Sashe 115
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta jinjina masa kai, Yusuf yai murmushi yace "'yar baiwa, ashe Allah ya amsa Addu'ar ki, ya baki abunda kike nema, hankalinki ya kwanta" yai maganar cikin farin ciki fuskarsa ɗauke da murmushi.
Ya rungumeta a jikinsa hawaye na zuba daga idonsa, Widad ta rirriƙeshi itama tana kukan tana faɗin "We miss you Daddy me and your unborn, munyi missing ɗinka sosai, we really suffered, banyi zaton zan sake ganinka ba, bam zaci zanyi rai zuwa wannan lokacin ba"
Ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka, Yusuf ya sake manneta a jikinsa shima yana zubar da hawaye yace "i miss you too Babyna, i miss you my Queen, I love you"
"I love you too my Husband"
Sosai suke kuka daga shi har ita kamsr ƙananan yara, ya sake ɗagota ya kalli cikin nata, ya rungumota jikinsa ya haɗe bakinsu yana kissing ɗinta, hawayen tausayawa kansu na zuba a idonsa, yayin da itama kukan take.
Ya cire bakinsa daga nata, yana share mata hawaye ya kalleta yace "ɗan sake maimaita min abunda kikace yanzu mana"
Murmushi tai ta miƙa hannunta itama fuskarsa, tana share masa hawaye "tace me kake so in sake faɗa?"
"kin san koda ina prison, kalmomin nan da kika dinga faÉ—amin ranar da aka kamani sun tsaya a zuciyata sosai my wife"
Fashewa ta sake yi da kuka tace "dan Allah Yoseef ka dena tunamin kayi zaman prison please, zuciyata zata tarwatse, am sorry Yoseef duk sanadina ne ka shiga mummunan yanayi"
Yusuf yace "ni dai a sake cewa ana sona please" yai maganar a Shagwaɓe.
Ta noƙe kafaɗa tace "Anƙi ɗin"
"Ya akayi kika fara so nane?"
"Nima ban sani ba ai, Yoseef dan Allah ka dawo gareni, akwai maganganu dayawa da nakeso muyi, kuma kaga nikaÉ—ai nake rayuwa ina farmhouse, kalli jikina duk ya kumbura, Yoseef zuciyata ciwo take, likitoci sunce idan nazo haihuwa ko dai muyi surviving, ko mu mutu gaba É—aya ko É—aya ya mutu ya bar É—aya"
"Shhhhh hakan baze faru ba insha Allah, zaki haihu lafiya, kinga a yanzu haka ina ta fama da Umma saboda ke, kin san a rayuwa Umma bata son abunda ze taɓani, dan haka abune mawuyaci ta fuskanceni, saboda tana cikin kotu kika bada sheda a kaina, dan haka sena fara shawo kanta tukuna"
"Yoseef, umma bata sona kenan?"
"A'a ba haka nake nufi ba, taji ba daÉ—ine abunda kikayi"
"Dan Allah kayi mata bayani Yoseef, nasan kaika fahimceni kasan komai fa"
"Na sani my wife, kiyi haƙuri, zanyi ƙoƙari inzo har farmhouse ɗin in ganki, yanzu maida rigarki in rakaki mota, nasan Umma na daf da shigowa"
Ai gaba É—aya sun manga da batun Nurat, dan Widad ta manta ma da taga Nurat tare da Yusuf.
Ta tura baki tace "Nika ɗakko ka samin"
Ya harareta yace "zaki fara sani aiki ko?"
"Eh mana, tunda ka haÉ—ani da aiki ai dole Kayi aiki"
Yusuf yai dariya yace "lallai kinyi baki, mara kunya kawai"
"Ai kaika koyamin rashin kunyar"
"Allah yasa Hari ta jiki, Kisha baƙar magana"
Widad tace "Allah sarki Hari mutuniyata, ina jin bayin Allah nan sosai a raina, ina kewarsu mussman Hinduna da Gwaggo, in komai ya daidaita zamuje insha Allah"
Yusuf yace "kin san kuwa wannan Sunusin, mijin Jamila yaje ya bada sheda a kotu?"
Widad tace "Nasani"
"Ya akayi kika sani?"
Widad tai ajiyar zuciya tace "shiyasa nace maka ina son mu haÉ—u, ina da magana da kai sosai"
Tai maganar cikin Shagwaɓa tana tura baki.
Yusuf yace "Malama karki sa mu saki layi, matso in saka miki rigarki"
Murmushi tai masa ta ƙara matsowa daf dashi, sedai yaga abu kamar kwanciyar bulala yai duhu akan fatarta, wajen damtsenta.
"Baby meye wannan?"
Yai maganar yana kallon hannun nata.
"Bakomai, samin rigata in tafi"
Shiru yai yana nazarinta, idonsa ya kuma sauka akan gefen fuskarta, nan ma wani tabon ne a gurin, ya sake kallonta zeyi magana tace "waiya kake ƙaremin kallo hakane kamar yauka fara ganina? Bani rigata in saka tunda kallona zakai ba samin ba"
Yusuf ya riƙe rigar yace "bazan taɓa gajiya da kallonki ba" yai maganar yana sake janyota jikinsa, yana sa fuskarsa a wuyanta.
"Naji, amma ka ƙyaleni in tafi, hankalina ya kwanta tunda na ganka"
Haka ya saka mata rigar, ta ɗau hijjabin zata saka, ya dakatar da ita ya ɗaga rigar jikinta, ya sake kallon cikim nata, ya sumbaci cikin ta yace "I love you my unborn, karka waharmin da Mum ɗinka kaji Babyna, i love both of you"
Widad ta dinga masa dariya, wai yana surutu shi kaÉ—ai, kamar zasu cinye juna, ko sababbin masoya.
Nurat kam tana fita daga É—akin, waje tayi amma bata ga Khalila ba, se motocin 'yan sanda dake gurin, dan haka ta koma tsakar gidan, can nesa da É—akin da su Yusuf suke, ta zauna akan kujerar tsakar gida.
Sedai tana jiyo dariyar su, ta sunkuyar da kanta a tsakanin cinyoyinta, tai shiru tana tunani, tana son Yusuf so na haƙiƙa, tana sonshi saboda Allah, amma tasan tunda ya auri Widad abune me wahala ya saurareta, kuma ga dukkan Alamu Widad ma tana matuƙar sonshi itama, dan haka Yusuf babu lallai ya saurare ta.
A hankali ta fara hawaye, tana gogewa a hankali, tana addu'a a zuciyarta "Allah ka yaye min son Yusuf, Allah ka zaɓamin abunda yafi Alkhairi a rayuwa ta"
Jin abun nasu bana ƙare bane, yasa ta sake miƙewa ta fita waje, tana fitavtarar da Khalil ya dawo, ya kalleta yace "Ta Yusuf harkin fito ne? Ai bamu gaisa da Umman ba"
Nurat tace "Brother mutafi gida"
Yace "meyasa? Kefa kika damu in kawoki"
Nurat tace "ni dai mutafi gida kawai"
Tai maganar hawaye na ƙoƙarin tona asirin dake zuciyarta, a ɗan dirirce yace "ko wani abun Yusuf ɗin yayi mkki?"
Ta girgiza masa kai ta buÉ—e mota ta shige, cike da mamaki Khalil ya bita da kallo.
Umma ceta shigo layin hannunta ɗauke da ledoji, sedai ganin motar 'yan sanda a ƙofar gidan yasa gabanta ya faɗi, ta dinga nanata innalillahi wa inna ialaihi raji'un, hankalinta ya ɗan kwanta data hangi Khalil.
Ta ƙaraso inda Khalil ke tsaye, tace "Khalil lafiya kuwa? Naga motar' yan Sanda?"
Khalil yace "lafiya ƙalau Umma, sunce min wani aiki sukeyi, Nurat na kawo ku gaisa kuma bakya nanma ashe"
Umma tace "Ai da kun shiga Yusuf yana nan ai"
Yace "Ai ita ta shiga É—inma, amma ta fito"
Umma tace "A'a ban yadda ba, Nuratu fitowa zaki mu shiga mu gaisa"
Nurat tace "Umma yamma tayi ai"
Umma tace "a'a, ai ga Khalil nan Tare kuke kuma ga mota fito maza"
Nurat bata son tayi sanadin da zata gusar da farincikin dake zuciyar masoyinta, amma babu yadda ta iya, Umma ta haifeta bekamata ta bijirewa umarninta ba.
Nurat ta fito daga motar, tabi bayan Umma suka shiga gidan, sedai suna shiga suka tarar Yusuf da Widad sun fito, yana riƙe da ƙugun Widad suna murmushi cike da kulawa da juna.
Suna yin tozali da Umma, Yusuf ya saki Widad da sauri, ita kanta seda Widad ta tsorata ganin kallon da Umman take musu.
Umma ta kalli Widad tace "kinzo ki sake kulle shin ne kokuwa? Ko prison ɗin kike son ya koma?"
Widad ta kalli Yusuf, ta sunkuyar da kai.
Umma tace "ya kikayi shiru baki bani amsa ba? Kinzo ki sake maida shi prison ne, bayan duk wahalar da ya sha saboda ke, ki kaje kotu kika bada sheda akansa, banda Allah yasa wannan yarinyar Nurat da ɗan uwanta sunyi masa ƙoƙari suma da yanzu shekaru talatin zeyi a kurkuku "
Widad ta É—aga ido ta jefi Nurat dake bayan Umma da wani matsiyacin kallo, wanda yasa Nurat jin kayan cikinta kamar sun koma bayan ta, a hankali ta silale ta fice ba tare da Umma ta lura ba.
Umma ta kalli Yusuf tace " kai kuma na dawo kanka, mara zuciya kai har abunda yai saura tsakaninka da wannan yarinyar, saboda rashin zuciya tana mace amma ta biyoka har gida? Idan na ƙara ganinta a gidan nan duk abunda nayi mata ita siya, yakamata ma hukuma tai mana tsakani da ita, tunda Allah yasa dai an gane baka da laifi meye kuma na cigaba da bibiyarka, kowa se yayi hanyarsa Allah ya bada lada "
Yusuf yace 'Umma dan Allah kiyi haƙuri, Widad aurenta nayi mata tace, amma..
Umma ta katse shi tace " kai kasan wannan, ni ban san da haka ba, iya sanin da nayi baka da wata mata, Ni Nuratu nake fatan ka Aura, dan se tafi wannan yarinyar sauƙin kai "
Widad ji tayi zuciyarta ta buga da ƙargi, tankar Umma ta soka mata mashi, take taji ta tsani Nurat, dama ga abunda mahaifinta yai mata, gashi kuma yanzu tana bibiyar mijinta, hawaye ya fara zarya a fuskar Widad, a hankali ta sanya takalmanta tai waje.
Yusuf kamar ya ɗora hannu a ka ya kurma ihu haka yake ji, baya son kukan Widad yana matuƙar ƙaunarta, amma Umma na son datse igiyar farincikin dake tsakanin su.
Umma ta kalle shi tace "wato da Nuratun tazo gidan nan wulaƙanci kai mata saboda wannan yarinyar ko? Farar fatarta na ɗaukar maka ido kana nema ka gayamin magana saboda ita ko Yusuf?"
Yusuf ya girgiza kai, Umma tace "duk abun kaga nayi bazanyi dan in citar da kai ba, wannan yarinyar idan ta ƙara raɓarka za'a iya samun matsala, ka manta da ita kawai ka nemi wannan yarinyar Nurat, dan se tafi waccan tausayi, kuma dama kaga Auren naku mutane na shakku a kai, tunda ba kowane yasan da wani kunyi Aure ba, kayi haƙuri ka rabu da yarinyar nan, Allah ya zaɓa maka mafi Alkhairi kaji yaron kirki, bana son abunda ze sake ɗaga mana hankali tashin hankalin da muka shiga ma ubangiji Allah ya yaye mana ya kiyaye gaba, Allah yabaka mace tagari mafi Alkhairi a rayuwar ka "
Ta miƙa masa wata ƙatuwar leda tace " yawwa ga wannan, yadine guda uku masu kyau da shadda biyu, idan anyi sallar magariba dare yayi ka kaiwa magaji ya ɗinka maka, ga takalma nan ma, hadda sabon agogo na siyo maka, ka ƙara akan kayanka, sonake nan kusa ka koma gurin aikinka"
Jiki a sanyaye yasa hannu ya karɓa yace "Nagode Umma"