← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 127

Sashe 82

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amal ta janyo Jakarta, wadda yace tayi accident da ita, ta duba amma itama taga babu takaddar a ciki, amma tai ajiyar zuciya tace  "nima nazo maka da buƙata ta, amma kaƙi amincewa, dan haka kowa ha riƙe buƙatarsa, bazan bayarba gara asirin kowa ma ya tonu a huta"

Yace "Subhanallah, hadda mamanki fa"
  Tace "har ita ɗin"

Yace "dan Allah kar muyi haka dake, ki bani takaddar nan na riga na cewa Bukar na karɓo takardar yace in kai masa, kuma yanzu inzo ince bahaka ba, baze sauraramin ba"

Amal tace "Ai gara karya saurara makan, kamar yadda nima baka sauraramin ba, kuma baka karɓi buƙata ta ba"

Yace "dakata, yanzu idan na karɓi buƙatar taki shikenan?"

Am tace "A'a ai kuma mun wuce wannan maganar yanzu, zan baka takadda bisa sharuÉ—a, yanzu abu na farko zan gaya maka Account Number É—ina, ina son inji wasu kuÉ—i masu nauyi, domin inci kaji in warke da wuri daga raunin daka min"

"Shikenan zan turomiki, yaushe zanzo in karɓa"?

Tace "turo É—in tukuna in gani mana"

Yace "shikenan naji"

Ta kashe wayarta, lumshe ido tare da faɗin "Alhamdilillah, cikin sauƙi Allah ya kawomin hanyar da zan rama cin zarafin da kayi min, tabbas inaga yadda takkadar nan nayi, dan babu ita a jakata, amma a haka zan maka rashin mutunci in rama"

Alert ne ya shigo wayarta, ta É—aga ta duba 500k ne, ta jinjina kai tace yanzu aka fara wasan

Seda yayi mata kira biyar, sannan ta É—aga a fusace tace "wai meye ne?"

"dama cewa zanyi, kinga alert É—in?"

Tace "na gani, amma sunmin kaÉ—an, na kuma raina"

Ta katse kiran tare da kashe wayarta gaba É—aya, ta kulle É—akinta da key, tai kwanciyarta.

Tunda suka taho Yusuf bece uffan ba, yai shiru yana saƙawa yana kwancewa a zuciyarsa, tabbas duk sunan da za'a kira shi dashi, ko a tuhume shi dashi, bashi da abunda ze kare kansa dashi, tabbas shi dai tunda ya tashi a rayuwarsa a siraɗin ƙaddara yake, daga wannan ya faɗa waccan, daga waccan ya faɗo wannan, haka ya sunkuyar da kansa yana ta tsabihi ga Allah, akan ya sauƙaƙa masa wannan lamarin.

Sun shigowa cikin garin kano, akayi hanyar babbar headquarter hukumar 'yan sanda dake garin kano, motarsu Widad kuma tayi wani gurin, ai tana ganin haka ta kuma fashewa da ihu, tana bori tana kuka tana   "ina zaku kaishi? Ina zaku kaimin mijina? Beyi laifin komai ba, babu abunda yayi muku, ku ƙyalemin mijina wayyo Allah na Yoseef duk nice sila, saboda ni ka shiga wannan tashin hankalin, Dan Allah ka yafemin Yoseef, Allah ka fitar da mijina daga sharrin Azzaluman nan, Allah ga bawanka ka fitarmin da mijina"

Ta ƙarasa maganar, tana wani irin kuka me taɓa zuciya babu wanda ya kula ta a cikin 'yan sandan suka cigaba da tafiya.

Wani ofishin' yan sandan aka tafi da ita, suka fito da ita daga mota zuwa gurin 'yan sanda, idanunta sun kumbura sunyi ja saboda kuka.

Wani ɗan sanda yace  "gata yallaɓai, yanzu muka shigo gari, shi an wuce dashi headquarter, ita kuma gata"

Ɗan sandan ya kalleta yace  "Good, Madam congratulations, you are now free, mun cetoki daga hannun wanda sukayi garkuwa dake"

"Niba garkuwa yayi dani ba, wanda sukayi garkuwa dani daban, Yoseef ceto na yayi, shine ya temakeni beyi garkuwa dani ba, ka gaya musu suje su sakarmin mijina"

Ɗan sandan yace "koma dai ya akayi, wannan ku ta shafa ke dashi, muba abunda ya dame mu, zamu rubuta sannan mu sanar da duniya cewar, munyi namijin ƙoƙari gurin bincike mun gano wanda yayi garkuwa da Widad Nasir Daula, kuma ba wani bane face direbanta, wanda ya kasance ɗansanda, yaje gidansu yai basaja dan yayi garkuwa da ita, nasan hakan ze sake ɗaga darajar rundunar mu a ga namijin ƙoƙarin da muke, ba dare ba rana gurin kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma "

" Shut up!!! "

Ta faɗa cikin ƙaraji, tace " idan har ina raye ina numfashi, ko komai nawa ze ƙare se Yusuf ya fita, babu wanda ze cutarmin dashi, baku isa ba azzalumai ma cuta, lokacin da aka yi garkuwa damu muna buƙatar taimakk, babu wanda ya taimakemu na kusa rasa rayuwa ta, se yanzu da yayi komai ya gama, Allah yasa ya kare rayuwata, shine za'a masa sharri wallahi bazan lamunta ba, he's my Husband "

Ɗan sandan nan yace  " ku ɗaukemin wannan mahaukaciyar daga gabana, a tafi da ita Asibiti a duba lafiyarta, sannan ku kiramin Ubanta Bulama tunda babu wanda yasan inda wancan yake "

Widad bata gane meyake nufi ba ta cigaba da kukanta, haka suka kawo Ambulance dan iya makirci, aka sheƙa mata wani abu ta sume a gurin, aka kira 'yan jaridu suka cika gurin, aka ɗauki Widad aka saka ta a motar Agajin gaggawa wato Ambulance suka tafi da ita.

Jaridu kuwa da sassafe shafin farko, hotunan Yusuf ne da Saleh, musamman na Yusuf ɗaure a cikin sarƙa ya sunkuyar da kai, gefe ga hoton Widad da aka ɗauka an fito da ita daga ofishin 'yan sanda an sata a ambulance, daka kunna gidan radio, labarai ko talabijin babu abunda zaka fara ji se
  "Me dokar bacci ya ɓige da gyangyɗi, kuma ƙarshen tika tiki tik inji hausawa A yaune  jami' am tasaro sukayi nasarar cafke jami'in ɗan sandan nan na farin kaya wato Yusuf Bashir Maitama, wanda yayi garkuwa da 'yar gidan fitaccen me Arziki nan a gida da wajen Nigeria wato Nasir Daula,' yan sandan sunyi nasarar gano shi ya sace ta tare da ɓoyeta a wani ƙasurgumin ƙauye dake garin Bauchi, 'yan sandan sun ceto Widad Nasir Daula, wadda ke cikin mawuyacin hali, da zauwansu basu yi wata wata ba aka kira motar Asibiti aka tafi da ita domin duba lafiyarta, zamu ci gaba da bibiya da kasa kunne domin jin wani mataki hukuma zata ɗauka akan wannan ɗan sanda, wanda ake tunanin har shi Nasir Daula ɗin shine yai garkuwa dashi, mu dai anan se muce Allah ya kyauta, yai mana tsari da irin wannan jam'ian tsaro a cikin al'ummar mu"

Nan fa gari ya É—au É—umi, aka dinga cece kuce, wasu na Allah wadai suna Tsinewa Yusuf, yayin da wasu ke a bari a ga abunda bincike zeyi tukuna.

Widad kam bata sake sanin inda kanta yake ba, inda har a gadon Asibiti aka bita aka dinga É—aukar hotunan ta, ga fuskarta tayi ja saboda kuka, da gajiyar tafiyar hanya, amma aka dinga É—auka ana watsawa duniya wai tana cikin mawuyacin hali, hannunta É—auke da drip.

Alhaji Haruna ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba a taɓa raina masa hankali kamar yadda akayi yau ba, ya kira layin Hajiya Halima, Ramlah na zaune a falo wayar ta fara ringing, Mummy tana ciki tana amsa wata wayar dan haka ta ɗaga wayar tasa a kunnenta tace "Hello"

Yace "Yawwa Amal ce?"

"No Ramlah ce"

"Dan Allah idan Amal tana kusa É—an bata wayar muyi magana"

Tace "tana É—akinta, bari in kai mata"

Ta miƙe ta tafi ɗakin Amal, amma ɗakin a rufe harta kashe fitila ma "

Ramlah tace " gaskiya tayi bacci, dan ta rufe É—akinta ma ta kashe fitila"

Yace "Yasalam"

Ramlah tace "ya dai? Akwai matsala ne?"

"A'a babu wata matsala, ina son muyi magana ne kawai"

"to ka gayamin saƙon in bata mana"

Yace "A'a karki damu, idan ta tashi na sake kira"

Ya kashe wayar yace "Amma dai Allah ya Tsinewa yarinyar nan, kaga min shegiyar yarinya mara albarka" ya ciji yatsa yai ƙwafa yace  "dani kike zancen wallahi, kema sema wulaƙantaki,"

Amal ta ɗau wayarta ta tura masa saƙo tace "ka cigaba da kiran Mummy, kana cewa kana son Magana dani, wallahi idan baka yi wasa ba sena gayamata abunda kayi min, kuma kasan halinta sarai, kasan buyaginta zata maka abunda kai kanka zaka kasa gane kansa, dan haka muddin ba zaka cika sharaɗina ba, wallahi ba zan baka ba na gaya maka, kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan, nima a account dina ina da wanda suka fisu"

Ta kashe wayarta ta sake kwanciya, ya duba message ɗin, yaja wata ajiyar zuciya yana cije leɓe, totally ta riga ta gama raina masa hankali, yama rasa me zeyi ko me zece.

Yana nan tsaye yana tunanin mafita kiran wayar Bukar ya shigo wayarsa, ya É—aga jiki na tsuma, yace "Hello"

"Haruna, yau muna da zama na gaggawa, cikin dare dan haka duk ku tattaru"

Yace "harda Halima?"

"banda ita, sannan kazo min da wannan takaddar, zamuyi magana a kai itama"

Daga nan ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya yakice gumi, yana huci Amal ta masa rashin mutunci, dan kawai abu ya shiga tsakaninsu se tayi masa haka?.

Mutan ƙauyen da Widad suka zauna suka dinga taradaddi, kowa da abunda yake faɗa wasu suna dama megari yayi wauta, wataƙila dama can 'yan fashi ne ko wasu masu laifin ne, amma daga zuwansu ya karɓesu, be san daga inda suke ba.

Hindu kam kuka, kamar wadda aka kama uwarta, ita kanta Hari gaba É—aya jikinta a sanyaye yake, wunin ranar gidan daga masu koke koke, se masu salallami, Hanne kuwa ko a jikinta.

Koda Sunusi ya dawo, Jamika ta gaya masa abunda ya faru, dan haka yace dole gobe insha Allah ya tafi kank, yaje yaji ba'asin abunda ya faru.

Jamila tace "dan Allah karkaje, kar kaima a kama ka, dan na san da kana nan wataƙila da kai zasu haɗa"

Sunusi yace "da nayi musu me? Kince an kama Saleh, kuma Saleh shiya kawo su nan, meyasa aka kama shi, dole zanje inji"

Daddare megari ya tara iyalansa yace  "to wannan bayin Allah dai, ni dai a ɗan zaman da mukayi dasu, ban tunanin mutane ne marasa gaskiya, ko makamancin haka, zamanmu da su ma mu alkhairi ya zame mana a garin nan, dan haka dan Allah ina roƙonku da kuyi haƙuri ku dena kuka, kukan ya isa haka, Hasana nasanki da son 'ya' ya kuma zamanmu dasu jin shaƙu dasu sosai, dan Allah kidena kuka kiyi musu Addu'a, Hindu Baffa kema kukan ya isa haka, muyi musu Addu'a, Allah ya basu mafita sannan Hari a samo makulli a rufe musu ɗakinsu, kar wanda ya sake shiga tunda da kayansu a ciki "
Chapter 82 · 0% Book details