← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 127

Sashe 120

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Isa yace  "ga Amal, ka lallaɓa da ita mana"
  Nura ya haɗe rai yace  "Agolar? Uwar me taci balle ta bani, suma yanzu suna fama da kansu, sun saida koma, komai ya ƙare musu, an kashe babban ɗa, uwa ta tafi hannun hukuma, ita wannan ga rashin lafiya, waccan ga shaye2, komai ya ƙare, ni nayi mamaki ma da Gimbiya ta ƙyalesu har yanzu zaune a cikin gidan nan, ai dama shi ramin mugunta idan zaka ginashi, seka gina shi gajere, dan wataƙila kai zaka faɗa "

Isa yace " babu wanda yafi bani mamaki, se Alhaji Bulama ubangiji Allah yayi mana tsari da azzalumai kamarsa, yanzu duk yada yake da Daula, da soyayyar da yake nunawa Daula, ashe azzalumi ne mufuki, na ƙaryane zagon ƙasa yake masa, gaskiya mun shiga haƙƙin Widad na ganin aibunta, ashe tana da dalili akan ƙin mutane, ji wannan asara fisabilillahi "

Nura yace " bari kawai Isa, duniya babu gaskiya, mutane mun lalace se fatan shiriya, amma tabbas gaba ɗaya mutanen nan sunyi tarayya a cikin ƙaddarorinsu, Alhaji Daula, 'yarsa da kuma Yusuf daya shiga rayuwarsu daga baya, sedai fatan Allah yasa bakin wahalrsu kenan, kuma Allah ya bayyana Alhaji Daula "

Isa yace " Ameen ya Allah "

Yusuf da Widad kuwa, seda suka sha yawonsu a gari, sannan ya kaita suka É—akko kayanta suka dawo gida.

ÆŠakin Umma ya kai akwatin kayan nata ya ajiye, ita dai UMMA bata tanka musu ba, tana ganin Yadda suke rawar kai akan junansu, da nan nan da juna cike da tsantsar kulawa da soyayya.

Yusuf yace  "Umma kinci Abincin dare ne?"

Umma tace  "eh naci, ga naku can a flask"

Yusuf ya ɗakko flask ɗinAbinci ya kawo, tuwon Alkama ne miyar kuɓewa Umma dafa, Yusuf yana zubawa Widad kamar zata shiga cikin kwanon, saboda yadda yawunta ya tsinke.

"Yoseef dan Allah ka zuba da sauri mana, kana yi a hankali fa, kuma ni sonake inci"

Tai maganar a ɗan Shagwaɓe, Yusuf ya kalli Umma, amma yaga hankalinta baya kansu, kuma tana jin taɓarar da Widad ɗin keyi.

Yusuf a hankali yace  "bazanyi saurin ba"

Ta harari Yusuf tana tura baki, ya zuba mata tuwon nan, miyar ta sha kifi, ya samat man shanu, yadda Widad ta duƙa tana zuba tuwon nan yafi komai bawa Yusuf mamaki, ci take kawai ko magana ba tayi.

Yusuf yace  "wai baki ƙoshi bane har yanzu?"

Widad tace  "wallahi ban ƙoshi ba, rabona da Abinci inci cikakken Abinci cikin kwanciyar hankali, tun ranar da muka baro ƙauyen nan, bana samun Abinci inci, ga Abincin yayi daɗi Sosai"

Yusuf yace "ikon Allah, yanzu ke tunda kike gurin Bulaman bakya cin Abinci?"

Widad tai murmushi me ciwo tace "Yoseef, bana son tuna abunda ya riga ya wuce, ban zaci zan kuɓuta ba, na sha wahala fiye da tunaninka, banda duka da baƙar azabtarwa ba abunda nake sha a hannunsa, ga ɗansa kuma Fahad, daya dinga nema yaci zarafina, bana samun abunda nake so inci, komai bayamin daɗi, shiyasa na masa wannan tabon da wuƙa a fuskarsa, ko zan rage raɗaɗin abunda yayi min"
Gaba ɗaya jikin Widad yai sanyi tace "ƙaramin tuwon nan, yunwa nakeji ban ƙoshi ba"
Ya sake zuba mata, ta dinga cin abunta, ba wata kunya ko kara seda taji tayi ƙyat babu sauran gurin zubawa sannan ta haƙura, ta tashi taje fridge ta samo ruwa me sanyin gaske, ta zauna ta sha abunta ta wanko hannunta tazo ta zauna tana hutawa.

Yusuf yace "Sannu da aiki"

Widad tai murmushi ba tace komai ba.

Abincin data cine ya fara taso mata, tai shiru ta kasa magana, Yusuf ya zuba abunda ta rage yana ci.

Cikin hanzari Widad ta tashi ta fita, ta dinga amai, seda ta amayar da duk abunda taci, Yusuf yabi bayan ta da sauri.

Tayi amai sosai, Yusuf ya temaka mata, ta gyara jikinta ta kuskure bakinta.

Umma ta fito daga É—aki tace "garin yaya take amai haka? Ko bata da lafiya ne?"

Widad tace "A'a Umma, lafiyata ƙalau"

Yusuf yace "inaga ko over feeding ne da tayi"

Umma tace "in ba hali, ko Asibiti zaka kaita saboda dare"

Widad tace "A'a, base munje Asibiti ba, ya lafamin ma"

Umma tace "shikenan, kije kwanta ki huta"

Widad taje ta canza kayanta, zuwa na bacci ta sake burma ƙaton hijjabinta, ta nemi guri ta kwanta a ƙasan carfet.

Umma ta shigo ɗakin ta ga Widad a kwance a ƙasa tace "tashi ki hau kan gadon mana"

Widad tace "A'a Umma, bana jin daɗin kwanciyar kan katifa, bayana ciwo yake nafison kwanan ƙasa"

Umma tace "shikenan"

Widad dukda basar da ita da Umma take, amma taji daÉ—in ganin yadda Umman, ta nuna mata kulawa.

Umma taje É—akin Yusuf tace "bani bargonka guda É—aya, a shimfiÉ—a nata tace bata son kwanciyar kan gado"

Yusuf yace "yawwa Umma, naji ana cewa za" ayi tafiya da weekend, amma ina za'aje ne? "

" ban sani ba, meya hana ka tambayi matarka? Bani bargo ni"

Yusuf ya miƙa mata bargon, ya ja bakinsa ya tsuke.

Umma ta gyarwa Widad gurin kwanciya, ta kwanta.

Nurat kam gaba ɗaya damuwa ta addabeta sosai da sosai, bata jin daɗin zaman gidan gaba ɗaya, gashi ta saka duk mutan gidan a damuwa, ganin yadda taƙi sakin jikinta, Nurat tai tunani taga damuwa bazata maganta mata abunda ke damunta ba, ta tashi ta fito falon gidan.
Ba kowa a gidan, duk ma'aikata ne sun tafi gurin aiki, ƙannen Khalil kuma duk suna kudancin Nigeria suna karatu.

Nurat ta gyara ko'ina na gidan, tayi girki yaje tai wanka ta dawo falo tana kallo, duk a ƙoƙarin ta na kauda damuwar dake ranta.

Wajen ƙarfe biyu Khalil ya dawo gida, ganin Nurat a falo tana kallo yasa yaji daɗi, ba kamar da ba da kullum tana ɗaki, ya ƙaraso yana mata murmushi yace "Sisyna, masha Allah, wannan kyau haka"

Tai murmushi taje ta karɓo kayan hannunsa, tana masa sannu da zuwa tana masa murmushin nan nata me ɗaukar hankali.
Yaji inama ace matarsa ce.

Nurat tace "Sannu da zuwa, kaje kai wanka kazo yau nina yi girki kaci Abinci"

Khalil yace "ashe yau da shagali, zanci Abincin 'yar auta"

Nurat tai murmushi, taje ta kai masa kayan É—akinsa, dake kusa da falon.

Bayan yayi wanka yai salla, ya fito ya zauna a falo yana jiranta, ta shigo da sallama hannunta É—auke da kulolin Abinci, ta tarar da Khalil ya zubawa wayarsa ido.

Nurat tace "inyee, da alama wannan matashin barrister ya shiga soyayya, hoton wa ake kallo haka?"

Ya É—ago ya kalleta yace "kalleki, wai hoton wa nake kallo, niwa zan kalla"

"Nifa dama baka taɓa nunamin budurwarka ba, gaskiya yakamata kayi aure haka, haba seka zama tuzuru tukuna, dan kaga Mama ta shagwaɓaka ne, da Abincin ta, ta koraka bakin gate a maka ɗaki, sannan a dena baka abinci zakayi aure"

Khalil yace "kice azabtar dani za'ayi kenan? Hmm ni tsoron matan yanzu nake Nurat, soyayyar gaskiya tana wahala, shiyasa ni ban taɓa budurwa ba"

Nurat tace "No akwai soyayyar gaskiya mana, kai dai kawai kace tsoron 'yan mata kake yi, you can't toast a lady"

Tai maganar tana dariya, Khalil ya girgiza kai yace "Eh naji É—in, yanzu dai in kin matsu inyi Aure ki samo min budurwa, sannan ki dinga rakani zance"

Nurat tai murmushi, seda fararen haƙoranta suka bayyana tace "ba budurwar da zata aureka kuwa a haka, in dai sena raka ka zance"

Ta zuba masa Abinci, yanaci yana kallonta, yana jin kamar ya gayamata yana Sonta, sedai yasan zuciyarta tana tare da Yusuf.

Da Safe Widad ta tashi, Umma tana bacci ta tafi É—akin Yusuf, yana kwance yayi É—ai É—ai akan gado, yana baccinsa.
Ta kalli É—akinsa, É—akin tsaf dashi, kamar É—akin wata matar ga Mirror, da gado wardrobe komai tsaf dashi.

Ta ƙarasa kan gadon nasa, ta zauna ta ƙura masa ido, Wani murmushi take ganin yadda yake baccinsa hankali kwance, kamar wani jariri ya ɗan ciko daga ramar da yayi, sedai shima jikinsa duk tabon duka daya sha a prison.

Hannu ta kai tana shafa gefen fuskarsa, tai ƙasa sa muryarta tace "Hubbyna ka tashi muna jin yunwa fa"

A hankali ya buɗe ido ya kalleta yace "ke kin fiye takura, haba Babyna wace irin yunwa ƙarfe shida na safe?"

Cikin shagwaɓa tace "ni dagaske yunwa nakeji, ka tashi yunwa nakeji"

Yusuf ya noƙe kafaɗa, yana ɗora kansa akan cinyarta yana lumshe ido.

"Wallahi idan baka tashi ba, zan zauna se Umma tazo ta gamu a nan tare"

Ba shiri Yusuf ya miƙe zaune, yace "rufamin Asiri, tashi muje"

Widad ta dinga dariya, har sunje bakin ƙofa, ya juyo ya kalleta ya rungumota jikinsa yai kissing ɗinta yace "good morning"

"Morning, ka tashi lafiya?"

"Alhamdilillah, ya babyna?"

Tace "yana nan yana jinka"

Yai murmushi, suka fito tare suka shiga kitchen.

Suka feraye dankalin hausa tare, suka dafa tea, suka shiga suya Tare, hirarsu kawai suke kamar suka É—aine a gidan.

Yusuf so yake ya saki layi, amma Widad na kakkarewa tana hanashi.

Umma kuwa tuni motsinsu ya tashe ta, amma bata fito ba karta takurasu, suka gama sukayi wanke wanke suka gyara komai tsaf.

Widad na shiga É—akin ta tarar Umma ta tashi, Widad tace "Umma ina kwana"

Umma tace "lafiya ƙalau, ya jikin naki?"

Widad tace "naji sauƙi"

Umma tace "Allah ya ƙara sauƙi"

Duk yadda Umma take basar da Widad, Widad bata nuna mata taji haushi ba sam, tana girmamata sosai, sedai bata iya kara ta ɓoye soyayyarta ga Yusuf ko a gaban Umma ne

Wajen ƙarfe goma na safe, ciwon ciki ya kama Widad, tun tana mazewa seds Umma ta gane.

Lokacin Umma ta aiki Yusuf, baya gidan amma ganin Yadda Widad ke murƙusus yasa Umma ta kira shi a waya.

Da hanzari ya dawo gida, ya tarar Da Widad ta durƙusa tana kuka, se numfashi take da ƙyar.

Yusuf ya É—agota yace "Widad, lafiya kuwa?"

"Yoseef cikina, ciwo yakemin"

"Wai anya ma kina zuwa Asibiti awo?"

Umma tace "Awon me kuma?"

ÆŠan dirircewa Yusuf yayi, dan Umma bata san da ciki a jikin Widad ba, saboda kullum cikin zumbulelen hijjabi take.

Yusuf yace "ina nufin, taje likita ya ganta"
Chapter 120 · 0% Book details