Sashe 34
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gwaggo tace "Amarya ba kyau maida hannun kyauta, ai basu isa sun biyaki abunda kike koyar dasu ba, jin daɗin abunda kike musu ne yasa suka baki, ki karɓa kawai"
Habi tace "yawwa Gwaggo, wallahi ba zamu biyata ba kam, amma dan Allah malama ki karɓa"
Da ƙyar dan Gwaggo tasa baki sannan ta karɓa, bayan tafiyar su Gwaggo ta cigaba dayi mata nasiha, na cewar zasu ga kamar wulaƙanci ne yasa bata karɓar abu idan sun bata.
Tafiyarsu keda Wuya kuma, megari ya shigo, yanzu Widad tana sakin jiki ta gaisheshi, harma wasu lokutan ya dinga tsokanar ta, ya shigo yara suka biyoshi da manyan ƙwarya, ɗaya an shaƙeta da ƙwan zabo, ɗaya kuma Nono ne a ciki, megari yasa Hindu ta kira Widad, ta fito suka gaisa yace "Nasan Malam Yusuf be dawo ba, ga wannan inji ɗalibansa suka ce a bashi"
Abun ya bawa Widad mamaki, mutanen ƙauyen nan sudai suna girmama malamai, kuma suna da rige rigen son suga sun kyautatawa mutane, saɓanin irin rayuwar da ake a birni, mutum yana ganin ɗanuwansa a matsala amma ya share, koma a haɗa kai dashi a cutar da mutum.
Widad ta karɓi kayan tace "to Baba, Yoseef ya gode sosai zan gaya masa idan ya dawo"
Megari yayi murmushi yace "bagwariyar 'yata, Yusuf ake cewa ba Yoseefa ba"
Widad tayi murmushi tace "na kasa gyarawa, kuma shima ai yafison in ce masa Yoseef ɗin, kona fara cewa Yusuf se in manta"
Megari yace "Ahh masha Allah, tunda me gidan da kansa haka yakeso gara a kira shi da hakan"
Widad ta ɗau kayan zuwa ɗakinsu, Hari tace "wai me gida duk kayan nasu ne gaba ɗaya mu kuma fa?"
Yace "ke dai Allah ya shiryeki, nan har siyar da ƙwan zabo kike a gidan nan dana kaji, baki taɓa dafawa kin bawa kowa ɗaya a gidan nan ba, a gabanki dai na faɗa nace ɗalibai da yake koyar damu a masallaci sune sukace a bashi, zalamammiya kawai"
Ya wuce É—akinsa yana cigaba da mita, Widad taje ta samu guri a É—akinta ta É—auki gyaÉ—ar da aka bata tana ci, Yusuf ya dawo ya tarar da ita.
"Gimbiya yau kuma me aka samu haka?"
"GyaÉ—a aka bani"
"kuma haka ake cin gyaÉ—ar?"
Raba gyaɗar take biyu da bakinta, idan ta fito shikenan, idan bata fito ba ta haɗa da ɓawaonta ta cinye kayarta.
Seda Yusuf yaci dariya sannan ya nuna mata yadda ake ci, tace "ga wannan kayan, Megari ya bani yace a baka inji ɗaliban ka"
Yusuf ya kalli yawan Nonon nan da ƙwan zabi aƙall zeyi guda hamsin, yanzu ma a hanya wani ya tareshi ya bashi Albasa.
Yusuf ya jinjina kai yace "Ni wallahi kunyar karɓar kayan nan nakeji Widad, nifa saboda Allah nake koyar dasu"
Widad tace "nima kaga duk yawan gyaɗar nan haka suka bani, nace bazan karɓa ba Mama taitamin faɗa"
Yusuf yace "gaskiya zan mayar, abun yayi yawa ai"
Widad ta Harare shi tace "ai sedai ka maida wannan albasar, amma baza'a maida wannan ƙwan da madarar nan ba"
Yusuf yace "kaga kwaÉ—ayayyiya"
"Eh naji, kawai kaje kace mungode"
Yusuf yayi murmushi yace "wai yau uwa ɗakina aka bawa kyauta ta karɓa, har take baza'a mayar ba, saɓanin da kana bata abu zata ce ka rainata, ko zaka cutar da ita"
Widad ta É—an ja ajiyar zuciya tace "baka manta faÉ—anmu akan kayan daka bani ba ko?"
Yusuf yace "ya za'ayi in manta? Sedai ya wuce a ai"
"daka san faɗan da Daddy yayi min akan abun da nayi seka yi mamaki, kamar ze dakeni, shi dai Daddy a rayuwar sa kar a wulaƙanta Yusuf, kar a ɓatawa me suna Yusuf rai, ya ƙwace kayan yace shi yana so, bayan ya fita naje na ɗauke abuna, na saka rigar saboda hankalinsa ya kwanta ya dena fushi dani, sedai daya ganni a cikin kayan seda yayi kuka, kasancewar Ammi na matuƙar son irin wannan shigar tasu ta dogayen riguna"
Yusuf yace "Allah sarki, ubangiji Allah yayi mata rahama"
Widad tace "Ameen"
"Amma yaushe zaki ƙarasamin labarin ne?"
"ba rana ba wata" tai maganar tana miƙewa.
Yusuf yaje yayi musu godiya da karamcin nan da suka yi masa, suka ce yafi ƙarfin haka a gurinsu, tunda yake koya musu karatu ai ya gama musu komai.
Yusuf haka ya karkasa kayan nan, yayi rabonsu a cikin gidan nan, Widad kam taji daɗin ƙwan nan da Nono, dan Abinci ma seta ga dama take ci.
A hankali ɗaliban Widad suka ƙara yawa, harda ƙana nan yara, ta koya musu na boko ta koya musu na Addini.
Yauma wajen ƙarfe biyar na Yamma, tana ƙoƙarin sallamar ɗalibanta ƙananan yara, sega Saleh yazo, Kallo ɗaya Widad tayi masa ta ɗauke kanta, jin Sallamar wasu ne yasa ta sake ɗaga kai ta kalle su, Saleh ne shida wani mutum, da wata mace da manyan Akwatunan su.
Mutan gidan ne suka ruÉ—e da shewa ganin mutanen da suka shigo tare da Saleh, da alama dai sun san mutanen, Maida kai Widad tayi ta cigaba da abunda take.
Matar ba zata wuce shekaru Ashirin ba, ta kalli Widad tace "Gwaggo ina muka samu balarabiya ne?"
Gwaggo tace "'yata ce itama, Allah ya bani"
Wadda suka kira da Jamila tun shigowarta, yara suka karɓi jaririyar bayan ta, ta kalli Widad tace "Sannunki" kallonta kawai Widad tayi tai shiru.
Jamila tace "ko bata jin Hausa ne?"
Hari tace "iya shege ne, tana ji sarai kulaki ne da ba zata yi ba, haka take wannan wulaƙancin"
Saleh ya kalli Widad yace "Barka da yammaci ranki ya daɗe"
Yanzu ma kallon Saleh tayi ta ɗauke kai, yai murmushi yace "Ina Yusuf ɗin yake ne?"
Ai kamar da yana magana da dutse, wanda suka shigo tare da Saleh yace "to wannan da alama 'yar Mulki ce dai"
Ƙarshe da Widad taga zasu takura mata gaba ɗaya seta bar musu tsakargidan ma, ta koma ɗaki.
Baƙin nan suka shiga ɗakin Gwaggo, suka ajijiye kayansu, mutan gidan sunata farincikin ganin Jamila, da mijinta da kuma jaririyarsu.
Saleh da mijin Jamila wato Sunusi, suka shiga turakar megari, bayan ya sallami baƙinsa ya shigo ya tarar dasu, megari yayi murmushi yace "Soja marmari daga nesa, ya akayi kuka haɗu?"
Saleh yace "A tasha na gano su sunzo hutu, muka hawo akorikurar shu'aibu tare ya kawomu gida"
Megari yace "Madalla, ya Jamilar ya meÉ—akin nawa?"
Sunusi yace "duk muna lafiya, gamu munzo muyi muku hutu"
"eh babu laifi, amma Nasan kun kwasarwa yarinyar nan iskar hanya, dan ko Arba'in basu rufa ba"
Sunusi yace "Baffa ya za'ayi, ta matsa ita dai tazo gida, kasan can inda muke babu hausawa sosai, zaman se a hankali gaba É—aya"
Megari yace "hakane, Allah yayi mana jagora gaba É—aya, Saleh ya ka baro binni, da mutan kanon Dabo?"
"kowa lafiya ƙalau, na shigo ma ban tarar da Yusuf ba, se ita matar tasa, nayi magana kuma ta shareni"
Megari yace "Malam Yusufa be dawo ba ai, aini tunda nake ban taɓa ganin Yarinya meji da isa kamarta ba, akwai mulki kam, ni kaina na daɗe bata saba dani ba, ko gaisheni ba tayi, ba ruwanta da kowa daga mijinta se Hassana (Gwaggo), se a hankali kuma ta fara sabawa dasu Hindu, se daga baya kuma na gane ɗabi'arta ce rashin yadda da saurin sabo, amma tana da kirki sosai "
Saleh yace " Ai Baffa baka ga komai ba, in dai mulki da ji da kaine, ba abunda ka gani, yanzu ai ta sakko ta saki jiki daku sosai, Amma ai bata da yadda sam"
Sunusi yace "to meyasa, nima daga zuwana na gani, Jamila na mata magana tayi banza da ita, kaima kayi mata ta share"
Saleh yace "idan na gaya maka wacece ita, seka riƙe baki abar maganar kawai"
Megari yace "waini yaushe zasu tafi ne?"
"Ka gaji da zama da sune?"
"Haba wane mutum, aini zuwansu garina Alkhairi ne wallahi, basu takurani ba sam, sedai ina tunanin kana ganin babu wata matsala zamansu anan É—in, nifa matsala ce bana so"
Saleh ya nisa yace "babu wata matsala Insha Allah Baffa, amma zamansu anan shine tsira da rayuwarsu, zuwa wani ɗan lokaci insha Allah zasu bar nan, ni dai fatana a cigaba da haƙuri dasu"
"Saleh aini zuwansu nan alkhairi ne, baka tarar da yara gidan nan ba? Da Asuba ko magariba shi Yusuf ya koyar da karatun Addini, gashi da ladabi, ba hantara ba cin mutunci yake gyaramana kwaɓar da mukeyi, da Yamma kuma ita ke koyar da yaranmu darussan boko, da Addini, kasan mu babu makarantu haka na muke zaune da jahilci se ɗan abunda ba'a rasa ba"
Saleh ya jinjina kai yace "Yanzu, ita ke koyar da yara karatun?"
"daka shigo ba kaga yara da 'yan mata a gidan nan ba, dukda gidan nan na mutane ne amma karatu take koya musu"
Saleh yace "Allah sarki rayuwa"
Se daf da magariba sannan Yusuf ya dawo, Yusuf be tarar da Saleh ba dan haka ya gaisa da su Hari ya wuce ɗaki, yana zuwa ya tarar da gimbiyar ta cika tayi fam, kallo ɗaya yayi mata yace "Subhanallah, me kuma ya faru? Ko nine na miki wani abu?"
Girgiza masa kai tayi tace "A'a, Saleh ne yazo na ganshi shi da wasu, na kasa yadda hankalina yaƙi kwanciya, ban san suwaye ba"
"To shine zaki É—aga hankalin ki haka? Ki bari muji ta bakinsa mana"
"A'a, nifa bana son irin wannan abun, ko dai musan suwaye, ko kuma wallahi bazan kuma kwana a garin nan ba, komai dare sena bar garin nan"
Yusuf yace "yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, zan masa magana idan mun haɗu a gurin salla"
Bata son tayarwa da Yusuf hankali, shiyasa ta ƙyaleshi, kamar yadda ya zata sun haɗu da Saleh a masallaci, bayan sun idar da salla, suka gaisa Yusuf yace "kwana biyu, yau kusan watanka guda rabonka damu"
Saleh yace "wallahi kuwa, abubuwa ne sun ɗanmin yawa, ai ɗazu naga gimbiyar taka, na mata magana juyin duniya taƙi kulani, a gaban mutane"
Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "kasan dama kuna takun saƙa da ita, kuma ta ganka da baƙi bata san kosu waye ba, dole ba zata kulaka ba"