɗaya ta fita, waya ɗayan da yanzu bata san a inda take ba, ta ɗakko wayar ta ganta a kashe, ta jona a jikin caji aikuwa ta kama.
Ta jona wayar ta koma ta zauna, a hankali tace "Yoseef am missing you, i have no one, help me to relay on you, ka yafeni ka dawo gare ni mana"
Ta yanke shawarar komawa tayi zamanta ita kaÉ—ai, ta cigaba da Addu'a Allah ya bayyana mata mahaifinta, kota rage wata damuwar, amma da kunya a gareta ta tinkari Yusuf a yanzu.
Gaba ɗaya damuwa da kaɗaici suka baibayeta, ta fito ta ɗau mota zata fita ɗaya daga cikin 'yan sandan dame gadinta yazo yace "ranki ya daɗe, ina zakije ne haka?"
"Fita zanyi" ta bashi amsa
Yace "ranki ya daɗe har yanzu kina ƙarƙashin kulawar' yan sanda ne, idan kika fita ke kaɗai hakan ze iya zame mana laifi a sama"
Widad tace "shikenan, dan kuna gadina bazan fita ba? Da can wake kula dani idan ba Allah ba? Ina kuna garin nan da saninku aka siye wasu daga cikinku akaci zarafin mijina, aka sacemu babu wanda yai yunƙurin kawo mana ɗauki, se yanzu zaka zo kana gayamin zancen banza? Ban fidda ran a sake dawowa a haɗa baki daku a cuceni ba"
Ɗan sandan yace " Allah ya temakeki, kiyi haƙuri kin san duk yadda kaso ga kamanta gaskiya, se an baka umarnin aimata wani abun daga sama kafin kayi, amma dan Allah kiyi haƙuri karki fita ke kaɗai, dan Allah ki rufamana Asiri, za'a iya ladabatar damu idan mukayi sakaci wani abun ya same ki, har yanzu kina ƙarƙashin kulawar jami'an tsaro ne"
Ta jefa masa key ɗin mota tace "kaini gidanmu, inda muke zaune"
ÆŠan sandan ya É—auki key É—in, yana mamakin wannan izza ta Widad, ta shiga bayan mota ta zauna, ta tuna idan Yusuf ze fita da ita, a gaban mota take zama, suna tafe wataran tana zazzaga masa masifa, ko kuma yana wani abun da ze bata haushi suyita faÉ—a.
Ta lumshe idonta tana jin yadda sonsa ke ƙara ratsa ilahirin gaɓoɓin jikinta, se yanzu ta yadda so babbar cutane, bata taɓa tunanin haka yake ba, bata zaci tayi sabo da Yusuf haka ba, tana jin ya zama wani ɓangare na rayuwarta gaba ɗaya, kobe nemeta ba doke ita ta nemeshi.
Suna zuwa ƙofar gidan, tace ya tsaya yayi horn, yai horn aikuwa Isa yaeƙo yaga waye, kawai ya hangi Widad a bayan motar, aikuwa ya gigice ya tafi da gudu ze buɗe Gate, ya dawo ya kuma komawa ya rasa mema zeyi.
Widad ta sauke gkass ɗin motarta tai masa nuni da yazo, ya taho da sauri jiki na ɓari yazo ya durƙusa yana faɗin "Allah ya temakeki, Allah ya tsare ki sharrin maƙiya" kawai ya fashe da kuka ya kasa cigaba da maganar.
Widad tace "Lafiya kuwa? Me yasaka kuka kuma?"
"ranki ya daɗe dole inyi kuka, tunda kika tafi babu ke babu Yallaɓai, gaba ɗaya gidan annurinsa ya ɗauke, muka shiga mummunan yanayi, katsam kuma se gashi kun dawo amma ba'a yadda akeso ba, a wani yanayi na daban abubuwa sun faru marasa daɗi ranki ya daɗe Alhamdilillah tunda dai kin dawo kuma kin kuɓuta "
Widad tace " Isa dukda mugayen halayena da kuke faÉ—a, dama zaku iya shiga damuwa dan na bar gida? "
Isa yace " A'a a'aha, ai ranki ya daɗe Hausawa sukace kada Allah ya kawo ranar yabo, amma wallahi zamanki a gidan nan ba ƙaramin haske bane, mungode Allah"
Widad tace "shikenan, kiramin su Nura da Murtalah"
Yace "ranki ya daÉ—e, bazaki shiga gidan bane?"
Tace "Eh, kiramin su"
Isa ya zabura da sauri hadda gudu, ya shiga gidan yana ƙwalawa Su Nura kira.
Aikuwa gaba ɗaya suka rankayo suka biyo shi, suna zuwa suka ga Widad bakinsu yaƙi rufuwa, suka zube a gabanta suna surutai kowa da abunda yake faɗa.
Haka nan Widad taji ƙwalla ta rasa ta mecece? Tai murmushi tace "Nagode Allah, tunda duk kun tsallake tarko da sharri na Bulama, naji daɗi Sosai da gudunmuwar da kuka bayar a kotu, gurin kuɓutar da mijina, nagode muku sosai Allah yasaka da alkhairi"
Murtalah yace "wai dagaske ranki ya daɗe Yusuf mijinki ne?"
Abun mamaki wai yau Widad na hira da maa'ikatan gidansu, matar da ko murmushinta ba'a gani idan ba na mugunta ba, ko tana gaban mahaifinta ba.
Widad tace "Eh mijina ne, ko akwai magana ne?"
Murtalah yace "A'a, abunne da mamaki sosai ranki ya daɗe"
Widad tace "IKone na Allah kawai, naji daɗi Sosai da kuka temaka da sheda a kotu"
Murtalah yace "Ai bakomai ranki ya daɗe, Yusuf mutum ne ya cancanci a temaka masa, tunda na tsinci takaddar nan na rasa ina zan kaita, saboda barazana da akewa duk wanda yai yunƙurin temakawa Yusuf, katsam sega lawyern Yallaɓai, ya gayyacemu gidansa a ɓoye yai tattaunawar sirri damu, a nan na bada wannan takaddar "
Widad ta jinjina kai tace " Masha Allah, ina godiya sosai da gudunmuwar ka, kuma insha Allah kuna da tukuici akan wannan gudunmuwar da kuka bamu "
Nura yace " Allah ya temakeki, wai yanzu dama duk abubuwan nan Alhaji Bulama ke shirya su, tabbas banga laifinki ba na ƙin mutane da kike, amma abun ya bamu mamaki sosai "
Widad tai murmushin takaici, har bata son yuna irin azabar da suka sha, tace " ya ake cikine? Me gidan namu yake ciki dan bazan shiga ba"
Nura yace "ranki ya daɗe, gida babu daɗi dan ya watse gaba ɗaya, bayan ɓatanku, Yallaɓai ya faɗi yai wata rashin lafiya, babu me zuwa gurinsa ko kula dashi se Anwar, shine yake masa komai yake jinyarsa, da aka sace Yallaɓai a gadon Asibiti ma aka kama shi, akace da saka hannunsa ya sha wahala sosai, Amma ya kula da Yallaɓai "
Jiki a sanyaye Widad tace " Allah sarki Anwar, yana gidan ne yanzu haka? "
Su Isa suka kalli Juna, jin bata san meyafaru ba.
Isa yace " ranki ya daÉ—e, Amma kin san an kama Hajiya ko? "
Tace" Eh na sani "
Yace" to dama ya bar gida ai tuntuni, takaddar daya bari ai ita Murtalah ya tsinta, ranar da aka yi zaman ƙarshe a kotu, muna nan 'yan sanda suka zo a motoci suna ta jini ya, na buɗe musu gate sukazo suka shimfiɗe Anwar, an gano shi a wani gida yake rayuwarsa yana kasuwanci a can cikin Jos, aka kawo shi an kasheshi ta hanyar caka masa makami a gefen cikinsa, sedai babu wanda yasan wanda ya kasheshi, amma a ranar kukan da Hajiya Halima take kamar dasa hannun shi Bulaman dai a kisan"
Ai tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta dinga jujjuya kai tana maimaita innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Ya Allah, Yaya Anwar ubangiji Allah ya jiƙanka, naso na sameka a raye in maka godiya riƙemin amana da kai, amma zan dawwama yi maka Addu'ar samun salama a kabarinka, kana daga cikin mutanen da bazan manta dasu ba a rayuwata, Allah ya yafe maka Yaya Anwar"
Kuka yaci ƙarfin Widad, yayin da suma duka jikinsu yayi sanyi sukaji mutuwar tamkar yanzu akayi ta.
Widad cikin kuka tace  "Murtalah ka sameni a farm House gobe in Allah ya kaimu da yamma, nagode muku Allah yasaka da alkhairi nagode sosai"
Ta kasa ko rufe ƙofar motar, se kuka da take yi, Isa ya rufe mata ƙofar motar, ɗan sandan nan ya ja suka tafi, suna tafe tana kuka, dan Mutuwar Anwar ta da keta fiye da tunani.
Yusuf ya É—an warware, Suleiman ya kwashe su a mota domin sujewa Nurat gaisuwa, da yake an kwana biyu da rasuwar mutane duk sun watse se tsilla tsilla.
Kahlil yai musu iso har wani katafaren falo, aka kira Nurat, Nurat ta fito cikin Ƙaton hijjabi, tana ganin Yusuf ta kasa magana se hawaye haɗe da murmushi daya ƙwace mata.
Ta durƙusa har ƙasa ta gaida Umman Yusuf, Yusuf yace "Nurat ya ƙarin haƙuri kuma?"
Nurat tace "Alhamdilillah"
"Allah ya jiƙanta yasa ta huta"
Nurat tace "Ameen"
Nan duk sukayi mata gaisuwa, Umma tace "dama munzo muyi miki gaisuwa ne, kuma zamuyi zuwa na mussman muyi miki godiya '
Yusuf yace " Nurat, ban san me zance miki ba, wanda ze nuna irin tarin godiyar dake bakina ba, a sanadiyata ga abubuwa marasa daɗi sun faru dake, Nurat dan Allah kiyi haƙuri, ban san mema zance ba"