Sashe 32
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka cigaba da hira, ba tare da sun yi faɗan da suka saba ba, bayan sun kammala Yusuf ya gyara gurin, yaje yayi wanka sannan itama ta ɗau bokiti taje ta karɓi ruwan wanka, Hari taita mita wai zuwa yanzu yaci ace Widad tana wanka da ruwan sanyi, amma dan gajeren fi'ili kullum se an bata ruwan ɗumi.
Widad bata saurareta ba ta tafi wankanta, bayan ta fito ta shiga É—aki, ta ajiye bokitin ta nufi shimfiÉ—ar ta domin sa kaya, tana hasakawa da fitila taga Yusuf kwance akan katifarta, daga shi se gajeren wando, ya lumshe ido da alama bacci nema ya É—auke shi, da farko seda ta firgita ganin sankacecen mutum dogo kwance a gurin, daga baya kuma taga Yusuf ne.
Ƙafarsa ta haska taga ciwon da yaji yana warkewa a hankali, sannan ta hasak jikinsa, tun daga kansa har fuskarsa zuwa ƙirjinsa da ƙafafunsa, lulkuɓe suje da dogayen gashi.
Inda akwatinta suke a gefen Yusuf ne, gashi ya kwanta a gurin, kuma bata son ta tasheshi dan da alama a gajiye yake, ta zarwle hijjabin jikin ta ta shanya saboda a jiƙe yake da ruwan wanka, tazo ta zauna kusa da Yusuf tana son ta ɗakko Akwatin, amma se taga kamar ze tashi, ta ɗan ƙura masa ido, duk ya rame se dogon hancinsa da yake tsaye kyam, ga ƙasumba data fara fito masa wadda da bashi da ita (kasancwarsa jam'in tsaro, basa tara gemu) .
A hankali hannunta yana rawa, ta kai hannunta kan sajensa, wanda yake a kwance kamar na Fulani, a hankali ta dinga shafa gashin ta gangaro har ƙirjinsa inda gashin yafi yawa, ta dinga wasa da gashin a hankali, tana yi tana zancen zuci, yunƙurawa tayi zata ɗauke hannunta taji ya riƙe hannunta, zaro ido tayi a firgice tace "dama idonka biyu?"
Gaba ɗaya ya janyo ta jikinsa, ya kwantar da ita akan katifar, yace "me kike yi ne tun ɗazu? Duk abunda kike ina jinki fa"
Haɗe rai tayi tace "ɗagani Malam, wai baka san kana da nauyi bane?"
"Ya za'ayi in sani, kin zauna tun ɗazu se taɓani kike"
"jika wai se taɓaka nake, me zan taɓa wannan gashin daka tara duk abun ƙyama ma, abun amai shine ɗin zan taɓa, ni cikani in sa kaya, kar towel ɗina ya cire"
Dariya yayi, ya haska fuskarta da fitila yace "meye abun ƙyamar? Gashin jikin nawane abun ƙyama ko kume me?"
Rufe idonta tayi tana tura baki, ya kama hannuta ya ɗora akan Ƙirjinsa, yace "da abun ƙyamane dabe burgeki kin taɓa ba"
Tace "meye abun burgewa anan, sakarmin hannuna ko in tsige gashin nan É—aya bayan É—aya"
"gaki na gashi ai, yi yadda kike so dashi my Queen naki ne ai"
"Sarkin daɗin baki, da zakayi politics se an zaɓeka saboda wannan daɗin bakin naka"
A kunnenta yace "ko banyi politics ba, dama ban iyaba amma ina fatan ki zaɓeni a matsayin abokin rayuwarki Weeeedaat, ina sonki masoyiyya ta, na taɓa soyayya a baya amma yanzu nake gane a baya shirme nayi, yanzu ne nake Soyayya, saboda ban san takamaimai a ina nake jin sonki a cikin zuciya ta ba"
Shiru tayi ta ƙanƙame Yusuf tana saurare kalaman da yake gayamata, sedai tun ba'aje ko ina ba, al'amarin ya fara canza salo zuwa wani abu daban, da fari kamar Widad zata dake daga baya kuma tace bata san zance ba, ta tubure masa gaba ɗaya, but Yusuf he shows her the superiority of a Man.
Tashi tayi zaune, ta janyo bargo ta rufe jikinta, tana neman towel ɗinta, yana daga kwance ya kai hannu ze taɓa ta Amma ta bige hnnunsa, tana ta faman zumɓura baki, zaune ya tashi shima zeyi magana, amma ta fashe da kuka.
yace "Am sorry please, dan Allah kiyi haƙuri, is not intentionally kuskurene mun riga munyi shi sedai.. "
Katseshi tayi ta hanyar cewa "eh dama is not intentionally mana, tunda maye kake, kullum haka kake cemin is wasn't intentionally kuma bayan kana sane, kuma karka sake cewa munyi kuskure kayi dai"
Yusuf yace "jimin mara kunya, amma ina kwance kika zo inda nake ai"
"kazo inda nake dai, waye yace kazo ka kwantamin akan katifata?"
"Amma dana kwanta akan katifarki, shine akace ki zauna kina taɓani?"
Rasa me zata ce tayi, kawai ta fashe da kuka Yusuf ya lura kukan Shagwaɓa ne kawai takeji, amma yace "shikenan am sorry, ya isa haka kukan, ba zata sake faruwa ba, semu kiyaye gaba"
Ƙwacewa tayi daga jikinsa tace "ka kiyaye gaba dai, kawai nayi wanka na zan kwanta, kawai ka ɓatamin"
Ta cigaba da ƙunƙuninta, ta miƙe ta sake zura hijjabi tayi waje, yayin da Yusuf ya koma ya kwanta yana murmushi, dan shi wasu lokutan wannan rigimar tata birge shi take.
Taje bakin rumfar da ake girki ta tsaya daga baya, Hari tayi daren Abinci tana ta tankaɗe zata tuƙa tuwo, Widad tace "a zubamun ruwa zan wanka"
Ta ɗago ta kalli Widad tace "sannu Agwagwa, ko kuma ince tarwaɗa sarkin wanka, ba ɗazu Yaya ta zuba miki ruwan kikayi wanka ba?"
"Eh wani zan kumayi" Widad ta bata amsa
"waike sau nawa kike wanka a rana ne? Ke ko É—an tsallaken nan bakya yi, kullum se kinyi wanka, ni a rana ma bansan sau nawa kike wankan ba, kuma yanzu ko Awa biyu ba'ayi da wankan naki ba kin kuma É—akko bokiti kin dawo"
Widad tace "Allah ya kiyaye inyi fashin wanka, an gayamiki kowa irinki ne? Kawai mutum ya zauna be wanka ba har ya kwana ya tashi, ni ki zubamin dan Allah"
Hari tace "ko dame kike yawo bazan baki ruwan nan ba, wannan wane irin wanka ne sekace me iskokai?"
"Zaki zubamin ruwan ko sena gayamiki abunda yasa zan kuma wankan?"
"Ina ruwana da abunda yasa zaki sake wanka, keta shafa mace sekace wata kifi kullum cikin ta'annati da ruwa, ba dare ba rana, haba ni matsa ki bani guri"
"Hari za'aji kanmu dake a daren nan fa, kin fiye samun ido da shisshigi gaskiya, zuciya ta na gaya min in faÉ—i wani abu"
Hari tace "aike in mutum ya biye miki yana tsaye ze bar musulunci seya sake wankan shiga musulunci"
Widad ta nemi guri ta zauna a tsakar gidan, Hari ta tashi taje ɗaki ɗakko abu, dukda Widad bata san hayaƙi haka ta toshe hanci, taje gaban murhun ta ɗebi ruwanta ta ƙara gaba.
Hari na fitowa taga Widad ta kwashe ruwa fiye da rabi, nan ta tsaya ta dinga zazzaga masifa, Widad ta fito ko takanta bata bi ba tai wucewarta É—akinsu.
Gwaggo ce taita bawa Hari haƙuri, saboda yadda ta wage maƙogoro tana ta zazzaga bala'i a daren nan, kuma Widad ta shareta tana ta surutu.
Wani daddaÉ—an bacci ne yayi awon gaba da Yusuf, dan duk neman maganar data fita tayi be sani ba, kallonsa tayi taga baccinsa ma yake yi.
"Tasarmin daga kan katifa, zan saka kaya in kwanta" tai maganar tana dukan filon da yake kai, a hankali ya motsa, ba tare da yace komai ba ya miƙe ya bata guri, shima ya fita dan yin wankan, ba tare da yasan me Widad ɗin taje ta aikata ba.
Umman Yusuf tana zaune tana lazimi, ta kunna radio, dan gaba ɗaya ji take duniyar ta mata faɗi saboda rashin Yusuf a gidan, ba ta jin daɗin komai, ji take ta rasa wani sashi me girma, Tana ta laziminta hankalinta ya ɗauke, jin an ambaci cikakken Sunan Yusuf a radio yasa ta dawo daga tunanin da take yi, ta maida hankalinta kan radion ta ɗakkota ta ƙaro sautin.
Rahoton da aka faÉ—ane na bincike ya tabattar da Yusuf ne yai garkuwa da Widad dan ya karÉ“i kuÉ—in fansa yasa tayi jifa da radion a gigice, jikinta ya hau rawa, take ta fashe da kuka tana girgiza kai, cikin kuka taceÂ
"baze yuwu ba, Yusuf ɗina ba haka yake ba, ni ɗana baze taɓa aikata wannan mummunan aikin ba, innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wayyo Allah ɗana, wayyo Yusuf aikin ɗan sand be maka rana ba, wannan aiki da kayi yayi silar rushewar farincikinmh, yau nayi baƙinciki fiye da wanda muka rayu a ciki ni da kai, wayyo Allah ɗana, Allah ka kuɓutarmin da Yusuf "
Sosai take kuka, kamar zata shiɗe haka tayi zaman daɓaro tana ta rusa uban kuka babu me rarrashinta, gwanin ban tausayi.
Amal idanunta har sun kumbura saboda kukan da tayi, Hajiya Halima ta shigo É—akin ta tarar da ita tace " Haba Autan Mummy, kukan ne har yanzu baki dena ba, haba Amal É—ina"
Tai maganar tana rungume Amal a jikinta, ta cigaba da cewa "haba Amal, meye abun kuka, dan Allah ki cire yaron nan daga ranki, kinfi son Asirin Mummy ya tonu a idon duniya? Kin san bani kaÉ—ai ba har ku ta shafa, duk fafatukar nan da nake danku nake yi"
Amal tace "Mummy, nasani amma abun yayi yawane, haba Mummy ki duba lamarin nan fa ki gani, Abunda akayiwa Yusuf yayi yawa Mummy"
Hajiya Halima tace "ke bafa sharri akayi masa ba, tunda akace ya gudu daga hannun wancan mutanen meyasa basu dawo ba? Kina ta kuka akansa, shi kuma ba kya gabansa sam, kina kallon yadda ya dinga yanƙwanaki, yana wulaƙantaki shida waccan fitsararriyar mara mutuncin, suka dinga wulaƙantaki bama ke kaɗaiba harni ba kunya ba tsoron Allah suka dinga cin mutuncinmu, dan haka meye a ciki dan suma an musu? Ki dena kukan nan kinji, ki share hawayenki, danku nake wannan faɗi tashin, ki dena kuka kina ɗagamin hankali kinji"
Amal ta jinjina kai, tana share hawayen Fuskarta.
Haka nan Yusuf yaji jikinsa yayi sanyi, kamar wani abu yana faruwa, jiki a sanyaye yaje yayi wanka ya dawo É—aki, Hari tana ganin ya shiga banÉ—aki da bokiti tace
"la'ilahaillalah, ta tabatta Wudas bata da kunya yarinyar nan, innalillahi kai Allah yayi mana maganin wannan zamani, Taɓɗijan ashe abunda yasa ba yau gobe cikin sintirin banɗaki take yin wanka, to Allah ya maganta"
Babban abun takaicin, Hari ba a hankali take magana ba, Yusuf ji yayi kamar karya fito daga banɗakin nan saboda nauyin maganganun Hari, a matuƙar kunyace ya fito ya wuce ɗakinsu, Widad ta lura kamar jikin Yusuf a sanyaye yake, kamar wani abu yana damunsa.