← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 127

Sashe 105

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ramadan ya zauna yana share hawaye, tare da baƙincikin abunda mahaifinsu ya aikata, tausayin mahaifiyarsu ya mamayeshi, ya kalli ɗan uwansa yace  "yanzu Fahad yaya zamuyi mu gayawa Mummy wannan maganar? Itama taje a binciki lafiyarta tunda wuri?"

Fahad yace "Ramadan abunda nake ta tunani kenan, na rasa abunyi gaba ɗaya, ban san ta inda zan ɓullowa wannan maganar ba, da ƙyar idan Mummy bata ɗauka ba, dan babu wanda yasan tun yaushe yake tare da ita, suke mu'amala"

Ramadan ya dafe kansa, ya dinga jujjuya kansa cike da ƙunar rai, ya fice jiki a sanyaye daga ɗakin Fahad, zuciyarsa na masa wani irin zugi da takaici, gami da tausayin mahaifiyarsu.

Shirye shirye sukayi nisa, akan ɗaukaka ƙarar Yusuf, manyan lawyoyi da masu kare haƙƙin ɗan Adam suka shiga lamarin, suna ta tattar hujjoji da shedu wanda suma zasu gabatar, a sake sharia'r Yusuf.
Yayinda Widad ke zaune a inda take ɓoye, inda Bulama yake ɓoye da ita, take communicating da mutane a waje, ta hanyar Sabuwa me aiki, taita aikenta da takadda ba tare da Sabuwa tasan ma'anar hakan ba, ga cikinta ya ɗan ɗaga sosai ya fito, dan sosai yake motsi yanzu, sedai duk lokacin da cikin ya shiga wani watan, se wata matsala ta taso, kodai yawan amai, ko ciwon kai, ko rashin son Abinci, haka Widad keta wahala tana ƙumbiya ƙumbiya da cikin a hijjabi kar wani ya gani, ga Bulama ya shafe kwanaki bezo ba, tunda yayi mata barazanar kama mahaifiyar Yusuf bata sake ganinsa ba.

Bulama kuma yaga canji a tattare da yaransa, abun da ya bashi mamaki be wuce yadda Ramadan É—in dayake nutsatse yabi sahun Fahad ba, sam basa gaisheshi ko kallon inda yake basayi, balle ya saka ran wani abu na kirki ya shiga tsakaninsu dashi, suka dena shiga cikin gidan ma sam.

Bulama yace "Sarah, kin lura da yadda yaran nan suka canza gaba É—aya a gidan nan? Na rasa me nayi musu, sam basa shiga harkata sun dena ko gaishesni, ko wani abun sukace nayi musune?"

Hajiya Sarah tace   "ni dai bani da masaniya akan komai, ni Ramadan yafi bani mamaki ma, nasan ba haka yake ba, amma ban san yadda akayi shima ya ɗauki wannan mummunan halin ba, amma dan Allah kayi haƙuri, zanyi magana dasu insha Allah"

Bulama yace "shikenan, yakamata kam"

Daga nan ya kintsa ya fita, bayan fitarsa Hajiya Sarah taje har BQ ta samesu,
'Fahad, wani abu nake gani wanda na kasa gane kansa, meye dalikinku na dena kula mahaifinku ne?'

Fahad yace "babu komai"

"ƙarya kuke yi, akwai dalili idan ba haka ba, meye na wannan shareshin da kuke yi?"

Ramadan zeyi magana, Fahad ya girgiza masa kai yace "Mummy, kin san daddy da yawan faÉ—a, komai ya gani se yayi magana, se yayi mita da faÉ—a, shiyasa muke É—an janyewa kawai"

Tace "Ai ba yanayi ne dan ya takuda muku ba, dole idan kukayi ba daidai ba a tsawatar muku, dan haka bana son wannan abun da kuke, a gyara dan ya fara zargin koni nake saku kuke masa haka"

Fahad yace "to insha Allah, zamu gyara"

Bayan fitarata, Ramadan yace "Fahad meyasa ka hana a gayamata?"

Fahad yace  "Ramadan, ba'akowane irin yanayi ake gayawa mutum magana ba, ka bari zamu gayamata '

" Aikuwa bashi da amfani ko mun gaya mata, nasan aikin gama ya gama, ya riga ya cutar da ita "

Fahad yai shiru be kuma cewa komai ba.

Jini fa yaƙi tsayawa Amal, gaba ɗaya ta ɗashe tayi fari, ta kira doctor Hamisu a waya, ya rubuta mata magani, taje ta siya amma idan ta sha wuni take a kwance tana jiri, gaba ɗaya tayi wani iri, tambayar duniya taƙi gayawa Hajiya Halima abunda ke faruwa.
Tana kwance ta lallaɓa, zataje Asibitin da aka cire mata cikin ganin Likitan, se taga message nata shigowa wayarta, tana dubawa me zata gani? Kuɗinta na Account ake ta kwashewa, ta tashi a gigice sedai ba wani abu data iyayi an kwashe kuɗin nan tsaf, sakamakon wani website data shiga, akace ta saka BVN Number ɗinta, kuma ta saka akayi amfani da shi aka kwashe kuɗin nata.
Ta fito falo a gigice tana kuka, Hajiya Halima tace "ke lafiya kuwa?"

"Mummy kuÉ—ina, an kwashemin kuÉ—ina a Account"

Ramlah tace "ke kuwa kina me? Garin yaya?"

"Wani website ne, na shiga na saka BVN ina ga ta nan aka kwashemin kuiÉ—n, gashi nayi investing kusan million biyar a wani business shima an kwashe ma shiga uku"

Hajiya Halima tace "million goma kuma? A kna kika samu million goma?"

Sekuma ta dawo hayyacinta, ta shiag inda inda, cikin tsawa Hajiya Halima tace  "magana nake miki, a ina kika samu million goma?"
Tai shiru tana tura baki, "zakiyi magana ne? Ko kuma sena tashi na tattaka ki?"

"Alhaji Haruna me yamin fyaÉ—e, ni kuma na sace masa kuÉ—i a account"

Ramlah ta buɗe baki, Hajiya Halima ta miƙe tsaye  "ya miki fyaɗe kamar yaya?"

Nan Amal ya kwashe komai ta gayamata, har jinin da take ta zubarwa tunda aka cire cikin.

Nan da nan jikin Hajiya Halima ya É—au rawa, ta kasa magana ma gaba É—aya, ta dinga bin Amal da Ramlah da kallo.

Tunda mutane suka ji batun Yusuf zeyi appeal, suke ta ɗokin sake zaman ganin shari'ar nan, ranar da za'a fara sauraren ƙarar kotu ta cika maƙil, musamman jin labarin a ƙarƙashin jagorancin gogaggaun Matasan lawyoyi dodannin Azzalumai za'ayi shari'ar, kotu tayi maƙil assurance ɗin da Bulama ya samu a gurin Justice A dutse, da kuma su Barrister Sadik yasa ya je kotun da ƙwarin gwiwarsa, sedai duk da haka bashi da wani karsashi, saboda Alƙalin koyun bashi da wasa, balle ka tunkareshi da wata maganar cin hanci Justice Muhammad Mustapha.
Shikansa Yusuf yayi mamakin ganin, manyan lawyoyin da sukazo dan tsaya masa, da yawa a radio yake jin sunayen su, sekuma a dandalin sada zumunta, amma yau gashi gasu wai zasu tsaya masa, a iya saninsa ba kowa ke iya ɗaukarsu shari'a ba, saboda lawyoyine masu tsadar gasme, kuma basa tsayawa shari'ar Azzalumai, to ta yaya akai shi suke son tsaya masa? Bayan ta bayyana ƙarara shi me laifine?.

Barrister Adam A Adam ya fito gaban alƙali ya gabatar da kansa a gaban alƙali, sannan ya kalli kotu yace  "sunana Barrister Adam A Adam, ni lawyer ne me zaman kansa, ina daga cikin tawagar lawyoyin da zasu tsayawa wanda ake ƙara, don bashi kariya, a tare dani akwai hujjoji da shedu da zasu tabattarwa da alƙali cewar wanda ake tuhuma, be aijata ɗaya daga laifukan da ake zarginsa dasu ba, idan kotu ta bani dama ina buƙatar ganin Sada, wanda yace Yusuf ya kai masa mota ya siya "

Sada ya fito yana rarraba ido, dan kallo É—aya zakayiwa Barrister Adam A Adam kasan babu wasa a tare da shi, sannan abune mawuyaci a kada shi a shari'a, saboda gogaggen lawyer ne, kuma É—an gwagwarmaya.

Barrister ya kalli Sada yace " ko zaka iya gayawa kotu sunanka, da abunda ka sani akan wanda ake zargi?"

Sada ya maimaita abunda ya faɗa a kotun baya, Barrister Adam yace  "wow, ko zaka iya gayawa kotu wame irin motoci Yusuf ke kai maka gyara daga gidan Daula?"

Sada yace "motocine dai, kamar su jeep su Honda da sauransu"

Barrister yace "wace irin mota ce Yusuf ya kai maka ta gidan Daula ka siya?"

"Prado ce" ya bada amsa

"wow, kasan irin wannan motocin se gidan attajirai irinsu daula kam, amma ya akayi ka siyi motar da kuÉ—inta ya haura naira million talatin a matsayinka na bakanike?"

"Amm ai, ai, ai dama bani nake...

Objection ya me shari'a cewar Barrister Sadik, " Barrister Adam yana ƙoƙarin jefa tsoro da razani a zuciyar sheda, kuma ai shi arziki sirrine, dan mutum yana ƙaramar sana'a shikenan baze mallaki dukiya ba? "

Justice Mustapha yace  "tambayoyin da Barrister Adam yakewa Sheda, zam basu kauce ba dan haka wannan ƙorafin be karɓu ba, cigaba da aikinka"

"Nagode ya mai girma me shari'a" cewar Adam A Adam.

"Sada, waye megidanka da ya sai motar?"

"Amm, wa.. Wani oganane ubangidanane"

"Amma meyasa kuka sai motar, bayan kun san Yusuf bashi da arzikin daze mallaki wannan motar?"

"Amm, ai, ai dama bece min satota yayi ba, kawai yace in siya nace masa bana siyan mota, na haÉ—ashi da me siya na zata ko bashi motar Alhaji Nasir yayi, kasamcewarsa mutum me kyauta"

Barrister Adam yace "hakane, ina neman alfarma da kotu ta bani dama dan gabatar da wata ƙwaƙwarar sheda da zata tabattar da abunda Sada ya faɗa ba gaskiya bane"

Aka bawa Adam dama, aka shigo da Nura, aka tsayar da Nura a gurin Tsayuwa, Barrister Adam yace  "ko zaka gayawa kotu sunanka"

"Sunana Nura Idris"

"Kasan wannan" aka nuna masa Yusuf, Nura ya jinjina kai alamar eh, "wannan fa?" aka nuna masa Sada, Nura yace "A'a"

"toko zaka iya shedawa Kotu, abun da ka sani game da abunda ake tuhumar Yusuf dashi?"

Nura yace "kamar yadda na faɗa sunana Nura, kuma nine direban Alhaji Nasir Daula, kafin zuwan Yusuf ya fifita Yusuf sama da kowane ma'aikaci a gidan, na shekara a ƙalla tara ina aiki a gidansa, a haƙiƙanin gaskiya idan mota ta lalace a gidan Alhaji Nasir, Har gida ake zuwa a gyara ta, kuma Yusuf baya kai gyaran mota iya abunda nasan yanayi, shine tuƙa 'yaf gidan Alhaji Nasir Daula, sekuma shikansa Alhaj Daulan wasu lokutan, kuma idan mota ta lalace ma ba' a fiye barinta a gidan ba, gyara ta ake a bayar da ita, dan haka gaskiya ni ban san wannan bawan Allah ba, kuma a gidan Alhaji Nasir Daula, babu irin motocin daya faɗa, manyan motoci na alfarma su ake hawa a gidan Alhaji Nasir"

Barrister Adam yace "Malam Nura muna godiya, ban sani ba ko Sada yana da abun faÉ—a?"

Sada ya soma inda inda, yana kallon inda Su Bulama suke, akace ko su Barrister Sadik suna da abun faÉ—a? Sukace babu.
Chapter 105 · 0% Book details